Free chapter 路 Read without an account
PAGE 7
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 7
"Daddy ina wuni."
Jin ya yi shiru yasa na ce.
"Beenafah ce Daddy.."
Daga can 蓳angaren Daddyn cikin nuna kamar alamun mamaki ya ce.
"Beenafah?"
"Eh Daddy ni ce. Daman Ciwon Ammie ne ya tashi har ta fito titi aka ha蓷a da tsausayi sai mota ta bigeta, to munfi sati uku a asibitin Janbulo kuma jibi zamu wuce Sokoto domin tana cikin halin jinya sosai har karaya ta samu a hannunta na dama...."
"Allah sarki! Allah ya ba ta lafiya."
"Amin. To Daddy daman..."
Da sauri ya tare numfashina da fa蓷in.
"Dan Allah ki dakata mini Beenafah! Kin fi kowa sanin ina wurin aikina yanzu haka, yakamata ki ri茩a sanin lokutan kirana, mts!"
Daga haka ya yanke kiran ba tare da ma ya tsaya ya saurari maganata ba. Bayan na tabbatar ba 茩ara kira zai yi ba yasa na mi茩awa Baba mai shago wayarsa a sa蓳ule ina mai tsiyayar da ruwan hawaye masu cike da 蓷aci da ba茩in cikin daddy na juya na koma gida.
Ina shiga na tarar da Malaman islamiyyarmu su hu蓷u tare da 蓷alibansu rututu suna yi wa Ammie addu'a.
Zaunawa na yi nima tare da su har aka kambala addu'ar, sannan na gaishe da Malaman na kuma yi musu godiya. Wallahi har cikin raina na ji da蓷in ganin su da kuma 茩aunar da suka nuna a garemu. Hakan sai ya mantar dani ba茩in cikin daddy da na dawo da shi daga shagon da naje.
Bayan mun rako su, a bakin gate Ra'is ya kalleni ya ce.
"Beenafah shikenan dai da gaske kin yafe Islamiyyar ko?"
Girgiza kaina na yi ina murmushin 茩arfin hali na ce.
"Ba haka ba ne Ra'is, nima ina son islamiyya amma kuma dole ce tasa na barta, idan ina da rabo watarana zan dawo."
"To Allah ya taimaka, Allah ya bata lafiya. Kuma dan Allah ina ro茩o; Bahrain yana daga cikin yara masu haza茩a da muke alfahari da su, a daina wasa da makarantarsa, idan yazo sati biyu cikakke sai an samu tsawon kwanaki bai zo ba, kinga hakan dole zai yi affecting 蓷insa, domin da zaran an wuce shi an wuce shi ba za'a dawo baya saboda shi ba."
Jinjina kaina na yi a raina ina jin ba da蓷i na ce.
" Haka ne Ra'is, wallahi duk abinda ka fa蓷a gaskiya ne, to amma ko yanzu ina 茩ara baka ha茩uri domin uzuri ne wanda ban san ya zan yi ba,amma In Sha Allahu za'a gyara."
" To Allah ya bada iko. Allah ya bata lafiya mai albarka."
"Amin Ra'is, na gode sosai Allah ya saka da alheri."
Akan hanyarmu ta dawo daga rakiyar su na cewa Bahrain.
"Kai ne ka ce su zo duba Ammie?"
Girgiza kai ya yi yana ri茩e da hannuna ya ce.
"A'a. Ina zuwa Ustaz ya ce mini miyasa na daina zuwa kwana biyu, shine na ce mishi muna asibiti an kwantar da Ammienmu ba lafiya,shikenan ya ce na wuce na zauna, to ana tashi sai ya kirani ya ce mini za su taho tare dani duba Ammie."
"Allah sarki! Allah ya saka musu da alheri."
"Amin aunty Beena. Ustaz ya ce addu'a waraka ce, indai aka dogara ga Allah akayi ta addu'a ciwo kowane iri ne za'a warke..."
"Wannan haka yake Bahrain, Ustaz gaskiya ya fa蓷a, muna kan addu'ar akodayaushe, Allah yasa mu dace amin."
Ha茩i茩a koda na taso ni 蓷in na kasance mai 茩wazo sosai ta kowanne fanni, da hakan na kafe manyan burika guda biyu a cikin raina wanda both Ammie da Abbie suke kan wannan burin su ma. Sai dai kana naka Allah yana na shi iko,ta dalilin rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki dare 蓷aya,yasa dole na ha茩ura da nawa mafarkin domin ba zan bar mahaifiyata ita ka蓷ai ba na fita makaranta, amma kuma na 蓷auki al茩awarin bai wa Bahrain cikakkiyar kulawa da goyon baya akan islamiyya da bokonsa, mafarkina da ban samu damar cikawa ba sai ya cika mini shi inda rai da rabo. 茒an wanda na samu Allah yasa masa albarka ya hore mana hanyar kulawa da na Bahrain.
***
Washe gari Ina zaune a bakin famfo misalin 茩arfe goma sha 蓷aya na safe ina wanki na ji ana ta bubbuga 茩ofar gate 蓷inmu. Cikin mamaki na je ina tambayar waye ne.
"Ashiru ne..."
Kafin ma ya iyarda rufe bakin sa cikin farin ciki na je na bu蓷e. Turus na yi ina kallon taron bataliyar da yake tare da su.
Murmushi ya yi ya ce.
Shima dai murmushi ya sakar mini tare da kallon su ya ce.
"Iyayena ne da 茩annaina Beenafah. Cewa suka yi suna so su zo su ga Ammie da jiki."
Cikin nuna zallar farin ciki na ce.
"Allah sarki! Sannunku da zuwa....Ku shigo ciki dan Allah."
Tare muka shiga har ciki inda Ammie ke kwance akan katifa saman varendar, ga waya a gefe sautin karatun al茩ur'ani yana ta tashi mai taushi da sanya nutsuwa.
Daman a nan na fito da ita kusa da ni domin na ri茩a hango ta da kyau kada na barta a 蓷aki ita ka蓷ai. Tunda muka dawo daga asibiti bacci ya 茩aurace mini domin dole nayi kaffa-kaffa kada ta yi 茩o茩arin fama ciwon hannun ta da akayi 蓷ori. Cikin ikon Allah kuma, tunda muka dawo daga asibitin, lafiya 茩alau take babu alamun motsawar yanayin ta har yanzu, ko don sanadiyyar zafin ciwon da take ciki ne oho! Koda yake kuma babu abin da ya gagari Ubangiji, Allah na gode maka, Allah ka 茩ara bata lafiya da nutsuwar ruhi amin.
Tabarma na shiga na 蓷auko musu na baza ta a gaban su na ce su zauna. A hankali na taimakawa Ammie ta tashi ta zauna sannan na gaishe da su, bayan mun gaisa na kalli Ammie na ce.
"Ammie wa蓷annan iyayen Yaya Ashiru ne da 茩annensa suka zo duba ki."
"Allah sarki! Sannun ku da zuwa.."
A tare duk suka amsa suka gaggaisa sannan 蓷ayar dattijuwar dake gefen Yaya Ashiru wacce da alama ita ce mahaifiyarsa domin sun yi kama sosai ta ce.
"Sannu Hajiya! Ya jiki? Ashe kuma wasu 茩addarori ke ta faruwa?"
"Wallahi kuwa. Jiki mun gode Allah."
"Ubangiji Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne."
"Amin. Na gode Allah ya saka da alheri."
茒ayar ce ta kar蓳a da cewa.
"Ai Ashiru yayi mana bayanin duk abin da ya faru, abin takaici abin ba茩in ciki mutumin da ya ka蓷eta ko dai ya fito a mota yace Allah ya sawa茩a bai yi ba. A lokacin da ya ka蓷eta dama tafiyarsa ya yi da abin ba zai dame mutane ba da ace wai sai da ya tsaya ya ga an sakata a Napep tsabar iskanci sannan ya juya ya wuce,wannan wane irin rashin imani ne?"
Take na ji takaicin mutumin nan ya dawomin sabo a raina, wanda bayan su Daddy da wasu tsirarrun mutane; shine mutum na gaba da tsana a rayuwata.
"To ya za'a yi! Tunani da hankalin mutane ya banbanta, kowa da irin yanda Allah ya halicce sa. Abu mafi muhimmanci shine tana raye bata mutu ba, Fatanmu shine Allah ya bata lafiya."
Cewar Yaya Ashiru yana mai 茩ureni da kallo ganin yanda lokaci 蓷aya yanayina ya canza.
Ni kuma jin wannan furucin yasa na 蓷an saki raina na kalli yaran da ke wurin wanda ciki har da sa'annina da ma wa蓷anda suka girme mini na ce.
" Yanzu Yaya Ashiru wa蓷annan duk gidanku 蓷aya da su?"
Dariya suka yi dukkan su sannan daga baya ya gya蓷a kan shi ya ce.
"茦annina ne! kin gansu su tara cif,akwai biyu da sukayi aure, bayan su kuma akwai Maza uku mata biyu wa蓷anda su ne yayyuna. Wa su kinga Mamansu nan, wa su kuma kinga ta su Maman nan. Kuma ita wannan...Umma muke ce mata." Cewa da maman su, sai kuma ya nuna 蓷ayar ya ce. " Ita kuma wannan, Ayya muke kiranta."
Murmushi na yi ina jinjina kaina na ce.
"Masha Allah. Ban ta蓳a ganin irin wannan familyn ba."
Cike da mamaki 蓷aya daga cikin 茩annen nasa ta ce.
"Ba ki ta蓳a gani ba?"
Bakin gaskiyata na gya蓷a mata kaina na ce.
"Da gaske nake miki. Duk familyn da nake gani,Mama da Baba, mostly yara uku, yara biyu, highest yara biyar haka..."
"To amma..."
Da sauri Yaya Ashiru ya katseta da fa蓷in.
"Fa'iza ya isa haka, ku tashi mu tafi na mayar daku na koma wurin aikina."
"Ni kuma tambayata 蓷aya ce, dan Allah duk wannan gashin da nake gani naki ne?"
Cewar wata 茩aramar yarinya wacce iyakarta may be sa'ar Bahrain.
Dariya muka sake fashewa da ita dukkanmu sannan na saka hannu ina 茩ara janyo zaren gashin kan nawa na gya蓷a mata kaina na ce.
"Eh, gashina ne mana. Kema ai kina da shi..."
Lokaci 蓷aya Yaya Ashiru ya mi茩e yana fa蓷in.
"Ji wata tambayar shirme dan Allah? Ku tashi mu tafi please."
Jinjina kai Ayya tayi ta ce.
"Haka ne kam, ku tashi mu tafi. Allah ya 茩ara bi da lafiya."
"Amin Yah Allah mun gode sosai, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Allah ya mayar daku gida lafiya."
"Amin yah Allah Hajiya."
Daga haka suka mi茩e suna ta yiwa Ammie addu'a na rako su har bakin gate.
Kallona Yaya Ashiru ya yi bayan sun wuce bakin Napep 蓷in ya ce.
"Yaushe za ku tafi asibitin? Kin san fa an ce ku gaggauta tafiya."
Jinjina kaina na yi na ce.
"Haka ne, in sha Allah zuwa jibi zamu tafi kamar yanda suka ce."
"To Allah ya kai mu, In Sha Allahu zan zo zuwa 茩arfe shida na asuba na kai ku tashar."
"Na gode sosai Yaya Ashiru Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."
"Ba komai Beenafah, Allah ya bata lafiya."
Bayan na dawo daga rakiyar su na zauna inda nake na ci gaba da Wankina ina 茩ara girmama kirkin Yaya Ashiru da familynshi. Daman ashe akwai family irin haka mai yawa da suke rayuwa so simple. Ga shi dai ha蓷uwa 蓷aya tasa tamkar mun yi shekara da sanin juna.
***
Daren da ana gobe zamu tafi Sokoto Sai misalin 茩arfe tara na fita na je wurin Baba mai shago na ce ya kira mini Daddy sanin cewa wannan lokacin shi ne lokacin da na saba samunsa a gida,sai dai kiran duniya an yi amma ya茩i ya 蓷auka kuma bai kira ba har kusan tara da arba'in na dare.
Tsintar muryar Baba mai Shago na yi yana fa蓷in.
"Beenafah ya 茩i ya 蓷aga wayar nan fa. Ya kamata ki koma gida hakanan,ki fa蓷amin koda ya kira daga baya mi zan fa蓷a masa?"
Jiki sanyaye na ce.
"Kawai ka ce mishi Beenafah ce ta so ta yi magana da shi kuma ta koma gida."
Daga haka na juya jiki a mace na fara tafiya, ina kan hanya ina tafe ina lissafi, abubuwa duk sun isheni, lissafin ku蓷i na shiga kamar wata zararra, gaba 蓷aya ku蓷inda ke account 蓷inmu sun tafi, har so na yi na ce ayi mini checking balance amma tsoro hanani. Ga term ya yi na biyan ku蓷i both islamiyya da boko dole zan yiwa Bahrain registration kamar yanda nayi last term, ko yanzu idan har Daddy bai tallafa mana ba, ku蓷in nan sai mun wayi gari ba ko sisi, dole mu tattala su mu shiga yin sana'a da su kamar yan da Aunty Husaina ta shawarceni....
Ina cikin tunane-tunane ban ankara ba kawai na ji habshin Kare da gudu ya biyo ni, ba shiri na shiga falfalawa ina mai fashewa da kuka domin na tsani kare a rayuwata, ina tsoronsa sosai ko ganin sa idan nayi hankalina ta shi yake. Ina hango wa su mutane bakin wani gate da alama masu gadi ne, suna zaune a benci na nufe su ba shiri, wurin na tsallaka lambatu zuruf na fa蓷a ciki gwiwata ta bugu haka 蓷an yatsan 茩afata.
Take 蓷aya daga cikin su ya 蓷aga sandarsa ya kori Karen sannan suka yo kaina a tare mai sandar ya mi茩a mini hannu na fito ina ta kuka suna ta faman yi mini sannu.
"Ke ko yarinya ina za ki je da daren nan?"
Cikin sheshsheka na ce.
"Gi...gig..gida zan tafi."
"To ina ne gidan na ku?"
"Wan can titin na baya."
"To muje."
Ba musu na shiga gaba shi kuma ya bi ni a baya bai tsaya ba sai da muka kai 茩ofar gida ya ga na shiga sannan ya koma.
Tsayawa na yi na yaga gefen 蓷ankwalina na 蓷aure babban yatsan 茩afata da ya kwaile yana zubar jini, sannan na duba gwiwata ta dama wadda naga itama ta goge sosai.
Bakin famfo na je na wanke fuskata na goge da hijabina sannan na shiga gidan, ina gudun kada Ammie ko Bahrain wani ya ga yanayina kuma ban so hankalin su ya tashi.
Gaba 蓷aya daren ranar ban yi wani baccin kirki ba kasancewar raunukana da suka kwana suna mini azabar zogi da ra蓷a蓷i, sai da na lala蓳o Rub na shafa nasha maganin ciwon jiki sannan na 蓷an samu sau茩i.
***
Katamfe Extension,
FCT Abuja,
Nigeria.
Daddy yana zaune a cikin sabon gidansa da ya saya ya sake renovating kira ya shigo wayarsa, kamar ya san cewa Beenafah za ta sake kiransa da wannan numbern sai ya yi saving 蓷inta. Yana ganin sunan da ya yi saving da ita ya buga tsaki ya mayar ya ajiye.
"Alhaji, Hafiz ya ce mini ya yi ta kiran ka amma ba ka 蓷aga ba, lafiya kuwa?"
Cewar Mummy dake shigowa 蓷akin yanzu 蓷auke da trayn slize fruit a hannunta. A hankali ta ajiye saman glass center table 蓷inda yake gabansa sannan ta samu wuri cike da 茩asaita ta zauna a kusa da shi.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.
"Wallahi ban lura ba, da yake Beenafah ce ta tasani a gaba da kira shine na ajiye wayar, to ina ga lokaci 蓷aya kiran ya shigo da na ta."
Wani irin 蓳ata rai ta yi ta ce.
"Ita kuma da kullum kwanan duniya ba ta gajiya da 蓷orawa mutum lalura, kamar gare su babu ta yanke cibi. Shegiyar yarinya kawai. Mts!"
"To yanzu dai ai an kai 茩arshe, bata ganni ba, waya kuma sai idan na ga damar yin picking zanyi. Miye Hafiz 蓷in ya ce?"
"A'a, cewa ya yi yanata jiranka baka aika masa da ku蓷in ba tun jiya."
"Kash! Wallahi kinga kuwa na manta ne, amma gobe In Sha Allah zan tura masa."
"Allah ya kaimu."
Suna nan a zaune suna fira sai ga su Husaina sunyi sallama sun shigo,bayan sun gaishe da su suka samu wuri suka zauna.
Kallon su Daddy ya yi ya ce.
"Ya na ganku duk kunyi wani iri? Any problem?... Uhm! Hassana, miye matsalar?"
茒an yatsina fuska Hassana ta yi cike da mulki ta ce.
"Ni Daddy problem 蓷ina 蓷aya ne, ni dai bana son driver yana kai mu school, na fi so a bamu mota mu ri茩a zuwa da kanmu, wallahi most of our friends duk da Mota suke zuwa da kansu..."
"Drivern yana da matsala ne?"
"Eh Daddy, baya zuwa da wuri, ko yau har kusan magrib muna hanya, ga shi wani irin ba茩auye da shi Daddy, ni wallahi yana kofsa mana..."
Mummy itama dai ta蓳e bakin ta yi ta ce.
"To Allah na tuba daman wanda ya girma a 茩auye bai ta蓳a zuwa gari irin Abuja ba ai dole ya yi 茩auyanci wallahi. Ni fa, ko Biba don dai ta iya aiki ne kuma Humaida na sonta kawai yasa na ke zaune da ita, amma da ba don haka ba wallahi banga dalilin da zai hana na koreta ba. Saboda haka, Alhaji kawai ka yi musu yanda suke so su ma su shiga cikin tsara su kece rai ni kamar ko yaushe."
" To shikenan, gobe idan Allah ya kaimu zan ce ya dam茩a mu ku key a hannun ku... "
Cikin shagwa蓳ewa Hassanar ta ce.
" Haba Daddy dan Allah! Nile University fa! ... Ni gaskiya wannan motar ta yi mana local da yawa sai dai a saya mana sabuwa er yayi.."
"To kar ki damu in sha Allahu gobe-goben nan za'a kawo muku sabuwa...."
Daga haka ya mayarda kallon shi gun Husaina wacce tayi tu茩un-tu茩un da rai tun 蓷a zu ya ce.
"Husainata ya dai? Ko ke wannan tsarin bai miki ba?"
Girgiza kanta ta yi cikin yanayin ta na ko in kula ta ce.
"Ba komai Daddy, ni duk wannan baya gabana, fatana shine Allah ya bamu sa'a. Duk yan da akayi dai-dai ne."
Tsaki Mummy ta ja tare da girgiza kai ta ce.
"Shashasha kawai, marar wayau."
Daga haka suka koma firar su hankali kwance suna nisha蓷i.
***
茦arfe shida na safe a 茩ofar gidanmu ta yi wa Yaya Ashiru kamar yanda ya yi al茩awari.
Hankali a tashe ya kalleni ganin yanda nake 蓷ingishi ya ce.
"Beenafah lafiya? Miye ya sameki a 茩afar?"
Murmushi na yi na ce.
"Wallahi tsautsayi ne, jiya da dare ina tafiya ban lura ba na fa蓷a lambatu."
"Dan Allah ki ri茩a kulawa kinji ko? Allah ya 茩ara tsarewa."
"Amin, na gode."
Bayan mun isa Tashar, da kan shi ya shiga layi ya amso mana ticket 蓷in motar da zamu hau.
Bayan ya bani a hannuna ya kalle ni ya ce.
"To amma Beenafah miyasa za ku tafi da Bahrain? Karatun sa fa yana samun cikas sanadin wannan uzururrukan? Sannan yanzu ba'a san odar dawowar ku ba"
"Hmm! To Yaya Ashiru ya zan yi? Dole na tafi da shi domin bani da inda zan bar shi..."
Kai tsaye ya ce.
"Wannan karon ki bar shi a hannuna mana, sai na kai shi gida wurin su Umma.."
Da sauri na girgiza kaina na ce.
"A'a. Gaskiya ba zan iya ba..."
Cikin nuna zallar mamaki ya ce.
"Beenafah ba ki yarda dani ba ne?"
茒an guntun murmushi na saki sannan na girgiza kaina na ce.
"Ba haka bane Yaya Ashiru.."
"To idan ba haka bane miye ne? Ki bani shi, na yi miki al茩awarin kai shi islamiyya kullum tare da boko. Na kai shi na dawo da shi har ku dawo. Dan Allah ki yarda dani."
"Ka yi ha茩uri Yaya Ashiru, amma ba zan iya barin Bahrain ako'ina ba."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"Shikenan. Allah ya tsare ya kai ku lafiya yasa kuma a dace."
"Amin. Na gode sosai."
"Ina wayar hannunki?"
Cirowa na yi na mi茩a mishi. Nan naga ya bu蓷e wayarsa ya ciro simcard ya saka ya kunna sannan ya mi茩o mini ya ce.
"茒ayan MTN 蓷ina ne na saka muku, zan kira ki In Sha Allahu."
"Na gode sosai Yaya Ashiru, na gode."
Kallon Bahrain ya yi ya ce.
"Bahrain! Allah ya tsare ka ji ko? Allah ya bai wa Ammie Lafiya."
"Amin Yaya Ashiru, sai na dawo."
Har ya juya zai tafi, a hankali na kira sunan sa ya juyo idanuwana cike da ruwan hawaye na ce.
"Na gode Yaya Ashiru.."
Da murmushi a fuskar sa ya kalle ni ya ce.
"Ke! Miye kuma abun kuka a nan? Ki tabbata kin ajiye wayar a kusa dake zan kiraki."
"To Yayana na gode, ina gaida Umma da Ayya, da Fa'iza..."
Dariya ya fara mini yana gya蓷a kai, jin nayi shiru ya sanya shi cewa.
"En hen! Da Fa'iza... Da wa kuma?"
Dariyar nima nayi na ce.
"Da wacce ta tambayeni cewa gashina ne.. Da ma sauran da ban sani ba."
"To duk za su ji In Sha Allahu. Bye-bye, Allah ya tsare."
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍