Free chapter · Read without an account

71

by Fatima Xarah · FARAR TASKA

Yana zaune bakin gado sanda ta shigo, suna haɗa ido taji hankalin ta ya tashi ainun, tsoro da firgici ya bayyana a fuskarta, tasa hannu tana kare jikinta, ya tsura mata ido cikin tausayin kansu, idan yace abinda Hajajju ta basa bai yi tasiri a jikinshi ba yayi qarya, haka kallon surar jikinta ya ƙara jefa shi a wani hali, but he can control himself, bazai iya kasancewa da ita ba, a hankali cikin muryar raɗa yace "zo nan", ya faɗa tare da nuna mata kusa da shi, kamar bazata je ba ta soma tafiya a hankali har zuwa inda ya nuna mata tana kame jikinta, cikin tsoro ta zauna tana hawaye, ya dube ta yana faɗin "kina da wanda kike so? tayi saurin girgiza kanta, domin babu shi a halin yanzu, dama soyayyar makaranta ce acan qauye da take da classmate ɗin ta, Kuma tun ciwon Ummy har kawo yanzu ta manta dashi, yayi jim yana kallonta qasa qasa cike da sha’awa, yace" saboda baki da wanda kike so kika yarda aka miki aure dani? Tace "nima bansan zaa yi ba sai bayan an daura auren", ya dafe kansa, yayi shiru kaɗan kafin ya dago yana kallon ta, hau gadon da kyau ki kwanta, bazan iya hantara ko wulakanta ki ba saboda jinin Meelah ce ke, kuma baki da laifi akan komai, amma sai kin yi haquri dani ina son ƴar'uwar ki, zaki iya zama dani a hakan? Tace "Meelah ma tana son ka sosai, kullum bata da damuwa sai taka, kuma kullum acikin kuka take, mun yi deciding zan zo ka sake ni itama Jameel zai sake ta sai ka aure ta", yaji wasu hawayen tausayin Meelah, yace "ko na sake ki Deejah Hajajju bazata taba bari na auri Meelah ba tunda bata son ta", Deejah ta buɗe ido cikin mamaki tana kallonsa, ya gyada Kai a hankali kamar ƙaramin yaro, "saboda bata son ta, ta hana aure na da ita, amma ke tana son ki, kuma kada ki sanar da meelah hakan, na haqura zan zauna dake amma kece zaki san yanda zaki mantar dani Meelah, ki koyamin yanda zan so ki, ni kuma zan so ki da zuciya ɗaya tare da baki kulawa, kawai ina son zuciyata ta manta da meelah ", Deejah ta share wasu hawaye ganin ƴar uwar ta bazata taba samun abinda take so ba, cikin rawar murya tace" ni bansan yanda zan mantar dakai Meelah ba, kuma ni ban san yanda zaka so ni ba", yayi murmushi kaɗan kafin yace "je ki kwanta, ki rufa jikin ki da kyau saboda sanyin na'ura, naga Hajajju bata baki kayan kirki kika saka ba", a kunyace ta matsa daga gare sa kafin ta hau gadon gabaki daya ta lullube, ya tashi da ƙyar saboda irin abinda yake ji a jikinsa, bayi ya shiga ya sakarwa kansa shower, ya ɗauki kusan 10minutes a hakan kafin ya fito, idanunsa akan ta da alama ta fara barci, ya shirya cikin kayan barcin sa kafin ya hau gadon, addu'a yayi sosai kafin ya koma karshen gado ya kwanta zuciyarsa a jagule.

Washe garin ranar da sassafe kafin kowa ya tashi tayi wanka ta shirya ta fice daga gidan zuwa school, ko da Muhairah ta tashi bata ganta ba duk tunanin ta tana bayi ko kuma falo, duk ta duba bata nan, sai ta nufi ɗakin umma bata nan, haka ta fito a sanyaye tana tunanin inda zata je da uwar safiya haka, ko da yake jiya da dare kafin tayi barci ta sanar da ita idan zasu fita shopping da suka yi magana ta same ta a school su je, babu tantama school ta fita da uwar safiyar nan domin ta gujewa haɗu wa da Yaya Jameel, ranar ma duka lectures da aka yi babu wanda ta mayar da hankali ta gane, daga kuka sai tunani, munira da Aimana suna kokarin su na ganin sun kwantar mata da hankali tare da rarrashin ta har lokacin da Muhairah ta zo school ɗin, Muhairah ta fito mota da Affan yanda Meelah zata gane ta, aikuwa fitowar ta a motar ya saka Meelah tashi da backpack ɗin ta tana kallon su Aimana tace "ready to leave", munira tace "har an zo ɗaukar ki ne" ta gyada kai a hankali, suka rakata har gurin mota, cikin girmamawa suka gaida Muhairah ba dan ta girme su ba sai dan daraja ta aure dake kanta, itama ta amsa da murmushi tana kallon Meelah tace "your friends? Meelah ta gyada kai tana kallon su tare da nuna Muhairah tana faɗin" sister in law ", suka cika da mamaki, Meelah ta shiga motar lokacin da Muhairah ta zagaya ta shiga, su munira suna kallon su cikin murmushi da burgewa suna daga masu hannu har suka bar gurin. Abbot Kinney Boulevard suka nufa, har taso tace mata suje FH Boutique na Feenah Sai tayi nauyin baki, ta tabbata duk abinda zasu dauka ba lallai bane Feenah ta yarda su biya, gwara suje inda zai ji a aljihu sa kuma ta bata masa rai da saka kayan tunda ance baya so, haka Muhairah ta dage gurin zaba mata designer dresses, casual wear, street wear, har da traditional wears, shoes, handbags, jewelries, skin care, perfumes kala kala masu sanyin ƙamshi, Sai abin ya dawo bawa Meelah mamaki ganin uban kayan da take haɗawa kamar wacce ta shirya zama na din din din da yayanta, ta dubi Meelah tana faɗin "hope baki manta da atm card nashi ba kada muyi abin kunya? Meelah ta bata card ɗin tana faɗin" dama zan baki ne, wancan deal da muka yi mgn is canceled" meyasa? Muhairah ta tambaya tana kallonta da mamaki, kin fasa sakin ne? Tace "innar'mu tace zata yafe ni idan na kashe auren, bansan ya zan yi ba kuma ni bana son zama dashi", ta soma hawaye, Muhairah tace "we will find another way, bari muje gida sai muyi mgnr", Meelah ta jinjina kai, suka je suka biya kuɗin aka kwashi kaya aka loda masu a bayan mota, suna isa gida yana kokarin fita daga gida, Hassana na bayan shi sai shagwaba take masa wai bai kamata ya fita yau ya barta ba tunda a jiya ta tare, yana gani Muhairah ta soma fito da kaya, Meelah na tsaye dauke da Affan tana ciro iya wanda take iyawa, cikin mamaki ya dubi Muhairah yana faɗin "ina kuka fito da kaya haka? Muhairah tace" daga shopping muke, mun je na siyawa Meelah duk abinda take so ne, take your card", tayi maganar tana bashi atm ɗin shi, bai karbi atm ɗin ba cikin tuhuma yake kallonta kafin yace "yaushe kika dauki atm din ban sani ba, and da izinin waye zaki ɗauki matata ki fita da ita batare da sanina ba", Meelah da jin haka taji wani ƙunci a ranta, ta ja ƙaramin tsaki wanda ya saka shi kallonta da sauri, Muhairah kuwa turo baki tayi a shagwaba tana faɗin "ka shige daki tare da matar ka tun safe har yaushe ka fito na sanar da kai zamu fita, ai ba laifi bane tunda matarka aka kashewa kuɗin", ya bata fuska kaɗan yace "ita Hassana meyasa baki je da ita ta siye duk abinda take so ba", kafin Muhairah tayi magana Hassana tayi caraf tare da riqe hannunsa tace "No need love, I only want your company, nafi so muje tare, kai ma kasan babu dacewa naje da yara siyayya bayan ina da kai, you are enough for me", daga Meelah har Muhairah kallon takaici suke binta dashi, Jameel ya karbi card ɗin shi yana hararar Muhairah, ya juya zai shiga mota, Hassana tace "yaushe zamu je siyayyar Ina buqatar skincare da perfumes", cikin bacin rai da takaicin abinda Muhairah tayi masa domin shine ya cancanci ya kai Meelah shopping ta dauki duk abinda take so a gaban sa amma taje tayi masa shigen sauri, yace da Hassana "sai sanda na sami lokaci", Hassana ta soma buga ƙafafu cikin shagwaba alamar bata gamsu da amsar sa ba, Meelah sai kallonta take cikin mamaki qatuwar mace da shagwaba, Muhairah ta dubi Meelah cikin bacin rai tace "sai ki tsaya kina kalle kalle bazaki tayani shigo da kayan ba, ba'a son yawo da yara amma an iya kwaikwayo da ɗabi'ar su", taja tsaki, Hassana ta dube ta zata yi magana tuni Muhairah tayi cikin gida da kaya a hannunta, Meelah ta dauki wanda zata iya tabi bayan ta saboda Affan dake hannunta. Umma sai farinciki take da yanda taga Meelah ta sake da Muhairah yanzu, masu saka furnitures har sun zo sun sakawa kowa a bangaren shi, an qara gyara gidan yayi kyau sosai, Zaid yazo saboda a gobe zasu tafi har Umma, sosai Meelah ta shiga damuwa sun yi sabo da Muhairah cikin lokaci ƙanƙani kuma zata tafi ta barta, Muhairah tace "kullum zamu yi video call, muna ganin juna and gisting kada ki damu, you will only miss my presence Amma muna tare kullum a waya", da wannan hankalin Meelah ya kwanta kaɗan tace "kince idan muka zo gida zaki gayamin mafita da zan bar yayan ki", Muhairah tayi jim kaɗan kafin tace "just try kiyi duka abinda na gaya maki ɗazu, saka qananan kaya always a gidannan da wadannan turaren kada kiyi wasa dasu a jikin ki, kinga koda qatuwar matar sa ta saka qananan kaya kada ki dauka tayi saboda ta burge mijin ne tana yi ne dan ki dauka yana so kiqi masa, she don't want you, so komai zata iya, ke kuma ki saka saboda kawai baya so kuma zaki bata masa, idan wannan bai yi aiki ba, just meet him, ƙi cire tsoro ki gayamishi ya nema maki mafitar da zai rabu dake batare da maman ki taga laifin ki ba, nasan yaya da hangen nesa he will think for the solution ", Meelah tace" nifa bazan iya saka wannan kayan ba, but zan iya samun sa akan ya nema mana mafita", Muhairah tace "not bad, ki saka kayan ba sai kin fita ya gani ba, kiyi kwalliya ki zauna a daki shikenan, ni zan riqa kira ina ganin yanda kayan yayi maki kyau a jiki, pls kada kice ba zakiyi wannan ba kin ji friend", yanda Muhairah tayi maganar ya saka taji bazata iya mata musu ba, sai ta gyada kai alamar ta amince, Muhairah taji daɗi tana fadi a ranta idan baki fita ba ai shi zai shigo dakin ya gan ki dasu, sun jima a daren suna hira ta ban kwana kafin su kwanta, washe gari har da hawaye sanda suka tafi, Umma tayi wa jameel fada sosai akan Meelah yayi mamaki yanda Umma tasan irin abinda ya aikatawa Meelah, kuma ta roqe shi yayi adalci ya kula da yarinyar da kyau cos Hassana ba qaramar yarinya bace zata iya kula da kanta.

Tun bayan tafiyar su da two days suka fara exam, bai kara saka ta a idanun sa ba yanda bata zama a gidan, a school duk hanyar da zai ganta bata bari, sanda zata dawo gida bayanan da ta shiga sashen ta take rufe ƙofar falonta bazata qara fitowa ba sai washe gari, abincin kirki bata ci tunda bata iya girkawa ba, kullum acikin shan tea take, suna waya da Feenah jefi jefi taji ya Meelah ko ta kwantar da hankali ta amma bata ji alamar hakan ba, suka kammala exam kullum tana a ɗaki kwance, daga waya da Muhairah sai su Munira, tana kiran Ummy idan bata ɗaga ba sai ta kira Audi, su jima yana kwantar mata da hankali akan auren ta. Kallo ɗaya zaka mata ka gane tayi wata irin rama ta fige lokaci ɗaya, ranar tana zaune a falo taji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar, tasan ta rufe da key sai ta cika da mamakin ganin sa ya shigo alamar yayi amfani da wani key daban, kenan duk tsawon wannan lokacin zai iya bude kofa ya shigo amma yake kyale ta, idan hakane menene amfanin rufe ƙofar, ya tako a hankali har tsakiyar falon yana kallon ko ina yana yatsina fuska, komai a hargitse kamar wacce ta tara yara a gida, ya tabbata tun sanda aka mata gyara bata taba gyara ko ina ba, ga dinning duk ta cika da cups da take amfani dasu a maimakon ta kai su kitchen, sai ya soma tunani nema mata mai aiki tunda bazata iya ba, shikam bazai iya zama a inda babu tsabta ba, ya zauna yana kallon yanda ta rame cike da mamaki yace "bakya cin abinci ne? Kamar bazata yi magana ba sai tace" I hate cooking, Kuma ban iya ba, and I don't want to", ya jinjina kansa yana mamakin inda mace ke cewa bata son girki, amsa uku ta bashi acikin tambaya ɗaya, yace "idan ke bakya so, ni kuma waye zai bani abinci a duk sanda nake bangaren ki", ta yatsina fuska tana bata rai, tace "Ai kana da mata sai ta riƙa maka girki.... ya katse ta, ke da kwana da miji sai ita ta miki girki, kin ga dacewar haka? Kwana da miji ta maimaita tana masa wani kallo, ya kauda zancen yana kunna laptop ɗin sa fuskarsa babu walwala yace" kwana biyu da kika ga na ɗaga maki qafa bana neman ki saboda na baki lokaci kiyi karatun exam ɗin ki cikin kwanciyar hankali, ashe ba karatun kike ba tunda kika iya faduwa jarabawa haka", hankalin ta ya tashi, zuciyarta ta soma bugawa da karfi da karfi, jikinta ya dauki rawa sanda ya juyo mata da fuskar laptop ɗin tana duba scores ɗin ta, ta fadi kusan guda uku ciki kuwa harda nashi, hawaye suka cika idanunta, sai kuma ta fashe da kuka mai tsanani, jikinsa yayi sanyi, yace "gayamin damuwar ki Meelah, menene ya saka kika faɗi jarabawa bayan na duba duka performance naki na baya baki taba faduwa a exam ba, duk wadannan da kika fadi a yanzu sai kin yi resitting nasu, cikin kuka tace" kai ne, saboda bana son ka, bana so na zauna tare da kai", wannan kalmar ya gaji da jinta a yanzu, yace "laifin kine ai mun yi deal dake, ki bada kuɗin ko a yanzu kike son saki zan baki idan kin shirya abinda zaki gayawa Ummy kada tayi fushi dake", ya ƙara dagula lissafin ta, ta tsananta kukan ta sosai kamar zata shiɗe, faɗuwa jarabawar nan ba ƙaramin taba zuciyarta yayi ba, ta tabbata da a gaban Hussein take babu abinda zai hana masa dukan ta ko nuna mata tsantsar bacin ransa, to akan me ma zata fadi jarabawa idan tana tare dashi, wanda kusan kullum suna tare yana encouraging ɗin ta, yace "bar kukan muyi magana dake, am tired of your childishness, tunda baki da abinda zaki bani na baki saki wanda kinsan ko giyar wake nasha bazan taba maki shi ba sai ki ajiye mgnr sakin a gefe, dan babu mai raba mu sai Allah ko da zaki mutu da tsanata a zuciyar ki, bayan sakin gayamin abinda kike so, wallahi zan maki shi idan har zaki dawo da walwalar ki, kuma zaki maida hankali ga karatun ki, kina shekara ta qarshe a karatun ki kuma kike son bata karatun, ban ji daɗin wannan result ba Meelah ", ta dago da kanta tana share hawayen fuskarta batare da ta kalle shi ba, ya tsurawa fuskarta ido kafin yace" ki gayamin ko menene ina ji, amma kada ki qara cewa bakya sona na san da wannan, sabon abu nake son ji daga gare ki", a hankali cikin muryar kuka tace "bana son ganin ka, stop showing your self to me, Kuma Idan har kana so na da gaske kamar yanda kake faɗa, pls ka daina lecturing a school ɗin mu, nesanta kanka daga gare ni shi kaɗai zai saka na kwantar da hankali na nayi karatuna like before.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.