Free chapter 路 Read without an account
23
by Kansa'u Bello 路 MATAR MANYA
*馃挀MATAR MANYA馃挀*
*By*
*OUM FATIMA*
*GAJEREN LABARI*
*PAGE 24*
*BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM*
"Assalamu alaikum." Kairiyya ta fa蓷a daga can 蓳angaren lokacin data 蓷auki wayar.
"Bestie!". Na kira sunanta muryata na bayyana halin da nake ciki.
"Bestie kina lafiya kuwa? Meya faru kuma?." Tayi min tambayoyin duka a lokaci 蓷aya cikin damuwa. Zayyane mata duk abinda ke faruwa nayi a 茩arshe nace "Ya kike ganin zan iya aiki a 茩ar茩ashinsa bayan duk abinda ya faru a tsakaninmu".
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Kin bani tsoro Bestie, nayi tunanin wani mummunan abu ne ya same ki ko yara." Kairiyya ta 茩are maganar cikin samun natsuwar jin cewar ba wani mummunan abu bane ya samu aminiyar tata ba
"Kawai ina cikin damuwa ne Bestie amma ba abinda ya same mu."
"Na fahimta, amma ki sani cewa wannan wata damace kika samu wacce kika da蓷e kina burin samunta, kada ki bari wani personal issue ya hanaki cika burinki na taimakon Iyayenki, abinda zakiyi kawai shine ki kama kanki kiyi abinda ya kaiki ba ruwanki da shishi-shigi ko nuna cewa wata ala茩a ta ta蓳a shiga tsakinku dashi tunda shima bai nuna hakan ba, idan kikayi haka shike nan kin ja mutuncinki zakiyi aikin ki cikin kwanciyar hankali domin gina rayuwarki ta gaba daya iyalanki." Kairiyya ta 茩are maganar cikin bata 茩warin gwiwa.
"Na gode sosai Bestie zanyi hakan in sha Allah." Na fa蓷a mata ina jin 茩warin gwiwar yin amfani da shawar da suka bani.
******* Washe cike da 茩warin gwiwa na tashi tun da safe nayi duk abinda na san inayi sannan nayi wanka na shirya tsaf cikin doguwar rigar leshi 蓷inkin T bubu, dai-daita 蓷aurina nayi na soke ya zauna 蓷as tamkar 蓷auka akayi aka 蓷ora shi.
A gur-guje mukayi breakfay Abba ya wuce damu ya sauke yara a makaranta nima ya ajeni wurin aikin sannan shima ya wuce nasa wurin aikin.
Ofishin marketing manager na fara zuwa shine yayi min jagora har Office 蓷in da zan yi aiki a cikinsa wanda bani ka蓷ai bace mu biyar ne Maza uku Mace 蓷aya ni cikon ta biyun.
Gabatar dani yayi a garesu a matsayin sabuwar ma'aikaciyarsu da zamuyi aiki tare, suma gabatar da kansu sukayi a gareni sannan aka nuna min sit 蓷ina da zan maye gurbin kaishi da Allah yayi mata rasuwa sannan aka gabatar min da fayil fayil na ayyukan da zan fara. Zama nayi da Bismillah bakina 蓷auke da addu'ar neman taimako a wurin Allah na fara dubawa 蓷aya bayan 蓷aya.
Ranar haka na yini aiki na ba wasa don so nake na dai-daita abubuwa, Sallah kawai naje masallaci nayi ko ta kan abinci da abokiyar aikina mai suna Raihana tayi min tayin zuwa ban bita ba nayi mata godiya na koma Office naci gaba da aikina.
Koda lokacin tashi yayi nice 茩arshen fita saboda sai da na tsaya na tattare wasu takardun ina son 茩arasa su a gida. A 茩afa na ri茩a takawa har na fita daga Companyn gaba 蓷aya na tsaya don neman abin hawa saboda nace Abba ba sai ya dawo 蓷aukata ba ba zan dawo da kaina.
Dai-dai lokacin da nake 茩o茩arin tsayar da adai-daita sahu motarsa ta fito daga Companyn, yana hakimce a baya direbansa na tu茩ashi shi kuma yana duba wani aiki a cikin laptop 蓷insa. Kamar ance ya 蓷ago kansa sai kwai idanuna a cikin nasa, sar茩e idanunsa yayi a nawa yana min wani irin kallon da sai da nayi da 茩yar na fisge idanuna na fa蓷a adai-daita sahun ina ce masa "muje."
苼oyayyar ajiyar zuciya ya saki lokacin da mai adai-daitar yaja suka bar wurin, yau tunda safe da yazo yake zuba idon ganinta amma ko mai kama da ita bai gani ba. Har ya fara tunanin ko dai bata zoba ta fasa amsar aikin, sai kuma ya ganta dai-dai lokacin daya fito shima zai tafi gida.
Rufe laptop 蓷in yayi ya ture komai ya kwantar da bayansa saman makarin kujerar motar ya lumshe ido yana kokawa da abinda ke neman fin 茩arfinsa, yana a wannan yanayin har suka isa gida wanda yana zuwa ya haye sama kota kan Aliya dake can 蓷akinta ana faman kwalliya don tarbar miji bai biba ya shige 蓷akinsa ya kulle.
Fitowarta kenan cikin sauri don ta tare shi ta samu har ya shige ya rufe 茩ofar, sororo tayi tana tunanin abinda ya same shi saboda duk da cewa ba sonta yake ba amma yana 茩o茩arin sauke ha茩茩in aure dake wuyansa.
Harta 蓷aga 茩afa zata masa knocking sai kuma ta fasa ta sauka 茩asa don ha蓷a masa abinci kafin yayi wanka ya sauko, sai da ta gama ha蓷a komai ta zauna jiransa. Jin shirun yayi yawa yasa ta haura saman tayi masa knocking. Sai data jima a bakin 茩ofar kafin yazo ya bu蓷e mata, 蓷aure yake da towel jikinsa na ra蓳ar ruwa alamar daga wanka ya fito.
"Am dama naga ka dawo baka yi min magana bane." Tayi maganar tana zuba masa ido.
"Bana jin da蓷i ne." Ya bata amsa a ta茩aice.
"Ayya sorry Allah ya sauwa茩a, ko in kawo maka abincin nan?."
"No kije zan sauko." Ya fa蓷a yana maida 茩ofar ya rufe. Ajiyar zuciya Aliya ta sauke ta juya ta tafi tana addu'a da fatan ganin ranar da zata samu gurbi ko yaya yake a zuciyar bawan Allahn nan.
******** Naci gaba da gudanar da aikina cikin kulawa da taka tsan-tsan, duk wata hanyar da zata sani yawan ha蓷uwa da Suhail ko ke蓳ewa da shi bana binta. Idan har mun ha蓷u to aiki ne ya ha蓷amu, ko ana general meeting ko kuma zan kai wasu takardu Office 蓷insa kuma shima bana yarda in tsaya daga gaisuwa ba abinda nake 茩arawa zan fice.
Haka zai bini da kallon takaici wanda nake fassara shi da cewar kallon tsana ne yake min, wanda ba ka蓷an ba hakan ke kayar min da gaba
Albashina na farko kamar yanda nayi al茩awari da zuciyata haka na kaisu na dire a gaban Abba da Mamy nace "Gashi nan albashina ne na farko, ku saka min albarka."
"Masha Allah, Allah ya sanya albarka ya 茩ara maki 茩warin gwiwa." Abba da Mamy suka fa蓷a.
"Ameen." Na amsa cike da jin da蓷i na mi茩e zan tafi Abba ya kirawo ni. "Ina kuma zaki je? Dawo ki 蓷auki ha茩茩inki mana." Abba ya fa蓷a yana nuna min ku蓷in dana aje.
"A'a Abba wannan naku ne, dama nayi al茩awarin cewa albashina na farko na kune ka'ida Mamy, kuyi min addu'a kawai ita nake bu茩ata." Na fa蓷a ina du茩ar da kaina.
"A'a ina ba za'ayi hakan ba, ya za'a yi kiyi aiki tu茩uru kuma sannan ki bamu ku蓷in duka, haba dai." Abba ya fa蓷a.
"Ai kuwa dai Abbansu, Nima abinda ke raina kenan nake son fa蓷a." Cewar Mamy itama.
" Kun can-canci fiye da haka Abba domin duk wata nasara dana samu kune tushenta, don Allah kar kuce a'a." Na fa蓷a ina jin abinda nayi dai-dai ne har cikin zuciyata.
"To shike nan tunda kin dage bari mu 蓷auki wani abu daga ciki sai musa albarka sauran kuma ki 蓷auka kiyi abinda ya dace dasu wannan hukunci na yanke." Abba ya 茩are maganar yana dibar ka蓷an daga ciki ya mi茩a wa Aunty Zali.
Tunda Abba yace hukuncin daya yanke kenan ba yanda na iya nasa hannu na 蓷auki ku蓷in na fice daga 蓷akin. Da yamma na nemi izinin zuwa gida wurin Abba da Mamy basu hanani ba, har su Ameerah na nemi alfarmar tafiya tare dasu ta barmu da shara蓷in mu dawo da wuri.
Wanka nayi musu na shirya su tsaf gwanin sha'awa suna ta murnar Auntynsu zata fita unguwa dasu. Nima shiryawa nayi tsaf cikin doguwar rigar wani material mai kyau nayi rolling mahaifinsa na 蓷auki jaka da takalmi wanda suka hau da wankan nawa muka yiwa Mamy sallama muka fice.
Duk inda muka bi sai an kallemu domin kuwa ba 茩aramin kyau muka yiba Masha Allah, ga yaran kyawawa suma 拼an ku蓳ul-ku蓳ul dasu sai surutu suke min har muka isa bakin titi inda zamu sami abin hawa. Wata ha蓷a蓷蓷iyar motace ta wuce ta gabanmu har ta wuce sai kuma ta dawo da baya.
A hankali ya sauke gilashin motar ya le茩o kansa yana cewa. "Sannunki dai 拼anmata." 茒auke kaina nayi tamkar ban ganshiba na kama hannun yaran ina 茩okarin wucewa ya bu蓷e motar ya fito ya sha gabana yana cewa.
"Am baki jiba, magana fa nake maki." Ya fa蓷a yana zuba min ido tamkar zai cinyeni dasu.
"Au dani kake wai ai naji kace 拼anmata ne ni kuma kaga babar 拼anmata ce." Na fa蓷a ina nuna masa Ameerah. Murmushi yayi yana cewa "You are jocking ba, nace in ba damuwa ku shigo na sauke ku."
"Akwai damuwa to, don haka bama bu茩ata!." Na fa蓷a a fusace saboda ya fara hasalani. Hannun yarana na kama na kauce da nufin muyi gaba mu samu abin hawa ya 茩ara shan gabana. A matu茩ar fusace na 蓷ago ina watsa masa wani mugun kallo nace.
"Malam wai miye kake yi haka, nace Bama bu茩ata kabi ka isheni sai kace dole haba don Allah." Na 茩are maganar a masife ina komawa ainahin Salmata ta baya. Magana zai 茩ara yi na 蓷aga masa hannu nace. "Bani wuri in wuce kona maka rashin mutunci." Na 茩are maganar ina zaro masa manyan idanuna da suka sha kwalli.
Hannu ya 蓷aga alamar saranda yana kaucewa a hanyar. Tsoki na saki na figi hannunsu muka yi gaba ina mita a raina, tamkar wani soko haka ya saki baki ya bita da kallo yana mamakin masifarta.
Ajiyar zuciya Suhail dake zaune a cikin mota yana kallon duk abinda ke faruwa tsakaninta da saurayin ya sauke. "Azababbiyar yarinya." Ya furta a 茩asan makoshinsa yana lumshe ido da tunanin cewa ashe har masu ku蓷inma yanzu sauke musu masifar take saboda kallo 蓷aya yayiwa saurayin da suturar jikinsa da motar da yake tu茩awa ya san ba daga 茩aramin gida ya fitoba.
Da wannan tunanin a zuciyarsa yaja motarta da yake tu茩awa da kansa ya nufi unguwarsu saboda yana son ganawa da Babansa ne.......