Free chapter · Read without an account

Page 5

by SaNaz deeyah · SUMAYYA

SUMAYYA

Wattpad@SaNazdeeyah_

Arewabooks@sanazty

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[tushen mu'amula tagari]

```Page 5```

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce "Baiwar Allah zauna"

"Malamin asibiti dan Allah karka damu da zamana, ka faɗa min halin da 'yata take dan girman Allah. Habi ce ta kalleta ta ce "Amarya idan fa ba nutsuwa kika yi ba, ba zai faɗa miki ainahin abinda ke damunta ba"

"To bari na zauna" Ta furta tana zama a kujerar cikin tashin hankali.

"To a sakamakon gishiri da tasha mai yawan gaske hakan ya taɓa mahaifarta, wanda har ya yi affecting cikin jikinta ya lalace, sannan ita kanta mahaifarta ta samu matsala wanda akwai buƙatar a mata aiki idan ma anyi babu yuwuwar ta ƙara iya ɗaukar wani cikin" Gabaɗaya salati suka ɗauka, yi suke suna nanatawa amarya har da hawaye.

Likita ya cigaba da faɗin "Abinda ya bani mamaki shi ne wane irin gishiri ne tasha haka daya lalata ciki faraɗ ɗaya, da buƙatar ku bincika dan da alama tasha ne dama saboda cikin, ciwukan da hakan yaja mata a ciki suna da yawa hajiya gaskiya ta yiwa kanta babbar illa"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, meyasa Sumayya ta kasa ɗaukar ƙaddara, meyasa zata mana haka?" Amarya ta faɗa cikin kuka.

"Amarya sai haƙuri aikin gama ya gama yanzu kawai hanyar samun lafiya za a nema" Ta mayar da kanta ga Likita. "Yanzu mene abinyi Doctor?"

"To mun turata theater za a mata wankin ciki da kuma abinda ya samu, daga nan kuma sai dai mu turaku asibitin masu yoyon fitsarin, acan ne Likitocin da suka shafi wannan ɓangaren za su duba su ga abinda ya dace su mata"

"Batun mahaifar fa?"

"Gaskiya ta gama ɓata mahaifarta, dan ba zata ƙara ɗaukar ciki ba, ko da ta ɗauka ba zai fi wata biyu ko uku zai zube, ai ta zama weak yanzu tayi laushin da ba za ta iya riƙe ciki ba, kuma yawan ɗaukar da zubewar ciki kan iya haddasa mata babbar matsalar da zata iya rasa rayuwarta ma"

Da sauri Amarya ta tashi ta fita.

Tana tsaye a ƙofar tana goge hawaye Habi ta fito "Waye ya yi ma Sumayya wannan huɗubar? Ni na san ba tunaninta bane"

Kuka Amarya ta rushe dashi a fili tana faɗin "Yanzu haka Sumayya za ta mana, daga ni har mahaifinta mun ɗauki ƙaddarar data sameta amma sakayyar da za ta mana kenan"

"Amarya dan Allah kiyi haƙuri, yaro ne ka haifeshi baka haifi halinsa ba" Hannu Amarya ta saka a ƙirjinta "Ƙirjina zafi yake Habi, Sumayya so take ta kashe ni" "Ki bar maganar nan dan Allah zuwa komai ya lafa, kiyi haƙuri ki daure." Hannu ta saka tana goge hawayen da yake zubar mata a kan kumatu, tana jin wani irin ɗaci da raɗaɗi a zuciyarta.

**** ****

Yana buɗe labulen ta ɗago kai a tsorace, dan dama ta san shi ne shiyasa ta tsorata. "Ke Atika ki faɗa min gaskiya idan kin san inda suka je"

"Wallahi Baffa ban sani ba, ni mun fita ne ina dawowa naga basu nan" Ranshi ya ƙara ɓaci ya fita.

Hadiza na tsaye a ƙofar ɗakin Amarya yana fitowa ta kalleshi "Malam dan fa naga kamar baka son laifinsu ne, amma babu yadda ban yi da Amarya akan karta je asibiti amma Habi ta zugata tayi kunnen uwar shegu damu ta fita."

Zulai ta ƙara da faɗin "Sani tayi ko ta fita ta dawo babu abinda zai mata shiyasa take abinda taga dama" Bai tanka su ba kawai ya wuce ya basu guri, rai a ɓace. A ƙofar gida ya kira Lurwanu ɗaya daga cikin almajiran daya bari a gida da zai tafi gona. "Kana nan Amarya ta fita?"

"Eh Malam naga ta kamo Sumayya da ita da wata mata sun saka ta a napep"

"Ina suka je ne?"

"Wallahi ban sani ba, amma na ji sunce a kaisu asibiti" Kai Malam ya gyaɗa rai a ɓace.

Maryam tana zuwa bakin ƙofar ta ɗan russuna ta ce "Malam barka da yamma" "Yawwa Maryam ko?" "Eh Baffa ni ce, ina wuni" "Lafiya lau, ya iyayen naki?" "Lafiya lau" Miƙewa tayi zata shiga ya ce "Ai basa nan sai Atika kawai, nayi tunanin ma kin san ina suka je"

"Wallahi ban sani ba, tun jiya rabona da ita"

"Allah sarki, to ki shiga Atika tana ciki" Shiga tayi jikinta a sanyaye dan yadda taga fuskar Malam Bala a haɗe babu alamun fara'a. Ba kamar idan tazo yana amsa mata magana fuska a sake.

Tana shiga Atika ta bita da ido tana amsa mata sallama. Zama tayi tare da faɗin Atika ina Sum..." Ai bata ƙarasa ba Atika ta damƙeta ta fara duka, ihu Maryam ta fara, da ƙyar ta ƙwaci kanta ta fita tsakar gida da gudu, aikuwa anan ta cimmata ta hau ruwan cikinta tana naushi. 'yan gidan kowa ya fito amma an rasa wanda zai ƙwaci Maryam har sai da Malam ya shigo ya ɗauke Atika daga jikin Maryam.

"Ke baki da hankali me kika mata haka?" Ya furta yana kallon Maryam da take goge jinin dake fita ta hancinta, ga kuma ciwo a gefen idonta, jikinta duk ƙasa da cakwali.

"Tambayarki nake me tayi miki ko sai na miki shegen duka za ki faɗa?"

Turo baki Atika tayi tare da cewa "Baba itace ta cewa Adda Sumayya ta jiƙa gishiri tasha cikin jikinta zai zube, kuma tunda Adda tasha ruwan gishirin take ta ciwon ciki" Salati aka hau yi, Baffa ya kalli Maryam ya ce "Maryama da gaske ne abinda Atika ta faɗa?"

"Baffa wallahi gani nayi ta dawo har asibiti ta saka na rakata, likitan ya ce ba zai zubar ba, shi ne nace ta gwada na gishiri saboda na ga wasu suna yi" Gabaɗaya gidan aka ɗauki salati, Baffa ya kalli Atika ya ce "Je ki samo mata wasu kayan ta saka, kuma kar na kuma jin kin daketa"

"Baffa a...." "Kul! Kin san dai bana son musu ko, to ki wuce ki ɗauko mata kaya ta wanke jikinta ta saka" Rai a ɓace Atika ta kalleshi sannan ta wuce ɗaki.

Asibiti

"Yanzu zaku iya tafiya gida, ga ledar fitsari nan mun saka mata, zata taimaka wajen hanata yin zarni, amma sai kun riƙa kula sosai, daga zarar ta cika to a cire." Amarya dai bata ce komai ba, bayan hawayen da ta kan saka hannu ta goge, haka Sumayya ma, ta kasa cewa komai sai hawaye kawai.

Kai ya girgiza ya ce "Hajiya karku damu, ciwonta ai ana warkewa, kuma aikinsa kyauta ne anan, kafin dai a samu hanyar yin ne kun san yadda ƙasar tamu take, shiyasa ma nace idan kunje ku nemi Dr Ibrahim insha Allahu komai zai zo muku a sauƙaƙe, kuyi haƙuri za ta warke"

Sai lokacin Amarya ta kalleshi da jajayen idanunta ta ce "Mungode malamin asibiti Allah ya saka" Tana gama faɗa kawai ta miƙe ta fita, hakan ya tabbatarwa da Sumayya ran mahaifiyarta ya ɓaci. A sanyaye ta miƙe ta fita, a bakin ƙofar ta sameta, bata ko kalli inda take ba. A raunane Sumayya ta ce "Iyarmu dan Allah ki...." Hannu ta ɗaga mata. "Bana son jin komai, wuce muje gida, dan na tabbatar ran Malam ya gama ɓaci tun safe muke nan babu ko wayar da za a sanar masa."

Haka suka tafi kowa da abinda ke saƙawa, a bakin layinsu Habi napep ya tsaya, ita ta biya kuɗin sannan ta ce "Insha Allah idan kun shirya zuwa can asibitin sai ku min magana na muku jagora, sannan Amarya sai kin yi haƙuri abinda za ki fuskanta dan na san kishiyoyinki tuni sun gama zuga Malam"

"Babu damuwa Habi, nagode sosai" "Karki damu ai an zama ɗaya."

Ƙofar gidan danƙam yake da almajiran Malam suna karatu, kuma kowa idonshi akan ɗan sahun yake hatta shi Malam ɗin. Suna sauka suka shige gidan. "Kamar kumbo kamar katanta" Hadiza ta faɗa tana zuge zogale a zaune tsakar gidan tare da Rafi'a. Basu kulata ba, Zulai ta fito tana faɗin "Waye anan?" Kallon su tayi tana faɗin "Lallai kin kai, aikuwa yau kema kin san Malam ba zai ɗauki shashancin nan ba" Bata ko kulasu ba, saboda abinda ya dameta, kawai ta kunna kai cikin ɗakin. "Iyarmu sannu da zuwa" Atika ta faɗa tana tashi zaune. Kai kawai Amarya ta gyaɗa, sannan tayiwa kanta mazauni a gefen gadon. Sumayya a sanyaye ta ƙaraso gabanta ta tsugunna "Iyarmu..." "Sumayya bana son jin komai daga gareki." Tana direwa Malam ya buɗe labulen ɗakin.

"Basira!" Ya faɗi sunan Amarya kai tsaye, abinda ya bawa Sumayya da Atika mamaki kenan, dan Malam bai taɓa faɗar sunanta ba tunda suka taso suka ji yana ce mata Amarya, wani lokacin kuma ya ce Malama. "Ina kuka tafi da Sumayya tun safe.?"

"Malam wani irin ruwa ta riƙa fitarwa da jini, na tsorata sosai gashi baka nan, sai na fita na kira Habi, da tazo ta dubata sai ta bani shawarar sai mun kaita asibiti, to shi ne muka kaita anan aka faɗa mana cewar tayi ɓari, kuma..." "Dakata Malama" Ya furta cikin tsawa wadda gabaɗaya sai da suka tsorata.

Hadiza ta kalli Zulai ta ce "Da alamu fa yau asirin da aka daɗe ana yiwa Malam ya karye"

"Ba mamaki kuwa, tunda yau gashi yana yiwa Amarya faɗa muryarsa har tsakar gida" "Ai yanzu zamu huta da iskancinta, gara ya nuna mata kurenta, munafuka kullum ta riƙa nuna tafi kowa tsoron Allah"

"Sai dai bariki tunda mu a 'ya'yanmu babu ɗan iska, babu wanda ya taɓa ɗebo mana abin kunya."

Yana huci yake kallonta, sannan ya juya ya kalli Sumayya wadda tayi saurin sauke kanta ƙasa. "Ki dai faɗa min kinje kin zubar mata da ciki amma ba ki tsaya raina min hankali ba" "Haba Malam wannan wace irin magana ce, akan me zan zubarwa da Sumayya ciki?" "Saboda shege ne baya da uba" Ɗan runtse ido Sumayya tayi, taji furucin nasa ya doketa sosai. "Malam, kai da bakinka kake faɗar haka?" "Na faɗa ko ƙarya nayi? Ni naje na ɗaukota da kaina, ban nuna damuwata a kai ba, dama tun tuni ina kokwanto ne saboda gidan nan suna ta faɗa min in tuhumeta, amma saboda kar zafin ya haɗe mata na ƙyaleta duk hakan bai isheku ba sai da kuka kaini bango" Shiru ba wanda ya iya magana. Shi kuma ya cigaba da faɗin "Sanin kanki ne bana yadda aje asibiti dan banma yarda dashi ba, amma saboda rashin mutunci irin naki kika tsallake, sau nawa ana ɓari a gidan nan ke kanki kafin ki haifi Sumayya ai kinyi ɓarin za kice baki san yadda yake ba, to wallahi yanda kika tsallake kika tafi kin tafi da igiyar aurenki."

"Baffa!" Sumayya ta furta a kiɗime.

"Ki rufamin baki dalla, kema naki hukuncin na zuwa" Ya sake kallon Amarya ya ce "Ki tattara na sakeki saki uku kuma kada ki ɗaukar min yarana, yadda kika zo babu su haka za ki koma babu su" Fuuu ya fice ya bar ɗakin. Jin haka ya saka Zulai da Hadiza yin shiru dan kar su yi magana tasu tayi zafi.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda Amarya ke ta nanatawa, Sumayya da Atika kuka kawai suke, yunƙurin miƙewa Amarya take amma bata samu damar hakan ba dan a gurin ta zube, tuni suka hau salati sukayi kanta.

5 hours later

Suna zaune Atika ta rungume Sumayya tana hawaye. "Ina suke su fito su mata sallama" Shi ne abinda kunnuwan Sumayya suka jiye mata. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda ta furta cikin matsanancin kuka, ta kuma miƙe a tsorace.

"Dan Allah Iyarmu ki tashi, dan Allah ki rufa mana asiri ki tashi iya" Shi ne abinda suke faɗa suna kuka. Adduar da aka ce su mata ma basu yi ba sai jijjiga gawarta kawai suke, hakan ya saka aka janyesu tare da ɗaukar gawar "Ki yafe min Iyarmu, ki yafe min Allah ya yi miki rahama" Shi ne abinda Sumayya ta faɗa cikin kuka, sai kuma ta dire gwiwoyinta a ƙasa tare da riƙe ƙirjinta.

***** *****

"Umma ba zan iya zuwa ba, da wane ido zan kalli Sumayya, na rantse da Allah ni sam ban yi da niyyar kisa ba, nayi haka ne dan na ceto ta daga damuwar da take ciki."

"Aikuwa dole kije mata, saboda rashin zuwan naki kin san ba ƙaramar matsala zai jawo ba, ki shirya maza kije kafin ma lokacin ya ƙure, tunda dai baki samu sutura ba" Cikin kuka Maryam ta ce "Ko jiya dana je gidan fa tana nan, amma yanzu ace ta rasu" "Yo ai dama haka Allah yake ikonsa, lokacinta ya yi"

Tunda napep ya sauketa a ƙofar gidan take kuka, a haka ta shiga cikin gidan da kuka, kowa yana kallonta, dan an ma yi tunanin ɗaya daga cikin 'yan uwan Amarya ne, dan sune suka shigo gidan da kuka. Fuskarta rufe da hijab haka ta wuce ta shiga ɗakin, duk da a cike yake amma a haka ta raɓa ta isa kusa da Sumayya ta sake fashewa da kuka.

Atika miƙewa tayi tare da faɗin "Ki tashi ki fita, duk kece kika ja mana ke kika kashe mana Iya keda Baffa" "Atika meye haka? Maryam ce fa? Meyasa baki da hankali, meyasa kike irin maganganun nan?" "Adda ina son Iya ta dawo" Jin haka ya saka Sumayya shiru suka ƙara fashewa da kuka, kowa ɗakin kuwa ya tausaya musu.

Maryam kuwa a gidan ta kwana tare da Sumayya da Atika, dan kusan ita da Atika sune suke ta ɗawainiyar zubar da fitsarin da ledar ta cika sai su zuba a poo su watsar.

Sai da aka yi sadakar uku kuma gida ya ɗan fara raguwa sai 'yan uwan Iya, wanda su suka cigaba da karɓar makoki, Maryam ma ana yin uku ta koma gidan mijinta, sai dai kullum sai ta kawo abincin sadaka safe, rana da dare.

Washe garin bakwai kuwa abubuwa suka fara dagulewa dan 'yan uwan Iya babu ma wanda ya yi yunƙurin ɗaukarsu, dan dama itama Atika ba wata lafiya ba, idan ta botse kamar mai aljanu haka take, ansha kaita magani katsinar ma, ita kuwa Sumayya yoyon fitsari, kuma Amarya ita kaɗaice a gurin mahaifiyarta wadda dama tuni ta daɗe da rasuwa, mahaifinta ma haka ya rasu ba jimawa, to 'yan uba ne jingim gabanta da bayanta, kuma haka suka tsallake bayan sun yi masu nasihar su zauna lafiya kuma su riƙa yiwa mahaifiyarsu addu'a tare da jaddadawa Sumayya batu na zuwa asibitin masu yoyon fitsari, sai dai a ƙarshe sun ƙara da zasu riƙa zuwa ganinsu, a cewarsu sun san Malam Bala ba zai yarda su ɗauke su ba, dan haka su yi haƙuri su zauna.

SaNazdeeyah_🌸

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.