Free chapter · Read without an account
Their Baby To Protect
by NorthernAngel · His Rose
sai 12 tafara jin cikinta na kukan wani azababben yunwa sai a lokacin ta tuna rabonta da abunci tun breakfast, abunda batayi a rayuwar ta indai ba azumi take ba toh ita ko rashin lpy take sai taci abunci, kuma wani abun mamaki tunda tazo gidan nan babu wanda yabata ko ruwa balle abunci.. tabb! tafaɗa a hankali dan ita wlh tasan indai ta kwanta bata sama cikinta abunci ba toh da kyar in zata kai gobe
miƙewa tayi ta fita daga bedroom ɗinta ta fito palour ɗin, hasina ce a zaune tana kallo, wuce ta Zara tayi ta nufi dining area inda anan take tunanin hanyar kitchen take
hasina tana ganin Zara tawuce ta tashi tabi bayan ta, har cikin kitchen ɗin tana aika mata wani kallo tace “ke” banza Zara tayi da ita saboda ta cikinta take, jikinta har rawa yake saboda yunwa
“ke ba kya ji ne ina magana or are you deaf? mema kikeyi a kitchen ɗinnan? uban wa yabaki izinin shigowa nan ɗin ko angaya miki gidan ubanki ne nan ɗin” hasinah tafaɗa cike da neman masifa
“ba gidan ubana bane kamar yanda kema ba gidan naki uban bane, gwara ni ma da ubana ya mutu ya barmin gida da dukiya bamu je muna laɓe laɓe da kwaɗayi ba gidan wan uwar mu, wan uwar ma ɗan uba saboda zuciya ta mutu, anu ofia kawai” cak hasinah ta tsaya a gurin tana kallon Zara kamar an dasa ta tama kasa motsawa saboda tsaban shock, she never saw that coming, bata masan Zara najin hausa haka ba
tana nan a tsaye Zara ta bangaje ta ta wuce ta nufi kofar fita daga part ɗin gaba ɗaya saboda abuncin nasu ma ya fita ranta kuma batajin ko 1 minute zata iya ƙarawa a part ɗinnan dan wllh zata iya ɗurawa kowa na cikinsa ashar ba ruwanta
tafiya ta farayi cikin compound ɗin a zuciye ta ɗan yi nisa tafara jiyo taku a bayan ta da sauri ana cewa “in kin cika shegiya ki tsaya”
bata tsaya ba kuma bata ma juyawa ba, saboda ita tunda take a rayuwar ta bata taɓa faɗa ba, batama san yanda ake dambe ba, ita dai kawai ta taso batada tsoro ne kuma tanada baki so bata yarda ta tsaya ba dan bata san me hasinar zata mata ba
cikin daren nan haka take tafita cikin compound ɗin ƙaton manor ɗinnan wanda ko halitta ɗaya babu, kowa ya shige, tana jin hasinah na biyota itama da sauri, kusan 7 minutes tana tafiya sai gashi tafara hango part ɗinda tasan na yan mazan gidan ne, ai zuwa lokacin saurin ta tafara haɗashi da gudu itama hasina da taga tana gudu sai ta dafa mata dan bataso ta isa gurinsu Omar bata kama ta ba
ai kuwa Zara na ganin hasina tafara gudu itama ta ƙara gudu ai kuwa abunka da ɗoguwa sai cilla kafar take nan da nan ta karasa part ɗin da sauri ta mirɗa kofar amma kuma sai tajita a rufe, wani erin bubbugawa ta farayi da karfin gaske tana jijjiga kofar kamar zata cire saboda hasina ƙara matsowa take tana gab da samunta
“yaya, yayaaa open the door for me, bikoo” (please)
hasina ce ta ƙaraso gurin daidai an buɗe kofar kafin Zara ta shiga hasina ta riko ta, wani ihu Zara ta kurma sai da gurin ya amsa zuwa lokacin duk mazan sun gama fitowa, Ahmad daya buɗe kofar da sauri ya shiga tsakanin su yana cire hannun hasina daga yar vest ɗin jikin Zara, ai kuwa da gudu Zara tayi cikin palourn tana shiga tafaɗa jikin Omar da tagani a tsaye yana kallon komai, zage zagen hasina ne kawai yake tashi a gurin itama ta shigo cikin palorn tana cewa “ki maimata abunda kika ce karamar yar isaka yar arne”
ran Zara sosai ya ɓaci da sunan da hasina ta kira babanta dashi nan take ta nemi tsoron da taji ta rasa, fitowa tayi daga jikin Omar dayake rungume da ita ta ce
“ai gwara ni arne ya barmin gidan zama, zuciyar sa bata mutu ba ya bar duniya matsiyaci sannan kuma bai barni da laɓewa gidan yan uwan uwa ba”
wani yunƙuri hasina tayi zata kamo Zara ahmad ya rikota yana cewa
“wai whats going on ne, ke hasina daga zuwan yarinya zaki fara bullying ɗinta metayi miki?”
“tambaya na ma kake me tayi mun ya Ahmad kai bakaji maganganun da take gaya mun ba wlh sai kin bar gidannan yau ɗinnan” kafin Ahmad yayi magana sukaji muazzam yayi cikin tsawa yace “enoughhh” duk sukayi shiru ya karaso inda suke ya kalli ko wannen su kafin yace “hasina meya faru?”
“Wai ya muazzam daga naga yarinyar nan tashiga kitchen by this time na tambaye ta me zatayi kawai tafara zagina wai ai ba gidan ubana bane cin arziki muka zo nida uwata wai harda cewa cin arzikin ma a gurin ɗan uba” da sauri muazzam ya kalli Zara yana mamakin a ina duk tasan wannan, shi da badan yaji ma ta faɗi wasu daga cikin maganar yanzu da bakinta ba da sai yace karya hasina take mata
“Rose where did you get that from?” ya tambaya
“yaya karya takeyi, she started it” zara tafaɗa trying to defend herself
“that’s not what i ask you, a ina kikaji maganganun da kika gaya mata nace” yafaɗa cikin tsawa
wani erin baci ran Zara yayi, wato ma wanda ta faɗawa hasinar ne ya musu zafi su basu ji sanda ta kirata da yar arne ba kenan, juyawa kawai tayi ta nufi kofar fita palorn zata fita taje ta ɗauko key ɗin motar ta ta bar musu gidan su
“Get back here, ina miki magana zaki tafi are you stupid?” Muazzam yafaɗa cike da bacin rai da masifa, hasina ta kalli Zara tana wani victorious smile tana tuna maganar da ummi tafaɗa mata na cewa wata kusar tafi wata
tsayawa kawai Zara tayi zuwa lokacin tafara kuka, wani maraici takeji yana taso mata
“Enough muazzam, enough! why are you shouting at her without even hearing her side of the story? come here rose” Omar yafaɗa yana ƙarasowa inda Zaran take ya kamo hannun ta zuwa kan sofa ɗinda ke cikin palour inda sai a lokacin Zafar dake tsaye shima bai ce komi ba ya motsa bin
bayan su Omar da Zara yayi inda suka zauna shi kuma ya tsaya a gabansu yana kallon Zara
“tell me what happen?” Omar ya
tambaye ta cikin lallashi
ransa wani mugun tafasa yake da kalaman da yaji hasinah ta faɗawa kanwar sa amma ya danne so yake yaji bayan wanda yaji dame dame tafaɗawa Zaran kuma
“i got hungry, rabon da naci abunci tun breakfast, da nazo gidan nan ma no one offered me even water shine na tashi da kaina na tafi kitchen ɗinsu…” tiryan tiryan Zara tafaɗi abun da yafaru har zuwa sanda Ahmad ya buɗe kofa ya gansu
miƙewa kawai Omar yayi ya nufi inda hasina take a mugun hasale yafara magana
“this should be the last day you’ll try to lay your hands on my sister, kina hauka ne? kar…..” bai ƙarasa ba Zafar ya katse sa da cewa
“Let me handle this Omar, hasina zo” hasina ta tsaya kallon Omar da mugun mamaki dan bata taɓa tunanin zaiyi mata haka ba,
ahankali ta juya ta kalli Zafar kafin tafara tafiya inda yake da mamaki dan tasan shi sam baya shiga erin abubuwan nan, shi ko magana zata iya ƙirga sau nawa magana tashiga tsakanin su, tana isa gaban sa yace
“tell me what happened” yafaɗa calmly
nan fa ta fara koro ƙarya da gaskiya tana gayamai har ta gama Zafar yace mata
“okay yanzu what I want to know is why did you follow her here? I mean what exactly are you mad about?” ya tambaye ta
“ya Zafar I just told you how she insult my late father fa” hasina tafaɗa rai a ɓace
“and so? ke wace da baza’a zageki ba? or are you the only one that knows how to insult people’s parents? ko kuma akwai ƙarya acikin abunda kikace ta gaya miki ɗin?” Zafar yafaɗa cike da rainin hankali
“in ma akwai ƙaryan ai self defence ne, kin zageta ta rama ko an angaya miki asali kika fita ne?” Omar yafaɗa a zafafe
“bama karyan aciki, ke gidan ku ne nan ɗin?” Ahmad yafaɗa shima cikin rainin wayo
Zafar ne ya matso dab da ita yana cewa
“let me get this straight, listen and listen carefully, she have more power than you’ll ever have in this house, so this should be the last time you will try to bully her coz this is not your toxic father’s house da zaki wani biyota zaki daketa kaman yarki”
“ai naso kin daketa ki sha mamaki na hasina” Omar yafaɗa har lokacin zuciyar sa zafi take masa
“please allow my sister to breath in this house hasina, ita bata saba da faɗa ba, all she know is love all her life, so kar kuzo ku koya mata halin nan naku na faɗa da zagi da gori” muazzam ne yafaɗa dan shima tun ɗazu zuciyar sa ke mai suya kawai dai yaso yayi kara sai kuma yaga bazai iya ba
“ai shine, don’t spoil her aura with your bad energy” Ahmad yafaɗa
“ku barsu, let them do whatever they want, just know that if cross this girl in this house, it is me that you cross” Zafar yafaɗa maganar mai cike da ma’anoni wanda babu wanda ya fahimta sai Zara da take zaune tanajin wani erin sanyi aranta da kuma wani mugun son zafar dake ƙara shigar ta
“sannan i don’t know maganganun da kikaji a gidan nan but her father is a muslim like your father dan haka kika sake danganta ta da kalmar da kika faɗa ɗazu toh dake da wanda yafaɗa miki maganar zaku ga bacin rai i don’t care ko wayeshi kuma komai girmansa” muazzam ne ya faɗa kuma sarai hasina tagane me yake nufi kenan ko ummi ce tafaɗa mata
“the only the diffirence between your father and hers is that her father is not a drunkard” Zafar ne faɗa cike da cin zarafi, so yake itama taji zafin da Zara taji lokacin da tacema babanta arne
kuma yasan hakan da yake shine kawai zai kwatar wa Zara ƴancinta cikin gidansu dan yasan halin kowa
“kamanta ya Zafar there is another difference which is rose’s father is rich” Ahmad yafaɗa cikin son kuntatama hasinah shima harda dariya yake
zuwa lokacin sosai hasinah ke kuka tana kallon yanda garadan maza har huɗu suka zagaye ta suna gasa mata maganganu cike da cin zarafi kamar ba yar uwar su ba akan kawai ta taɓa ‘bare’ acewarta
lallai sai alokacin hasinah tasan gatan Zara ya wuce tunanin ta
ita zaran ma da ake akanta zuwa time ɗin tana kwance kan 3 seater tana kallon su kamar tasamu tv ranta fesss
“Right! now get out before i change my mind and throw you out of this estate gaba ɗaya” Omar yafaɗa ba sani ba sabo kamar ba budurwarshi, danshi gaba ɗaya ta sire masa lokaci ɗaya ko ganin baya son yi
“yea, and tell all the women in this house what i said about crossing this girl, now get lost” Zafar yafaɗa yana mata wani kallo
da gudu hasina ta juya ta fita tana kuka sosai har ta isa part ɗinsu