Free chapter 路 Read without an account
27
by Kansa'u Bello 路 MATAR MANYA
馃挀MATAR MANYA馃挀
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 27
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
Kaina a lullu蓳e yake cikin lafayar da Mamy ta na蓷a min lokacin da take tayani shiryawa shi yasa ba zan 茩arda komai ba game da gidan da aka kawo ni. Ni dai naji lokacin da muka tsaya bakin 茩ofa aka yi horn mai gadi ya bu蓷e muka shiga farfajiyar gidan da ban san ya take ba, a hankali Baba Lami 拼ar'uwar Mama ta fito dani daga cikin motar ta kama hannuna muka nufi 蓳angaren dama.
Sama naji mun fara haurawa wanda hakan ya tabbatar min da cewa upstairs ne, wata 茩ofar aka tura muka shiga ta zaunar dani saman gado, nasiha suka 茩ara yi min kafin sukayi min sallama suka tafi. Hawayen da suka zubo min na share sannan na bu蓷e fuskata ina 茩arewa 蓷akin kallo, sosai 蓷akin ya 茩awatu da tsadaddun furnitures da aka zuba a 蓷akin sai 茩amshi yake yi masha Allah.
Ajiyar zuciya na sauke ina godewa Mamy da Abba saboda irin Namijin 茩o茩arin da suka yi wurin zuba min kayan 蓷akin, bani da abinda zan iya saka musu dashi da ya wuce kullum in ri茩a yi musu addu'a da fatan alkairi. Tashi nayi na ware lafayar na shiga toilet nayi alwala na fito na mayar da ita tsaf na tada sallar isha'i da aka kira, ina gamawa na 蓷ora da shafa'i da wuturi.
A nan inda na gama sallar ina lazumi bacci ya 蓷auke ni ban sani ba, kusan 茩arfe 10:00pm naji alamar an bu蓷e 茩ofar an shigo, a firgice na tashi zaune ina murza idona zuciyata cike da tsoron wanda zan gani a matsayin Mijina. Ba zata, firgici da kuma mamaki suka kamani a lokaci 蓷aya saboda wanda na gani a matsayin Mijin nawa. Don haka na bu蓷e baki da nufin yin magana amma na kasa sai mui-mui nake da bakin ina nuna sa da yatsa.
"Rufe bakin ba mafarki kike ba, wanda kika tsana 蓷inne dai a matsayin Mijinki a karo na biyu kuma ko zaki mutu tsabar 茩iyayyar da kike min sai dai ki mutu a 蓷akin nan." Suhail ne mai wannan maganar, yana gama fa蓷a kuma ya aje laidojin daya shigo dasu ya fice abinsa ba tare daya 茩ara cewa komai ba. Duk da cewa zuciyarsa ba haka take bu茩ata ba amma dole ne ya bata lokaci domin sanin meye a zuciyarta game da shi kafin komai.
茒akinsa dake 蓳angaren ya shige ya maida 茩ofa ya rufe yana rintse idonsa yana jin nauyin da yake dako a 茩irjinsa na tsawon shekaru yana zagwanyewa, "Alhamdulillah" ya furta a hankali sannan ya taka ya nufi cikin 蓷akin da aka 茩awata shi da tsari mai kyau...
Abinda ya faru shine.....
Lokacin da Suhail ya dawo rayuwar Baba ya taimaka masa tsakaninsa da Allah ya cire shi daga cikin tsananin rayuwar da yake ciki ba tare daya duba abinda ya faru a baya ba, sosai hakan ya motsa zuciyar Baba ya 茩ara tabbatar da nagarta da kuma mutuncin yaron.
Ya rasa ta wace hanya zai saka masa shine ya yanke wannan hukuncin saboda har cikin zuciyarsa yana son ha蓷a jini da yaron saboda nagartaccen mutum ne daya can-canci aso shi. Da ace yana da wata nagartacciyar 拼ar bayan Salma to da tabbas ita zai bashi, sai dai kaf a cikin yaran babu wadda ta kama koda farcen Samar ne musamman yanzu da rayuwa ta koya mata darasi ta 茩ara shiga hankalinta, tana kuma bakin 茩o茩arin ganin ta kyautata masa domin goge wancan tabon data dasa masa a zuciya. Alhamdulillah ta samu fiye da abinda take nema a gareshi domin kuwa a tsakaninsu in banda addu'a da fatan alkairi babu wani abu da zai ce tayi masa na rashin kyautawa tun bayan wancan.
Don haka ya nemi alfarmar zama da Suhail da Mahaifinsa. A gidan Malam Umaru Mahaifin Suhail suka ha蓷u, bayan sun gaisa kai tsaye yazo da bu茩atarsa ta sake bawa Suhail 蓷in auren Salma a karo na biyu bayan ya tabbatar musu da sauyin dabi'u data samu a halin yanzu.
Jim Malam Umaru yayi yana nazari kafin yace "Amma Malam Shehu mai yasa ka yanke wannan hukuncin? Baka gudun a mai-maita irin kuskuren da akayi a baya na yin auren ba tare da amincewar yarinya ba kuma mummunan abu yazo ya biyo baya?."
"Subhanallah Malam in sha Allah abu makamancin hakan ba zai faru ba sai dai alkairi, domin kuwa Salmar ta canza ta kuma gane kuskurenta. Wan can ma da ya faru 茩addara ce amma tayi nadama sosai." Saurarawa yayi kafin yaci gaba da cewa "Dalilin da yasa na yanke wannan hukuncin shine ina son ha蓷a zuri'a da yaron nan saboda yaron kirkine mai nagartar da kowa zai so ha蓷a zuri'a da shi, dalili na biyu kuma shine ina son in masa wani abu wanda zan ji a raina cewar na kyautata masa, duk da cewa na san har abada ba zan iya biyansa alkairin da yayi a gare ni ba. To sai dai a kaf cikin yarana bani da mai nagartar da tafi Salmatu a halin yanzu, kamar yanda na fa蓷a abinda ya faru a baya 茩addara ce da kuma 茩uruciya, amma yanzu komai ya sauya." Malam Shehu ya 茩are maganar zuciyarsa fes da kyakkyawar niyar kyautatawa wanda ya kyautata masa.
Sosai Malam Umaru ya amince da dalilan da Malam Shehu ya kawo, sannan kuma har zuciyarsa shima yana son Salmar kuma shi shaida ne akan sauyin data samu domin har gida tazo ta nemi gafarar abinda ta aikata musu, wanda Babar Suhail tayi mata korar kare a gidan. Shi kam ta 蓳angarensa bashi da matsala ya amince sai dai ya san inda darun yake wurin Baba ne, amma duk da haka ya san yanda zai tan茩wara ta ta amince.
Sai dai ba zai yi gaggawar yanke hukunci ba dole sai an ji ta bakin yaro domin shine mai ikon zabar abinda ya dace da shi. Don haka Malam Umaru yace.
"Na gamsu da bayananka Malam Shehu sannan kuma a 蓳angarena na amince, sai dai ba zan yanke hukunci ba har sai da amincewar yaron tunda rayuwarsa ce." Gaba 蓷aya ido suka zuba wa Suhail da tunda suka fara maganar kansa ke 茩asa bai ce komai ba kuma ba wanda zai iya gane yanayin da zuciyarsa ke ciki.
"To Malam Suhailu kaji abinda muka tattauna a kai, shin zaka iya amsar kyautar da nayi maka a karo na biyu ko kuwa, kar kaji komai idan baka bu茩atar hakan ka fa蓷a kanka tsaye ba abinda zai faru." Malam Shehu ya 茩are maganar yana kallon Suhail.
Shiru yayi kansa a 茩asa nauyin Malam Shehu na kamasa wanda har yaji cewar ba zai iya masa musu ba, domin ko a baya bai 茩ishi ba. Hasalima shine ya tsaya masa har aka yi auren, idan duk aka ture wannan ma zuciyarsa ta amince da hakan domin har abada ba zai iya 茩in Salma ba ko me zata zama a rayuwa saboda soyayyarta 茩addararsa ce ya san da hakan tun suna 茩uruciya. Shi yasa ko a wancan lokacin ya kasa rabuwa da ita har sai da aka tursasa masa.
Ganin shirun yayi yawa yasa Malam Umaru ta蓳a shi yace "Kai muke saurare kayi shiru." Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya bu蓷e baki zuciyarsa na shiga maban-bantan yanayi yace. "Na amsa Baba kuma na gode, ba zan ta蓳a 茩in amsar abinda ka bani ba." Wani irin farin ciki ya kullu蓳e zuciyoyin Iyayen nasa suka shiga hamdala suna saka masa albarka, kafin suka tattauna yanda 蓷aurin auren zai kasance......