Free chapter · Read without an account
Page 7
•••SANADIN MAHAIFINA•••
Wattpad@SaNaz_deeyah
Arewabooks@sanazty
Facebook@Habibtyn Habibi
YouTube: ***
Tiktok: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
Shafi na 7
________________📲Yau tun safe ta tashi ta shirya, misalin ƙarfe 10:30am ta fita tare da tarar adaidaita sahu zuwa asibitin da aka kwantar da Sa'ad, domin tun ranar bikin nata bata ƙara zuwa ba saboda tashin hankali da ake ciki wanda har a lokacin hankalin nata bai kwanta ba.
Da fargaba ta tura ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Hanne dake ƙoƙarin miƙawa Sa'ad ledar pure water ita ta juyo tana amsa sallamar. "Amarya yau kece a nan daga yin bikin" murmushi kawai tayi tare da jan kujera ta zauna.
"Aini fushi nake dake Hannatu tunda kinƙi yarda kizo inda nake"
"Ba haka bane, so nake sai an sallameni sai inje har gidanku Farhan ta rakani gidanki"
Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba, kawai ta kawar da maganar da faɗin "Ya jikin nashi?"
"Da sauƙi wataƙila ma a sallamemu nan kusa"
"Allah ya sa kaffara ne"
"Amin." kallon Sa'ad ɗin tayi kafin ta ƙara cewa "Sannu Allah ya baka lafiya"
"JANNAT...." Ya kira sunan nata cikin wata irin murya mai cike da damuwa.
Tsawon seconds 15 sannan ta kawar da kanta gefe daga kallonsa. "Kiyi haƙuri akan abinda ya faru, na san na ɓata muku biki"
"Abinda ya wuce ya wuce Sa'ad, ni lafiyarka itace tafi damu na."
Suna nan zaune Umma ta shigo, Jannat da sauri ta russuna ta gaisheta.
"Jannat mene kika zo yi nan?"
"Umma dan Allah kiyi haƙuri, a yanzu haka an ɗaura auren Khalil da ƙanwata Farhan ba dani ba, na bar auren Khalil saboda halin da Sa'ad ke ciki, amma kuma mahaifina har yanzu ya kasa fahimta ta."
Murmushi Umma tayi tare da zama tana kallon Jannat, lallai kin cika ƴar halak kuma a tagari, a yanziu kam zan baki fuska sosai. Yanzu kin faɗawa mahaifin naki cewa Sa'ad kike son aura? Domin ya fara samun sauƙi ma"
Kanta ta sauke tare da cewa "A dalilin haka, mahaifina ya koreni daga gidan sa, kuma yace babu ni babu shi, yanzu haka a hotel nake zaune"
"Hotel? Jannat meyasa? Meyasa zaki bijirewa maganar iyayenki a kaina? Kada ki manta sune sanadin zuwanki duniya"
"Bani da yadda na iya Sa'ad, Umma tace muddin na auri Khalil ba kai bani, sannan likita ya tabbatar da cewa zaka iya samun matsala idan har ba ayi maganin damuwarka, na san nice damuwarka shine na bada gudunmawata dan ganin na ceto ka" Ta faɗa tana zubda hawaye.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Umma dan Allah meyasa zakiyi haka?"
"Saboda na isa inyi ɗin, wai kai Sa'ad baka da hankaline? Kana tunanin zan barka ka cigaba da shiga ƙuncin rayuwa har inzo in rasaka?"
"Amma a sanadin haka Jannat ta shiga ƙuncin rayuwa, kalleta Umma, kina gani kin san tana cikin damuwa"
"Damuwarta ai ta ƙare tunda ga ka" ta faɗa sannan ta kalli Jannat tace "Mu ɗan fita Jannat zanyi magana dake."
Tashi tayi tana goge hawaye sannan ta fita, Umma ta kallesu tace "Ina zuwa."
Tana fita Sa'ad ya kalli Hannatu yace "Wai meyasa Umma take haka ne?"
"Ni kaina abin na bani mamaki, Allah sarki Jannat wallahi tana cikin damuwa"
"Yadda Jannat ta faranta min nayi alƙawarin nima sai na faranta mata"
"Allah ya baka iko"
"Amin."
A farfajiyar asibitin suka tsaya, Umma ta kalleta tace "Jannat kun kawo mu asibiti amma kuma kunyi ƙoƙari, domin wanda zaki aura shi ya bada kuɗi isassu kuma yace idan har sun ƙare ba'a sallanemu ba ayi masa magana haka likita yace."
Ajiyar zuciya kawai ta sauke, Umma ta ɗanyi murmushi tace "A yanzu kam bamu da matsalar kuɗi, kuma kinga jikin Sa'ad da sauƙi sosai"
a sanyaye Jannat tace "Allah ya ƙara sauƙi"
Amin yarinyar kirki. Amma Jannat da mutumcinki mene ya kaiki hotel zama? Shin baku da dangi?"
"Dangin mahaifiyata ƴan Maiduguri ne, dangin Mahaifina ne kaɗai a nan, kuma naje gidajensu amma sunƙi yarda in zauna"
"Saboda kawai kin zaɓi Sa'ad?"
Kai ta gyaɗa alamar eh.
"Taɓɗijam! Jannat karki kamar matsa miki nake, amma wallahi ba zan baki auren Sa'ad marayan Allah ba tare da amincewar mahaifinki ba"
Zaro ido tayi ta kalli Umma dan ta tabbatar da furucin nata.
"Jannat daga nan ki koma inda kika fito, kada ki ƙara zuwa wannan asibiti har sai mahaifinki ya amince da aurenku, to haka za'a kawo mana ke fanko babu komai, ba zai wuyu ba."
Kallon Umma tayi rai a ɓace tace "Da farko na ɗauka so na kuke tsakano da Allah shiyasa kuke ta ƙoƙarin shigo dani cikin rayuwarku, ban taɓa jin son Sa'ad ba, amma tausayinsa ya saka na amince na kuma dage kan bazan auri mutumin da muka daɗe muna gina soyayya ba, amma tun a yanzu na fahimta kuma na gane inda kuka dosa, kuɗin mahaifina kuke so bani ba"
"Jannat wallahi ba kuɗinki muke so ba, amma albarkar auren nake so ki samu, Jannat kinyi ƙoƙari kuma zan baki auren Sa'ad amma kafin nan dole sai kin kawo mana wakili, wanda zai ɗaura miki aure"
Murmushi tayi mai ɗauke da hawaye sannan ta ce "Nagode Umma"
"Yauwa mu koma ciki ko?"
Murmushi kawai tayi.
1week later
Tana jera kayan tea a saman dinning table, ya fito rataye da brief case ɗinshi. "Yayana barka da asuba" ta furta fuskarta ɗauke da fara'a.
"Barka dai" ya faɗa yana nufar hanyar da zata sadashi da farfajiyar gidan.
"Amm....Yaya Khalil na gama haɗa maka breakfast kuma naga kana ƙoƙarin fita"
"Idan naje office zan sha tea"
"Amma..."
"Farhan kada ki sakani yin abinda ban ga dama ba" ya faɗa sannan ya fita.
Kan kujera ta koma tare da fashewa da kuka. "Wannan wace irin rayuwa ce shiyasa bana son nayi aure dan babu wani jindaɗi a cikinsa."
Wayarta taja ta kira Safina. "Hello Safina?"
Daga ɗayan ɓangaren Safina tace "To sarkin kai ƙara me kuma ya faru?"
"Safina wallahi ina tunanin Yaya Khalil ba zai taɓa sona ba, baya ko cin abinci na"
ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Kin san me zakiyi?"
"Da dare kawai ki saka kayan bacci kice masa lallai a ɗakinshi zaki kwana, idan ya nuna bayaso ki ce zaki haɗa shi da Mommynsa to ko da babu abinda zai shiga tsakaninku zaki ɗan ga canji, daga nan kuma a hankali zaki ga ya ware, kedai kawai ki daure ɗin"
"Shikenan Safina zan jarraba"
"Ki cire kunya, ki daina ganin wai shi yayanki ne kinji ko"
"To shikenan, yaushe zaki koma school?"
"Yau mana, dan wallahi gida nake so na leƙa"
"Ki gaida min da Jannat dan in na kirata ma bata ɗauka ban san meyasa ba"
"To ai nima dai haka ne, amma zan faɗa mata"
"To shikenan nima maybe jibi na shigo school"
"Allah ya kaimu"
"Amin."
******
Kuka ta fashe dashi sannan ta tashi tayi side ɗin Daddy, Mommy nayi mata magana amma sam taƙi kulata. Tana ƙarasawa kai tsaye ta tura slicing door ɗin ta shiga. Yana zaune yana kallon labaran NTA, gaban shi kuma center table ne an ajje plate cike da yankakkun fruits.
"Lafiyanki kuwa kika shigo min ɗaki babu ko sallama?" ya faɗa yana kallon Safina.
Zubewa tayi a ƙasa cikin kuka tace "Dama na kawo hakan zata iya faruwa sai da naji a jikina cewar Jannat bata gidan nan, Daddy me yayi zafi da zaka koreta, ina zata wanda ya wuce nan?"
"Safina har kin kai matsayin zuwa gabana kina jera min wannan tambayoyin? Ko kema baki da kunya kamar Jannat ɗin?"
"Haba Daddy wannan ba adalci bane ta........." bata ƙarasa ba taji saukar wani mahaukacin mari daya gigitata. Cikin tashin hankali da ruɗewa ta ɗago ta kalli Mommy data shigo wanda itace ta wanke Safina da mari.
"Baki da hankali ashe? Mahaifin naki kike kira da mara adalci, wannan ba tarbiyyar dana baku bace, kuma bazan taɓa lamunta ba."
Cikin kuka tace "Amma Mommy ta ya zai kori Jannat daga gidan nan, idan ya koreta taje ina, dan na faɗi gaskiy......" kwaɓe bakinta Mommy tayi sannan tace "Idan kika ƙara furta wata mummunar kalma akan mahaifinki sai na saɓa miki."
Murmushi Daddy yayi sannan ya kalleta yace "Kin gama ko akwai sauran bayani a bakin ki?" shiru tayi kanta a ƙasa tana shashsheƙar kuka. "Nace kin gama bayanin ko kuma skwai sauran magana a bakin ki?" nan ma bata ce komai ba. Ranshi ya haɗe tamkar bai taɓa murmushi ba ya fars magana cikin ɓacin rai, "A ko da yaushe shiyasa nake sakawa Farhan albarka domin itace ƙaramarku amma kaf ta fiye min ku, bana saka mata doka ta tsallake amma ku da zarar na faɗi magana sai kun musu, ni mahaifinki kike faɗa min cewa bani da adalci nayiwa ƙanwarki rashin adalci ko, to shikenan insha Allahu dake da ita ɗin na fidda hannu a al'amuranku, kuma yadda kika faɗamim magana mara daɗi kema zaki ga abinda zai faru dake mara daɗi, ina mahaifinki saboda baki da ɗa'a har ki kalli kina idaniyata kice min mara adalci, to ai yanzu kema kina da gida ki ɗauki Jannat ki ajjeta acan kema ai dolenta ce."
Cikin dakiya Mommy ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Alhaji dan Allah ka daina yiwa ƴaƴanka baki, ko ya ya furucinka zaiyi tasiri a kansu ne dan Allah"
"Babu wanda nayiwa baki a cikinsu, domin ban tsine masu ba, kawai ina faɗa musu ne idan har suka min to ƴaƴansu sai sun masu"
"Safina bashi haƙuri" Mommy ta faɗa tana kallonta. "Oh haƙurin ma sai kin ce ta bani."
"A'a Daddy kayi haƙuri nima ina da niyyar baka haƙurin, ina jira ka huce ne, amma Daddy wallahi ban faɗi maganar dan tayi maka zafi ba, Jannat tana da ƙaracin shekaru dan Allah ka duba lamarin"
"Idan har maganar Jannat zaki cigaba da zo min da ita, to tabbas kullum zaki riƙa ganin ɓacin raina"
"To kayi haƙuri ka gafarceni Daddy" ta faɗa tana haɗe hannayenta cikin kuka.
"Na haƙura, amma daga yanzu kisan irin kalaman da zaki riƙa yi wa mahaifinki"
"Insha Allahu zan kiyaye"
"Tashi kije Allah ya maku albarka"
"Amin Daddy" ta faɗa tana goge guntun hawayenta sannan ta tashi ta fita.
Girgiza kai yayi tare da furta "Allah ya kyauta!"
"Amin Alhaji, am.... Dam...dama ina so nayi magana da kai akan Jannat"
"Kin san nace a daina kawo min magana da ta shafi wannan fitsararriyar"
"Dan Allah kayi mata afuwa, bana so Jannat ta lalace idan ta rasa matsugunni"
"Ki tashi ki bani guri, ban hanaki bin Jannat ba amma ki sani idan har kika bita to kema kin bar gidan nan."
Tashi tayi idanunta cike da ƙwalla ta bar ɗakin, a ƙofar fita ta ci karo da Ummu. "Lafiya meke faruwa ne? Naga Safina ma tana falo tana kuka"
"Babu komai" Mommy ta faɗa sannan ta wuce kawai.
Ummu na zama ta kalleshi tace "Amma Alhaji ya kamata ka duba wannan lamarin, Na san wannan damuwar tasu akan Jannat ne dan Allah kayi haƙuri ka dawo da ita"
"Kamar yadda kuke son Jannat haka nima, dan haka ku barni in hukuntata"
"Hukuncin yayi tsauri domin an ce a hotel take zaune ka hana kowa ya karɓeta, zaman ƴa mace a hotel ba mutumci bane, wasu har sun fara tunanin ko kayi disowning ɗinta"
"Nina haifeta taya zanyi disowning ƴar dana raina a hannuna gudan jinina, ina so in hukuntata ne ta gane cewa ita duniya babu tabbas domin du wancan da take iƙirarin tana son ɗansu zamu ga wanda zai tsaya mata a matsayin maɗaurin aure."
"Ka dai yi haƙuri"
"Zan haƙura bayan na gama hukuntata, dan haka ku daina min maganarta"
"Allah ya kyauta."
*****
"Please dan Allah ki ɗaga Jannat" Safina ta faɗa tana goge hawayen idanunta.
Mommy da ta fito zama tayi a gefe tana kallon Safina kafin tace "Kin sameta kuwa?"
"Taƙi ɗaga kirana, kuma na san tana gani wallahi, amma zan sayi wani layi in kirata"
"Ban san meyasa Jannat bata ɗaga kiranmu ba, Ni kawai zan fita ɗauki Jannat in haƙura da auren, domin bana son rayuwar ƴaƴana ta salwanta."
"Haba Mommy idan kin tafi me mutane zasu ce, bana son a ɓata image ɗin wannan gida, dan haka zan ɗauke ta ta koma gidana kafin Abba ya haƙura"
"Kina ganin mijinki zai yarda da haka, bana so kema kizo ki samu matsala da mijinki"
"Mommy kada ki damu insha Allah babu abinda zai faru, kawai ki cigaba dayi mana addu'a"
"Shikenan ubangiya yayi muku albarka, yasa ku gama da duniya lafiya"
"Amin Mommy, bari na tashi na tafi idan yaso duk sai na biya ko gurin masu sai da katin waya na ari waya na kirata, duk abinda ake ciki zan sanar dake"
"To Allah dai yayi mana jagora"
"Amin."
*****
Tana tsaye jikin mirror tana tsane ruwan fuskarta da ƙaramin towel. Wayarta da ta fara ringing ta kalla tare da ɗauka. Ɗagawa tayi gami da karawa a kunne. "Hello" jin muryar Safina ne ya saka ta ƙara ganin number.
"Jannat mene muka miki da kike ƙin ɗaga wayata"
Shiru tayi na ɗan lokaci kafin tace "Wallahi Safina bana son ɗaga muku hankaline"
"Kina cikin tashin hankali kina tunanin zan zauna cikin jindaɗi, wallahi idan har kina cikin ɓacin rai numa ba zan taɓa jindaɗi ba"
"Daddy ya koreni Safina, na raa madafa kowa naje gurinsa baya karɓata"
"Ya ilahi, yanzu dai kina ina?" "Ina Royal hotel"
"Okay ki jirani yanzu zanzo,mene room number naki?"
"Room 105"
"To shikenan gani nan"
Ƙarasa shiryawa tayi cikin kuka sannan ta kwanta a gado ta cigaba da kuka mara sauti.
30 minutes later
Jin knocking ne ya saka ta miƙe tare da buɗe ƙofar, aikuwa suka rungume juna suna kuka. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka goge hawayensu.
"Daga gida nake, amma har yanzu Daddy fushi yake dake"
"Na san nayi kuskure na bijerewa maganar Daddy, amma meyasa ya kasa haƙura dana bashi haƙuri,zuciyata zafi take Safina, na rasa tudun dafawa, kamar bani da dangi a kano"
"Kiyi haƙuri Jannat na san da ace dangin Mommy ne ba zasu taɓa yi miki haka ba,amma shima Daddy ɓacin raine ya saka shi faɗar haka kuma insha Allah zai huce"
"Har zuwa wane lokaci kenan? Haka zan ta zaman hotel mutumcina na ƙare zubewa a idon mutane"
"Zaki zauna a gidana har zuwa lokacin da zai haƙura"
"Haba Safina, ta ya ya zan zauna a gidan ki, sati ɗaya da aurenki, mijinki ma ba zai taɓa yarda ba"
"zai yarda insha Allahu, tashi ki haɗa kayanki kawai."
Mabiya wannan littafin kuyi haƙuri dan Allah wallahi na zama busy da yawa, akwai wani abu dana saka a gaba, ina fatan duk wanda ya karanta ya tayani addu'a Allah yayi min jagora akai.
SaNaz Ce✌️