Free chapter · Read without an account

PAGE 09

by Sumaiya M Tukur · SHAFUKAN ƘADDARATA .

⚡ SHAFUKAN KADDARATA ⚡

_*(Pages of my destiny).*_

STORY AND WRITTEN BY:

Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

PAGE 09.

Kai tsaye kaka Baushe gidan Baffajo ya nufa. Da sallamarsa ya shiga ya samu Hajjo zaune ta zabga tagumi, tun bayan da labarin abin da ya faru a gidan Inna ya zo mata. Tun farko abin da take gudu ke nan shi yasa ta ce kada a faɗa musu. Halin da Shatu ta shiga shi yafi komai ɗaga mata hankali, tun da abin nan ya faru bata taɓa ganin damuwar Shatu irin ta yau ba.

Amsa sallamar kaka Baushe ta yi, ta shimfiɗa masa tabarma ya zauna, ta ɗibo masa ruwa a randan sanyi ta kawo masa kafin ta zauna don su gaisa

Ruwan ya ɗauka ya sha kafin ya amsa gaisuwar da Hajjo take masa, ya dubi Hajjo da kyau ya ce "Mariya" ta amsa da "Na'am kaka Baushe"

Ya muskuta ya ce, "Faɗa min dalla-dalla abin da yake faruwa. Tas Hajjo ta kwashe komai da ya faru tun daga fari ta shaida masa, har da irin zaman da Shatu take yi a gidan na bauta ba abin da ta rage.

Nisawa kaka Baushe ya yi kafin ya ce "Amma shi ne baki sanar da ni ba sai da abin ya yi tsamari, ai da yanzu ba a kai ga haka ba, da an yiwa tufkar hanci tun tuni, amma yanzu ma bata ɓaci ba, kira min Shatun."

SHATU.

Muna tsakar gida labarin abin da ya faru a can gidan surukai na ya zo mana. Ban taɓa shiga tashin hankali ba irin na yau, jin ana ƙoƙarin sheganta min ciki tun bai zo duniya ba, ni kam na rasa me nayi wa Inna har haka, na tabbatar Inna ta na sane ta yi hakan don ta san cikin nan dai na Hassan ne.

Da fari nayi farinciki da aka ce za a sanar da su maganar cikina, don a yadda na san Inna take son ganin jikokinta na ɗauka hakan zai sa ta sauƙo daga dokin na ƙin da ta hau komai ya wuce, ashe abin ba haka bane, ƙiyayyar da take mini har ɗan cikina ta shafa. Hawaye ne kawai na ji suna rigegeniya da juna a kan fuskata, Hajjo ta riƙo ni tana rarrashi, buɗe baki nayi na ce "Hajjo wallahi ciki na ba shege bane da ubansa, me ya sa tun bai shaƙi iskar duniya ba suke son su shafa masa baƙin fenti? Me nayi wa Inna wanda ya sa har ɗan cikina bai tsira daga ƙiyayyarta ba?"

Share min hawayen Hajjo ta yi ta ce "Baki mata komai ba Shatu, wannan faɗan tsakanina da Zainaba ne, shi ne yanzu ya shafe ki, kiyi haƙuri kinji Shatu, ba wanda ya isa ya sheganta min jika, jika na ɗan sunnah ne ba shege ba, ki kwantar da hankalinki kinji ko."

Kaɗa mata kai kawai na yi na tafi ɗakina na kwanta, kuka nake bilhaƙƙi, har banji sanda Inna ta shigo tana ƙira na ba, sai da ta ɗaga murya ta sake ƙiran sunana kafin na jiyo, faɗa min ta yi kaka Baushe ne ya zo yake ƙirana. Da to na amsa na miƙe na biyo bayan Hajjo.

Zaune na hango sa kan tabarma, na je har inda yake na durƙusa na gaida shi. Bayan ya amsa na dawo gefensa na zauna. Allah ya sani ina kaunar tsohon nan. Nasiha ya min sosai mai shiga jiki ganin yanda duk na sanya damuwa a raina.

Hajjo ya ƙirawo ya ce ta kawo masa garwashi idan da akwai. Ba ɓata lokaci ta ɗebo masa a murhu, har gabansa ta kawo ta ajiye, wani ƙullin magani ya kunto daga jakarsa na fatar ɓauna ya barbaɗa a cikin wutan, sannan ya matso da shi kusa da inda nake zaune.

Ni dai zaune nake ban ko motsa ba, har zuwa wani lokaci kafin ya sake saka wani garin maganin, shi ma ya ɗan daɗe kafin ya kira Hajjo ta ɗauke rushin.

Bayan ta ajiye ta dawo ta zauna a inda muke, don ta san dole da bayani. Mai da kallonsa kaka Baushe ya yi kanmu ya ce "Wato babu wani alamu na maita ko aljanu a tattare da ita, ku kwantar da hankalinku komai zai zo ƙarshe da yardar Allah. Yanzu dai ku shirya ku je can fadar mai gari, nima ina nan tafe, yau za a yi ta ta ƙare.

Kaɗa kai kawai Hajjo ta yi ba ta ce komai ba, ta kamo hannuna ta miƙar da ni ta kaini har ɗakina ta ce na shirya, bari ta shirya ita ma sai ta fito mu tafi. Ban iya ce mata komai ba don duk jikina a mace, tunanin abin da zai faru a can fadar mai gari ita ta tsaya min a rai, ko me yasa ma kaka Baushe zai ce sai munje fadar mai gari oho. Haka na kammala shirina ina kananan tunane tunane.

Muryar Hajjo na ji tana tambayata ko na gama, nace mata eh tare da fitowa. Ina fitowa Baffajo ya shigo gidan shi ma ya shirya tsaf, da alamun ya san da maganar zuwa fada, nan muka ranƙaya muka tafi.

Muna isa can fadar mai gari muka gano taron mutane kamar wani abu ake na musanman. Wuri muka samu muka zauna muna fuskantar Inna da ahalinta, har da Huse da tagwayenta. Sunkui da kaina na yi na kasa ɗagowa in kalli kowa, duk a tsarge nake. Zuwa can mai gari ya fito aka mika masa gaisuwa, ba jimawa kuwa kaka Baushe ya iso shi ma.

Bayan kowa ya natsu mai gari ya buɗe taro da addu'a kafin ya ɗaura da jawabi.

"To jama'a kowa dai ya san abin da yake faruwa a karkarar nan game da yar gidan malam Bashari, abin da ya haɗa mu ke nan a yau, domin muna son gano gaskiya game da wannan al'amari, ba zai yiwu mu zuba ido haka kawai ana ɓarna a ƙasarmu ba, saboda haka ga nan Baba Baushe, kowa ya san shi, sanannen mai bada magani ne a ƙauyen nan har ma da maƙwabta da ya danganci ko wane ɓangare, yanzu ma kuma shi zai warware mana wannan sarƙaƙiyar."

Shiru wurin ya ɗauka kafin kaka Baushe ya miƙe ya yi ɗan jawabinsa kana daga ƙarshe ya ce"Idan ka san kana tare da maita kuma baka son tonuwar asiri a bainar jama'a tun wuri ka bar nan. Ganin ba wanda ya motsa ya sanya shi fara gudanar da ayyukansa. Ba jimawa kuwa wata mata ta zube a wurin, wani matashin saurayi ya bi bayanta, sannan sai wani ɗan karamin yaro ɗan shekara bakwai. Duk da ganin sun faɗi kaka Baushe bai fasa aikinsa ba har sai da ya ida kafin ya nemi wuri ya zauna, ya ce a ɗibo waɗanda suka faɗi a kawo masa gabansa, wani garin magani ya zuba a cikin rushin wuta da ya bukaci a kawo masa daga cikin gidan mai gari, nan take suka fara tari suna birgima.

Kaka Baushe ya dubi tarin mutanen sannan ya mai da kallonsa kan Inna wacce ta yi tsumu tsumu, ya dubi mai gari ya ce "To ka ga duk taron mutanen wurin nan babu wani me maita ko kanbun baka, sai wadannan mutanen guda uku da ke gabana a yanzu, sannan wannan saurayin ba maita gareshi ba kanbun baka ne, wannan tsohuwar dai ita ke da maita. Ko zan iya sanin a ina suke da zama?".

Mai gari da tunda ya ga bakin gidansa guda biyu sun faɗi ya sha jinin jikinsa, jin bayanin da Baba Baushe ya yi da kuma son sanin ahalin waɗanda suka faɗi ya daɗa dugunzuma hankalinsa. Da ƙyar ya buɗe baki ya ce "Waɗannan biyun dai baƙin gidana ne, ita kuwa wannan matar ban ma san ta a karkarar nan ba."

Wata ce daga can cikin taron mutanen ta ce, a ƙauyen gangare take dake maƙwabtaka da wannan kauyen, wucewa ta zo yi ta ga ana taro shi ne ta tsaya kallo."

Kaka Baushe ya shiga bankawa tsohuwa turare da magunguna, da ƙyar aka samu ta dawo hayyacinta, sai dai ta ce sam baza ta bar maita ba, gadon gidansu ne tun iyaye da kakanni, amma su basu cin mutum. Ba shiri mai gari ya sallameta ya kuma jaddada mata ko mai kama da ita kar ya gani a yankinsa, ta karkaɗe jiki ta ɗauki ƴar bakkonta ta wuce abin ta. Kan sauran ya dawo, ashe shi yaron a makarantarsu aka bashi ya ci, ko iyayensa ma basu sani ba. Magunguna kaka Baushe ya basu, da yake baƙi ne kwanansu biyu a gari, shi yasa zargi bai biyo ta kansu ba.

Bayan komai ya lafa, mai gari ya yi jawabi ya sallami mutane, bayan an wanke ni daga zargin maita da ake min wata da watanni, mutane dayawa sai da suka miƙa ban haƙurinsu ga Baffajo da ahalinsa kafin su tafi. Wurin ya rage daga mu sai su Inna. Kaka Baushe ya dubi Inna ya ce.

"To yanzu kin gani da idonki ko Zainaba, ba a yankewa mutum hukunci ba tare da tabbatarwa ba, yanzu wa gari ya waya, ina zaki da tarin alhakin wannan baiwar Allah. Ki gode wa Allah kuma ki gode wa Shatu, don yanda na shigo karkar nan a harzuƙe, ba domin ta dakatar da ni ba, yanzu da wani magana ake daban ba wannan ba."

Sunkuyar da kai Inna ta yi ta ce, "A yi hakuri Baba Baushe, mai faruwa dai ya riga ya faru, amma abin tambayar a nan shi ne, menene dalilin da ya sanya da Shatu ta tsallake jaririyar ta hau kuka, bayan ko tari bata yi ba kwana da yini. Wannan lamarin shi ne dalili na na faɗin Shatu ce ta kama ta, don kowa ma haka zai dauka."

Kaka Baushe ya ce, "Eh kowa zai iya ɗaukan lamarin a haka, amma kuma na ki sai ya haɗu da baƙin hali da ƙiyayyar da kika ɗaurawa ƴar mutane, kuma lallai hakan yana faruwa, amma dai tabbas babu maita a tattare da Shatu."

Kuka muka jiyo daga gefe, juyawar da zamu yi kuwa muka kalli Huse ce ke kuka harda shessheƙa. Tamabayarta mai gari ya yi ko mai ya faru. Ƴar ta ta nuna masa ta ce, "Ai to gata nan, tun ranar da abin ya faru bata sake lafiya ba, har yanzu da suke da watanni uku ita wuyanta ko tsayuwa baya yi, saɓanin ƴar'uwarta da har ta fara koyon zama, kuma ko ina muka je sai a ce mana shafar mayu ne."

Salati Hajjo ta sanya ta ce "Ai wai dama ƴar har yanzu mayun basu sake ta ba, ikon Allah, sai kuma gashi ana zaton wuta a maƙera, wa ya sani ma ko wani baƙin abin aka aikata ya waiwayo kan baiwar Allah."

Nan kuwa Inna ma ta hayyaƙo suka fara musayar baki, dama Hajjo a cike take da Inna da ahalinta.

Abu fa kamar wasa Hajjo ta ce wallahi sai ta ɗaure Inna, ba abin da zai hana ba ta yi shari'a da ita ba, kotun birni zata kaita. Tuni cikin Inna ya ɗuri ruwa, idan da abin da take tsoro to a bayan hukuma ne. A ka taru a na ba wa Hajjo haƙuri ta ce sam ba za ta haƙura ba, Inna kam zawo kaɗai ne ya rage bata yi ba a wurin, tuni ta jiƙe jagaf da zufa, duk kuwa da yanayin sanyi da a ke ciki. Da kyar da suɗin goshi a ka samu Hajjo ta haƙuram, hakan ma da sharaɗin sai Inna da ahalinta sun durƙusa sun ba wa Shatu haƙuri, shi ma kuma sai idan Shatun ta haƙura ta yafe musu to shi ke nan.

Duk izza da girman kan Inna sai ga ta gurfane gaban Shatu ta na ta faman bata haƙuri ita da tawagarta. Da hanzari Shatu ta ɗago ta ta ce "Har abada Inna ni kam na yafe miki, dama can ban riƙe ki ba." godiya Inna ta shiga zabgawa, Mairo kuwa baƙincikin wannan haƙurin da suka ba Shatu kamar zai yi ajalinta.

Bayan an kashe wannan wutar ne kaka Baushe ya karɓi yarinyar ya duba ta, sai ji muka yi ya ce, "Assha, to ai wannan bugun aljanu ne, ba wani maita a nan, ga abu nan a cikin idanunta, da a ce ma an magance da wuri ai da duk abin bai kai nan ba." Ya miƙa ma Huse yarinyar ya ce gobe ta kai ta can wurinsa akwai maganin da zai basu, suka masa godiya.

Faɗa mai kamar nasiha mai gari ya mana kafin ya sallami kowa, tun a wurin ya so ya sulhunta in koma ɗakina amma sam Hajjo ta ce bata san wannan zancen ba, ai na gama zama da dangin marasa mutunci. Haka Inna ma ta ce ai dama Hassan ya gama aurena, kar wai a ga an wanke ni daga zargi a tsanmani ta canza, tana nan a Zainaba da aka sani.

Ganin zasu sake tada wani bala'in ya sa Baffajo samu a gaba muka tafi gida. Zuciyata cunkushe da abubuwa guda biyu, farinciki da kuma damuwa.

A zahiri farinciki ya kamata na yi saboda rufuwar baƙar shafi daga shafukan ƙaddararta, sai dai kuma rufuwarsa dai dai take da buɗewar sabon shafi wanda ban san menene rubuce a ciki ba.

Haka muka isa gida, zuciyar Hajjo wasai, tun bayan faruwar wannan al'amari sai yau na ga cikakkiyar farinciki a fuskar iyayena, sai hakan ya danne nawa damuwar, muka haɗu muka yi ta murna. Ba jimawa kaka Baushe ya shigo ya mana sallama zai koma, magunguna ya bani irin waɗanda masu juna biyu ya kamata su rinƙa anfani da shi. Baffajo ya rakasa har marrabar ƙauyen namu da nasu, don kaka Baushe da kafa zai koma, idan dai ba wai nisan wuri ya yi nisa ba, baya taɓa hawa abin hawa.

Kwana biyu gidan namu baya rabo da baƙi, ƴan taya murna, da kuma masu zuwa bada haƙuri, muatne dayawa sun ji kunyar abin da suka aikata mana, musanman ma Baffajo, har limanci aka mayar masa amma ya ƙi karɓa ya ce ba damuwa, a bar malam muttaƙa ya ci gaba da jan sallah. Hakan kuwa aka yi.

Ranar kuwa sai ga Inna Zulai; Adda Habiba da kuma Indo sun zo wai dubani da bani haƙuri, har da matan Yaya Salisu. Hajjo bata nuna musu komai ba, ta musu tarba mai kyau. Bayan an gaisa ne naji Inna Zulai ta na baiwa Hajjo baki a kan tayi haƙuri ta janye maganar ƙin komawata, yanzu haka Hassan ɗin ma yana kwance ba lafiya ko kasuwa ya daina fita.

Ina ji Hajjo ta ce.

"Au wai shi Hassan ɗin ne ba lafiya, to Allah ya bashi lafiya, amma dai kam sai dai ya ɗau na annabawa, don kuwa Shatu baza ta koma gidansa ba. Duk haƙuri da ban bakin da Inna Zulai ta yi Hajjo ta kafe ta ƙi canza ra'ayi, har sai daga ƙarshe ta ce wa Inna Zulai, "Nikam Yaya Zulai, dubiya ku ka zo ne, ko kuwa dai dama maganar da ta kawo ku ke nan kuka fake da dubiya."

Inna Zulai ta ce "Haba Mariya wani irin zance ne haka, har ga Allah dubiya muka zo da ban haƙuri, wannan maganar ma da kika ji ina yi ni na sanya kai na ba wanda ya san da shi.

Ina daga ɗaki ina jin duk tattaunawar da suke yi, a gefe kuma Indo na bani labarin halin da Hassan ya shiga, duk sai na ji damuwa ta lulluɓe mini zuciya, ina son Hassan har cikin raina, don shi mutum ne mai daɗin zama. Da ina da iko da na roƙi Hajjo ta barni na koma gidan mijina, sai dai kuma bazan iya hakan ba. Ina ji ina gani suka tafi.

Zuciyata ta gama yanke min hukuncin na samu Hajjo kawai da maganar ko za ta sauƙo ta amince........ ✍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.