Free chapter · Read without an account
3
by Hajarah · ABUNDA KA SHUKA…!
Are we ready for a polygamous home? If yes....! Meet Alhaji Ibraheem's household.
It is a polygamous home, saboda haka sunada dan yawa dai haka, kowa na zaune cikin second palon Abba not the main one, except shi Abban, Naainah, Mamita da Affan dan sai ya iya sati bai shigo gidan ba dan ba'a nan yake zaune ba, shi bai ma girma cikin gidan ba balle "Sufyan zai koma gobe, and-" sai kuma Kamal yayi shiru ganin Bibeey na hararan sa "Forget it!" Sai kuma ya hade rai "Toh ae duk abunda ka yanke hakan za'ayi tunda dama kaika saba" Ummu ta sako baki dan karya ayi magana in suna waje itada Mama basu amsa ba "Sufyan zai koma duba Abba's company, if not in two days then cikin week innan" ya karasa yana maidawa Bibeey hararanta "Kamalu badai rashin kunya ba, kuma kai karda qannen ka suyi maka koh?" Dan siririn tsaki yayi dan wannan matan tanada tarin matsaloli "Zaku wuce Umrah keda Maa Kileey cikin satin nan kuma" ya fada dan sending nata far na kwanaki su huta suma "Alhamdulillah" Jadwah ta kama kirji dan mugun matsa musu wannan tsohuwan take "Uwarka ce zata wuce umrah bani ba" hade rai yayi Muhseen yace "Haba Bae, how could you insult Mum ah gabana?" Washe baki tayi dan duk gidan ba wanda takeso kaman Rafynaah da Muhseen, ba wanda ta tsana kuwa kaman Affan da Kamal "Toh Afwan, kasan ance dan kuka mey jawa uwassa jifa, toh Kamalu ne" yace "For the goodness sake my name is Kamal. Tafiya kuma ya zama dole" yana fada ya tashi "Tasleem meet me outside please" ya fada kafin ya juya zai fita "Alhaji zai dawo cikin gidan nan. Ae inda uwarka ke zaune bazaka tashi ka bata waje bata gama magana ba, amma saboda nika rainani baka daukeni a bakin komai ba tashi kayi ina zaune" Mama tayi maganan harda hura hanci, koh kallonta baiyi ba balle tasa a ranta zata samu amsa "Rafynaah na gidan nan kuwa?" Ummu da bata kaunan a zauna lafiya ta fada and as expected Kamal ya juyo yana bin yaran gidan da kallo "Ina Rafynaah?" Yayi tambayan yana kallonsu hakan yasa Tasleem komawa ta zauna itama "Toh in ma batanan sai mey?" Bibeey ta sauko baki aiko ran Ummu yayi fari dama burinta kenan, dan siririn tsaki yayi ya kauda kai "Fynaah is with Yaa Affan if am not mistaken ya shigo gidan dazu" Zaynab ta hade masa karya without knowing the perfect answer dan yaji yanda Fynaah take da mugun matsala, sun baro Fynaah makaranta tun dazu wai Aryaan yazo "Can you keep your mouth shut and lay some truths? Affan ne zai fita da Rafynaah? You are insane" in fa ran Bibeey yayi dubu Kamal ya bata shi "Yaa Kamal, eh Rafynaah batanan, but maybe-" kafin Mariam ta karasa ya tsareta "What says the time?" Ya tambayi Sufyan dake gefe ya ware kai "Few minutes to dinner, she might be having something important" Muhseen yayi saurin karban maganan kafin Sufyan yayi hakan "Aikin banza! Rafynaah dai kunsan koh kasheta kukayi gobe saita maimaita" Mama ta fada tareda jan tsaki ah karshe "Rafynaah tana tareda Yaa Affan" for the first time Tasleem ta amsa nan fa Bibeey taja tsaki, itafa apart from Rafynaah da Muhseen da takeso toh bata kaunan kowa gidan saidai na wasu yafi na wasu, sai kuma Yazeed daya fito daga cikin erta, toh shima yana ganin soyayyah "Kaidai Kamal anyi dan rainin wayo, damey Tasleem in tafi Mariam toh da zaka wani zage ka buga mata tsawa amma Tasleem tayi magana kayi shiru?" Mama ta fara bala'i, Ummu kam ita ta hada toh tana gefe tana enjoying show din "Bata fita da komai ba saida makirci" Ummu ta amsa sai kuma ta bita da harara, sauke fuska Tasleem tayi dan tana zaguwa cikin gidan ba laifi "Can we?" Ya bada hanunsa wa Tasleem kawae Bibeey ta sake baki, tashi tayi ba tareda basa hanun ba ta fita "Mijin tace" Bibeey ta fada tana binsa da harara "Badai za'a aureki ba" sake tsuke fuska tayi jin abunda Kamal yace "Inada miji nayi mey da mijin tace?" Muhseen dai shiru ya mata "Tasleem over y'all" yana fada ya juya shima ya fita, duk binsa da kallo sukayi saidai ba wanda yayi magana dan sunsan koh sunyi qannen Kamal bayansa suke bi, yana musu fadan dai amma suna maqale dashi dan Allah yanada saukin kai "Duk wanda yaga bazai iya ba.. ya iyace mu koma yanda muka fito" Mariam na fada ta tashi, eh da Bibeey takeyi kuma Bibeey tasan da haka "Kinyi ma uwaki" kallonta Mama tayi bata amsa dan duk cikin matan Abba ita Bibeey tafi so yasa take abunda taga dama, toh yanzu ma tasan zagin bahar zuci bane "Hello?! Meet the favorite human of the house" Zeezee da neman magana ta fada ganin Affan ya shigo, shi kadai yayi sallaman sa dan ba wanda yaji "BigMama. Been missing you" ya karasa ya zauna kusada kafan Ummu nan fa Bibeey ta dauke kai, inda ta kwantar da hankali ma shi ba gaidata zai ba "Lafiya lau Adeel. I missed you more" harda shafa kansa, and he just smiled, mostly in ana so aga dariyan sa toh sai yana tareda Ummu koh Mamita, ita Mamita abokiyar fadan sane suyi su shirya "Mama kuna lafiya?" Kauda kai itama tayi, toh inda sabo kowa na gidan yasan halin Mama ae "Rafynaah na gidan nan kuwa?" Ummu ta sake tambaya ganin bai shigo da ita ba, dama tasan basu tare kawae an fada a kare Fynaah ne "Tana ina?" Ya dago ya tambaya dan tasan definitely zaiyi "What? Rafynaah na cikin gidan nan fa" Muhseen ya amsa yana juyawa in pretense ganin reaction in Affan "Toh kai uban wani ke tambayan ina kake?" Bibeey ta chapke "For the goodness sake ban sako ki cikin magana na ba, that girl is- "Stubborn right?" Dan sirrin tsaki yayi ya tashi "Ina Yazeedu na?" Bibeey ta tambaya ganin ya tashi, bai ko kulata ba yace "Goodnight" yana fada yace "Erm.. Mashidah, take my supper to- "Toh dan iya, ba wanda yaci abinci balle kai kaci. Alhaji bai dawo ba tukunna" bai sake magana ba ya fita dan ya kula people of his house are trying to annoy him. Wajen Mamita ya wuce dan still Naainah taqi masa magana mey tsayi "Ina yini?" Kallonsa ta dan tsaya yi kafin tace "Toh badai kace mun sake fita zakayi ba?" Girgiza kai yayi kafin ya zauna "I am spending the night here" dan ajiyan zuciya Mamita ta sauke "Mey Naainah tace akai?" Girgiza kai yayi "She wants me here completely kuma tasan hakan bazai yiyu ba, people of the house are annoying" tabe baki Mamita tayi "Amma kaji abunda naji?" Girgiza kai yayi "Kasan dai Alhaji yace koh aure kukayi saidai ku cigaba da zama cikin gidan nan koh?" Dan tsayawa kallon Mamita yayi kafin ya fara dariya "Dole ae! Nikam ka raina ni kuma duk maganan daya fito a bakina karyane" saurin girgiza kai yayi "You will never be wrong, kawae dai nasan kin cike wasa" dan murmushi kawae tayi, zatayi magana tayi shiru jin kamshin turare and some sound na takalmi "You wait, and come here" ya fada dan definitely Rafynaah ce, ita fa karshen iskanci da turare take yawo. Ba musu ta karaso yanda suke tana sunkuyawa, kokarin cire takalmin ta rikesa ah hanu ta fara ganin yanda ya hade rai, tasan bazai daketa ba for sure dan Affan bai zauna gidan ba balle yayi duka amma tasan baida mutunci tsaf zaisa a mata dan banzan duka "Ina yini?" Ta gaidasa tana kokarin yin ladabin karya ya tsaidata "Daga ina kike?" Sosai hankalinta ya tashi ta rasa ta ina zata fara sai kuma ta kalli Mamita "Erm.. Yayar qawata ke biki Yaa Affan. Na tambaya kafin na fita. Ka tambayeta" tayi nuni da Mamita kafin ta zauna kusa da ita, sarai ba abunda ta fadawa Mamita dan ta fita Mamita ma neman ta take dan duk sun dawo makaranta banda Fynaah, amma tasan no way out dole Mamita zata rufa mata asiri "Toh wae karya zatayi in bata tambaya ba tace ta tambaya? Gaskiya Affan bansan hakan nan" Mamita ta fada ganin ya bita da kallo, dama Affan da Mamita sun saba daily fights "Mamita kina taking side" tace "Yo toh in barta ku kasheta? Yanzu na barka saidai ka kawo mun garinta ah tankade zaban laushi" girgiza kai kadai yayi dan shi yaushe ma ya taba wata yarinya cikin gidan "Try putting one large veil sometimes" bin jikinta da kallo tayi kafin tayi murmushin dole ta tashi "Yaa Affan are you till morning?" Gyad'a kai yayi kafin ya kauda kai. Ihun da sukaji ne Mamita ta tashi da sauri Affan yabi bayanta "Na tambayi Mamita" tayi saurin komawa bayan Mamita ganinta, itama Mamita ta kwaso kafa zatayi bala'i amma ganin Kamal ne tayi shiru, tasan yanzu haka rashin kunya Fynaah taso masa yasa ya doketa dan shi da wuya yake duka, ga Muhseen nan shi yake sawa ya musu dan banzan duka, Sufyan kam ma koh ba'a fadi ba dukan fitan hankali yakewa Rafynaah "Toh yanzu dukan na menene?" Ta dai kare tayi magana "Niiice mey laifi Mamita" tayi saurin karban laifinta, murmushi Kamal yayi after seeing her reaction "Toh ae sai ki cigaba da taurin kunne, kinga suka karyamun ke kap cikin su bamey aurenki dai kin sani" tayi maganan tana kokarin fita palon "Go get ready and meet us for dinner" dan sunkuyawa tayi ta wuce "Evening!" Affan ya fada tareda basa hanu su gaisa "Komai na Bibeey is ready, I can't withstand that woman" Kamal ya fara wa Affan bayani kafin suka fita, wajen Naainah suka koma dan wajen za'ayi dinner kuma har an taru "My love" Kamal yayi saurin karasawa ganin bright face nata amma tana ganin Affan ta tsuke fuska "Ina yini. Been missing your tasty cookings" Mashh tace "Then congratulations Yaya, it was cooked by Isabell" dan yatsina fuska yayi "Shedana iri da kala. Toh naga koh ciki zaka koma ba cikinta zaka koma ba" ita kuma iya fitina Bibeey ta amsa "Lord save me" kadai yace ya nemi waje ya zauna, Affan har lokacin na tsaye "A seat reserved for the house heir" Tasleem taja masa seat "Yara har guda nawa cikin gida a wani dake a ciro Affan kice heir. Munapuka" Mama ta dannowa Tasleem zagi, ita batada yaro namiji toh kan wani dalili za'a wani ce ga heirs bayan duk gida magada ne? "Karki kara zagar mun 'ya" tun wuri Naainah ta tsaidata, Bibeey dai bata amsa ba tukunna ta fara binsu da ido tana neman Fynaah "Ina er albarka?" Ta tambayi Mariam dake gefe "Bata karaso ba" ta bata amsa ah takaice dan ita bataga Fynaah ba "Raheem- "Abdulraheem!" ya gyara mata tareda bata dukkanin attention nasa, Naaynah kadai sai Abba sai kiransa da Raheem ya amsa dan ba yanda zaiyi yana correcting nasu with every single call, shi yafi so ah kira sunan in full "Ka dubo mun er albarka" Zeezee tace "Wow! Upon all his younger ones, shi din dai" nan fa ta dago magana aka fara kowa da abunda yake fadi "Excuse me" Sufyan ya sako baki "I would be of help" yayi saurin tashi "Yaya da kanka?" Mashh tayi saurin tashi itama "Adeel will refused to, but Sufyan would never- "Shuttup Armaan" Affan yayi saurin tsaidasa "Armaan mey haka?" Ummu tayi saurin chapkewa jin Affan ya amsa, ae karya itafa tana waje ace ran Affan ya baci ne, taya za'ayi ya cigaba da respecting nata? Bibeey dai na gefe tana motse baki, ita in an tambayeta dalili tayi aike wa Affan ya maidata banza. Sufyan zai bar wajen Fynaah ta shigo "Er albarka" Bibeey ta fara ganin Fynaah, side smile Jadwah tayi dan tasan more is coming indai Bibeey na waje, sai ta nemawa Rafynaah duka kafin hankalinta ta zai kwanta "Kai Kamalu tashi ka bata waje ta zauna" ihu Fynaah tasa ta matsa baya jin Bibeey na neman nema mata bala'i "Sitttt Yaa Kamal" tayi saurin fada amma koh kallonta dama bai ba daga ita har Bibeey'n "Ga Abba" ta fada kafin ta nemi waje ta zauna kaman muminar gaske "Sannu da zuwa" aka fara jera masa sannu "Na sameku duka lafiya? Allah yayi albarka" ya fada sannan ya zauna "Affan yaushe a gida?" Ya fada da cheerful expression dan sosai yakesan ganin Affan ya shigo, Bibeey che bataso yasa Affan ya fita hanyanta "Kayi masa magana ya dawo gidan nan Alhaji. In kuma ba haka ba saina bisa chan" Naaynah ta fada ah dame dan yanzu rashin zaman sa gida ya fara damunta, lokacin suna Abuja ya dameta saidai ba sosai ba tunda ah one of Abba's houses yake zaune amma Abba bai bashi gida a Maiduguri ba, kullum ya shigo Maiduguri yana hotel, toh ae duk abunda akace kansa ma ya zauna. Kallonta kadai Abba yayi sannan ya kalli Affan daya sauke ido "Let's eat and talk after that" duk shiru wajen yayi, Bibeey da Abba kadai suka fara cin abinci kowa ya cigaba da damuwan sa, daga masu chatting kasa-kasa kar aji muryansu sai masu amfani da waya, and within 10mins Abba ya tashi "Alhamdulillah. In kun gama ina neman ku" daga masu okay sai toh sai sure! Kowa dai da yayin amsan sa. Yana bari wajen kowa yabar abunda yakeyi suka dau spoons "Ban riga na gama cin abincin ba" Bibeey ta fada ganin kowa yayi shiri, ajiye spoon Naainah tayi tasan neman maganan Bibeey ya motsa "Wait! So you mean to tell me kema so kike a fara highlighting naki koh mey? People of my house are starved already kuma kike zancen ah jira ki gama? O- "Affan!!" Naainah ta tsaidashi "Kar ma yayi shiru, maras kunya. Ci abinci kede kinji" ta fada ganin Rafynaah na kallonta, sake sauke ido Rafynaah tayi dan itane Bibeey da Affan zasuyi fada ta shiga ah mata shegen duka? No Rafynaah nasan jikinta.
Duk sun gama kaman yanda Abba yace kuwa sun same sa "Affan zaka dawo gida kaman yanda kowa yake gida" Abba ya yanke hukunci, saurin sa hanu Affan yayi cikin kansa, Bibeey dai na gefe na kumbure-kumbure "My everything is in Abuja Abba, and you supported me, not only support you lead me to the way so why now please?" Shiru living room in yayi suna jin Abba da Affan na magana "I want you in Borno and in this house completely dan haka Bibeey keso. Tana san ahali waje guda" kallon Bibeey yayi and Rafynaah is doing the same "Kuma koh aure kukayi cikin gidan nan zaku zauna" tarin da ba niyyan Sufyan ya fara jin wannan zance "Go beyond cough Sufyan but my words remains unshaken" Abba ya fara ganin reaction na dukkan su "Duk abunda kace hakan za'ayi" ya amsa without a long silence, yasan tunda wancan matan ta sako baki Abba bai changing magana at any means "Kaman yanda nace Kamal kuma ya fadi nasan ya fadi. Tafiyan Sufyan na nan" dan yatsina fuska yayi dan fa good 5days baiyi shi cikin gidan ba gashi za'a ce ya koma, saida ya kalli Ummu tayi masa alaman ya amsa kafin yace "In Shaa Allahu Abba" dan murmushi Abba yayi kafin yace "Akwae mey magana?" Fynaah tayi saurin ce "Abba dama-" sai kuma tayi shiru ganin Affan ya zuba mata ido "Fada mana, kowa na fadin ra'ayinsa ke ace bazaki fadi ba?" Bibeey ta goya mata baya "Nace or you buy me a car? I wanted requesting tun ba yau ba" kafin Abba ya amsa Bibeey ta amsa "Gaskiya ya kamata kasai mata motan nan, duk qawayenta fa motan garesu. Da sun zo zaka ga sun fara dago mata key suna mata hali" girgiza kai kadai Mamita tayi jin Bibeey, ba Mamita kadai ba kowa bin Bibeey da Fynaah da kallo suke "Haba Bibeey! Kap matan gidan nan waye mey mota balle Rafynaah tayi mota? Nan Mariam da Tasleem basu ne gaba da ita ba? Toh Rafynaah awa kuma?" Gyad'a kai Abba yayi alamu dai ya gamsu "Toh banda rashin kunya ma su manyan nata basuce ga abunda suke so ba sai Rafynaah? Su drivers in da aka daukan muku ayi yaya dasu?" Harara mey jida lafiya Fynaah tabi Mama dashi "In anzo siya mata motan sai ku hana. Kasai mata mota" Bibeey harda zagewa ta bada umarni. Dan shiru Abba yayi kaman mey tunani, indai Bibeey ta cigaba da haka toh yanzu duk hukuncin da zai yanke kan Rafynaah bazai yiyu ba kenan? Banbancin da take nunawa ma yayi yawa "Za'ayi yanda kikece Bibeey" ya fada ganin har lokacin ta zuba masa ido "Gida duk haters. Baku qaunar cigaban dan uwan ku" Fynaah ta fada ganin Abba ya tashi wajen Kamal da Affan sun bisa, zata sake wani rashin kunya Mariam ta make mata baki "Don't-" Muhseen yayi saurin tsaidata ganin tana kokarin sake wani rashin kunyar "Dole kice mana haters ae tunda dazu mun dawo school mun barki da kato amma ba wanda ya fada" Jadwah ta tona mata asiri "Munapuka. Jaddoh niii? Allah ya is- "C'mon shut your mouth up. Gaskiya take fadi?" Sufyan ya tambaya da mamaki, juya masa ido tayi dan tasan dalilin sa na tambayoyi shi kam, ace Eh ne yayi mata duka dan aikin kenan kullum ba progress "Wlh wani cikin ku ya sake ya taba mun yarinya nida shi cikin gidan nan. Duk ido kanta?" Mamita ta chapke dan harda ita kesa Fynaah yin wasu abun, dan siririn tsaki Sufyan yayi ya tashi wajen dan dama Kamal da Affan sun bi Abba "Goodnight Bibeey. And my Mums" Rafynaah tayi saurin fada sannan ta tashi ganin Jadwah ta fice palon tabi bayanta "Ke tsaya!" Tayi saurin shan gabanta ta tsaya "Yanzu ku ah duniya bakusan rufawa dan uwa asiri bako?" Rolling eyes Jadwah tayi irin koh ah jikinta "Ki barta, bakin ciki take an baki mota" Zeezee da ta biyota ta fadi "Ah toh da sauran kallo indai ni zakiwa bakin cikin naki" Jadwah tace "Point of correction Zeezee! Ba'a riga an bata motan ba tukunna. And put in mind cewan in za'a kawo biyu za'a kawo. One for Jadwah of course" tayi nuni da kanta "You are bitter Jadwah. Follow me Zeezee" kawae Rafynaah tayi gaba abunta, ita akwae wanda ya isa ya daura mata damuwa ne a gidan "Yau ba game right?" Suna tafiya Zeezee ta tambaya "Toh Adda Mariam zaki tambaya ae, as per the table akwae amma maybe yana bukatan new design, another member of the house is back" tace "Toh zamu samu Yaa Muhseen yayi mana math or you join us?" Itafa Fynaah tanada abunyi ne, Zeezee kuwa ganin Fynaah zatayi mata shiririta sukayi separate ways. Fynaah na shiga wajen Mamita ta hadu da Sufyan palon dake sama, kauda kai tayi zata wuce yace "Ah cikin dokokin gidan nan kin sake karya uku cikin kwana biyu, kuma kin fi kowa sanin bamey yin hakan sai ke" shiru ta masa ta fara fiki-fiki da ido "Take note!" ya warning nata zai wuce taja tsaki ta zata ya gama wuce wa kawae taji slap, bata kula ba yayi ball da ita dan kaman jira yake daman shi ya karya musu Rafynaah ya aje gefe "Owch" tayi saurin rike baya dayan hanun kan fuskanta dan kukan ya kasa zuwa, belt taga yana kokarin cirewa tasa ihu "Ban sakewa-" bata gama rufe baki ba ya zuba mata "Shuttup" ya fada kafin yasa kafa yayi ball da ita tabi steps in ta fara gangarewa...
~~*~*
It's a peaceful living room dan ba za'a ce akwae mutane a ciki ba saboda yanda yayi shiru. An elderly man zaune ya zuba tagumi sai matan sa dake gefe wanda ita ba alaman damuwa tattare da ita, sai wani lad dake gefe rike da waya "Allah dai ya shirye ku, kai ace er uwarka bata dawo gida ba haryanzu amma hankalin ka kwance, ke kuma dama ba amfanin miki magana" ya fada da bacin ran ganin I don't care attitudes in da suke basa, kallon sa matan tayi ta tabe baki "Sabon abune ne a wajenka? Yarinya dai na fada maka lokacin dawowanta 10pm ne, amma baka yarda ba. Allah yayi ka gani da idon ka yau" ta fada tare da kauda kai "Nifa Haleemah bansan irin karyan nan, yarinyan musulmai kuma 'yata ce zaki ce tana raba dare a waje? Ni bansan karya" ya fada rai bace "Allah Daddy dagask-" kafin yaron ya karasa ya daka masa tsawa "Shut up stupid boy, waya tambayi ra'ayin ka?" Saurin chapke maganan tayi "Aa Abu Sadeeq, laifi dai duk naka ne saboda haka-" tsaki yaja hakan yasa tayi shiru "Kede Allah wadaran wannan halaye naki, dadin abun ke kika haifeta itama, yau inda wata ne ta haifa ta baki ki raina sai kiyi bayanan naki" tace "Eh, nina haifeta amma bani na b'ata taba" Sadeeq jin daily fights zai fara ya tashi zai bar wajen dan inda sabo an saba saidai Mahraa batayi laifi ba, shi Daddy haryanzu yaki yarda yarsa ke yawon dare "Ka duban waje, kace kar su yarda su hana kowa shiga dare baiyi ba ance 'yata bata shigo ba tunda sharri aka soma mata, zanga ta yanda zata fito ae" toh Sadiq yace yayi waje kaman yanda aka fada masa, yana fita tana shigowa compound in gidan hakan yasa ya tsaya ganin waye ya sauketa, bai gane waye ba dan koh securities din ba tambayoyi suka tsaya yi ba hakan yasa ya jira ta karaso "Ke kuma daga ina kike?" Har zata wuce ciki ta dawo baya jin maganan Sadiq tareda yin side smile mey cike da takaici "Sadiq? Sa'ar kace ni?" Ta fada tare da juyawa ganin wanda ya sauketa ya juya koh Aa, tsaki Sadiq yayi dan yau bai jin tashin hankali badan haka gaban saurayin nata zaisa taji kunya "In zaki wuce ki wuce" shiru tayi tana biting finger ganin motan yabar gidan "Waye shi wancan in?" Ya kuma tambayan ta ganin motan ya fita, sharesa tayi zata wuce ya tsaidata "Daddy na ciki" saurin komawa baya tayi "Yayan Hanny ne, ina gidan su tun dazu, yaga nayi dare yace zai kawoni" ta hade masa karya tun wuri jin Daddy nan, duk zaton ta Sadeeq zai tona mata asiri ne Daddy yabar bata yarda "Mahraa mana, kowa lada yake amma banda ke" rolling eyes tayi "In a gidan ku ake raba ladan in an bani ka kwace, maras kunya kawae" kafad'a ya daga yaja hancinta kafin ya koma ciki ta bisa da harara, irin rainin da Sadiq ya mata Allah ne kadai ya sani, dan karamin tsaki tayi kafin ta zaga ta baya, harta shirya karyan da zatayi. Sadiq na komawa yace ae ance masa Mahraa ta dawo tun dazu, girgiza kai kadai mahaifiyar su tayi tasan rufa mata asiri Sadiq yayi "Dama nasan karya kika shirya mata saboda bata ranki, jeka kirata" Daddy da bai gama yarda ba ya fada, da toh Sadeeq ya amsa ya wuce sama, and within 5mins sai gashi da Mahraa, ba wanda zaice daga yawo ta dawo dan nightgown ke jikinta sai hamman karya da take "Kar dai kice mun dagoki yayi ah bacci" Daddy ganin yanayin ta ya tambaya "Bacci nake Daddy, kawae yazo ya tasheni. Naji kaine ma yasa na fito" ta fada tana squeezing eyes "Mey karya Mahraa?" Barin abunda takeyi tayi tana kallonta "Haba Mummy Sadeeq, in nayi miki sai nayi wa Daddy? Ha'an" ta fada harda juya ido dan raini kam tayiwa Mummy shi iri da kala ma kuwa, saitan bakinta Sadiq yayi ya kwadeta kawae tasa ihu "Allah ya isa maras kunya, Daddy ka gani koh?" Aka bar Daddy da cewa "Ah gaba na? Sadeeq da hankalin ka? Ba Yayar ka bace?" Shiru Sadeeq yayi bai amsa ba "Toh ni ba'a gaban naka take zuba mun rashin kunya kana bin bayanta ba?" Yace "Miye abun rashin kunya dan tace ba karya takeyi ba? Je kiyi baccin ki Mamana" barin kama bakin tayi jin abunda Daddy yace "Kuma Sadeeq bai sake kwana daya cikin gidan nan, dole mutum ya koma makaranta" tana fada ta wuce abunta "In kene ubansa saiki maida sa ae" Mommy ta amsa "Babana je ka huta abunka" da toh Sadeeq ya amsa yabi Mahraa daki, tana kwance kan cikinta ta shafe fuska da wani night mask tana waya, jin an shigo ne ta kashe wayan tareda juyowa ganin Sadeeq taja tsaki "Wai mene ne ah duniyan nan mutum cikin gidan su baida sirri?" Ta fada cikeda jin haushin make bakinta da yayi dazu, gashi ba iya ramawa zatayi ba, dan sa hanu yayi ah kai "Erm.. Yaa Mahraa daman-" kafin ya karasa ta diro kan gadon "Allah kana karasawa zan zabga maka mari, wace Yayar taka? Nine zan tsaya ka cuceni?" Ta fada tana nuna kanta "Oops sorry, zan dawo in kin huce" yana fada ya karasa wajen vanity ya fara bude-bude, shi in an tambayesa abunda ta shafa fuskanta yake nema "Banison bincike mey kake nema?" Tayi serious question ah dole ita Babbar yaya, hancinta yaja da gangan saida ya kusan shafe mata duk na fuskan nata kafin yayi waje aka barta da Allah ya isa kafin ta koma kan gadon dan cigaba da waya, ita kanta batasan sanda bacci ya dauketa ba sleeping in her lively girlish room, sai waqa dake cigaba da aiki, dan waqa takeji tayi bacci.
Maras kunyan banza!!!
DAY POSTED: 14th September, 2024.
#AKS!