Free chapter 路 Read without an account
PAGE 13
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 13
Muryar Aunty Labiba na ji tana shigowa parlourn tare da su Hanan shirye cikin uniform 蓷in su na Islamiyya ta ce.
"Barrister Beenafah ce fa. Mai aikina wacce Adeel ke yawan yin maganarta."
"Oh! Allah sarki. Wannan ita ce Beenafah? Da yake kin san ban ta蓳a ganin ta ba sai yau.... Sannunki."
Fa蓷owa Hanan ta yi jikina cike da jin tsagwaron rigimarta da ta saba tace.
"Aunty Beenafah ta shi muje makarantarmu..."
Mi茩ewa na yi da sauri na nufi ciki janye da hannunta,muna shiga na rungumeta ina sha茩ar dadda蓷an 茩amshinta na ce.
"Wow...My Hanan! 茩amshinki mai da蓷i, uniform wankakku kuma gashi an goge su sun yi kyau, yau kin yi kyau kin ji ko tawan....amma kema kin san cewa ba zan iya zuwa makarantarku ba dan Allah kada ki ci gaba da rigima, ki je makarantarki kin ji ko?"
"To za ki tsaya har na dawo?"
"Sosai ma. Yi maza driver yana jira kar ki yi latti."
Daga haka ta fice tana mini bye-bye yayin da ta bar Adeel nan tsaye yana mai bina da kallo wanda da alama akwai abin da yake so ya tambayeni ko ya fa蓷a mini.
"Aunty Beenafah amma dai kin ta蓳a yin makaranta?"
Dariya ce ta su蓳uce mini ba tare da na shirya ba sannan na gya蓷a masa kaina na ce.
"Eh, na ta蓳a yi mana..."
"Aji nawa kike to?"
"Kamar ajin da kake yanzu."
"J.s one kenan?"
"Eh."
"Wace school to?"
"Ban sani ba.."
茒an Jim ya yi ka蓷an jin amsar da na bashi wanda a zatona zai sa kai ya wuce ne amma sai naji ya sake yi mini wata tambayar da cewa.
"Aunty Beenafah kinga karatun da kika koya mini ranar? Wallahi Uncle Daniel ya ce na iya sosai haka ma a islamiyya kullum yanzu ina cikin wa蓷anda suke saurin iya karatu saboda kina duba min"
Ina kan cire hijabina kawai na ce.
"To ka ji da蓷i..."
"To ke Aunty Beenafah duk ya akayi kika iya komai da komai?"
"Ta hanyar koya mana, kamar kai yanda ka ke yi."
"To ta ya ya?"
Hannayena na saka na ri茩e 茩uguna ina kallon sa na ce.
"Ban sani ba Adeel! Ban sani ba na ce. Ka wuce kada ka yi latti."
Na 茩arashe maganar ina mai yi masa nuni da 茩ofa.
"Allah baki ha茩uri."
Banza na yi masa tare da yin gaba na bar shi a nan. Zuwa gobe bai hana idan muka sake ha蓷uwa ya ci gaba da damuna da tambayoyin da har zai kai ga 茩ureni.
A kitchen na samu Aunty Hajjo na gaisheta sannan na tambayeta na ce.
" Ashe Aunty Hajjo Babansu Adeel a gidannan yake yau? Lissafina ya 蓳ace wallahi. Allah yasa kada Aunty ta ji haushin cewa na karya mata doka."
Girgiza kanta ta yi ta ce.
"A'a, ba a nan yake ba, ina ga tafiya Maman Tima tayi shiyasa yake nan...茒auki ga kaya can ki wanke in ji Aunty Labiba."
茒auka na yi naje na wanke mata na dawo da su sannan na wuce wurin aikina.
****
Aysha kuwa, Tun da Husaina ta kira ta, ba su 茩ara cikakken wata 蓷aya a birnin London ba. Daman fa蓷uwa ce ta zo dai-dai da zama domin auren 茩anwar Ahlan Firdausi saura kwanaki ka蓷an wanda bayan auren iyaka sati biyu zuwa uku azumi.
A Abuja suka sauka kamar yan da ta nemeshi alfarma domin a Sokoto ainahin gidan auren su yake sannan shi Ahlan 蓷in 蓷an Sokoto ne har iyayensa a can suke zaune. Shi ne ta ro茩i alfarma akan ya bari su fara sauka nan in yaso daga baya sai ta taho idan bikin ya tashi.
Sanin irin wahala da 茩uncin da ta shiga sai bai yi yun茩urin hana ta ba, sai dai kuma yace mata ba zai je gidan na su ba a yanzu, sai idan sun tashi komawa zai zo ya gaishe su.
Abin da Mummy ta yi har yau ya kasa mantawa, shiyasa yanzu ya 蓷auki hanyar yin baya-baya da Ita kada shima laifin Ayshar ya shafeshi.
Driver ne ya zo 蓷aukarta tare da Humaida da kuma twins.
Tana ha蓷a ido da su ta wani fashe da kuka da gudu taje ta rungume su. Su ma kukan suke kamar yanda ta ke yi tamkar za ta 蓷auke numfashi bama kamar Husaina.
Hannu Humaida ta mi茩a ta janyo Baffa tana fa蓷in.
"Come here my boy...Tun kana baby gashi ka dawo babba"
Mota Hassana ta nufa tana fa蓷in.
"Please every body should hold his tears please.....ku jira idan muka koma gidan sai ku ci gaba."
Motar suka nufa ba tare da kowa ya tanka mata ba suka shige sai gida.
Suna shiga gidan jiki na rawa ta fa蓷a jikin Mummy Zaliha ta fashe da wani irin kuka tana fa蓷in.
" Ki yafe mini Mummy...Dan Allah ki yafe mini, I promise you ba zan 茩ara yin abin da bakya so ba..."
Ta蓳e baki tayi still Ayshar na rungume a jikinta ta ce.
"Ah to! Mutum dai ya ga abin da zan iya, ni ba kamar sauran iyaye ba ce, yaro bai isa yace zai takani ba, 茦aryar sa wallahi, don har yanzu ban haifi wannan 蓷an ba, saboda haka sai ki kiyaye na gaba."
"In sha Allah Mummy zan kiyaye."
Zaunawa suka yi a tare sannan ta janyo Baffa a jikinta ta rungume shi tana mi shi murmushi tana fa蓷in.
"A'ah! Ga mu yau ga mutanen London... Ina Abbanka?"
Cikin jin wani sanyin farin ciki Ayshar ta kar蓳e zancen da cewa.
"Abban shi ya wuce Sokoto Mummy, sai dai idan ya dawo."
"To Allah ya kai shi lafiya. Shi ma ai Hafiz ya kirani 蓷azu ya ce mini in sha Allah satin nan mai zuwa zai dawo ya ganki..."
"Allah sarki! Allah ya dawo da shi lafiya."
"Amin. Ina Salma?"
"Salma tana can na ce Ahlan ya wuce da ita kafin mu zo, ta girma sosai, ina tsoro kada iyayenta su ce za su ri茩eta su yi mata aure."
Mi茩ewa Mummy ta yi tana fa蓷in.
"To idan sun ri茩e ta ba sai ki samo wata ba. Gari da yawa ai maye ba zai ci kansa ba. Ni 蓷aukar mai aiki da kuma korarta a wurina tamkar saka riga da cirewa ne...Ku tashi muje mu ci abinci, nasan matafiya na jin yunwa."
Haka suka zauna suna ta cin abinci, fa蓷ar irin farin cikin da Aysha ke ciki ma 蓳ata baki ne. Duk inda Mummy ta saka 茩afa tana tare da ita a wannan ranar hatta bacci 蓷akin Mummy ta yi shi tare da ita, komai ya dawo mata sabo.
****
Haka muka ci gaba da rayuwa komai na tafiyar mana a hankali dai-dai da matsayinmu, wanda shi ne silar farin cikinmu da walwalarmu.
Yau azumi ya rage saura kwana biyu.
Ina kan mopping Aunty Hajjo ta shigo ta mi茩o mini leda tana fa蓷in.
"Ga Kayan Azumina nan da aka kawo mini tare da an gani ana so."
"Kayan Azumi da an gani ana so? Miye hakan yake nufi to Aunty Hajjo?"
Kallon sama da 茩asa ta yi mini kamar dai wa can lokacin sannan ta ce.
"Wai ni kam, shekarunki nawa ne Beenafah?"
Kai tsaye na ce.
"Sha shida nake da kamar."
"To yanzu don Allah so kike ki ce mini baki ta蓳a gani ko jin kayan see I love ba? Da kayan azumi?"
Bakin gaskiyata na ce.
"Da gaske nake Aunty Hajjo."
Gya蓷a kanta tayi ta ce mini.
"To amma kin san aure ai?"
"Eh, munyi auren Aunty Aysha a lokacin."
"Ok to kamar haka, wanda yake so ya aureni ne ya kawo mini kayan azumi da kuma kayan tsaida shi a matsayin wanda zan aura, an yi mana engagement Kenan, daga haka har mu kai ga yin aure.."
"ohh! Na fahimta yanzu, Allah yasa alheri."
"Amin."
Aikina na je na ci gaba da yi. Bayan na kambala ina shirin zuwa gida sai Aunty Labiba ta dawo, daman yau koda na zo bata nan ta fita aiki.
Bayan mun yi mata sannu da zuwa ta kirani waje ni da Aunty Hajjo ta nuna mana kaya ta ce.
"Ga wannan, kowa ya 蓷auka ya kai gida. Ke Beenafah ga naki can kema Hajjo ga wanda za ki 蓷auka can..."
Godiya muka yi mata sosai sannan na fita har babban titi na samo mai Napep muka dawo gidan na 蓷auka na kai gida cike da jinda蓷i.
Da muka duba kayan ashe gero ne tiya goma, shinkafa tiya biyar,sugar tiya 蓷aya, dabino tiya 蓷aya sai kayan Tea wanda In Sha Allah idan muka lalla蓳a zai 蓷aukemu har 茩arshen azumi sannan da ku蓷i dubu goma.
Cikin nuna zallar farin ciki Ammie ta ce.
"Wallahi Beenafah kar ki ji irin yanda zuciyata ta yi sanyi. Mun gode wa Allah mun gode wa wannan baiwar Allah, Allah ya saka mata da mafificin ya raya mata yaranta ya kuma 茩ara mata zaman lafiya da Mijinta."
"Bari Ammie! wallahi ni ma da蓷i ya hanani ma yin magana. Aunty Labiba mutum ce,Allah ya saka mata da alheri."
"Aunty Beena ni dai bana son Kunu...in dai kina so in yi azumi duka kamar yanda kika ce to ni ba zan sha Kunu ba."
Dariya muka yi ni da Ammie sannan ta ce.
"Kai dai da kunu kam Bahrain akwai tsatstsaurar gaba sosai.."
"茩yale shi Ammie, samun wuri ne kawai, can da da bai ga kayan Tea 蓷in ba ai dole yasha ko baya so..."
Ammie na dariya ta janyo shi jikinta tana fa蓷in.
"Haba Beenafah...Autan na wa kike wa haka? Ya fa kusa sauke al茩ur'ani ga shi kuma zai 茩are primary ya je Js One... Ko don 茩o茩arin nan da ya nuna da 茩wazo ai kya masa abin da yake so ba tare da 茩orafi ba."
"Haka ne kuma Ammie, amma dai hakan ba shi ne zai sa yace ba zai ci abinda yake gaban sa ba."
Nan muka yi ta fira, muka ci abinci sannan Bahrain ya shirya ya wuce islamiyya.
Bayan na kambala sallar magrib, ina zaune da litattafan Bahrain ina dubawa Ammie ta zo ta tsaya a kaina tsawon lokaci ba tare da ta furta mini komai ba.
" Ammie kin yi shiru kina ta kallona..da wata maganar ne?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Beenafah, kinga dai tsawon shekarun da muka kwashe ina ta fama da ciwo, a hankali aka yi ta magani, sai ciwo ya yi kamar ya tafi sai kuma ya dawo baya, komai ya lalace mana, duniya ta yi mana 茩unci da zafi, a hankali sai ga shi kuma Allah cikin ikon sa yasa na samu waraka wanda a yanzu in sha Allahu, ina fata da ro茩on Ubangiji yasa 茩arshen wahalar da za ki yi dani kenan. To Alhamdulillah! Ga shi cikin ikon Allah abubuwa suna ta sau茩a茩a agaremu ba kamar can baya da muka baro ba a lokacin da kuma bamu tsamma ta ba. To ni shawarata a nan ita ce; Idan Ubangiji ya nuna mana bayan sallah lafiya, ya kamata ki koma islamiyya. Karatun boko ba dole ba ne kuma ba addini bane, abu ne mai kyau wanda yin sa yake da matu茩ar amfani idan an samu dama da lokacin yin sa. Amma idan damar hakan bata samu ba, sai a ha茩ura. Tun da har na samu sau茩i haka, ya kamata ki ha茩ura da bokon tun da kinga yanda rayuwar ke tafiyar damu, sai ki koma islamiyya, idan kin tafi kin gamo aikinki kin dawo 茩arfe biyu, ki yi duk abin da zaki yi ki gama 茩arfe uku ki wuce wurin neman ilimi, domin shi ne gaba da komai kuma shi ne rayuwa ko ince shi ne abin da aka gina 蓷an Adam domin shi."
Cike da jinda蓷in maganar da tazo mini da ita na ce.
" In sha Allahu yanda kika ce haka za'a yi Ammie. Allah ya 茩ara miki lafiya yasa mu dace."
"Amin."
"To amma kuma Ammie...barinki ke ka蓷ai wuni 蓷aya zungur..."
"Haba! Kar ki damu da wannan, ke da ke barina tun 茩arfe tara ko sha 蓷aya na safe kikai 茩arfe biyu ko ma fiye da haka, mi zai sa ki damu don kin fita neman ilmi. Yanzu ga Maman Fakiha a kusa dani, sannan kuma ga Jafaru da Hamza dake yawan shigowa akai-akai sun 蓷aukeni Uwa suna kulawa dani, suna yawan shigowa muna fira da su ba ma kamar Jafaru. Saboda haka kar ki damu in sha Allah lafiya za ki ri茩a dawowa kina tarar da ni babu abin da zai sameni."
" Shi kenan Ammie, Allah ya nuna mana."
" Amin Yah Allah. Ta shi ki ji茩a mana gero tun da yanzu kada a manta gobe a marka蓷o shi da wuri a Tace shi."
****
Unguwar Gwaza,
Gusau, Zamfara State.
Nigeria.
Babban gida ne mai yalwa wanda ke 蓷auke da doguwar verandar tare da jerin 蓷akuna. A gefen yamma, manyan Bayika ne guda biyu yayin da gefen gabas ke 蓷auke da babban madafar abincin gidan baki 蓷aya. 茦asa ce tur蓳aya ke malale a farfajiyar gidan wacce tayi fes sakamakon sharar da ta samu, ko'ina ya yi zanen tsintsiya ya yi kyau ga wata iskar da ke ka蓷awa tare da babban Iccen Mangwaron da ke farfajiyar filin gidan.
Kwance yake ya kinshigi蓷a da jikin bishiyar Mangwaron tare da lumshe idanunsa da alama bacci yake yi.
Umma ce ta zo ta tsaya a kan shi cike da mamaki a fuskarta ta ce.
"ASHIRU... Ashiru..kai Ashiru!"
Da sauri ya zabura yana mai share hawayen idanunsa ya kalle ta murya a sanyaye ya ce.
"Na'am Umma.."
Ha蓳a Umma ta ri茩e tana 茩ara girmama wannan al'amari na Ashiru ta ce.
"Au! Wai Kuka kake? Lallai Ashiru! Kai shikenan ba za ka ha茩ura ba kenan? Sai kace ba musulmi ba..."
Bokiti Ayya ta ajiye dai-dai inda suke tsaye suna maganar itama ta ce.
"Hmm! Ni wallahi tun da na yi tozali da su zuciyata ta cika da tababar cewa anya wa蓷an nan mutanen bil'adama ne kuwa? Sai ga shi a dare 蓷aya zargina ya tabbata, labarin su ya zama tamkar an yi ruwa an 蓷auke."
Cike da jin wani irin zafi a 茩o茩on ransa ya kalli Ayya ya ce.
" Ni dai dan Allah Ayya ku daina irin wa蓷an nan maganganun, wallahi bana jin da蓷insu sam! Beenafah yarinya ce 茩arama,kuma ita take 蓷auke da nauyin kula da mahaifiyarta da 茩anenta, sannan su 蓷in Mutane ne kamar kowa..."
Jinjina kai Ayya ta yi ta ce.
" To naji! Yanzu sai ka fa蓷a mini ina suke?....Ka tafi neman su an ce ba bu ma wasu masu kama da su da suka ta蓳a zama gidan, har su Fa'iza sun tafi amma kuma dai maganar 蓷aya ce ba'a san wasu masu kama da sunan ba. Wata 茩ila kuma sun koma garin su tun da dai kace su ka蓷ai ne su uku 茩wallin-茩wal..."
Cikin nuna 蓳acin rai Umma ta ce.
"Ai sai ya zauna nan ya yi ta 蓳atawa kansa lokaci! Tun da dai ba ya jin shawara. Tun da ka kasa samun su ka ha茩ura mana! Ka tashi ka shirya ka wuce Kano, yan da ka 蓷ebo 茩arfar nan ba tare da neman izinin sa ba ka tashi ka shirya ka koma. Tun ranar da ka iso garin nan ya kirani ya sanar mini cewa bada izininsa ka taho ba, saboda haka ka tashi ka koma ka ji na fa蓷a maka...abu tun ana na marmari har an dawo na 蓳acin rai, haba!"
Ta shi ya yi kawai ya 蓷auke ledar da ke gaban sa ya nufi 蓷akinsa dake 茩ofar gida ya bar su Ayya nan suna hala茩o茩o.
Tun ranar da wayarsa ta lalace ya kaita gyara akace gyaranta kusan dubu talatin ne, hakan yasa ya kira Babban Yayansa dake Kano, Yaya Nura akan cewa ya turo masa da ku蓷i wayarsa ta lalace, shi kuma Yaya Nuran sosai ya hau shi da fa蓷a yana fa蓷in bai ga amfanin Keke-napep 蓷inda ya saya masa ba, tun da in dai lalura ta wuce dubu goma baya iya magancewa kansa ita ko kuma wani na cikin gidan to ya tattara ya dawo kusa da shi ya shiga shago shima, idan admission 蓷in ya tashi daga can ya ri茩a tafiya. Daman tun da ya gama N.C.E yake zaune zaman jiran Admission na zuwa jami'a, ganin yana zaune a banza yasa yayan nasa ya siya masa Napep domin ya dogara da kansa kuma ya ri茩a taimakawa iyayen su da '拼an wasu lalurori na yau da kullum. Jin babansu da ma sauran mutanen gidan sun goya baya, hakan yasa dolensa ya shirya ya washegarin daren da ya kira Beenafah a waya. Bai 茩ara shiga tashin hankali ba sai da ya yi ta kiranta bata shiga abu kamar wasa.
Tunda ya tafi da 茩yar ya ga wucewar wata 蓷aya lafiya, haka ya ro茩i Yaya Nuran alfarma akan ya barshi ya zo gida yana da uzuri. Tun da ya sauka Gusau ya dire jakarsa ko minti 蓷aya bai 茩ara cikin gidan ba ya fita zuwa gidan su Beenafah. Sai dai kuma! Bai san cewa allon 茩addara ne zai juya da shi zuwa wani bigire ba bayan ya sauka a 茩ofar gidan na su.
Haka ya dawo tamkar wani mutum mutumi jin cewa wai babu ma wasu masu kama da wannan sunan a cikin gidan. Tamkar wani mai ta蓳in hankali haka ya dinga musu da mai gadi yana neman kai masa duka. Haka ya 蓷auki tsawon lokaci suna dragging 茩arshe dole dai ya bai wa kansa magana ya juya ya koma gida da tunanin cewa wata 茩ila suna asibiti har yanzu ba'a ba su sallama ba. Daman tun farko da za su tafi yaso ya bi su Sokoton Babansa da Umma suka ce ba su amince ba.
Haka ya share kusan sati yana zarya gidan su amma magana 蓷aya ce dai cewa babu wasu mutane a gidan ma su suna Beenafah.
Haka ya tattara ya koma garin Kano zuciyarsa cunkushe da ba茩in ciki da damuwar rashin samun su Beenafah. Kullum kwanan duniya sai ya kira Su Ayya cike da jaje suyi ta aikin ba shi magana mai tausasa zuciya. Sannan kullum su Fa'iza cikin zarya suke wurin neman su amma babu wani labari.
Haka ya rayu tsawon wata hu蓷u cikin damuwa na rashin su Beenafah, daga 茩arshe shi ne ya sake biyo hanya ya dawo 蓷a蓷蓷ake da kayayyakin siyayyar da ya jima yana yi musu musamman Beenafah, ba tare da ma Yaya Nuran ya sani ba.
Shi dai wa蓷an nan mutane sun zame masa 茩addara a rayuwar sa, da yana zaune hankalinsa kwance babu abin da yake damunsa, a lokacin da ya same su sai ya ji duniyar sa ta 茩ara fa蓷a蓷a, ta yalwata da wani wadataccen farin cikin da shi ka蓷ai yasan mi yake ji dangane da Beenafah da ahlinta. Sai dai kuma! Daga lokacin da ya rasa su shikenan ya gigice ya 蓷imauce, rayuwa ta yi masa 蓷aurin kazar kuku. Yarinya 茩arama! Mai 茩aramin tunani; duk da cewa bai san komai dangane da rayuwar su ba, yasan tabbas daga action 蓷inta tana da bu茩atar matallafi....Tausayinta yake ji, matu茩ar-matu茩ar tausayinta yake ji har ma Ammien da Bahrain. Kuma in sha Allah muddin ba numfashinsa ne ya yanke daga gangar jikinsa ba, har abada ba zai daina neman su ba.
Bayan Umma ta hasa mishi wuta, dole uwar na茩i ce za蓳i, haka ya tattara ya sake komawa Kano.
****
Tun da muka shiga azumi, tare muke aiki ni da Aunty Hajjo a kitchen bayan kowa ya kambala aikinsa da zai yi na yau da kullum.
茦arfe biyu muke farawa wanda watarana zuwa biyar mun gama kambala komai. Kuma tun da aka fara azumi komai na ci da sha idan mukayi sai Aunty Labiba ta bamu shi, wanda kayan amfanin da ta bamu iyaka ga Suhr muke amfani da su domin komai tana bamu.
Azumi na goma sha biyar ta kiramu ta bamu Atamfa bibbiyu da shadda 蓷a蓷蓷aya da ku蓷i naira dubu talatin-talatin ta ce kowa ya je ya yi 蓷in ki ya sai takalmi.
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍