Free chapter · Read without an account

12

by Azizat Hamza · MAIMUNATU Telar Mata

16

Ya zaro ido ganin gaba daya 'yan gidan suna tsaye kowa yasha ado har da masu aiki ba wani hadadden cake da yasha icing da light blue and white color ....Cikin wani salo na janhankali Sury ta karaso ta rungumeshi tace happy birthday bhai yayi dariya yace indeed a surprise ....ya karasa wajen cake din da aka yi rubutu na alfarma asamansa an rubuta MUBEEN @32 ya kashe wutan akasa tafi ana mai happy birthday ......ya yanka cake din ya fara bawa Hajiya Khadija kafin yasawa mom a baki sai kannensa Sury da Diyya .....nan fa kowa ya fara bashi gifts daganan akasaki kida zokuga yadda mubeen ya ke nuna bajintarsa a wurin .....karshe su mom sama suka hau suka barsu yayinda matan suka dage sai ya koya musu sabon dance step nashi haka kuwa akayi sai wajen 10 taro ya watse friends din su sury suka wuce gida .....a gajiye ya shiga dakin nashi bai wuce ko inaba sai bathroom ya sakar ma kanshi hot shower ya fito sanye da bathrobe milk color ya zauna gaban mirror yasha fa mai daya gama ya saka pyjamas nashi dark blue ya kwanta tunowa da cewa baiyi sallar isha ba yasashi ya mike zumbur ya shiga bayin yayo alwala ..daga nan yayi sallah ya fada gado wayanshi ya dauko ya kura wa hoton dake kan screen din ido yafi minti biyar kamin ya sunbaci hoton yace Good night Simran ....ya kwanta .

Karfe uku da rabi wayar gimbiya ya fara kara dakyar yakai hannunshi kan wayar dake kan bedside wardrobe nashi ya katse alarm din saidai karfe hudu Kuma wani yasake bugawa shima ya katse shi aikuwa hudu da rabi wani yasake bugawa wani ihu yayi tare da tashi daga gadon yadau wayar yafara kokarin cire alarm din saidai ya kasa Dan baisaba da karamar wayaba haka ya hakura ya tashi ya daure alwala yai raka'atanil fajr tare da yin azkar har aka kira asuba ya tashi yayi Dan bacci daya keji ya hanashi fita masallaci ...yana idda wa ya hau kan lallausan gadonsa sai bacci ......

Karfe takwas da rabi wayar ta fara kara ya dauka yakai kunne cikin maganan bacci yace waye ne daga daya bangaren akace gimbiya nake nema Hajiya Zainab ce jin ance Hajiya Zainab yasashi mikewa yace tsohuwa ina kwana ...Mubeen ta kira da mamaki yace yes a wani dalilin karikewa 'yar mutane waya ...cikin sakalci yace wallahi Hajiya wayan nan ta hanani bacci waccar bakar yarinyar ta manta wayarta a motana saina shigo dashi daki duk bayan minti talatin sai alarm ya buga har asubayi tun karfe uku ...dariya ta yi mai isarta kamin tace ja'iri kawai maganinka ai yanzu dai ka kaiwa 'yar mutane waya inason magana da ita ya marairaice murya yace not now Hajiya Babba sai da rana ....kut....lallai mubeen ka rika ta fada gamida kashe wayar .....salati yayi tare da mika kamin ya wuce toilet wanka yayi daya dau minti 20 kamin ya fito ya shafa mai ya fesa wani body spray ya dauko wani jar t-shirt nashi da bakin jeans yasaka yasaka wasu sneakers mai ja da baki kirar adidas ya fesa turare kala uku yasanya agogo na gold ya zura azurfanshi a yatsa ya dauka wayoyinshi ya sauko Falon kasa kai tsaye ya je yazauna a dining tare da danna kararrawa baifi minti biyuba wani saurayi ya fito sanye da uniform ya risina ya gaidashi good morning sir ko kallonshi baiyi ba yace morning Simon get my breakfast now... ok sir what would you like yace ehm coffee, veg sandwich and omelette ...baifi minti biyar ba simon yazo ya jera mai abinda ya bukata ya tafi yafi minti shabiyar kamin ya gama ci ya tashi ya hausama falon Hajiya Khadijah ya shiga yasameta tana aiki akan laptop nata ya tsuguna ya gaida ta ta amsa batare data kalli wurin da yake ba ganin ko kallonshi batayiba yasa shi tashi ya fita ya wuce dakin mom ta kokarin daura dankwali ya shigo cikin fara'a ya gaidata tare da cewa haba momcy wannan dauri haka saikace meshirin zuwa gasan dauri tayi dariya tace danma sauri nake ya yi Murmushi yace yaushe dad zai dawo ta ce gobe da safe jirgin karfe 10.......ya ce Allah ya kaimu amin ta amsa masa yace na tafi yawo mom sai yamma zan dawo tace to.......

Karfe goma da rabi mubeen ya isa kofar gidanmu kai tsaye shagon baba ya shiga ba kowa aciki sai baba da 'yar radionsa ya yi sallama tare da gaida shi baba ya amsa mai da fara'ar sa ....baba dama wayar tailor ce ta manta a motana jiya shine na kawo ya mika mai wayar baba ya karba yace angode ganin bai tafi ba yasa baba cewa da wani abu ne? ya shafa gashinshi yace Hajiya ta kira dazun tana son magana da ita so zata ga number din ya kare da 00 yace zan sanar da ita .....yana fitowa daga shagon nikuma zan shiga nawa shagon muka hadu na rasa dalilin dayasa nasakar mai Murmushi shikuwa ya wani hade rai ya karaso wajena yace your local phone disturbed my sleep last night ...na rasa me zance mashi kawai na kura mai ido ...well for being my hajiya's tailor I forgive you ya juya zai tafi kamar ance ya daga ido ya kalli sunan dake jikin shago na "Maimunatu Telar Mata" aikuwa yasa dariya rasa gane dalilin dariyar nayi sai da naji yana what a funny name nasan da sunar shago na yake har ya shiga mota bai bar dariya ba nikuwa saidanaji haushi a raina .......

Munyi waya da Hajiya ta tambayi yaushe zankawo dinkin nace mata nanda kwana goma tace sainazo .....sosai na zage na fara dinkinsu Hajiya Dan koda naga size din Baby sainaga Ashe saidai tafini tsayi kadan amma kusan duk size dina ne ....haka na tsaya na tsantsara musu dinki kwana na tara na kare su addu'a na Allah yasa Hajiya da 'yarta su yaba dinkin Dan kowa agidanmu ya yaba har yaya KB na kaiwa ya gani shima ya jinjinawa basirata......na kira Hajiya nace mata na qare su inaso in kawo mata in har tana gida murna tayi tace inbari gobe zata turo azo a daukeni Dan ta fita anguwa nace mata shikenan .....sosai nake fargaba

ar kaimata dinkin Dan ina shakkar hulda da masu kudi .....na sanar da umma yadda mukayi da Hajiya tace Allah ya kaimu ...nace amin......

17

Washe gari bayan nayi aikin gida na kammala komai na shiga wanka na fito shadda ta ta sallar azumin bara na saka light blue ce tasha aiki da farin zare na saka farin hijabi da farin sandal shoe nawa da yaya Alhassan ya siya mani nashafa farar powder da kwalli lip gloss na Dan shafa kadan na duba kaina a madubi gaskiya nayi kyau barinma manyan idanuna da kwallin ya kara fitar dasu ......na duba agogo goma saura kwata na zauna ina jiran kiran Hajiya ......

Yana faman shiga motarsa kenan yaji wayar sa na ringing ya dauka ganin Hajiya babba a jiki yasashi Murmushi 'yar tsohuwa wajenki nakeson zuwa amma naga kinyi missing nawa daya wa tai dariya tace ai faduwa yazo da zama dama so nake kamin wani aike ya bata fuska haba Hajiya gobe fa zan koma Abuja kawai zanzo sallama ne fa baga baby na gida ba tace to Mubeen ai batasan wajenba yayi tsaki a ranshi yace ok inane wajen tace mubeen so nake kaje ka dauko min gimbiya zata kawo min dinkina ya zaro ido kamar tana kallonshi yace Hajiya ba dai black girl din nan ba ni gaskiya bazan ita zuwa ba aisai ta raina ni so biyu ina zuwan gidansu fa .....tace bana son iya shege na baka minti shabiyar ka kawo min ita ta kashe wayar ....Ahhhhhh shit ya fada yana buga kofar motar ni wallahi Hajiya na shiga hancina fa taya zan rinka mata jigilar tailor dinta haka dai yaita murmuring shi daya har kofar gidansu maimunatu.....

Ina zaune a kan tabarma a tsakar gidanmu ina Dan tilawa almajiri ya shigo wai tela taje inji wani mai mota nace ya yake mutumin yace Dan gayu ne nai Murmushi nace cemai ina fitowa ya fita nikuwa na shiga dakin Umma na mata sallama dama jakar na kan tabarmar Dana tashi sai kawai na dauketa nayi waje Ganin jeep a kofar gidanmu yasa nadan ji tsoro karbar dinki Kuma azo daukana da jeep tun danake ma bayan motan haya zan iya irga sau nawa na shiga mota na leka shagon baba nacemai Hajiya ta turo a daukeni yace to Allah ya kiyaye nace amin na fito na karasa wajen motan na tsaya a kusa da kofar gaba amma ban bude ba kusan minti biyu kamin aka bude daga ciki Ganin wanda ya bude ne yasa rintse idona na kodai gizo yakemin Dan tun ranar da ya kawomin wayata nake sake muradin ganinshi gashi har kannena sun gane yadda nake yawan maimaita ayar da ta kare da "Mubeen" idan ina tilawa ....kasa shiga nayi saidayace inbaki da niyya ni zan wuce nace a ina zansa jakar yace a kaina na fara kokarin saka jakar a gaba ya ce don't you dare silly girl kawai je kisa a boot na bude....na karasa na saka jakar a boot din nazo nazauna a gaba ina kulle kofar da Dan karfi ya juyo ya kalleni yace to cire mini shi kiyi ado dashi a shagonki nidai bance komai ba muka fara tafiya can wayata ta fara ringing na dauka Ganin Hajiya ce na rusuna kamar ina gabanta na gaidata tace mubeen baizo bane nace yazo muna hanya tace saikun iso ta katse wayar ....na maida wayar cikin wani karamin purse dina mai fari da blue dabaifi naira Dari biyar ba .....ba abindayake tashi a cikin Motan sai wakar tose naina na Arijit Singh har muka Isa gidan ba wanda yace kala saini danake Satan kallonshi idan yana bin waqoqin Indian dake tashi a hankali a cikin motan.....

Mun shiga gidan yayi parking a parking space na gidan na bude kofa ina shirin fita ya rike hijabina na juyo a firgice ina kallonshi fiskarsa a daure yace saboda kina ganina a kofar gidanku har ya baki jinkai da ko sallama bazaki min ba dazaki shiga min mota balle gaisuwa irin ga driver naki ba to barikiji this should be the last time da Hajiya zata kuma hada ni dake inma kece da gulmarki kikeson ganina kike like wada Hajiya to ki daina Dan next time bazaki ji da dadiba .... Cikin mamaki nace mai Allah na gani nayi sallama dazan shiga saidai ka ki ko kallona bare ka amsa to sainaga tunda baka amsa na musulunci ba bazakayii ta al'ada ba .....ya ja hijabin da karfi harya shaketa yace you talk back to me again I'll smash your big head stupid kawai ya fada tareda sakemin hijabi aikuwa tuni idanuna suka firfito saboda tsoro na fita daga motar ina faman rarraba ido harya fito ya shige cikin gidan ko kallona baiyiba natsaya ina tunanin bude motar nadauka jakar naji saude tace gimbiya ki shiga ciki mana na juyo na kalleta nace bandau jakar ba tace karki damu zanshigo dashi sai a sannan muka gaisa nashiga gidan ina kara Ganin girmanshi Dan ranar danazo ban wani kare mai kalloba .....

Ina shiga na ga Hajiya na mai masifa kai mubeen haka akeyi saika bar bakuwa a waje yakara narkewa acikin lallausan kujerar yace Hajiya she's coming fa ...sallamata ta katse maganan da Hajiya ke shirin yi tafadada murmushinta tace sannu da zuwa 'yata ta karaso ta kama hannuna har kujera ta xaunar dani nikan mamaki take bani kwata kwata Hajiya Zainab bata da kyamar mutane ...na rusuna na gaidata ta amsa tana tambayana 'yan gidanmu nace mata suna lafiya tace sannu da aikifa kin wahala damu nace a'a Hajiya aikina ne ai tayi dariya tace da saude data shigo da jakar jeki taso min baby a daki tace to ta haura sama nikuwa nafara jin kirjina na bugawa daf daf daf ...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.