Free chapter 路 Read without an account
PAGE 4
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 4
Yau tun da muka wayi gari na 蓷auko wanki ina yi bayan Bahrain ya tafi islamiyya kasancewar yau Asabar ce. Ina cikin yi Ammie ta fito ta zauna tana tayani har kusan 茩arfe sha biyu saura na rana, bayan mun kambala na zuba mata ruwan wanka sannan na gyara wuta na sake 蓷ora ruwan zafi a tukunya daga nan na zari hijabina sai wurin Baba mai Shago.
Bayan na gaishe da shi ya amsa na ciro takardar da ke 蓷auke da lambar wayar Dr. Basheer na bashi na ce dan Allah ya kirasa ya ce masa Beenafah ce 蓷iyar Patient 蓷insa Mulaifa Zayd Hudaif.
Yana gama fa蓷a masa haka ya yanke wayar ko minti 蓷aya ba'a 茩ara cikakke ba sai gashi ya kira.
Cike da ladabi na gaishe da shi sannan na ce.
"Daman naga mun shigo Sati uku cikin na hu蓷u, shine na ce bari na tuna maka kada kuma a zo a samu matsala."
Daga can 蓳angaren ya ce.
"Haka ne gaskiya, to amma ai date 蓷inda za ku dawo yana nan rubuce a jikin takardar da na baki kamar yanda a ka saba. Na san tabbas satin da zamu shiga ne amma ban ri茩e date 蓷in ba, sai ki duba ki gani."
Gya蓷a kaina na yi na ce.
"OK to, In Sha Allah!"
"Sannan magana ta gaba kuma a ina ne za'a tura muku da ku蓷in?"
"Ina ga ka manta ne Likita, amma Numbern Account 蓷in tana nan jikin form 蓷inda aka bamu muka cike domin shara蓷inma shine, dole account 蓷in sai yana da ala茩a da Ammie to kuma na ta 蓷inne wanda Daddy ya bu蓷e mata na saka."
"Ok to. In Sha Allah, zan sanar da su cewa lokaci ya yi, zuwa gobe ko jibi za'a tura da su."
茒an rusunawa na yi ka蓷an tamkar ina a gabansa na ce.
"Mun gode sosai Likita, Allah ya saka maka da mafificin alheri ya biya maka dukkan bu茩atunka."
Ina gama wayar na mi茩awa Baba mai Shago na ce.
"Na gode sosai Allah ya saka da alheri Baba. Don Allah kada ka gaji dani, ga ATM card 蓷inmu ka ri茩e ta a wajenka, ina so ka taimaka ka bamu Shinkafa da Wake da Mai da Magi, wallahi yau kwana na biyu kenan bamu 蓷ora tukunyar abinci ba, dan Allah ka taimaka mana."
"Kayan kamar na nawa za'a bayar?"
茒an Jim! Na yi ina nazari sannan daga 茩arshe na ce.
"Ka kashe mana dubu biyar har da gawayi ma."
"To 蓷an jirani yanzu ina zuwa."
Ina nan a tsaye ya auna komai ya bani daga nan na yi masa godiya sosai na koma gida.
Ina zuwa na 蓷ibi Waken na gyara na zuba a tukunyar da na 蓷ora kafin na fita, daga nan na je na yi sallar Zuhr sannan na dawo na ci gaba da gyara shinkafa ina fa蓷awa Ammie yanda mukayi da Dr. Basheer.
****
Wasa-wasa tun kafin lokacin tafiyarmu ya cika nake zuwa neman Daddy bana samun sa wanda da alama ya yi tafiya ne. Har lokacin kuma ya cika muka shirye muka je Sokoto muka yi kwana 蓷aya muka dawo still bai dawo ba. Munyi kwana 蓷aya ne kacal kasancewar gwaje-gwajen da duk aka yi wa Ammie sun nuna komai lafiya, babu wata matsala mai yawa a wannan karon.
Dubu 蓷ari da hamsin ne ku蓷in tallafin da zamu ri茩a samu duk wata idan lokacin zuwanmu asibiti ya yi, hakan yasa koda muka dawo iyaka dubu sha biyu ne suka rage a hannuna domin tun kafin ma mu tafi na riga na kar蓳i kayan Baba mai shago sun kai na dubu takwas.
Addu'a sosai na shiga yi ina fata da saka ran duk inda Daddy yake Allah yasa ya dawo nan kusa.
Sai da muka cika sati 蓷aya da dawowa cif, a daren ranar misalin 茩arfe biyu da rabi na dare bayan na raka Ammie ban蓷aki mun dawo, kamar an ce na le茩a window kwatsam sai ga motar Daddy na hango an yi parking dai-dai inda yake ajiye ta idan ya dawo da dare.
Cikin wani irin farin ciki na kalli Ammie dake 茩o茩arin tayar da Salla na ce.
"Ammie Daddy ya dawo! Wallahi Daddy ya dawo. Zo.....Zo ma ki hango motar sa da idonki ki gani."
Na 茩arashe maganar tare da janyo hannunta kamar wata zararra ina nuna mata.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana mai bi na da kallo ta ce.
"Allah maji ro茩on bayinsa Beenafah. Ni ina ganin kada ma ki yi masa zancen kowane ku蓷i kawai ki yi masa zancen abinci, ina ga hakan kawai ya wadatar. Wallahi Ba na jin da蓷in yanda mafi yawan lokuta Bahrain yake zuwa makaranta batare da ya sanya komai a cikin sa ba... "
Hannayenta na kama guda biyu ina mai 茩ara kwantar da murya, na ce.
" Ba Bahrain ka蓷ai ba Ammie, har ke kina da bu茩atar wadataccen abin Ci da Sha domin 茩wa茩walwarki ta 茩ara samun nutsuwa da aiki yanda ya kamata..."
Cikin kalamai ma su nuna zallar karaya ta ce.
" Ina ma ace Abbie shima yana nan tare damu. Da yanzu komai na nan yanda yake, da yanzu Sajjad 蓷ina shima yana raye! Da...."
Hannuna na sanya da sauri na toshe mata baki tare da girgiza kaina ina mai fashewa da wani irin kuka, na ce.
"Kash Ammie! Ashe ba kullum ana miki nuni akan yarda da 茩addara ba? Har abada babu danasani a cikin hukuncin Allah Ammie, Babu fa wanda yake da ikon rubutawa kansa 茩addara fa ce abinda Allah ya nufesa da shi. Abbie addu'armu yake bu茩ata akoda yaushe. Sannan a kullum ina so ki ci gaba da sakawa a ranki cewa babu wani laifi da kika aikata, ba ki aikata komai ba. Ki yi ha茩uri Ammie na! Ki 茩ara ha茩uri, Allah yana tare da masu ha茩uri."
Ina gama fa蓷ar haka na rungumeta sosai ina mai 茩ara lafewa a jikinta yayinda zuciyata ta sake jin wani sabon tausayinta na da蓷a huda sassa da 蓳argon jikina.
Cikin tausasa kalamai masu 茩warara gwiwa na yi nasarar sanyata komawa bacci domin bana so abun ya 茩ara ta'azzara kada kuma a samu wata sabuwar 蓳arakarda ban san ranar fita ba.
Sai dai kuma ni tun wannan farkawar da na yi, ban sake runtsawa ba har gari ya waye wanda 茩arfe bakwai na safe ma a 茩ofar Mummy Zaliha ta yi mini.
Ina nan shanye a wurin tamkar wata garar kunya har misalin 茩arfe takwas da rabi sannan sai ga Daddy ya fara fitowa. Idonsa na sauka a kaina ya ce.
"A'a! Beenafah. Ke ce? Yanzu daman nake zancen aje a kira mini ke, kun ji ni shiru kwana biyu ba na nan tafiya na yi."
Wani irin sanyin rahama ne na ji ya ratsa zuciyata wanda har ban san lokacinda na lumshe idanuwana ba tare da cewa Alhamdulillah!.
Mummy Zaliha ce ta fito tare da Humaida da kuma twins 蓷inta wato Aunty Hassana da Hussaina. Dukkan su cikin shirin fita unguwa suke da alama ma ba garin za su tsaya ba ganin yanda drivern su da kuma Biba ke ta famar fito musu da jakunkunansu.
Ina ganin ta fito na shiga gaisheta har su Aunty Hassana wanda a da茩ile suka amsa min gaisuwar ta wa ba tare da ma sun ko kalli inda shirgina yake ba musamman Mummy har suka shige mota gaba 蓷ayansu suka wuce suka barni daga ni sai Daddy sai kuma Biba da ta juya ta koma ciki.
"Ki na jina Beenafah? Daman due ta wasu '拼an abubuwanda suka ta so, kamar transfer da na samu daga wurin aikina da kuma dalilin makarantarsu Husaina. Ha茩i茩a suna shan wahala idan bu茩atar zuwa gida ta kamasu saboda nisanda ke akwai daga Abuja zuwa nan Zamfara. Kin ga sai sun hawo jirgi daga can zuwa Sokoto, sannan daga can Sokoto su 茩ara hawo Mota zuwa nan kinga akwai wahala. To shi ne muka yanke shawara ni da Hajiya Zaliha cewa yakamata mu koma can domin ni in samu sau茩i su ma kuma su Husainar su samu sau茩i. A tai茩ace dai zamu koma Abuja da zama.... "
Zuciyata ce ta buga da 茩arfi har ban san lokacin da na mi茩e tsaye ba ha蓳a na rawa na ce.
"Abuja Daddy! To ni da Ammie da Bahrain fa?"
"Eh daman ku ai za ku ci gaba da zamanku a nan ne...."
Tamkar gilashin da aka rotsawa dutse haka na ji zuciyata ta tarwatse lokaci 蓷aya jin cewa wai mu a nan za mu zauna. Cikin matsanancin firgici na fa蓷a kan 茩afafunshi tamkar wata zararra ina mai fashewa da kuka na ce.
" Dan Allah Daddy ka rufa mana asiri kada ka bar mu a nan na ro茩eka. Daddy wa muke da shi da har za ka barmu a nan? Don Allah kar ka yi haka..."
"To cewa na yi ba zan cigaba da 蓷aukar nauyinku ba ne da har ki ke wannan kukan?"
"Ba zancen 蓷aukar nauyinmu ba Daddy. A duk fa蓷in Gusau kai ne ka蓷ai muka sani, ta dalilin ka muke zaune a nan..."
"Ki bari in mutu tukun Beenafah kafin ki yi 茩o茩arin binneni. Ni kin ji na ce miki kuna da wani bayan ni ne? Daman ina nufin ku zauna a nan kafin na tafi can na yi settling, daga baya idan komai ya daidaitar mini sai in aiko a tafi daku. Tsawon shekara hu蓷u cikin ta biyar nake 蓷auke da nauyinku a kaina; Ciyarwa, shayarwa, sutura, magani, hatta makaranta da na kashe ku蓷ina na saka ki 茩arshe asara nayi saboda daina zuwa da kikayi, na 蓷auki nauyin ciwon mahaifiyarki. Duk da haka ban gaji ba sai da na kwashi ma茩udan ku蓷i na bayar wurin yi wa jaririn da yake cikin zanin goyo aiki wanda sai bayan na gama wahala ya mutu. To yanzu dan Allah Beenafah duk irin wannan wahalar da na yi daku tsawon lokaci mi zai sa na kasa ci gaba da kulawa da ku? Kar fa ki manta har account na bu蓷e muku ina tura muku ku蓷i a ciki. To ko yanzu ba kasawa na yi ba, kuma ba zan fasa yi muku duk wani taimakon da na saba yi muku ba ko don kasancewarku jinin 蓷an uwana. Kawai dai idan na koma can tare da ku a yanzu, wahala 茩ara maye mini za ta yi domin rayuwar Abuja ta banbanta da ta Gusau, saboda haka ku yi zamanku a nan, ga gida nan babu mai tashin ku a ciki. Daga baya sai in aiko a tafi daku idan na shirya, kuma In Sha Allah zan ci gaba da tura muku ku蓷i kamar yanda na saba..."
Tamkar an jefo Ammie daga sama, haka na ganta kwatsam gaban Daddy tana yi mai wani kallon mamaki da al'ajabi na tsawon lokaci sannan daga 茩arshe ta fashe da kuka a hankali kuma ta koma dariya. Tayi kuka tayi dariya lokaci 蓷aya tare da nuna shi da yatsa tana fa蓷in.
"Dr. Bello Wazeer! Alhaji Mudassir Wazeer... Dr. Bello Wazeer... Alhaji Mudassir Wazeer... Bello.. Bello.. Dr.. Bello.."
Girgiza kansa yayi yana mai mayarda kallon sa gareni ya ce.
"Beenafah ki kamata ki mayar da ita ciki please. Sai kun ji Sa茩o in sha Allahu zuwa wata 蓷aya."
Sake matsawa na yi gaban sa bayan na rirri茩e Ammie cike da magiya ina wani irin kuka mai cike da 茩unci na ce.
"Daddy dan Allah dan darajar Allah karka yi mana haka. Daddy ko yanzu da kake tare damu ya muka 茩are ballantana ace ka yi mana nisa? Daddy Bahrain... Bah...."
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍