Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by Ummulkhairi murtala · RAYUWAR DU’A

Page 14

*~reeeyarh~*

    Dawowa  tayi inda mamma ta tashi, ni kike turowa baki, ni kuma yaushe, murmushi kawai yayi yace Allah ya shirye ki aljana, Ameen tace, ba wani labari ne, emmm, kin tabba ta, kai ta daga mishi, kinsan fa banason wannan abun ko, a hankali tace eh tana wasa da yan yatsonta, du’a dagowa tayi suka hada ido, da sauri tayi kasa da kanta.
     Ki dago mana, bata bashi amsa ba, du’a magana zamuyi.

    Du’a a ina kika san umar, dagowa tayi tace waye umar kuma, umar wanda yazo wurin ki jiya, ni a ina, kuma da yaushe, wayar shiya dauko ya nuna mata wani hoto, zaro ido tayi tace wannan hoton fah yaushe aka mini shi.

   Ina tambayar ki kina tambaya ta. shiru tayi alamar tana tunani, yaushe nasa kayan nan, gidan hajiya, duk a zuciya take tunanin, okay abokin uncle sadiq inaga shine umar. 

   Du’a kinyi shiru, nima bansan anyi hoton ba, bashi na tambaye kiba cewa nayi a ina kika san shi, abokin uncle sadiq ne, wana sadiq din, du’a kin san sadiq, eh, taya, kallon shi ta tsaya tanayi duk ya wani riki ce kadai ace akoi saurayin ta a cikin su, bawai basu da kyaun hali bane yasan su sosai. 

    Du’a how did you know sadiq, turo baki tayi tace, wai uncle sadiq, eh shi, mamma ce ta dawo, yace mamma harkin dawo, eh babana, shiririta take maka ko, murmushi yayi yace aa mamma, du’a tashi kije daki muna magana ne, tashi tayi ta shige daki. 

    Bayan sun gama waya da mamma har lokacin du’a bata fito ba, kiran ta yayi, saida ta kusa katsewa ta daga, hello, kinaji ina kiran ki shine kika ki dagawa ko, aa wayan na silent shiyasa, okay dazu muna magana.

    Tame, sadiq, okay saurayin, saurayin wa, cousin sister tane, wacce baka santa ba, sister yaya Ibrahim ce aunty zainab, okay shi kuma umar fa, tare suka zo, ba abokin shi bane ba.

    Eh abokin shine, toh ke gurin ki akazo da zaki fitah, hajiya fa suka zo gaidawa shine aunty tace nazo na rakata zata raka su mota. Okay na gane kice kema saurayi kika yi, ni kuma, eh gashi yayi posting dinki a story sa, kuma nasan kin gani, a ina.

    Kin fini sani, wallahi ban gani ba, ki fadi gaskiyya, Allah yaya ban gani ba, you mean baki da contact din sa, me zanyi da ita, okay shikenan ya huce.

    Kinsan sadiq yayan kishiyar ki ne, ni kuma nake da kishiya taya, toh ba tace soyayya muke ba, sai lokacin ziyada ta fado mata, tace Allah ya kiyaye nayi kishiya da wannan matar, yayan ta mutumin kirki amma ita.

    Shiru tayi yace ita me, ziyada fa ba mutuniyar banza bace kawai dai sone ya mata wawan kamu shiyasa take wannan abun, tana ruwa kawai sai na kama son wanda baya sona, Allah ya kiyaye aikin wahala.

     Kice nima shi nake yi, du’a baki san menene so ba shiyasa kike fadar wannan maganar, du’a so halitta ne, baka san lokacin shigar shi ba, baya shawara saidai kawai ya shige ka, dama Allah yace kada ka wulakan ta mutun dikda nasan ban wulakan ta ziyada ba.

    Amma Allah ya daura mini son wata na dandana yace ziyada ta dandana, muryar shi gaba daya ta canza, da alama yana cikin damuwa. 

    Yaya dama mami da gaske take da tace wata kake so, toh ka fada mata mana, bazan iya ba, yaya adam fah, du’a shima bazan iya fada mishi ba, toh ni ka fada mini zan fada mata.

    Aa du’a for now bazan iya fada miki ba amma zan fada miki wani lokacin, zaki tayani amso soyayyar ta ai ko, in sha Allah yaya karka damu, yanzu dai saikayi ta fadawa Allah kafin ka fada mata, in sha Allah du’a ina fatan ta amshi soyayya ta, Allah yasa yaya, Ameen. 

    Okay du’a barina kwanta saida safe, Allah ya kaimu, Ameen.

Bayan kwana biyu du’a yau zataje gidan su fatiha, fatiha na zaune a palo itada meeno du’a ta shigo, murmushi fatiha ta fara ganin du’a, besting kinzo, eh besting, meeno ce tace hajiya du’a kece kika zo, meeno ya kike, lafiya lau du’a ina mamma, mamma na gida, du’a waya kawo ki inji fatiha, yaya ne.

    Zama tayi suna hira mami ta fitoh, gaida ta tayi mami take tambayar ta ya mutan gida, lafiya lau mami, nan suka hau hira, fatiha tace bari naje na dawo, okay tana tafiya du’a ta fadawa mami abinda adam yace, okay shikenan ba matsala Allah ya kaimu lokacin.
       Da Ameen suka amsa itada meeno, meeno tace zamu sha biki, du’a tace kedai bari akoi shagali, sukaci gaba da hirar su.

   Bayan la’asar du’a tace mami bari naje wurin baffa, tam saikun dawo, futa sukayi suna isa suka gaisa da baffa, basu dade ba, baffa yace suje su gaida papa, har shashen papa suka je sai akace yana shashen hajja, suna isa papa da hajja na palo.

     Bayan sun gaisa fatiha tace bari taje daki wurin zainu dan taji muryar ta, du’a ke bazaki jeba, aa hajja, papa ne ya dago ya kalle ta, au dama wannan ce du’a, yar fatima ko, hajja tayi mishi alamar yayi shiru amma bai saurare ta ba, du’a tace eh nice, ai ance mini soboda ke fatima taki dawowa gida, a zuciya du’a tace ni na shiga uku yanzu harshi yasan maganar nan.

   Ci gaba yayida cewa du’a ki taimaka kafin na mutu, fatima ta dawo gida wallahi nayi dana sani korar ta inason diyata wallahi, du’a suman zaune tayi kenan wannan ne baban mamma, ita bata taba kawo hakan ba, nan abubuwa da yawa suka fara dawo mata, ga kamanin mamma da baffa. 

    Taya akayi bata taba tunanin nan ba, a hankali tace kaine baban mamma, kallon ta yayi da mamaki, shi a zuciya yace au bama ta sani ba kenan, eh nine, murmushi takaici tayi tace an yaudare ni, nagode, ta tashi tayi waje.

   Du’a du’a ina zaki hajja ke kiran ta, fatiha zo, zoki kira mini babar ki, da sauri fatiha da zainu suka fitoh daga daki, hajja meke faruwa, fatiha du’a kije ki kira maman ki, hajja mai ya samu du’a, du’a ta fita, da sauri fatiha ta fita amma du’a tayi nisa.

    Tana futa wasu zafafan hawaye suka sauko daga idon ta hanyar barin gidan tayi, sauri take tana tafiya tana tunani, wayar tace kadai a hannun ta amma jakar na shashen mami. tanaji fatiha na kiran ta amma ko juyowa batay ba, adedeta ta tsayar ta huce gida.

      Nace kayi shiru amma kaki gashi nan yanzu komai ya baci, fatiha dawowa tayi tace hajja mai yasamu du’a, fatiha kije ki kira mini maman ki nace, fatiha futa tayi ita abin duk ya daure mata kai tasan lafiya ta tafi tabar du’a amma ya akayi mai suka mata tana wannan tunanin taje shashen mami.

    Mami na zaune taga fatiha ta shigo duk tayi wani iri, dan ita tafiya kawai take amma batasan tazo ba, fatiha lafiya ina du’a, kuka tasa tace mami du’a ta tafi, ina gida nima basan me hajja ta mata ba, kuma hajja na kiran ki, saliti mami tayi tace shikenan komai ya baci. 

     Mami kamar ya inji meeno, meya kaiku shashen hajja, baffa ne yace muje mu gaida papa, da mukaje yana shashen hajja shine mukaje can.

    Dakko mini waya ta da alkabba a kan gado kiyi sauri, meeno ce ta tashi ta tafi ta dakko, mami na saka alkabbar taja hannun fatiha suka tafi shashen hajja.

  Hajja ta kasa zaune ta kasa tsaye papa na zaune akan kujera hajja ta warware mishi komai, mami ce tayi sallama, saida ta gaida su sannan tace hajja gani, safiyya kirawo fatima yanzun na.

    Mami kiran mamma tayi tasa a speaker, mamma na dagawa tayi sallama tace aunty safiyya ina yini, maryar hajja taji tana cewa yanzu ba lokacin gaisuwa bane ki tambaye ta ko du’a taje gida, mamma da sauri tace aunty safiyya mai ya faru, wallahi ban sani ba du’a tazo gida.

    Aa batazo ba, fatiha ta tsaya duk kanta ya kulle, papa tunda yaji muryar mamma ya shiga zubar da hawaye, safiyya bani wayar nan, mikawa papa wayar mami tayi, mamma najin muryar papa tasa kuka, fatima ki daina kuka dan Allah kinji kiji, a hankali mamma ta furta papa kayi hakuri dan Allah.

      Fatima komai ya huce dan Allah ki dawo gida kinji, sai yanzu fatiha ta gane kan zancen, kenan dama mamma yar papa ce, hajja ce tace kasa yarinya kuka fatima du’a ta dawo, a hankali tace aa hajja bata dawo ba, yanzu dai tasan komai baban ki ya tona asiri, hajja taya, nan ta fada mata yace akayi, ajiyar zuciya mami ta sauke tace ai shikenan komai ya kare.

    Zainu da fatiha sai kallon su suke, a hankali mamma tace gata ta dawo zan kira ku in anjima, okay nan suka kashe wayar, papa fatiha ya bawa wayar ta mikawa mami, nan suka zauna mami tace ai tunda ta koma gida shikenan, fatiha ce tace mami wai mamma yar gidan nan ce, murmushi tayi tace a auta yar papa ce, mami shikenan yanzu du’a ta daina kulani, aa fatiha baza ta daina kulaki ba in sha Allah.

     Mami sallama tayi musu ta tafi itama zainu ta tafi dan ta fadawa uwar ta, nan zance ya baza gida anga fatima.
Du’a na shigowa tace mamma kudi zanba mai adedeta a kan dinning taje ta dakko kudin ta bashi ta dawo koda ta dawo bata nuna wa mamma wani abuya faru ba, cewa tayi mamma bari naje daki kaina na ciwo, okay shikenan, ta huce daki.

     Mami na komawa daki fatiha ta tsare ta da tambayoyi anan meeno tasan meke faruwa,  kina nufin du’a cousin dinmu ce eh cousin diku ce meeno.  tashi tayi ta tafi daki, tana shiga daki ta kira yarima ta fada mishi duk abinda ya faru, ai shikenan mami komai ya baci amma zan kirata kuma jibi zan dawo, okay Allah ya kaimu.

    Tana zaune a dakin fatiha ta kira ta, ita duk zuciyar ta ta karaya, yace papa yake magana kamar zaiyi kuka, bata taba ganin papa ba sai yau, shima sosai yana kamada mamma, message ta tura mata tace besting i can’t pick your call now but kaiki damu ina lafiya ta tura mata.

   Ta ci gaba da tunanin ta kenan shiyasa yarima yace mata ta yafewa family din mamma. Mai yasa abin yazo mata a haka ita gaskiyya tana son besting ta zata iya daina kula kowa a gidan amma badda ita, mamma ce ta shigo, du’a kinyi sallah ne, aa mamma yanzu zanyi, tashi tayi, tayi sallah mamma na dakin, bata fita ba.

    Tana idar da sallar mamma tace du’a zo muyi magana,  mamma nasan maganar da zaki mini, mamma banso sai kuma ta fashe da kuka tace mamma dan Allah karki mini maganar kinji. 

   Shikenan bazan miki ba zonan daina kuka kinji, zuwa tayi ta zauna a gefan mamma ta daura kanta a kan kafadar mamma, oya stop crying my baby kinji, tam mamma kema ki daina, mamma batasan du’a taga tana kuka ba.

    Okay na daina mun bar maganar, shiru sukayi, suna zaune abbah ya dawo, ya tambayi su teema ina mamma, abbah tana dakin aunty du’a inji baffa, dee kuma tace abbah tun dazu aunty du’a bata fito ba kuma kuka take, dan sunji kukan du’a.

    Abbah da sauri ya huce dakin du’a, yana shiga ya tsaya a bakin kofa yadan jima kafin yayi sallama, dagowa sukayi suna kallon shi duk fuskar su tayi ja abinka da farare, karaso wa yayi ya zauna daga dayan bangaran, fatima meke faruwa, wani sabon kuka ne yazowa du’a tace abbah an yaudare ni mai yasa zasu mini haka abbah.

    Suwaye family din mamma mana, sai yanzu ya gane abinda take nifi, dan yasan yau taje gidan yasan lallai tasan sune family mamma, haba baby na akan wannan kike kuka, zonan daina kuka kinji,  matsawa tayi kusa dashi yace it’s okay kinga dik kin saka mamma cikin damuwa ko su teema na na palo duk sun damu dake.

    Ki daina kuka, tam abbah na daina, mamma itama tuni ta fara nata kukan, fatima kema kukan kike kenan shiyasa take yi, du’a ce ta juyo tace mamma ki daina kuka kinji. 

    Mamma sufa suka ja komai tun farko, kuma fah abbah ne ya rufe mata baki it’s okay du’a  don’t said anything kinji. 

  Maza kije palo sisters diki na neman ki, tashi tayi ta tafi palo ta zauna, fatima it’s okay stop crying kinji, ai komai yazo karshe, matsawa yayi kusa da ita yace daina kukan, ki shirya gobe na kaiki gida da kaina. kai ta daga ta kalli abbah, yace eh, abbah du’a baza ta jeba, okay shikenan ki bata nan da sati daya, zata huce kinji. tam shikenan toh zonan goge mata hawayen yayi yace yi murmushi matata, murmushi tayi ta kwantar da kanta kan kafadar abbah.

   Du’a na zama duk suka zo suka zauna a gefan ta, teema tace aunty du’a way are you crying, murmushi tayi tace teema na ba komai, baffa yace aunty du’a please tell us your problem kinji aunty, baffa ba komai kaina ke ciwo, amma kike kuka.

    Baffa, na’am aunty, kana so kaje gidan su mamma, aunty du’a ba kince mamma bata da kowa ba, murmushi tayi tace teema mamma nada family, suna ina, sunan kinsan suwaye, aa, su fatiha, baffa da dee ba gane kan maganar zasuyi ba teema ce ke ganewa, aunty du’a taya, teema zan fada miki but now I need to eat something, okay bari na zubo miki abinci.

   Tashi tayi ta zubo mata, aunty du’a gashi, dee tace aunty du’a nazo nayi feeding dinki, dariya tayi tace yanzu dee ni zakiyi feeding, eh aunty du’a, oya zo kiyi, tashi tayi ta dawo dafda ita ta fara bata abincin a baki.

    Suna na bata idan wance ya bata sai wance ya bata yaya ya shigo, toh fah yau kuma yaya nawa sisters dinta shagoba, murmushi tayi yazo shima ya zauna, teema ce ta tashi taji ta karo abincin suka zauna idan akaba wannan sai aba wannan dukan su sukaci suka koshi.

    Mamma daga kai tayi ta kalle abbah da tun dazu suka fitoh suna kallon su, murmushi sukayi, abbah ya ruko hannun ta suna isowa palon, abbah yace kanku kuka sani kun manta dani da mata ta ko, dee ce ta tashi da gudu tayi kan su, tace abbah ni zanyi feeding dinku ko, baffa yace aa ni zanyi, zama sukayi suka ci gaba da feeding juna, tashi sukayi su abbah suka tafi masallaci su kuma duk sukayi sallah.

    Du’a tayi farin ciki zama da family ta, yaya baisan meke faruwa ba, koda ta shiga daki ta dau wayar ta miss call din yarima ta gani, a zuciya tace koma inanan ba dagawa zan ba, koda suka dawo palo abbah yace kowa yaje ya shirya yau fitah zasuyi sunyi farin ciki.

   Nan suka fita sukayi shopping suka je suka sha ice cream, du’a sunsha hotuna sai kusan 10:00 suka koma gida, yau abbah ya canza wa du’a waya ya shiya mata iPhone 12.

    Nan mamma tace ta bawa teema wacce wayar, abbah da karya yarda aka bata wayar,  sunyi nisha di sosai.  Suna dawo wa kowa dakin shi yayi suka kwanta.

      Fatiha tunda taga message din du’a taji zuciyar ta tayi sanyi, koda adam ya kira ta saida ya gane tana cikin damuwa ya tambaye ta ta fada mishi komai, tab gaskiyya lamarin ya baci amma ba yanzu ya kamata du’a ta sani bah, dama ka sani eh teema, ai shikenan Allah ya kauta, Ameen sun dade suna hira sannan sukayi sallama.

    Koda ta hau online taga story din du’a sai tayi farin ciki dan taga tana nishadi.

  Washe gari sai kusan 11:00 du’a ta fitoh lokacin su baffa sun tafi school abbah ya tafi office yaya ma haka. Mamma na daki, aunty halima ina kwana, lafiya lau du’a kin tashi eh ina mamma, tana daki, bari naje tana tafiya, okay.

     Tana shiga daki mamma na waya da hajja, good morning mamma, morning du’a kin tashi, eh hajja zan kiraki anjima, no mamma kiyi wayar ki abinci zanje naci, okay shikenan inna gama zan fitoh tam, ta fuce.

    Zama tayi tana cin abinci kira ya shigo wayar ta, dagowa tayi tace besting na ya kike, lafiya lau besting ya gida, Alhamdulillah yasu mami, lafiya lau. 
   Du’a shine jiya ina kiran ki kika ki amsa wa ko, besting sorry I’m not in a good mood shi yasa, ai shikenan.

    Du’a kiyi hakuri wallahi ban sani ba da na sani ai saina fada miki, murmushi tayi tace fatiha kibar maganar kinji banson ta okay shikenan ya huce, okay bye zamuyi magana anjima, du’a ki gaida mamma, zataji in sha Allah. Daga nan ta kashe wayar. 

      Bayan ta gama wayar ta koma palo ta zauna mamma ce ta fitoh, nan ta zauna, du’a ta koma kusa da ita ta kwanta , kanta na kan cinyar mamma, yarima ne ya kira mamma yace yana so suyi video call okay ina zuwa, du’a dakko mini laptop dina a daki, tashi tayi taje ta dauko ta dawo ta kwunta.
T
       Mamma ajiye laptop din yarima ya bayyana, gaisa sukayi da mamma, du’a ko kallon inda yake batai ba, bayan sun gaisa yace du’a ba magana, tashi tayi tabar wurin, mamma tace du’a ba magana ake miki ba, ni kuma mamma, mamma ki barta, tashi tayi tabar palon.

Bayan sun gama waya da mamma ya kira ta amma taki picking.   

  Washe gari ya dawo, fatiha da meeno suka je dauko shi baba ya kaisu kusan 4:00pm ya dawo, nan mami tayi ta tarar rayar shi kamar jariri wai tayi missing din shi, da daddare yace fatiha da meeno su shirya zasu je gidan mamma gobe, sundan dade suna hira sannan ya tafi part dinshi.

     Du’a kuwa yinin farin ciki tayi dan su munira sunzo sai dare yaya Ibrahim yazo ya dauke su.

    Washe gari sai kusan 10;00 ta tashi, su dee na tafis, tana fitowa falo mamma na zaune, bayan taci abinci ta dawo ta kwanta kusa da mamma, kanta na kan cinyar mamma suna hira.

    Sallama sukayi du’a bata amsa ba dan ta gane muryar su, mamma tace a fatiha kune duk dan du’a ta tashi amma sai taga ta gara kwanciyar ta, zama sukayi suka gaisa da mamma, du’a tashi ki dakko musu abin sha, tashi tayi ta dauko musu mai makon ta zauna sai tayi daki tasa key, duk sunji karan key din.

    Yarima tunda suka shigo hankalin shi nakan du’a fatiha ma, meeno ce kadai take son ganin yaya, aiko Allah ya taimaka yana gida, babana kaga halin ta ko, mamma ki barta har yanzu yarinya ce.

        Yaya ne ya fitoh daga daki, yana cewa mamma wai ina wannan yar rainin hankali tun dazu nace ta kawo mini abinci amma ba ita babu labarin ta, fatiha ce tace yaya ashe ba nida besting kadai ne acici ba, sai lokacin ya kula da su, zama yayi kusa da mamma suka gaisa.

     Bayan sun gaisa yace ina mami, yarima har zuciyar shi yaji yana son yaya, tana lafiya, masha Allah, ba abinci zaka ciba, mamma ki barshi indan anjima naci aa kuje kuci tare, babana kuje kuci abinci, aa mamma muna gama breakfast muka fitoh, tashi kaje kaci abinci, wayar shi ya ajiye a gurin ya tashi.

     Yaya surika na kira, abinci ya dauko ya dawo palo ya zauna sannan ya daga wayar, hello Zahra na, mamma ce tadan bige shi tace tashi anan, Zahra tace babee yanzu karar ka mamma take, tana jinki a speaker yasa wayar, mamma tace yaran zamani Allah ya shirye ku, mamma ina kwana, lafiya lau surikar ya maman ki, lafiya Alhamdulillah.

     Meeno jikin ta duk yayi sanyi, yarima kuwa kallon ikon Allah yake yace yaya da mamma ke nishadi, fatiha ce tace kishiya ta ya kike, babee yanzu dama kishiyar nanan shine baka bani mun gaisa ba, gata nan ai kun gaisa ko, aa bata muyi hira, nan sukayi ta hira, yarima na danna wayar shi amma hankalin shi nakan du’a.

     Can tace ina sister, tana daki, idan ta fitoh kice ina gaida ta, okay zataji in sha Allah, yaya daya kusa gama cin abinci yace beb zamuyi magana anjima okay beb bye ta kashe wayar.

      Mamma wai ina du’a, tana daki, daki kuma tayi baki kuma ta tafi daki, mamma ta fada mishi abinda ke faruwa. 

     Number ta ya lalubo ya kira, yasa a speaker shi dabi’ar shice saka waya a speaker, hello yaya kayi hakuri, quiet ki fitoh yanzu nan, yarima saida ya kalle shi yace dama haka yake tab, meeno ma kallon shi tayi da mamaki dan bata taba tunanin yana da zafi ba, fatiha kuwa dama tasan halin shi.

Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️


Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.

   Nagode 
*~Book by Reeeyarh~*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.