Free chapter · Read without an account

28

by Kansa'u Bello · MATAR MANYA

💓MATAR MANYA💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 28

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

An sha daga sosai da Babar Suhail kafin ta amince da ƙyar shima ba da son ranta bane, saboda ɓacin ran da Mijinta ya nuna mata ne sannan. Amma har abada bata jin cewar zata kuma son yarinyar.

Bayan yin wannan maganar da kwana biyu Suhail yana Office kwatsam sai ganin Hanifah yayi, har ofishinsa tazo ta dasa masa rigima akan samunsa da bata yi a waya shine dalilin daya sa ta kasa jurewa ta taho gida. Cike da mamaki yake kallonta yama rasa abin cewa, haƙuri kawai ya bata a kan cewar uzurori ne suka yi masa yawa shi yasa.

Suna haka asalin mai Companyn ya shigo Office É—in da sallama, dattijo ne sosai mutumin kirki don haka cikin mutuntawa Suhail ya tare shi yana cewa " Dady ai daka kira ni ma zan zo in sameka ba sai kayi wahalar zuwa ba."

"Kar ka damu Malam Suhail ba komai ƙanwarka ce gata nan ta saka rigimar sai nazo da kaina na baka haƙuri." Dattijon ya faɗa yana murmushi.

Da mamaki Suhail yake kallon Hanifah dake ta masa murmushi. " I'm sorry ban gabatar maka da ita ba, wannan ƴata ce Hanifah ita kaɗai Allah ya bani, ban taɓa samun haihuwa ba sai a kanta bayan mun cire rai nida Mahaifiyarta. Lokacin da tazo min da maganar akwai wanda take so nayi matuƙar farin ciki sosai domin duk wani abu data kawo min tace tana sonsa nima zan amshesa da hannu biyu matuƙar ba abinda zai cutar da ita bane, domin bani da abinda yafi min ita. Itace ta sanar dani cewa ka gama karatu ka dawo gida don haka ta buƙaci da na baka aiki a wannan kamfanin, alhamdulillah kuma sai gashi naji daɗin aiki da kai domin kai ɗin jarirtaccen mutum ne mai ƙwazo, sannan kana da gaskiya da amana. Da shigowarka wannan kamfanin ka janyo mana nasarori masu yawa ba abinda zan ce maka sai dai godiya da fatan alkairi." Shiru ya ɗanyi na wani lokaci kafin yace.

"Abu na biyu kuma shine ina taya daughter bada haƙuri akan laifin da tayi ake ƙin ɗaukar wayarta, gashi yanzu ta baro karatunta da take gab da kammalawa ta taho saboda kai."

Sosai kunyar dattijon ta kama Suhail har ya kasa haÉ—a ido dashi, yana É—ago kai suka haÉ—a ido da Hanifah data zuba masa ido. Harara ya sakar mata ya kauda kai ita kuma ta sake masa murmushi.

"Ba komai fa Dady kawai aiki ne ya min yawa amma ba wani abu."

"To madallah godiya nake, sannan in ka koma gida ka sanar da Mahaifinka ina son yin magana da shi."

"In sha Allah Dady." Suhail ya faɗa yana jin faɗuwar gaba, me Alhaji ke nufi da yana son yin magana da Mahaifinsa. Kenan Hanifah faɗa masa tayi suna soyayya?. Dady na fita Suhail ya kalli Hanifah yace "Wane irin shirme kike yi haka ne? Me yasa zaki dawo gida ki baro karatunki? Sannan me kika fadawa Dady a kaina?." Ya ƙare maganar a zafafe saboda shirmen da tayi ɗin ya ɓata masa rai.

Ƙwal-ƙwal tayi da ido zatayi kuka ya ɗauke kansa yana jin rashin daɗin abinda tayi masan. "Kayi haƙuri don Allah na kasa jurewa ne kwata-kwata baka ɗaukar kirana, ƙarshe ma daina samunka nayi. Ni kuma shi yasa na taho gida na faɗawa Dady ina sonka kuma kaima ka amince ayi maganar aurenmu." Ta ƙare maganar hawaye na zubo mata.

Shiru kawai yayi yana kallonta ya rasa abin cewa, nauyin Mahaifinta da yake ji da kuma tarin alkairinsa a gare shi yasa ba zai iya hukunta ba akan abinda tayi masan. Amma dai ba kaɗan ba ta ɓallo masa ruwa.

***** Bayan tashinsa a aiki gidansa ya wuce inda ya samu Aliya da tarin ƙawayenta baje a parlon ƙasa sunyi kaca-kaca dashi sun yi ciye-ciye sun zubar. Abinda ta tsiro dashi kenan kwanakin nan na tara masa ƙawaye suci su sha su kafa gulmarmaki suna fasa mata kai ta auri mai kuɗi kuma ɗan'uwanta don haka tayi yanda taso ba wacce ta isa ja da ita.

Ita kuma ba ƙaramin fasuwa kan nata keyi ba duk da ta san bata gaban mijin amma haka zata yi ta musu ƙarya kala-kala don ta burge su. Suna ganin shi kowa ya shiga tai-tayinsa suka shiga gaishe shi a ɗarare.

Bai ko kalli inda suke ba yanhaye sama don abinda ke damunsa ya wuce wannan. Tashi suka yi suka mata sallama suka wuce bakinsu fal gulmarta saboda sha-sha-sha suka maida ta sun sani sarai ƙarya take shirga musu. Cikin ɗari-ɗari ta bishi ɗakin, sai dai tana zuwa har ya kulle ɗakin koda ta buga bai ko nuna yaji ba don haka hankalinta ya tashi ta nufi ɗakinta ta ɗauki waya ta kira Mamanta ta sanar mata cikin damuwa.

"Ke wace irin sakara ce da zaki rinƙa tara masa ƙawaye a gida kullum, kin san fa ba ko wane Namiji bane zai ɗauki wannan shirmen bare Suhail da kika san halinsa, sannan kin san da yanda aka yi wannan auren maimakon ki lallaɓashi ki shawo kansa ki tara abinda kika tara shine kika tsaya sha-shanci kina yiwa ƙawaye burga." Maman Aliya ta faɗa cikin fushi.

"Yanzu Mama ni dai miye abin yi don wallahi ransa ya ɓaci sosai?."

"Bari zakiyi idan ya huce kije ki bashi haƙuri da alƙawarin ba zaki ƙara ba." Tattaunawa suka ƙara yi Uwar na ɗorata akan hanya sannan suka yi sallama.

Sai da dare ta same shi a ɗakinsa ta duƙa har ƙasa ta bashi haƙuri da alƙawarin ba zata ƙara ba sannan ya haƙura komai ya wuce.

__________★

Washe gari Suhail ya ɗauki Mahaifinsa ya kaishi gidan mai gidan nasa kamar yanda ya buƙata. An musu tarba ta mutunci an karrama su sosai kafin Dady ya yiwa Malam Umaru bayani akan dalilin kiran, shiru Malam Umaru yayi yana tunanin wannan al'amari yaro ƙarami amma cikin ikon Allah girma ya kama shi zai aje mata har uku a ƙanƙanin lokaci.

"Ina saurarenka Malam Umar." Dady ya faÉ—a ganin yayi nisa a cikin tunani.

"To ranka ya daɗe abin ne yazo min a ba zata, na farko dai yaron nan bai daɗe da yin aure ba. Sannan kuma a halin da ake ciki yanzu akwai maganar dawowar Matarsa ta farko wacce ƙaddara ta raba su, shine nake ganin anya kuwa zai iya riƙe Mata uku a ƙananan shekarunsa, sannan kuma ita yarinyar zata amince ta zauna da shi da wasu matan?." Malam Umaru ya ƙare maganar cikin sanyin jiki don har ga Allah gani yake abin zai yiwa yaron yawa, mace ɗaya ma ya aka ƙare da ita bare har uku.

Maganar Dady ita ta dawo dashi daga tunanin daya tafi. "Ni a ganina wannan ba wani abu bane saboda Suhail yaron kirki ne sannan kuma jarirtacce na san zai iya kula da gidansa in sha Allah, amma dai gashi nan mu fara jin ta bakinsa, sannan itama yarinyar zan kirata muji in ta amince sai a tsayar da magana kawai." Ya ƙare maganar yana kallon Suhail da kansa ke ƙasa zuciyarsa na wani wajen da ban.

Tsananin girman Dady da yake gani ne yasa ya kasa musa masa akan tambayar da yayi masa yace. "Dady idan har ta amince zata iya rayuwa dani a hakan shike nan Allah ya bani ikon sauke nauyin da aka bani." Sosai Dady yaji daɗi yasa masa albarka sannan ya ɗaga waya ya kira Hanifah aka tambaye ta a gaban kowa. Jin cewar Suhail yana da aure sannan kuma ya taɓa auren wata a baya zai dawo da ita yanzu yasa jikinta yin sanyi sosai, amma sai dai ba zata iya haƙura da soyayyar da take masa ba don haka tace ta amince amma sai dai ba zata zauna gida ɗaya da matansa ba.

"Wannan ba matsala bace da yake gidan nasa part biyu ne, to sai ya sama mata wani wurin ta zauna." Malam Umaru ya faÉ—a.

"Kar ka damu Malam Umaru wurin zama ba zai zama matsala ba, akwai gidaje zai iya zaɓar wanda yayi musa ta zauna a ciki." Suhail ne yayi saurin cewa.

"A'a Dady zan sama mata da kaina ma babu Matsala." Murmushi Dady yayi yana ƙara ganin ƙimar yaron saboda gudun abin hannun wani da yake da shi. Kwata-kwata baya saka ido akan abinda ba nasa ba, tunda ya fara aiki dashi bai taɓa kama shi da rashin gaskiya ko almundahana ba, don haka yake matuƙar ganin girmansa da mutuncinsa yake kuma ƙara shiga zuciyarsa.

Basu tashi a wurin ba sai da aka tsayar da magana za'a É—aura auren gaba É—aya nan da sati É—aya har na Salmar, amma sai dai ita Hanifah ba zata tare ba zata koma ta kammala karatunta da baifi wata uku ya rage ba. Idan ta dawo sai ayi biki ta tare.

Bayan sun fito Malam Umaru ya buƙaci Suhail ya kai shi wurin Malam Shehu, bai yi musu ba suka nufi can. Bayanin abinda ke faruwa ya masa inda ya nuna ba komai yayi masa addu'a da fatan alkairi suka rabu akan za'a ɗaura auren sati ɗaya mai zuwa.

Wannan shine abinda ya faru kuma shine bayanin da Baba yayiwa Salma lokacin data kira shi a waya. Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da Baba ya gama sanar da ita abinda ya faru, wani sanyi taji a zuciyarta duk da cewa jikinta yayi sanyi sosai jin cewar su uku suke da Suhail É—in a halin yanzu.

'yanzu da ban aikata abinda nayi ba da yanzu ni kaɗai ce Matarsa muna zanmu cikin so da ƙauna yana nuna min soyayyarsa mai natsuwa da bani kulawarsa mai tsayawa a rai.' zuciyarta ke raya mata wannan.

A zahiri kuwa cewa tayi "ƙaddara ce tazo da hakan dole sai ya faru, Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar, sannan ka dai-daita tsakinmu cikin sauƙi, ka zaunar damu lafiya da abokan zamana.".......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.