Free chapter · Read without an account
Page 14
•••SANADIN MAHAIFINA•••
Wattpad@SaNaz_deeyah
Arewabooks@sanazty
Facebook@Habibtyn Habibi
YouTube: ***
Tiktok: ***
Facebook Page
***
Karku manta ku shiga links ɗin nan ku yi following handles ɗina
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
'''Shafi na 14'''
Ɗagowa yayi ya kalleta, itama kallon sa take idanunta cike da wasu hawayen. "Ƴar ka ta rasu yau, amma kallo kake abinka" juyawa tayi tana hawaye da sauri ya tashi ya biyota, tarar gabanta yayi sannan ta tsaya. "Karki saka wani tunanin a ranki Falmata, na kasa bacci shiyasa na kunna kallo dan in rage damuwa. Ta gefensa kawai ta wuce, ta nufi part ɗinta ta kira su Aunty Yana.
A yanda ta bar Jannat haka suka sameta. "Ko kaita asibiti zamuyi?" Mommy ta faɗa a ruɗe "A'a samo min ruwa kawai ki gani, a samo min mai sanyi." cewar Aunty Yana. Da sauri Mommy ta nufi fridge ɗin ɗakin ta ɗauko gorar ruwa mai sanyi ta kawo. Buɗewa Aunty Yana tayi ta zuba ruwan a hannunta sannan ta shafa a fuskar Jannat. Ajiyar zuciya mai nauyi Jannat ta sauke.
Khalil yana kwance a gado sai dai idanunsa biyu ya kasa ko da gyangyaɗi bare ya runtsa. Tashi zaune yayi ya saka pillow a bayanshi ya lula duniyar tunani. To waye ya yiwa Jannat fyaɗe da har za ta kamu da cutar yoyon fitsari? shine abinda ya furta a ransa. Fyaɗe ko Haihuwa sune suke haddasa yoyon fitsari, kenan Jannat fyaɗe akayi mata? To waye yayi mata? kan shi ya sake dafe wa da hannu. Ahmad yayiwa Jannat fyaɗe kuma ta sani ko Safina ta sani, gudun kar asirin sa ya tonu shiyasa ya gudu ya bar garin ko ƙasar. a firgice ya dira daga gadon lokacin da zuciyarta ta furta masa hakan. "Ya Allah ka sassautawa Jannat, baiwarka ce mai haƙuri, tausayi gami da kawaici" fridge ya nufa ya buɗe ya ɗauki ruwa mai sanyi, a gurin ya shanye ya yarda robar. "Ba zan taɓa bari a cutar da Jannat ba nayi alƙawarin sai na ƙwato mata haƙƙinta gurin duk wanda ya zalunceta"
Cikin kuka ta rike hannun Aunty Yana gam. Mommy ta zauna kusa da ita. "Jannat..." ta ambaci sunanta sannan ta saka kuka. Aunty Yana ta hau nasiha "Idan kina kuka ai zaki ƙara karya mata zuciya itama" "Da asuba zamu tafi asibiti kawai, bana son rasata, kina gani har yanzu bata dawo dai-dai ba ko magana fa batayi" Mommy ta ƙarasa maganar tana hawaye. "Ki kira likita yazo ya duba ta anan kafin a shafe makoki mu kaita asibiti." kai kawai Mommy ta gyaɗa.
Ana fitowa daga masallaci ta kira Doctor gida. Ya zo kuma ya shiga ya duba Jannat ɗin, idanunta a buɗe ta kafesu guri guda amma ba um ba um-um. Bayan ya gama auna ta ya kallesu ya ce "Tana fama da matsala ta damuwa da yawan tunani, kuma hakan zai iya sakawa ta zauce ta rasa tunaninta, domin jininta ya hau sosai Dan haka ku kiyaye ku riƙa yin duk wani abu da zai sanyaya mata zuciya" "To ai ka ga ƴar uwarta ce ta rasu dole dama ta shiga damuwa haka" Likita yayi ajiyar ya ce "Tun farko ma da ba'a faɗa mata ba, saboda wannan matsalar ta ta, ga hawan jini tana dashi at her age da bai kamata ace tana da damuwar da har zai iya haddasa mata ciwo kamar hawan jini" sai lokacin Mommy ta ce "Ba mu da yadda muka iya ne, wani sa'in damuwa ita take tunkararka ba kaine kake tunkararta ba, amma dai in sha Allah zamu kiyaye abubuwan da ka faɗa" "To Hajiya Allah ya bata lafiya, idan da hali a daina gaisuwa a gabanta dan zai iya ɗaga mata hankali" "In sha Allahu, mun gode."
*****
A hankali yake driving cikin nutsuwa, kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da yana cikin damuwa. Tun daya shiga layin gidan ya hango canopy har huɗu kuma ko wanne cike da mutane zaune akan carpets da aka shinfaɗa. "Allahu Akbar, dagaske dai Safina bata rayuwa, Allah yayi miki rahama yasa ke ƴar aljanna ce."
Yana yin parking ya fito ya gaisa da mutane dake gurin a zaune. Tashi yayi ya koma gefe ya kira number Farhan. "Hello" ita ta farayin magana kafin yayi "Ya ƙarin haƙuri?" "Mun gode Allah" "Allah yayi mata rahama" "Amin ya rabbi" "Dama ina so nayiwa Jannat da kuma Mommy gaisuwa dan tun da akayi rasuwar ban samu mun haɗu ba" "To bari naje nayiwa Mommy magana sai ka shigo ka san har yanzu gidan a cike yake" "Okay to ina jira." katse wayar yayi sannan ya koma rumfa ya zauna.
Knocking ƙofar tayi ta tsaya tana jiran a buɗe mata. Aunty Yana ce ta buɗe. "Lafiya?" ta faɗa tana kallonta. "Baki gane ni ba? Ni ce Farhan ƙanwar Jannat" "Oh Farhan kece fuskarki ta kumbura haka, ku daina kukan kar wani ciwo ya kamaku" wasu hawayen ne suka sake zubo mata sannan ta ce "Mommy na ciki?" "Eh tana ciki shigo" kai ta saka cikin ɗakin, duk da cewar da turaren wuta da kuma ƙanshin freshner amma akwai zarnin fitsarin. Tana shiga amai ya taho mata, da sauri ta guntse baki tayi toilet da gudu. Sosai tayi amai, Mommy ta bi ta ciki, tana ɗauraye baki, a sanyaye Mommy ta ce "Ki toshe hancin naki ki fita kinji" ƙi tayi suka fita daga toilet Mommy ta sake faɗin "Farhan ki je waje saboda kina da larura" Farhan ta kalli Jannat dake kwance idanunta a buɗe amma bata cewa komai. "Mommy ita fa ƴar uwata ce, kuma inda ni ce a cikin yanayin da take ciki fa?" "Hakane amma dan Allah ki fita" "A'a Mommy" samun guri tayi ta zauna, ta kalli Jannat ta ce "Jannat meya sameki?" kallon Mommy tayi ta ce "Naga bata magana Mommy" "Bata da lafiya sosai" "Allah ya ƙara sauƙi" "Amin" "Mommy dama Yaya Khalil ne ya ce yana son ya shigo yayi maku gaisuwa ke da Jannat" "To ko fitowa zanyi saboda ance ita Jannat a daina gaisuwa a gabanta" "Gidan a cike yake, naji mutane ma suna ta nemanki, ƴan gaisuwa na ƙara zuwa" "Nagode amma a yadda jikin Jannat ya matsanta ba zan iya tafiya in barta ba, ki kirashi zan fito ƙofar ɗakin amma ki biyo dashi ta ƙofar baya" Da to ta amsa sannan ta miƙe ta fita.
Tare suka jero, a ƙofa suka tarar da Mommy a tsaye, har ƙasa ya durƙusa yayi mata ta'aziyya cikin girmamawa ta amsa masa. "Amm..... Mommy zai shiga ya duba Jannat ɗin na faɗa masa ba a yi mata ta'aziyya" Mommy dai bata so hakan ba amma ba yadda ta iya haka suka shiga.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya furta a fili cike da damuwa. Hawayen da yayi niyyar ɓoyewa sune suka samu damar fitowa. Ya janyo hanky yana gogewa. Farhan kuwa mamaki abin ya bata kawai ta saki baki tana kallonsa.
Addu'a sosai yayi mata sannan ya fita, Farhan ta mara masa baya da saurinta. Ya ɗan bar bakin ƙofa kaɗan ya tsaya, a gabansa ta tsaya ta kuma kafe shi da idanu. "Wai kukan mene Yaya Khalil? Safina mun rasa ta sai dai kawai addu'a take buƙata daga garemu" ta furta tana sharar hawaye. "Halin da Jannat ke ciki, ya sakani damuwa na kasa ɓoye hawayena" cak ta tsaya galala tana kallonsa. "Idan har ina raye ba zan bar Jannat ta wulaƙanta ba" "Yaya Khalil bana so ka shiga maganar da ba taka ba, domin abinda ya samu Jannat matsala ce babba" "Abinda ya shafi Jannat nima ya shafeni, ina son Jannat ba zan bari ta wulaƙanta ba, kuma koma wane yayi mata wannan ɗanyen aikin wallahi sai na ɗauki fansa, wannan alƙawarine" Yana faɗa ya wuce ya barta anan tsaye. Lumshe ido tayi tana cije baki ranta a matuƙar ɓace.
Bata koma ɗakin da Jannat ke ciki ba, side ɗin Ummu ta nufa, zuciyarta na harbawa da sauri. Tana shiga bedroom bata damu da duk mutanen dake ciki ba tana shiga ta fashe da kuka. Aikuwa aka yo kanta, wasu na rarrashinta wasu na mata nasiha, su a duk tunaninsu tunawa tayi da mutuwar Safina. Aunty Mammy ɗago ta tayi tana share mata hawaye ta ce "Haba Farhan kin san kina da larura amma kike wannan kukan, dan Allah kiyi haƙuri, a yanzu Safina addu'a take buƙata. Tsayar da kukanta tayi ta cigaba da hawaye kwanciya tayi ta runtse ido lokacin da taji zuciyarta na harbawa kamar za ta fasa ƙirjinta ta fito.
Sai da ta sha kukanta ta ƙoshi sannan ta ɗauki waya ta tura masa text.
Yana zaune a cikin mota ya kunnata saboda AC ya kwantar da kujera, tsananin damuwar da yake ciki ba za ta saka ya zauna a gurin makoki ba. Text ɗin daya shigo wayar sa ya ɗauka ya duba. Yaya Khalil yau na tabbatar da baka so na, a gabana kake faɗin cewa wai kana son Jannat, dama na san auren dole akayi maka kamar yadda akayi min, amma ni na haƙura na zauna da kai tsakani da Allah kai kuma ashe har yanzu kana kallon macen da bata ƙaunarka da fuskar soyayya, nagode da abinda kayi ka sakeni kawai sai ka auri Jannat. nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya gama karanta saƙon Farhan. Ajje wayar yayi ya dafe goshi tare da yin salati a fili. Kiyi haƙuri ba haka nake nufi ba, amma na san a yanzu ba zaki taɓa fahimtata ba.
*****
Hanne na zaune tana wanke-wanke, Umma na daga gefe kan kujera tana tsintar wake. "Hanne kiyi sauri ki gama a ɗora abincin nan da wuri" "To Umma" ta faɗa tana cigaba da wanke kwanukan. Sa'ad ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa sukayi ya ja kujera ya zauna kusa da Umma tare da ajje ledar hannunsa. "Umma na sayo kifi ne ayi girki dashi saboda ita bata son nama tafi son kifi" murmushi Umma tayi ta ce "To ba damuwa Allah yayi albarka" "Amin Umma" Hanne dai taɓe baki tayi ta juya idanunta tana ƙoƙarin mayar da hayen da suke neman zubowa.
A falon Umma ta same shi zaune kan carpet ta dubeshi tana daga tsaye. "Ada nayi tunanin Jannat bata da adalci lokacin da ta fara ƙoƙarin barinka" sai kuma tayi shiru. Ɗagowa yayi ya kalleta "A yanzu fa?" "Yaya maganar gaskiya ba ayi wa Jannat adalci ba, ta sadaukar da soyayyar ta saboda kai, amma a yanzu cikin ƙanƙanin lokaci kana soyayya da ƙanwar abokinka kuma har ma za ta zo gaida Umma" "A lokacin dana so Jannat babu irin cin mutuncin da mahaifinta bai min ba, kuma a yanzu gashi wadda nake so daga ita har iyayenta suna nuna min ƙauna" "Amma ai Jannat babu irin wahalar da bata shanye ba duk saboda kai, lokacin fa ba sonka take ba kawai ta tausayawa halin da kake ciki, kamar yadda kace mahaifinta ya maka, to itama haka kana asibiti Umma ta wulaƙanta ta, haka mahaifinta har korar ta yayi wannan daliline ya saka ƙaddara ta faɗa mata, kaine sila Yaya amma a yau ka guji Jannat" "To munafuka, aku sarkin magana, ai dama tunda naga kin lallaɓo kin biyoshi ɗaki na san akwai tuggun da kike son yi" "Haba Umma yanzu gaskiyata sai ta zama tuggu?" "Kenan in aurawa ɗana macen da ta lalace tun a waje ko?" "Aka lalatata dai, Umma duk da ke mahaifiyata ce ba zan daina faɗa miki gaskiya ba" tana kaiwa nan tayi hanyar waje, za ta wuce Umma ai kuwa ta saka hannu ta dawo da ita sannan ta tsinka mata mari. "Duk ranar da kika ƙara maganar wata Jannat a gidan nan sai na ɗaga miki nono" tana gama faɗa ta wuce ta bar ta nan tsaye riƙe da kumatu. Sa'ad kuwa kan shi a ƙasa bai ƙara cewa komai ba. Juyawa tayi ta kallesa tayi ƙwafa sannan ta wuce ta bar ɗakin itama.
SaNaz Ce✌️