Free chapter · Read without an account

30

by Azizat Hamza · MAIMUNATU Telar Mata

49

Ganin bamai jinta ne yasa ta fita da gudu tayi part din Sakinan tundaga yadda take buga kofan kasan akwai tashin hankali

Mom da tun tafiyar mubeen ta kwanta taji bugun kofa da yadda Hajiya ke kwala sunanta tana Sakina . ...Alhaji....

Da salati mom ta tashi ta zari hijabinta tayi waje a kofa suka cikaro da Hajiya da tuni ta firgice,

Miya samu Alhajin bata iya bata amsa ba sai cewa take asibiti,muje asibiti ,Alhaji ba lafiya

Dukkansu da gudu suka nufi part din Alhajin suna zuwa suka ga Ilyas da Ahmad ('yan uwan Alhaji ne dake zaune a gidan) suna shirin fita dashi suma ihun Hajiya ya tadasu daga bacci

Dukkansu hudu suka nufi asibiti cikin tashin hankali dan har lokacin Alhaji baya motsi...

Da gudu aka shiga dashi emergency sai lokacin mom ta lura Hajiya ko dankwali bata dashi

hular dake kanta ta cire ta sawa Hajiya tare da cewa Ilyas yaje gida ya taho masu da hijabi da wayoyinsu

Har lokacin Hajiya a bircike take duk tunaninta bai wuce ta dalilinta Alhaji ya shiga wannan hali

.......koda ya Isa gida a kan kujera ya sameni ina bacci, Poor thing I know she waited for me

Dauka na yayi ya shiga daki dani ya ajiyeni, yajamin duvet dama an fara sanyi, addu'a ya tottofamin kamin ya manna min peck a goshi goodnight my tailor

Ya na fita daga dakin na bude idona nayi Murmushi dama tunda ya daukeni na tashi amma ban nuna maiba ....

Sanda Ilyas ya kawo wayar har lokacin likitoci basu fito ba gashi Hajcy ta musu missed call yafi ashirin

Mom ta gyara nitsuwarta ta kira Hajcy da layin Dad

Tana dauka tace Aliyu kana lafiya!

Mom tace Hajiya ba Alhajin bane

Oh Sakina kiyi hakuri na dameku da dare haka dazu ina bacci nayi wani mummunan mafarki tun lokacin hankalina bai kwanta ba gashi ina Neman layinku bakwa dauka ina Aliyun?

Mom tace Hajiya kiyi hakuri wayar duk suna silent ne yanzu na tashi na shiga toilet shine naga wayar na haske kafin na dauka ya yanke shine na kira

Toh Aliyu fah?

Hawayen idonta ta goge tace yayi bacci Hajiya acikin magungunansa harda me sa bacci, ya dade da bacci Hajiya ki kwantar da hankalinki

Hajiya tayi ajiyar zuciya tace Sakina gobe yana tashi ki ce ya kirani kinji

Mom tace Insha Allah tare da katse wayar dan kar Hajiya ta gano ta ...

Lokacin da likita ya fito office dinsa ya kirasu dukkansu biyu

Gaskiya Alhaji is in critical condition, bansan me akamai ba ya tada maihankali bayan kunsan yanada heart failure, baya buqatan hayaniya .

Heart failure .....inji Hajiya ...when? How?

Mom ta kalli likitan plz doctor yanzu ya jikin nashi

Well yanzu Alhamdulillah mun mai allura yana bacci saidai gaskiya zamu riqe shi for a while saboda yanada buqatan Hutu cause any slight mistake can cause his life

Mom tace zamu iya ganinshi, yanzu

Gaskiya sai gobe just relax tashi yayi yabar office din

Mom ma tashi tayi danta kwantar wa su Ilyas hankali dan sunso su shigo ita ta hanasu

Hajiya ce ta cakomo ta ta kwalla mata wani wawan mari mom riqe da quncinta tace Hajiya lafiya !

Sakina Ashe ke munafuka ce kinsan Alhaji yanada heart failure amma Baki sanar dani ba how dare you

Cikin tsananin baqinciki mom ta zage ta wanke Hajiya da mari ta sake ta dauke ta da wani marin abinka da fara har fiskar tayi jaa jir

Karki kuskura ki sake tunanin zaki kirani munafuka in kyale ki, wallahi indai akan mijina ne bazan ragar miki ba nasan bani da hadi da sarauta amma nasan sarauta ba hauka bane dan haka ki kama kanki

Ke har kin isa kice min munafuka, yaushe kika fara damuwa da mijin da zaki wani tada hankalin karya anan

Kisani duk abinda ya sami Alhaji kene ummul aba'isin komai ta juya ta fita daga office din tabar Hajiya da zafin mari da takaici

Washe gari mom ce ta kira mubeen bayan ya dawo daga sallar asuba tace yazo asibiti,

Ina tilawa ya shigo yacemin zai je asibiti baisan mai ya faru ba amma koma miye zai kirani ya sanar dani na mishi Allah yasa dai lafiya ya Kuma yaye mana koma minene

Sanda ya Isa mom kemai bayanin komai, dan Hajiya ta Dade da komawa gida wai zataje ta kawo breakfast,

Haba mom shine Baku kirani tun jiyanba

Kayi hakuri son naga baka Dade da tafiya ba ga gajiyar tafiya besides akwai maza a gidan saisa bamu damuba

Gaskiya mom it's not fair ba wani uzuri dazai hanani zuwa da Daren nan bayan inada raina da lafiyata ...

Ok son I'm sorry kasan abu da tashin hankali

Zuwan Hajcy ne ya katse musu hirar

Sakina, Mubeen, ya jikin nashi ina fatan ba wata matsala

Mubeen ya riqe hannunta ya zaunar da ita ki kwantar da hankalin ki Hajcy dad is fine

Yanzu likita ya shiga duba shi

Likitan na fitowa yace Zasu iya shiga ya farka amma banda hayaniya

Da sauri suka shiga kowa na eager yaga Alhajin

Tsakanin jiya da yau har ya fada

Hajcy ce ta riqe hannunsa daya da babu cannula a jiki tace Aliyu ya jikin,ina ke maka ciwo?mi zaka ci? Hawaye na gangaro wa daga idonta

Murmushi yayi yace a hankali kidaina kuka

Bataji mai yace bama Saida ta kai kanta kusa dashi taji maganan

Murmushin yaqe tayi tace na daina

Hajcy da mom sun koma gida dan shirya wa aka bar mubeen a asibiti

Lokacin da Hajiya ta dawo da kwandon breakfast ta shigo

A tsanake suka gaisa da mubeen

Ta qarasa bakin gadon tace Alhaji mai zakaci na kawo maka breakfast Nina girka da hannuna

Kauda kansa yayi gefe Ganin yaqi kulata yasa tacewa mubeen ya bar dakin, ba musu ya bari

Har qasa ta tsugunna ta fara bashi hakuri amma ko uffan bai ceba Kuka take a haka Hajcy ta shigo ta sameta

Shigowar Hajcy yasata tashi ta fita batare da ko gaisuwa ba

Hajcy bata tambayi miya faru ba dan tasan koma minene yanzu ba lokacin bincike bane lokacin qaninta ya samu lafiya ne ...

.........tunda ta tashi saude tace Hajcy ta fita bata damuba dan tasan koma ina hajcynta taje inta dawo zataji amma tayi mamakin dataga hajcy ce ta yi breakfast da kanta

Tanacin breakfast message ya shigo wayarta tana dubawa taga numbar bigheaded ne ya turo

Tsaki tayi kafin ta bude:

"Good morning jewel,

Hope your night was perfect,and your dream sweet as honey......

I'm sorry for everything, even if don't believe me, I never mean you harm, I'm sorry that I caused you pain, I'll accept any punishment you'll give me just to make it up to you

I'm sorry again"

Ta karanta message din yafi sau goma daga karshe ta ajiye wayar tare da cewa rubbish, kawai wani salon yaudaran kane ,I won't forgive you.....

Sai da yamma mubeen ya dawo gida yayi wanka ya shirya mukaje asibiti tare dan gaida dad

Anan na wuni daga baya baby tazo tare da yaya Haidar

Da dare duk yadda baby tayi abarta tayi kwanan asibiti mubeen ya qi da fushi ta tafi ko magana bata minba

nima naso nazauna amma mubeen yaki yasa aka maidani gida

Washe gari da wuri na tashi na fara hadawa dad dambun shinkafa,tare da kunun gyada, keke napep na hau na wuce asibiti amma me ina zuwa akacemin an sallamesu basu dade da tafiya ba ....

Gida na wuce cike da mamaki dan a yadda naga dad jiya bawai jikin nashi yayi sauqi bane

Dana isa mubeen na kira yace min in zo falon dad suna nan

Falon a cike yake da 'yan dubiya da kyar na iya gaishesu, a gefen mom na rakube tace maimunatu ki shiga mana Alhaji na daki nace toh

Ina shiga naga mubeen zaune agefen gadon da dad ke kwance ,

Gaisheshi nayi nace Dad ya jiki yace da sauqi 'yata

A hankali yace kamar qanshin dambu nakeji

Nace ee dad dambu ne na maka da kunun gyada

Yayi murmushi yace yanzu yaya ta tafi gida ta girkamin ashe kin riga kinyi ki zuba min naci,kai kuma Muhammad ka kira Hajiya kace ta fasa girkawan 'yata ta kawo

Yace ok dad

Dakaina na ringa bashi a haka har Hajiya ta shigo ta samemu

Harara ta watsa min kafin tace in tashi in fita zata bashi duk da matarsa ce amma naji haushi tinda shi da kansa yace in bashi

Ina fita tayi yunqurin bashi amma ya kauda kai yaqi ci duk yadda tayi yaki ci karshe ta fashe da kuka amma baice komai ba

Ganin haka mubeen ya karba plate din daga hannunta ya ci gaba da bashi ba musu ya fara ci....

Ranar Abba suka zo dashi da Khalid inda yace ranar Wednesday zai fitar da Dad waje duk yadda dad yaso yayi convincing dinshi akan baya son fita yaqi, mubeen da mom sunyi supporting din hakan dama bawai likita ne ya sallame suba dad ne ya takura a maidashi gida ...

Su baba na ma sunzo gaisuwa naji dadi da mom ce ta tare su ba Hajiya ba sosai dad ya nuna farincikinsa da ganinsu

A gidan na kwana, bangaren mubeen na sauka, mom ce ma tace karna koma gida tunda mubeen na gidan

Washe gari jikin dai da sauki dana je gaisheshi, fita nayi ganin dakin ya cika da manya, ina falo tare da baby

Nayi deciding Sakina,mubeen da Khalid su zasu bi Alhaji dan haka kowa ya shirya,

Alhaji Abubakar Nima zan bisu cewar Hajiya dake zaune gefen gado

Hajcy ta amsa mata jinya za aje ba wani abu ba dan haka mutane ukun ma sun isa

Batace komai ba dan batason tasake batawa Alhaji rai .....

Muhammad kiramin qaninka inji Dad dake kwance yayinda mubeen ke goge masa jiki da towel ....ok dad

Video call sukayi sun dade suna hira harda mubeen dinma shawarwari da nasiha ya musu akan zumunci dukkansu biyu maganganun dad dinsu ya sanyaya musu jiki.

Later that day ........

Zaune suke da lauyan Dad, mubeen da Abba tattaunawa suke sosai abin duk ya sa jikin mubeen sanyi,yadda Dad ke bada wasiyya kamar mai shirin barin duniya ....

Ban gane ba yaya idan har kanason hada auran Khalid da Zainab abin farin cikine amma Kace yanzu, yaya kabari idan Allah ya baka lafiya sai ayi auren ...inji Abba

Tari Dad ya fara sai jini ya fara fitowa daga bakinsa,a tsorace mubeen ya fara kiran sunansa yana Dad! Dad! Lafiya barin kira likita,

Riqe hannunsa Dad yayi ya daure yace No barshi kawai gobe sai ka kirashi yanzu dare yayi,

Towel yasa ya goge masa fiska yace dad ka kwanta ka huta abar zancen auren nan kamar yadda Abba yace in Mun dawo daga Germany sai ayi auren plz Dad ...

Hannu yasa ya kira Khalid dake tsaye jikin bango duk ya rikice da maganar dad din

Khalid ya matso kusa da gadon yace gani Dad

Dad yayi Murmushi ka kularmin da Zainab dina bata samu kulawata ba yaya ce ta zama mata uwa da uba, saisa nakeson mata gatan da baza ta manta dani ba,,,

Akwai kudi ajikinka

Aljihunshi ya lalumo ya fidda wallet nashi dubu uku ne aciki ya ce dad dubu uku ne

Dad yace dubu uku yayi wa 'yata

Ganin abin bana wasa bane yasa mubeen shima duba aljihunshi ya Ciro dubu biyun dake ciki ya miqa wa Khalid ....

Batare da bata lokaci ba aka daura auren

Khalid Abubakar Abdullahi

Da

Zainab Aliyu Abdullahi

Bisa sadaki dubu biyar atake adakin inda Mubeen ya zama waliyyin Zainab Dad yazama na khalid

Abin kamar a mafarki .......

....Angel wallahi jina nake wani iri kaman an daura min abu akaina,I felt different all of a sudden,

Relax baby Dad zai sama lafiya Insha Allah daga gobe jibi in sun tafi komai zai zama normal, Dad zai dawo da lafiyar shi, healthy and hearty ....

Allah yasa gimbiya zanyi missing din dad sosai Kuma kema zakiyi missing din MB

Yes dear zan missing dinshi sosai

Huh huh my angel is in love now I'm happy for you, mintsininta nayi tace auchhh bhabi

Yau Talata

As usual da mukaje gaida dad yana kwance saidai yadda na kalleshi na mugun tsorata gaba daya ya chanza,ya rame da kyar ya iya amsa gaisuwar mu ...

Baby tayi kissing nashi a goshi tace Dad inada test yau amma ina gamawa zan dawo muyi hira sosai kaji dad get well soon

Har zata tafi ya kira sunanta Zainab! Ta tsaya tare da juyowa fiskarta dauke da Murmushi ta riqe hannunshi tace yes my Daddy

Yafi Minti biyu yana kallonta kafin ya nisa yace "kiyi biyayya wa mijinki "

I promise you Dad duk mijin dana aura zan masa biyayya, like I will do to you Dad don't worry

Allah ya miki albarka 'yata

Amin muka amsa gaba dayanmu

Nikan duk jikina yayi sanyi

Ina zaune a daki mubeen ya shigo,gaisuwan jinya na mishi tare da cewa bhayya na kawo maka breakfast ne

Zama yayi akan gado yace tailor I felt weird tun jiya dad was acting strange imagine ya aurar da baby wa khalid

Dafe kirji nayi nace aure Kuma yaushe!

Yes tailor baby is now married to khalid, bama shi kadai ba he is saying strange things imagine jiya yana cemin son idan rai yayi halinsa inaso kamin wanka kaji, imagine yana tunanin mutuwa yanzu he's just sixty fah he still have a life to leave

Amma gaskiya da mamaki yanzu baby ta zama amarya kenan, Allah ka qara ma Dad lafiya

Yace amin

Wanka ya shiga yayi kafin ya fito naje nakawo masa da breakfast amma tea kawai yasha yace tailor I can't eat bayan dad baici komai ba tun jiya da dare, he refuse to it ...

Koda ya shiga daki Hajcy ce ke gefenshi tana riqe da hannunshi, mom da Hajiya duk suna zaune a gefe

Aliyu kaci abinci mana koda kadan ne ..

Na yafe wa kowa duk wanda nake bi bashi na yafe musu,

Na yafe wa kowa ....... Jini ne ya fara fita daga bakinshi da sauri mubeen ya qarasa daya gefen ya riqe hannunshi Dad plz kar Kace komai Abba ya tafi kawo likita they'll be here soon .....

Mom da Hajiya ma sun hau kan gadon kowa ya tsorata da maganganun Alhajin

Kalmar shahada Hajcy ta fara maimaitawa haka ma mubeen cikin ikon Allah Alhaji ya fara karanta Kalmar shahada wadda ta kasance Kalmar shi ta karshe a duniya kafin Allah ya dauki ranshi .....

Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'oun, Allah ya karbi ran Alhaji Aliyu Abdullahi Waziri Jama'are, Bauchi ..... .

Kuka su Hajiya suka fara Hajcy ce kawai ta ke maimaita Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun,

Mubeen yayi addu'a ya rufe idon mahaifinshi daya rasu tare da gyara mai kwanciya shida Hajcy suka rufe shi gaba daya .. .

Wayarshi ya dauko ya kira Abba ya na dauka yace hello Mubeen munma iso gamu nan shigo wa

Ok kawai yace ya kashe wayar ...

Tun daga falo suka Tarar dasu mom daketa kuka jikinsu yayi sanyi

Abba yace ina mubeen Hajcy ce tace yana dakin jiki a sanyaye shida doctor suka shiga dakin ....

Dad do you remember dana sayi fili kaje ka gani I told you Dad nace idan na Gina gidan nan kai zaka fara gani, when I made all the plans I first show it to you Dad, why don't you wait a little longer an kammala gidan Dad saura kadan Dad I want you to be the first to see it, Dad all you said yesterday bankai na riqe Iyalenka ba I still need you Dad, I'm still your small kid that you take to school, that you hold my hands to masjid,I still need you Dad I'm not capable of any reaponaibility, I need you now more than ever ...

Mubeen. Abba ya dafa shi addu'a yake buqata yanzu .....

**

Mutuwa is real, I will die,he will die,she will die,we will all die.

Allah kajikan musulmai dasuka Riga mu gidan gaskiya amin,ka sa mucika da imani, ka gafarta mana zunubanmu amin ya Allah.....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.