Free chapter · Read without an account

Page 20

by SaNaz deeyah · SUMAYYA

SUMAYYA

Wattpad@SaNazdeeyah_

Arewabooks@sanazty

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[tushen mu'amula tagari]

```Page 20```

Ƙofar take bugawa amma sam Ayrah taƙi buɗewa, har sai da suka kira daya daga cikin ma'aikatan gidan wani ya ɓalla ƙofar, suka sameta tana kuka tana ɗaura gyaluluwanta a jikin fanka.

"Kashe kanki za kiyi Ayrah?"

"Daddy babu mai ƙaunata gara na mutu" Ta furta cikin matsanancin kuka.

"Muna sonki" ya furta yana rumgumeta, tasha kuka sosai shi kuma yasha rarrashi tare da faɗa mata illar abinda take shirin aikatawa.

"Kamal ɗin ma yazo Mommy" Nihal ta faɗa tana dawowa daga taga zuwa kan kujera, ita kuwa Mommy rai a ɓace ta kafawa ƙofar ido. A sanyaye ya yi sallama dan kallo ɗaya za ka masa ka gane yana da damuwa. Da ido kawai Mommy ke binsa har sai daya samu kujera ya zauna, kafin ya gaisheta.

"Mene yake faruwa a gidanku da ka ɓoye min har tsawon sati biyu muna ta neman Sadeeq?"

Kafin ya yi magana Daddy ya fito, dan haka gabaɗaya kallonsu gareshi ya koma. Har ƙasa Kamal ya duƙa ya gaidashi sai dai maimakon amsa kawai sai jin saukar mari ya yi, da sauri ya riƙe kuncinsa. Nihal ganin haka ya sa tayi saurin tashi ta bar parlour.

"Mene gaskiyar abinda ke faruwa naji wasu maganganu marasa daɗi?" Shiru ya yi baice komai ba.

"Kayi magana ko na maka hukuncin daya fi wannan." "Daddy wallahi gabaɗaya setup ne"

"Setup?" Daddy ya sake faɗa.

"Eh kuma ba wani bane face Laila da Sumayya, Daddy sun yi amfani da damar su ta ganin ina shaye-shaye suka ƙulla makirci kawai dan su rabani da Jidda, amma sam babu abinda ya haɗani da matarsa"

"Karka raina min hankali, nayi magana da ita Jidda da iyayenta, amma taƙi tayi magana sai kuka, sannan ta rantse ba zata koma gidanka ba, har mahaifinta ya tabbatar mana da lallai sai dai a raba auren, sannan ita Hamdiyya Sadeeq ya saketa ya kuma tafi bamu san ina ya yi ba wayoyinsa sam basu shiga dole kaine zaka faɗa mana gaskiya"

"Daddy wallahi duk makircinsu ne amma ni sam babu abinda nayi kawai sun yi amfani da shaye-shayen da nake sun san idan suka faɗa masa zai yarda saboda shi dama yana da saurin yarda"

"Idan har na bincika na gane gaskiya ranka zai yi mummunan ɓaci"

"Na amince Daddy" Ya faɗa a ɗan tsorace.

"Ni dai auren yarinyar nan ya zame mana masifa, domin duk shi ne abinda yabi ya hargitsa lissafinmu, wallahi na tsani Sumayyar nan ni dama tun a farko ma bata min ba."

"Yanzu dai ba wannan ne a gabanmu ba, kuma babu wanda zamu bawa gaskiya a yanzu."

******* *******

"Kin yi babban kuskure Hamdiyya, ni nayi tunanin tunda kin yi aure za ki ajiye duk wasu makaman yaƙi."

Ajiyar zuciya tayi sannan ta janye pillow data ɗora a cinyarta ta kalli ƙawarta "Mansura shi fa shaiɗan da kike gani ba rago bane, ni kaina yanzu nadama nakeyi da tunanin ruɗin shaiɗan dana bi"

"Ni wallahi Sadeeq ɗin ya fi min Kamal ɗin ma"

"Ni duk bama wannan ba, wallahi in kin ga yadda aka sakoni gaba a gida za ki sha mamaki, Abba fa har yanzu bincike suke kan lallai sai sun san dalilin daya saka ya sakeni, ni dai ce masu nayi ba laifin dana masa"

"Idan kuwa suka gano wallahi sai sun tsine miki"

"Faɗa ma ɓata harshe ne Mansura, ina cikin gagarumar matsala wallahi ko baccin kirki bana samu nayi"

"Ai duk laifinki ne anyi rufa-rufa anyi auren amma sai da kika nuna hali maimakon ki tuba"

"Wallahi Mansura sai na koma gidan Sadeeq"

"Kin san darajar rantsuwa kuwa?"

"Sosai ma, ai sai dana rabu dashi nake jin mugun son shi"

"Lallai Hamdiyya na yarda shaiɗan ya gama fitsare miki kai, taya za ki koma gidan mutumin da a yanzu babu aure tsakaninku?"

"Zan yi auren kisan wuta kafin ya dawo, na san ya gudu ne saboda ɓacin rai amma tabbas zai dawo"

Baki kawai Mansura ta saki tana kallonta.

****** ******

Kallon kwalbar yake, sannan ya kalli abokinsa Muktar yana lumshe idanunsa da suka masa jajir. "Na kasa daina damuwa Muktar ji nake kamar na kashe kaine"

"Amma idan kasha baka jindaɗinta?"

"Tana mantar dani komai"

"To itace maganin matsalarka kasha wannan yanzu za kaji ka manta komai"

Kai Sadeeq ya gyaɗa sannan ya ɗaga kwalbar nan sai daya tabbatar ya shanye tas sannan ya dire, ya kai dubansa ga Mutkar.

"Ka ƙara min da wata"

"No ai yanzu a level ɗin farko kake ba zaka iya ɗaukar kwalba biyu ba zata iya haukataka ka dai bari ta gama ratsaka sosai."

Kai ya fara ɗan bugawa, idanunsa suna ƙara juyewa.

"Hamdiyya ta cuce ni, wai me ta gani a jikin Kamal?" Ya furta da maye. Muktar murmushi ya yi tare da faɗin "Ta fara aiki kenan!"

"Ai wallahi in na zama sarki sai na sa an kamo min ita ka ga haka?" Ya furta yana sauka daga kujerar tare tanƙwashe ƙafafu.

"Haka zan saka a ɗaureta in kaita can wani gurin" Sai kuma ya fashe da dariya.

"Ka ga muje ɗaki ka kwanta"

"Jiniyar mota nake ji ko har na zama gwamna Muktar?"

"Sadeeq ka zama, ai dama kai gwamna ne, muje ka huta"

Ya kamashi ya nufi ɗaki dashi yana ta sambatu.

Yana kwantar dashi a gado ya girgiza kai "Allah sarki Sadeeq kai da baka son shaye-shaye kuma ka gujeni saboda ina yi amma yau gashi ka dawo gidana saboda damuwa na fara banka maka kayan maye, sai dai wannan ne kaɗai hanyar da zan iya fitar da kai daga damuwar da kake ciki.

****** ******

A sanyaye ta fito daga ɗaki, ta zauna kan kujera tare da sauke ajiyar zuciya. Mami kallonta tayi tare da faɗin "Ba zaki daina damuwa ba Hafsat?"

"Mami hankalina ba zai taɓa kwanciya ba sai na tabbatar an ga Sadeeq"

"Amma ai kin san Sadeeq ba yaro bane, duk inda yake ma dole zai bayyana"

"Cikin damuwa ya tafi, ina tsoron kar wani abu ya sameshi"

Murmushi Mami tayi tare da faɗin "Hafsysy kenan, ni dai Allah ya nuna min ranar da zan ga aurenki da Sadeeq shi ne farin cikina"

Hannu ta saka ta rufe fuska tana murmushi. Wayarta da ta fara ringing ta kalla. "Nihal ce" Ta faɗa tana kallon Mami.

"Ki ɗaga ki ji, Allah yasa dai lafiya"

"Amin" Ta furta tana ɗaga wayar.

"Hello, Nihal ko an ganshi ne?"

"Eh to ku san haka, amma dai Daddy ya ce yana son ganinki"

"Ni kuma"

"Eh yanzu, yana gida"

"To gani nan zuwa" Tana hanging ta kalli Mami ta ce "Daddy ne ke kirana, ina tunanin akan ɓatan Sadeeq ne"

"To kiyi maza kije, Allah yasa a dace"

"Amin."

A yadda ta shiga parlourn sai da taji tausayinsu ya kamata, gabaɗaya suna zaune kamar masu zaman makoki. Daddy ta fara gaisarwa sannan Mommy, ta ƙarasa kusa da Ayrah ta zauna.

"Hafsatu!"

"Na'am Daddy" Ta furta kanta a ƙasa.

"Bayan abokan Sadeeq na nan garin baki da wani abokinsa da kika sani ko da a yanzu basu tare?"

Shiru tayi kafin ta ce "Gaskiya Daddy babu sai dai akwai wani abokinsa a Zaria yana yawan min maganarsa, amma gaskiya bani da tabbacin suna tare a yanzu kuma bana jin zai je gurinsa"

"Meyasa?"

"Baya da hali mai kyau, wannan dalilin ne ma ya saka suka samu matsala da Sadeeq"

"Ya sunanshi kuma a wace unguwa yake a Zaria?"

Shiru ta ɗanyi na wani lokacin kafin ta ce "Eh to kamar dai sunansa Kabir amma gaskiya ban san wace unguwa yake ba"

"Kabir!?" Daddy ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Amma kuma babu sunan mahaifi ko wata inkiya?"

"Sai dai ko a tambayi Nasir amma ni indai zai faɗa min Kabir yake cewa"

Shiru Daddy ya yi tare da dafe kai.

Saƙo taga ya shigo mata, tayi saurin dubawa. Hafsat ina son ganinki. Ɗan kallon Ayrah tayi taga ba ita take kallo ba, kafin ta sauke ajiyar zuciya kawai.

Bata daɗe a gidan ba, ta dai ji ance Nasir zaizo dan haka ta tashi tayi musu sallama.

Driving take cikin nutsuwa har ta ƙarasa farawa. A ƙofar gate ɗin ta danna horn ta ɗan tsaya na mintuna kafin Muktar ya buɗe mata.

"Barka da zuwa"

"Barkanmu dai Muktar ya Sadeeq ɗin?"

"Yana ciki bai ma daɗe da tashi ba"

"Okay bari na ƙarasa." Shiga tayi da motar ta parker sannan ta fito. Tare da Muktar suka jera har zuwa parlorn dake gidan. Kallon Sadeeq kawai take kafin ta samu guri ta zauna, kuma har lokacin bata daina kallonshi ba.

"Sadeeq dan Allah karka fara rayuwar da baka fara ba tun farko"

"Hafsat so kike na mutu? So kike zuciyata ta buga?"

"A'a, kawai ina so ka daidaita rayuwarka ne, shaye-shaye ba mafita bane"

"Ni shi ne mafita ta, idan ina ganin Kamal zan iya kashe sa Hafsat"

"Na yarda, shiyasa ma da ake nemanka ban nuna na san inda kake ba, saboda na baka time ka fita daga damuwar da kake ciki, amma abinda kake aikatawa ganganci ne da rayuwarka, yanzu idan har su Daddy suka ganka ka fara rayuwar nan kana tunan hakan zai musu daɗi? Ko kana tunanin ni zan fita ne dana san inda kake naƙi sanar musu, meyasa ba zaka min adalci ba?" Ta furta da alamun kuka.

"Iya adalcin da zan iya miki kenan Hafsat, idan nasha ina jin damuwata ta tafi"

"So kake ka haukata kanka kenan?" Ta furta lokacin wasu siraran hawaye masu zafi suka zubo mata.

"Kin ga ni ba wannan ba, akwai gayen dana bawa numberki, za ki ɗaukesa kuje shopping ya sayi duk abinda yake so, zan baki ATM ɗina ko kuma nayi miki transfer? Saboda idan kun gama za ki ƙara masa da kuɗin cefane"

"Wannan ba shi ne dalilin daya saka kai yi min kiran gaggawa ba, ka faɗa min menene?"

Shiru ya yi, ta ce "Hmm! Sadeeq ai na gama karantarka"

"Muje mota nayi miki bayani"

"Okay."

Kallon mamaki kawai take bin sa dashi lokacin da taga yana kuka da idanunsa kamar wani ƙaramin yaro, tabbas ta san abin ya taɓa shi sosai dan bata taɓa ganin Sadeeq yana damuwa ba, mutum ne da zai yi wuya ka ga ɓacin ransa.

"Sadeeq ya isa haka ni na fahimceka"

"Ke kaɗai ce za ki fahimce ni Hafsa amma ni na san bayan ke babu, Hafsa soyayyar Hamdiyya ta saka na tafka babban kuskure a rayuwa nayi abinda Allah baya so duk dan na faranta mata"

"Dalili ne ya kawo hakan ba da gangan ba"

"Na san ai haramun ne amma na aikata, ashe ni ba sona take ba ta cutar dani, me kike tunanin zan yi bayan shaye-shaye? Ƙwaƙwalwata zata iya samun matsala haka zuciyata"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda Hafsa ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya.

***** ****

Yana kwance yana waya ta shigo, ranta a ɓace ta kalleshi sannan ta dire masa takarda a gabansa, yana waya ya ɗago yana kallonta kafin ya ce "Ina zuwa zan kiraka" Ya yi hanging yana kallonta. "Baby"

"Babu wata Baby, ka faɗa min dalilin daya saka kaje ka saka aka juya min mahaifa, oh baka son ka haihu dani ko?"

"No ba haka bane" Ya tashi yana ƙoƙarin riƙota ta fuzge tare da faɗin "Ni haihuwa nake so shiyasa naje asibiti ba tare da ka sani ba, kuma sun tabbatar min da mahaifata a juye take, kuma ba a dai-dai take ba"

"Ya ina ƙoƙarin lallaɓaki kina wani fuzgewa"

"Wallahi dole ka biya a dawo min da mahaifata yanda take"

"Ke dakata malama! Ya za ki sakani a gaba kina faɗa kamar wani ɗanki, na juya mahaifarki ne saboda ban aure ki dan na haihu dake ba, ni na aureki dan kawai mu yi soyayya ba tare da kin haihu ba bare naji sonki ya ragu"

"Ƙarya kake"

"Ni nake ƙarya?"

"Eh ɗin...." Wani mari daya wanka mata sai da taga duhu, tayi suman tsaye na wucin gadi kafin ta buɗe idanunta ta kalleshi.

"Kina 'yar talakawa ke har wani zaɓi gareki, yanzu ne za ki shiga sahun sauran matan domin amarci ya ƙare, idan na ƙara ganin kinzo min da wannan maganar sai na saka an kai min ke ɗakin duhu na saka 'yan tauri sun cire min mahaifar taki gabaɗaya"

"Wallahi baka isa ba" Ta furta a haukace sannan ta juya kawai ta warto kwalbar humra akan mirrow ta ɗaga kuwa zata kwaɗa masa ya goce sai ta daki bango ta tarwatse, baya-baya ta fara, shi kuma yayo kanta a fusace kawai ya ga ta zube ta fara karkarwa idanunta sun jujjuye bakinta na fitar da kumfa.

**** *****

Ƙafa kawai yake girgizawa a bakin motarsa idanunsa akan gate ɗin gidan su Laila, tana fitowa ta hange shi, tayi murmushi tare da folding hannayenta ta ƙarasa gabansa. "Ashe kaine ka aika a kirani, ni dai nayi mamaki dan na san wanda zai zo gurina ai ba zai kasa samun number way..." "Dalla dakata, ba surutunki nake buƙata ba" Kallonshi kawai tayi tare da yin ƙwafa.

"Laila ke kika lalata aurena ko?"

"Ai na san babu wanda zaka zarga sai ni, Jidda ma tazo har gida kan na yafe mata amma naƙi"

"Akan me zata zo? Ke ɗin banza, me tayi miki da har zata nemi yafiya"

"Ka ga malam ya isheka haka, kai ba ubana bane da zan fito ka tsareni da faɗa ban tanka maka ba, to ya isheka haka"

"Nayi miki faɗan idan ta kama ma duka zan miki"

Dariya tayi kafin ta ce "Nan fa ɗaya wallahi ƙaryarka tasha ƙarya Kamal"

"Haka kika ce ko?"

"Eh hakane nace"

"Ki jira yadda zan lalata rayuwarki"

"Ai ni dama rayuwata tuni ka gama lalatata taka ce dai bata lalace ba sai yanzu, kuma ni a hakan ma har yanzu ba a biyani ba, alhakin matarka daka ɗauka ko iya shi kana tunanin zai barka ka zauna lafiya bare nawa alhakin daka ruguza rayuwata da shaye-shaye da bin maza"

"Dama can ke 'yar iska ce ni ɗorawa nayi daga inda kika tsaya"

"Kaine ƙungurumin ɗan iskan daka fara lalata tawa rayuwar ai"

"Hmmm" Kawai ya furta tare da juyawa ya shiga mota.

Tana nan tsaye ya figi motar kamar zai taka ta, taja tsaki kawai tayi cikin gida. Tana shiga ta tarar Mommy bata parlour dan haka da sauri ta faɗa bedroom tare da fashewa da kuka, bata taɓa tunanin irin wannan ranar za ta zo ba, bata taɓa tunanin Kamal ba zai dawo gareta ba, ta ɗauka yanzu zuwan da ya yi neman afuwa ne, taso ya bata haƙuri ta haƙura ko dan ta aureshi ta rama abinda Jidda ta mata, sai gashi ashe zuwa yayi yaci mutuncinta.

Naji ƙorafinku akan littafin nan dan haka na saka promo na sati guda kacal zan sayar dashi a ₦300 kacal VIP kuma ₦500 daga yau 08/06/2024 zuwa 15/06/2024 ku biya a saka ku a group bana son katin waya ta accout za a turo.

1 Week Promo hurry up!

Pay via:

Halima Adamu Salahu

7035111671

Opay

Send the evidence of payment through my whatsapp number ***.

Saura 5 pages free pages su ƙare ku hanzarta ku saya.

SaNazdeeyah_🌸

#Shareplease

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.