Free chapter · Read without an account

Matar khalees 33

by Nusaiba Ibrahim Rimi · Matar Khalees

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 33

Kwanan Deeja da dawowa ta ja Afra suka nufi gidan su Umaima ko nace gidan su Najeeb,sun sha mamakin a halin da suka same shi,yayi haɗari ya faɗo daga mashin ya gamu da matsalar spinal cord,ko iya tashi bayayi, mahaifiyar shi mai jinyar shi

Da sallama suka shiga parlourn da Afra ta rinƙa bin shi da kallon mamaki ganin yadda ya sauya,suka gaida mahaifiyar tashi,da ke bin su da idanu,ta amsa da fara'a, Deeja ta gaishe da najeeb da ke kwance yana jin jiki,don bayan wannan matsalar har da brain cancer da ta kama shi,ya amsa cikin rawar murya, Afra kam ko kallon banza bai samu daga gare ta ba, Deeja ta kalle shi tace

"Am dama gidansu umaima muke son zuwa,to bamu san address ɗin ba,shine nazo idan Allah ya sa ka sani ka sanar mana"

Shiru Najeeb yayi na ƴan sakwanni kamar bazai ce komai ba,ƙwalla ta tarar masa a idanu,cikin karayar zuciya ya fara bayani

"Umaima ƴar garin taura ce,tana zaune a wani family house mai suna gidan cheɗiya,kaf garin su ansan gidan,sai dai umaima bata ji dadin gidan ba,don haka ko Ni bani da tabbacin zaku same ta ko bazaku same ta ba"

Deeja ta miƙe tana faɗin"zamu jarraba zuwa mu gani,in Sha Allah zamu same ta"daga nan tayi wa mahaifiyar shi sallama ta dire mata kuɗi 20k, mahaifiyar shi sai godiya take kamar zatayi wa Deejan sujjada, shima Najeeb cikin karayar zuciya yace

"Deeja,ki yafe min,kinga yadda rayuwa tayi dani,idan kika haɗu da umaima itama kice ta yafe min,don na cutar da rayuwar ta da yawa"

Deeja ta goge ƙwallar idanun ta tace"na yafe maka"sannan ta fice daga parlourn, Afra ta biyo bayan ta

Kai tsaye Deeja ta nufi taura jihar Jigawa,daga ita har Afra suna fatan Allah yasa su ga umaima

Basu wani sha wahalar gano gidan ba,amma da suka tambayi wata mata da ke tatar gasarar koko ina Umaima?sai ta yatsina fuska tace"bata dawo daga kasuwa wajen sana'ar ta ba,sai dai ko ku jira ta ko ku bi ta"Deeja da Afra suka kalli juna suka sake kallon matar,Deeja tace"babu matsala zamu jira ta,inane ɗakin nata?matar ta nuna musu tsohon ɗaki mai tsohon ƙyaure batare da ta sake magana ba

Allah yaso da bishiya a kofar ɗakin umaiman, Deeja ta koma mota ta ɗauko musu babbar dadduma suna hira suna shan iska,babu wanda yayi musu tayin ko ruwan sha,in da Allah ya taimake su suna da ruwan gora a mota,shi suka sha sukayi,Deeja ta ɗauko musu ƙatuwar dadduma sukayi alwalar azahar sukayi sallah. Zaman awa biyu da mintuna sukayi umaima ta dawo, Deeja tana bawa afra labarin Cambridge University ta hango Umaima tana shigowa gidan,shiru tayi tana kallon yadda ta fice a hayyacin ta tayi duhu sosai,tana sanye da atamfa da hijabi da suka ji jiki,amma fes take,fuskar ta ma babu alamun damuwa sam a tare da ita, Afra ma kallon ta takeyi,har taje wajen wata igiya ta kwaso kayan shanya sannan ta nufo ƙofar ɗakin nata

Sam bata kula da wasu a zaune ba sai da ta ƙara matsowa, Deeja ta fara gani,don tafi saitin inda take tahowa,ƙamewa tayi tana kallon Deeja da tunanin ko mafarki takeyi, Deeja tayi murmushi ganin irin shock ɗin da Umaima ta shiga ta miƙe tana murmushi ta rungume ta, Umaima ta ƙanƙame Deeja tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya,afra ma ta miƙe tazo ta rungume ta, Umaima ta haɗa su duka ta rungume tana kuka,sai da ƙyar ta ɗago tana kallon Deeja tana faɗin"Allah Sarki Deeja!ina kika shiga ne?yadda na ɗauke ki ba haka kika ɗauke Ni ba,na shiga tashin hankalin ɓatan ki,ki yafe min Laifuka na Deeja......"maganar Tata ta katse saboda kukan da jaririyar bayan ta ta fara tana mutsu mutsu,wadda Allah bai sa Deeja da Afra sun kula da ita ba

Sakin Deeja tayi ta ɗanyi baya tana sauko da babyn,kallo ɗaya Deeja tayi wa jaririyar ta waro idanu tana faɗin"umaima haihuwa kikayi?"

Murmushi umaima tayi,Deeja ta amshi yarinyar tana ƙara kallon ta,bata da maraba da mahaifin ta Imran, Umaima ta ɗauke daddumar da suka shimfiɗa da suka shimfiɗa ta buɗe ƙofar ɗakin ta suka shiga cikin ɗakin

Siminti ne malale a ɗakin,amma duk ya faffashe,daga gefe kuma yaloluwar katifa ce da aka shimfiɗa mata zanin gadotsoho,sai dai ɗakin ƙal yake,dama umaima ba daga nan ba wajen tsafta

Cikin rawar jiki ta dauko murhun ta na gawayi tana ƙoƙarin hura wuta, Deeja ta dakatar da ita, Umaima tayi murmushi tana kallon Deeja tace"ko dai bazaki iya cin cimar mu ta ƙauye bane?"

Da sauri Afra ta kalle ta,nan da nan hawaye suka ciko idanun ta,tace "Umaima yau ke kike kiran kanki ƴar ƙauye?"

Umaima ta waro idanu tana murmushi tace"to da Ni ɗin ƴar ina ce?nan ce mahaifata,nan ce mahaifar baba na,kinga kuwa bani da inda yafi nan"bata ƙara sauraren su ba ta cigaba da ƙoƙarin hura wutar ta, Deeja tace"mu fa ba yunwa mukeji ba,ki zo mu zauna, magana zamuyi tukunna"Umaima tace"duk da haka dai sai mun ci abinci tukunna"tilas Deeja ta ƙyale ta, Umaima ta ɗora musu faten tsaki da yaji yakuwa da gyaɗa

Bayan ta gama a kwano ɗaya ta zuba musu,ta ɗebo musu ruwa a ƴar randar ta,suka ci a tare suna hira,bayan sun gama ta kwashe kwanukan don wankewa, Deeja kuma ta gyara wajen, Umaima tana shigowa tace"kai!daga zuwa kawai sai ki fara aiki?"

"Ke dai zauna kawai Umaima"a cewar Deeja,babu musu ta zauna tana fuskantar Deeja

Deeja tace"umaima me ya faru bayan tafiya ta?kuma dama kina da ciki kika taho baki gayawa Imran ba?ya na ganki haka?me yake faruwa ne?"

Murmushi mai ciwo umaima tayi,ta karɓi jaririyar ta daga hannun Afra,ta fara shayar da ita,ta jingina kanta da jikin bango ta fara magana cikin sanyin murya

"Iyaye na dukka biyun na rasa su ina ƙarama, mahaifiya ta ta rasu ina da shekaru biyar, lokacin da ƴan uwan ta suka zo gaisuwa bayan an share makoki sun so tafiya dani,amma mahaifi na yace a'a, tabbas ran ƴan uwan mahaifiya ta ya ɓaci,ƙarshe dai baayi rabuwar daɗi ba,don baba na jadaddawa ya rinka yi ƴa tashi ce babu mai raba su,dangin shi suka shiga maganar suka ƙara dagula lamarin

Haka dangin mahaifiya ta suka koma garin su suka barni a hannun mahaifi na,babu irin gatan da baiyi min ba, makaranta boko da islamiyya da kanshi yake kai ni,ya zauna yayi hira dani,yayi wasa dani,don sam bana iya shiga cikin yara kamar kowa nayi wasa,don haka idan mahaifi na bayan na dawo daga makaranta ɗakin mu nake shigewa nayi ta wasanni na da kayan wasan da baya gajiya da siya min

Haka rayuwa ta kasance har tsawon shekaru uku,a lokacin ina da shekaru takwas,a wannan lokacin ne nasan ma'anar rashi duk da ƙarancin shekaru na,don a shekarar ne na rasa mahaifi na bayan rashin lafiya da yayi ta kwana ɗaya"umaima ta kasa cigaba saboda kukan da yafi ƙarfin ta,da alamu har yanzu tana jin zafin mutuwar,su kansu Deeja da Afra kuka sukeyi,Deeja ma mutuwar mahaifin ta ce ke dawo mata

#Nusy_bee

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.