Free chapter 路 Read without an account
PAGE 8
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 8
Muna isa suka tarbemu kamar yan da aka saba suka kai ta Female Psychiatric In-patient Ward. Nan take suka fara assessing nata wanda Dr. Kenna ne da sauran nurses suka du茩ufa akanta tare da likitocin orthopaedic na Psychiatric hospital 蓷in.
Bayan sun gama bata duk wani taimakonda ya kamata, Dr. Kenna ya kirani zuwa Office 蓷insa wanda ya kasance cikin manyan likitocin da suke kulawa da ciwon Ammie.
Tare da Bahrain muka shiga Office 蓷in muka zauna.
Bayan ya gama duk rubuce-rubucen da zai yi ya rufe ya kalleni ya kira sunana a hankali da cewa.
"Beenafah!"
茒agowa na yi na kallesa na ce.
"Na'am Likita."
"A yanzu mun duba mahaifiyarki, kuma Thank God her condition was stable now and it's improving. Magana ta gaskiya mahaifiyarki tana bu茩atar cikakkiyar kulawa ta 茩wa茩walwa tare da ci gaba da kula da karayar da take hannunta dama kuma sauran abubuwan da duk suka danganceta da ku gaba 蓷aya. Because of this reasons, dole za ta zauna a nan a茩alla tsawon wata biyu zuwa uku. Idan ta ci gaba da yin responding da kyau ta hanyar magunguna da Psychological support, za mu iya ba ku sallama da shawarwarin yan da za'a ci gaba da kulawa da ita kamar yan da aka saba idan kuka koma gida..."
Nan dai ya 蓷auki tsawon lokaci yana mini bayani da 茩arin shawarwari da kuma hanyoyin da zamu bi wurin ganin ciwon nata ya warke baki 蓷aya.
Cikin ladabi bayan ya sauke maganarsa na gya蓷a kaina, zuciyata cike da fargaba na ce.
"Mun gode sosai Dr. Kenna, In Sha Allah zamu yi iya 茩o茩arinmu."
"Yauwa... Yanzu ga wannan."
Ya 茩arashe maganar yana mi茩o mini takarda, bayan na kar蓳a ya ce.
"Yanzu za ki je ki biya wannan ku蓷in, mun riga mun yi amfani da duk abinda muke bu茩ata a yanzu."
"Ok to. Na gode."
Tare da Bahrain muka fito ina ri茩e da hannun sa wanda muna tafe ina duba takarda wacce ke 蓷auke da abubuwan da ya ce sun yi amfani da suka kama dubu tamanin da bakwai da 蓷ari hu蓷u.
Haka muka ci gaba da zirga-zirga har dare sannan muka je inda aka tanadarwa patient relatives, domin idan suna 蓷akin jinya akan magani to ba'a barin kowa tare da su sai malaman jinya kawai. Shimfi蓷a muka yi muka kwanta misalin sha biyu saura na dare bayan munyi addu'a.
Jim ka蓷an da kwanciyata na ji abu na zuuu! A 茩ar茩ashin jakar kayanmu da na dun茩ule na 蓷ora kaina na yi matashi da ita. Tashi na yi na bu蓷e jakar na tarar ashe waya ce ke ringing wacce shaf! Na manta da ita.
Koda na 蓷auko kiran ya riga ya yanke. Ina dubawa naga 32 miss calls wanda na tabbatar ba kowa bane illa Yaya Ashiru kuma wallahi bakin gaskiyata na manta da ya saka wani simcard a wayar. Ina kan mayar da wayar a jaka na sake jin wani ringing 蓷in yana tashi.
茒auka na yi na kara a kunnena tare da yin sallama na ce.
"Yaya Ashiru...."
"Haba Beenafah dan Allah! Duk kin 蓷aga mini hankalina, tun kuna hanya nake kira ba'a 蓷aga ba sai yanzu."
"Allah sarki Yaya Ashiru! Ka yi ha茩uri dan Allah, ni wallahi na manta ma da wani zancen waya."
"Ok. Da fatan kun isa lafiya?"
"Lafiya 茩alau muka iso Yaya Ashiru, har an bata gado an duba ta. Kuma Alhamdulillah Likita ya tabbatar mini ana samun sau茩i sosai."
"To masha Allahu, na ji da蓷in wannan labarin, Allah ya bata lafiya."
"Amin yah Allah."
"Ina Bahrain?"
茒an le茩a fuskar sa na yi ka蓷an sannan na jinjina kaina na ce.
"Gashi nan a gefena ya yi bacci."
"To Ki kula kin ji ko?"
"In sha Allahu Yaya Ashiru na gode sosai da kulawa."
***
Satinmu biyu a asibitin aka cire mata POP 蓷in hannunta da aka yo mata aikinsa tun daga Gusau, bayan sun tabbatar 茩ashin ya soma ha蓷uwa aka sake yi mata physiotherapy domin kada hannun ya samu matsala,kuma Alhamdulillah komai yana kan tafiya dai-dai, sau茩i sai 茩ara samuwa yake.
Bayan munje mun biya ku蓷i muka samu wani wuri a farfajiyar asibitin muka zauna munata kallon yadda mutane ke ta zirga-zirga. Idan an wuce da wannan kalar marar lafiyar Jim ka蓷an za ka ga an wuce da wani wanda matsalar shi ta fi na 蓷a zu.
Tun da muka zauna nake hankalce da yanayin Bahrain, sosai ya shige gashi, cike da nutsuwa yake kallon kowane patient da aka wuce da shi. Jinjina kaina na yi na ce.
"Bahrain ka gani ko? Hakan ya 茩ara tabbatar mana da cewa ba mu ka蓷ai ke fama da irin wannan jarabawar ba. Sai mu godewa Allah domin ko a cikinsu yanayin Ammie yana da sassauci sosai. Kuma In Sha Allahu duk ranar da Allah ya ce ta warke gaba 蓷aya za ta warke da ita da ma sauran ma su jinyar baki 蓷aya. Addu'armu Allah ya 茩ara ba su lafiya baki 蓷aya ya yaye musu wahala...."
"Aunty Beenafah da gaske Ammie kenan za ta warke kaman yan da Dr. Basheer ya ce mana jiya ko?"
Murmushi na yi mai sauti ina jinjina kaina na ce.
"Sosai kuwa Bahrain, In Sha Allahu.."
"To Aunty Beena daga zaran ta warke da gaske muma za mu koma Abuja inda su Humaida?"
Tamkar ya kwa蓷a mini guduma a tsakiyar kaina haka na ji saukar kalamansa lokaci 蓷aya. Kwata-kwata ban yi tsammanin wannan tambayar ta sa ba a wannan lokacin.
"Aunty Beena..."
"In Sha Allah Bahrain, kada ka damu watarana muma zamu je har ma gaba da Abuja..."
Cikin zumu蓷i ya ce.
"Da gaske Aunty Beena? Ina kenan?"
Hannunshi na jim茩e a na wa ina mai 蓳oye hawayena tare da 茩ir茩iro wani murmushi na ce.
"Ni ma ban sani ba Bahrain, amma In Sha Allah idan har ka yi 茩wazo sosai a makaranta to watarana tabbas wannan mafarkin naka zai cika...."
Shekarar Bahrain goma a duniya amma wallahi idan ya yi mini wata tambayar rasa nake yanda ma zan yi na amsa masa tambayar. Haka muka zauna yana ta mini tambayoyi wanda ban yi nasarar tserewa daga gare su ba sai da kiran Yaya Ashiru ya shigo wayar hannuna wanda shima mun jima muna magana da shi sannan daga 茩arshe na yanke wayar bayan mun gama.
Yaya Ashiru mutumin kirki ne wanda ban ta蓳a ha蓷uwa da irin sa ba a duniya kuma har na mutu ba zan sake ha蓷uwa da mai kirkin sa ba. A yanzu yana daga cikin manyan ginshi茩an da suke taka muhimmiyar rawa wurin ci gaban farin cikinmu. Duk da cewar baya tare damu, muryar sa kawai da hikimar iya zancen sa a waya tana wadatarmu. Wata irin sha茩uwa ce ta shiga tsakaninmu wanda a kullum sai mufi hour muna magana a waya, bama kamar idan dare yayi, sai mukai kusan sha biyu muna fira har sai idan ya ji alamun bacci ya fara kamani sannan zai yi mini sallama ya kashe wayar.
***
Misalin 茩arfe biyar na yammar ranar juma'a Mummy ta fito cikin kyakkyawan ado ita da Humaida da alama fita za su yi.
Wuri ta samu ta zauna domin jiran Daddy wanda shi ma yana ciki yana shiryawa yayinda Humaida ta fice zuwa 茩asa.
Sallama Biba ta yi a hankali ta shigo parlourn. Wata uwar harara Mummy ta shiga jefa mata har ta 茩araso ta dur茩usa a gaban ta.
"Lafiya?"
Murya a 茩asa sosai ta mi茩a mata wayar da ke hannunta ta ce.
"Daman Humaida ce ta ce na kawo miki wayar ki Aunty Aysha ta kira..."
Da 茩arfi ta warce wayar tana fa蓷in.
"Don kin kawo mini waya dole sai kin wani zo kin dur茩usa a gabana? Shegiyar munafuka!..."
"Yi ha茩uri Mummy..."
"Dan Allah tashi ki bani wuri.....ke tsaya dai!"
"Ko kin 蓷aga kiran Ayshar ne kin yi munafurcin da ki ka saba?"
Da sauri ta girgiza kanta ta ce.
"Wallahi na rantse da Allah Mummy ban 蓷aga ba. Ai tun da ki ka yi fa蓷a na daina 蓷agawa."
"Ta shi ki bani wuri."
Tun da Aysha ta fara kiran wayar Mummyn bata daina ba har yanzu. Sai da ta ga dama sannan daga 茩arshe ta 蓷aga wayar sama-sama ta ce.
"Ya akayi?"
Cikin murya mai sar茩e da kuka daga 蓳angaren Ayshar ta ce.
"Mummy Barka da wuni!"
"Barka.."
Shiru ne ya ratsa tsakanin su na tsawon lokaci wanda babu abin da ke tashi daga cikin wayar sai sautin muryar kukan Aysha tamkar za ta 蓷auke numfashi tsabar damuwa da tsananin ru蓷anin da take ciki.
"Wai lafiya kike nema ki kashe mini dodon kunne?"
"Mum.. Mu.. Mummy!"
"Mts! Fita zan yi fa, kina 蓳ata mini lokaci."
Cikin wani irin ra蓷a蓷i ta ce.
"Ina kewarki Mummy, ina kewar Twins da Humaida."
"Na ji..."
"Mummy Baffa ma yana gaida ku."
Ta蓳e baki ta yi tace.
"Na ji sai an jima... Ni wallahi dama daina kirana kikayi da ya fiye mini alheri Aysha mts! Na tsani na ci wallahi. Shi dai mutum gashinan bashi da zuciya. Da wata ce ke tsawon lokacin nan yakamata ace kin ma manta da ni...."
"Mu...mmy! Kin ta蓳a ganin '拼ar da ta yi zuciya da mahaifiyarta?..."
"Nawa akayi?"
Da 茩arfi ta runtse idanuwanta tana girgiza kai tamkar tana a gabanta ta ce.
"Ni kam ba zan iya ba...Ba zan iya ba Mummy!"
Katse wayar ta yi ganin Daddy ya fito ta 蓷auki Jakarta Hankalinta kwance suka fi ce zuwa shan Ice-cream 蓷in su da suka shirya.
***
Sai da muka sake share sati tara a asibitin wanda yanzu Alhamdulillah, Ammie ta samu sau茩i sosai fiye da baya tare da taimakon Dr. Basheer da sauran ma'aikatan da ke wurin har muka kai ga samun takardar sallamarmu, domin a yanzu, hannunta ya warke tare da duk wasu raunukan da suka sameta. 茦wa茩walwarta komai ya yi fiye da za to wannan karon wanda har Dr. Basheer ya bamu tabacci cewa idan har ta ci gaba a haka in sha Allahu komai zai koma dai-dai tamkar ba'a yi ba. Sai dai kuma, an sake shimfi蓷a mana sabbin dokoki fiye da na baya ma akan yanda zamu ci gaba da kulawa da ita da kuma kula da shan maganinta yanda ya kamata. Sannan follow-up 蓷inmu zai dawo every four weeks a nan FMC gusau kamar yanda na nemi alfarma idan zai yi yu,kuma sai gashi sun amince mana domin sau茩a茩awa garemu tun da yanzu babu wani matallafi.
A wannan karon gidan sa ya kaimu har da Ammie bayan an bamu sallamar yace muyi wanki mu shirya kayanmu da kyau sannan mu koma gida.
A lokacin da zamu baro asibitin har kuka na yi domin ta riga ta kasance tamkar gida a gareni mai bani farin da yaye mini damuwata fiye da gidanmu dake Gusau. Sai dai kuma, a wannan karon in sha Allahu zan 茩ara jajircewa da taka-tsan-tsan da duk wani abu da zai zamto barazana ko shamaki ga lafiyar Ammiena. Daddy ma, na jima da yanke hukuncin daina neman sa har abada duk wuya duk da蓷i.
Da dare bayan matar Dr. Basheer ta shigo. Mai kirki da ita, ta saka aka kawo mana abinci mai rai da lafiya sannan ta ce mu ba su wuri zata yi magana da Ammie. Bayan mun fita suka zauna tsawon lokaci suna tattaunawa sannan daga 茩arshe ta yi mata sai da safe ta wuce.
Kallon Ammie na yi wacce ke zaune akan sallaya tana lazimi na ce.
"Ammie.. Mata mai kirki ko?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Ai ba matar ba Beenafah, har mijin na ta mutumin kirki ne. Ki duba yanda ya yi ta fa蓷i tashi akanmu tamkar wa su danginsa. Kai! Ai wallahi ba zan daina saka wannan mutumin a addu'a ba Beenafah, domin ya cika 蓷an kirki..."
Cike da murmushi na ce.
"Ammie kamar Yaya Ashiru ko?"
Gya蓷a kanta tayi ta ce.
"Sosai kuwa."
"Idan muka koma zamu iya tafiya gidan su Ammie?"
"sosai. In Sha Allahu babu abin da zai hanamu zuwa gidan su Ashiru domin ya yi mana halacci..."
Kallon Bahrain na yi wanda ya du茩ufa sosai akan waya yana ta dannarta ba ji ba gani na ce.
"Wai kai miye kake yi da wayar nan tun 蓷a zu? Please ka ajiye ka zo muci abinci..."
Sai yanzu ya taso da wayar a hannun sa ya na wani simi-simi tamkar an tsoma Kaza a ruwan zafi ya mi茩o mini yana fa蓷in.
"Aunty Beena kalla yanda wayan nan ya yi..."
Da sauri na fisge wayan ina fa蓷in.
"Miye wayan ya yi Bahrain?"
Shiru ya yi mini kurum yana bina da ido.
"Oh my God!... Ammie wallahi ya rufe simcard 蓷innan dole sai an saka wasu code zai bu蓷e."
"Subhanallah! Garin ya ya haka Bahrain?"
Hawaye ne suka gangaro daga idonsa yana mai 茩ureni da kallo ya ce.
"Dan Allah ki yi ha茩uri aunty Beenafah wallahi ni ma ban san lokacin da na danna hakan ba."
Ajiyar zuciya na sauke sannan na jinjina kaina na ce.
"Ba komai. Kawai dai damuwata 蓷aya ce akan Yaya Ashiru, idan ya kira bai samu ba zai ji haushi. Amma thank God tun da gobe zamu koma..."
Kallona Ammie ta yi ta ce.
"OK yasan cewa gobe zamu koma 蓷in?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"Ya dai san cewa cikin satin nan ko zuwa next week za'a bamu sallama amma bai san cewa yau ne ba domin kinga abin kamar daga sama ne tunda ko mu bamuyi expecting ba, kuma tun jiya da ya kirani bai sake kira ba,daman kuma da wayan Umma ne ya kirani yace mini wayarshi ta fa蓷i ta ci screen tana wurin mai gyara, to ina ga bai samu ya amso wayar ba har yanzu."
Daga nan ba wanda ya sake cewa komai har muka gama cin abinci muka yi shirin kwanciya bacci.
Washegari, da wuri ya kaimu tasha ya saka mu a mota cike da tarin alkairan da baki ma ba zai iya furta kalaman godiya ba sai dai muyita yi masa addu'a har 茩arshen rayuwarmu.
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍