Free chapter · Read without an account
33
53
Abubuwa da dama sun faru bayan Daren ranar, Imran ya koma india haka kuma su Abba sun koma Abuja, baby ma ita da hajcy sun koma gidansu ....
But everything was never the same again ......
Har wayau kullum addu'a tah akan samun soyayyar mijina ne Duk da yadda mubeen ya sake dani amma kullum cikin fargaba nake ji nake kamar simran zata bullo any moment ta dauke min mubeen dina ....
AMINA IHSAN ABUBAKAR ABDULLAHI.....
Tun da aka sanar da hadin ta da yaya haidar ta shiga tashin hankali saidai koda suka koma Abuja Abba da Ammi basu ragwanta mata ba sun nuna mata ko ta amince da haidar na Allah da Annabi kotayi na dole wasa wasa ta dangana ta bawa kanta hakuri ta rungume qaddara ta fara kula yaya haidar dan randa ya fara zuwa hira ce mata yayi ta daukeshi a matsayin friend dinta so that she will be free with him hakan kuwa akayi yau da gobe suna waya,chatting,haka duk sati biyu zaije Abuja yayi 2days yanzu haka sun shaqu sosai zaka iya cewa soyayya suke .....
ZAINAB(BABY)ALIYU ABDULLAHI....
Duk nasiha da shawarwari baisa ta dena tsanar Khalid ba duk sati yana zuwa bauchi haka Kuma texts messages dayake mata ba zasu irgu ba dan koya kira bata dauka inko ya kira da wani layin tanajin muryarshi zata katse wayar,duk sadda yazo ta dinga kirkiran uzuri na makaranta dazai occupying dinta kenan duk da agaban Hajiya zata gaishe shi ta mishi ya aiki amma fa in hajcy bata nan ko tarinta bazai jiba shikan ya saba kullum addu'a yake Allah yasa ta soshi amma ina kamar qara qinshi take, gashi dan walwalarta ma datake agidan idan yazo dainawa take ita da idan tana gida kayanta basa wuce bum short, mini skirt,ko mini dresses, amma yanzu kullum cikin hijabi take in yazo weekend har ya tafi hijabi har qasa zaka ganta dashi gashi dama tunda ta koma makaranta hajcy ta hana ta fita da gyale hijabai manya ta kawo mata su take sawa in zata je lectures,
Kullum hajcy na nutsar da ita gameda zamantakewar aure amma ita da ada takeson ji yanzu ta tsani irin hirar .....
Ko nima idan na fara mata magana akan aure a waya katse wa take inko chatting muke to bazata sake kulani ba. Nima Ganin haka na kyaleta .....
SURAYYA(SURY)ALIYU ABDULLAHI ....
Tunda sury ta koma Abuja ta dena walwala yanzu kam bayan gaisuwa ba abinda ke hadata da Khalid, badan ta hakura ba saidan ba yadda ta iya ..
Ranar da kamal ya fara zuwa hira ruwan da aka wanke kayan miya tazo ta zuba mai ta zage shi tatas tace kar ya qara zuwa amma ina Washe garima sai dayazo haka ya sha jira bata fito ba data fito kuwa juice din da aka kawomai ta tsiyaya ta watsa mai Murmushi kawai yayi yace ina sonki surayya
Walaqanci dai kalakala takemai idan yazo dama ammi ke takura mata ta fita randa ammi batanan kuwa bazata fita ba gashi bata amsa wayarsa saboda shima ta chanza layi amma sai daya samo numbarta ...
Wasawasa har wata biyu wata rana taje bauchi taje har Jama'are gidansu kamal ta mawa mahaifiyarshi rashin mutunci, matar arziki ko uffan bata ceba da qannen kamal ma Zasu tanka mata hanasu tayi ....haka ta xagesu talas ta dawo
Kamal baisan me yafaru ba sai wata qanwarsa ce ke gaya masa ranar ya dau alkawarin rabuwa da sury tunda abin nata ya tashi daga kanta ya koma kan mahaifiyarshi
Ranar dayazo gidansu bayan ta gama zaginshi tas ya shaqo wuyanta yace Surayya you have cross all limits zan iya daukan duk wani walaqanci daga gareki amma cin mutuncin mahaifiyata bazan dauka ba ki Sani ni kamal Muhammad idan har saboda inasonki kika samu guts dakikaje kika zagi mahaifiyata toh ki sani na janye nemanki na haqura koda kekadaice mace a duniya na hakura ya saketa yayi tafiyarsa ...
Tun daga lokacin bai sake zuwa ba dayayi sati Abba ya kirata yace saiki zuba ruwa a qasa ki sha tunda kin kori kamal ya janye nemanki dayake toh kisani bawai dan kamal ya janye zaisa na fasa aurar dake a lokacin dana diba ba dan haka inkina da wadda kikeso ki turo amma aurenku tare dasu ihsan ba fashi inkuwa baki turo kowa ba in lokaci yayi duk da wanda na ga dama zan hadaki tashi ki ban wuri marar hankali ubanki ya nema miki gata ke kince tsiya kikeso ...
Haka sury ta kasance da fargaba gashi dama ita ta saba yiwa samarinta rashin mutunci dan haka kowa ya gudu wadda ke da niyya ma idan 'yan gulma suka gulmata halinta sai mutum ya janye gashi tun tafiyar kamal bai sake waiwayarta ba yau kusan wata biyu hankalinta ya fara tashi ta fara damuwa akanshi texts dinshi kadai take karantawa taji sauqi dan ma gogewa take na baya baya da bata goge ba sukadai take dashi
Kalamansa da yadda yake bayyana soyayyarsa gareta sunsa ta fara damuwa dashi yanzu takai saita karanta messages din a rana yafi sau hamsin harta haddacesu ...
Ranar tana kallon hotunan wayanta taga wani hoto da mubeen ya dauka da kamal yayi masifar kyau koba komai kamal ba fari bane amma Kuma irin shiny black din nan ne ko ince like black American saidai in any aspect he's handsome itama ba fara bace sosai dan dama a gidansu MB,baby,da Zahra,ne kawai farare kamar larabawa amma sauran farinsu da dan duhu...
Text da hoton kamal sun zame mata abin kallo kullum tamkar ibada amma girmankai ya hanata nemanshi ta bashi hakuri kar ya rainata dama fa ita matsalarta dashi wai dan talakawa ne amma ko kadan ba makusa a tattare dashi ....
Wasa wasa har ihsan ta gano ta tace mata ta kirashi ta bashi haquri ...
Akan me? Inji sury
Saboda kin fara sonshi mana Kuma kinmai rashin mutuncin da ba kowa ne zai dauka ba ..
Nidai bana sonshi amma dai zan bawa mahaifiyarshi hakuri koba komai nayi nadama tunda nima bazanso wata ta zagi mahaifiyata ba Kuma nima macece wata rana zan zama uwa
Oho dai ke kika sani amma what I'm seeing in your eyes is love ..
Haka ta shirya ranar Jumu'ah taje bauchi ranar asabat ta wuce Jama'are ko fada bata jeba ta wuce gidan su kamal koda taje ta samu yaran sunje makaranta dan haka ba hayaniya gashi da alama Mama mahaifiyar kamal bacci take dan tayi sallama ba a amsa ba Ganin tsakar gidan da dan datti yasa ta fara shara chan mama ta farka hafsa bakije haddar bane ba nace kibar sharan ba zanyi in na dan rintsa kadan sury tace mama ba hafsa bace jin ba hafsa bace yasa ta tashi ta leqo tana ganin sury ta ganeta tace a'a kece lafiya dai ko ..
Sury ta tsugunna har qasa ta fara bata hakuri kan zagin da ta mata
Mama tace ba komai ni ya wuce a wurina ai mahaifinki abinda ya mana ya fi karfin inyi fishi dake, tashi abinki na yafe miki
Saida ta zauna tace dama mama kinsan dad dina ne
Mama tace kwarai kuwa mahaifinki tare da malam (babansu kamal) tare suka yi yarinta abokinshine sosai saidai malam baiyi karatu mai nisa ba kasuwanci yake koda ma Alhaji yake qasar waje duk sanda yazo jama'are sai yazo gidannan yaci dambu ko tuwon biski ...to Allah baiyi malam mai tsawon rai bane amma koda bayanan Alhaji bai dena zumunci ba duk randa yazo sai ya mana abin alkhairi kinga gidan nan da ginin qasa ne Alhaji ne ya gyarashi haka,Kuma duk yarana shiyake daukar nauyinsu har Allah ya masa rasuwa koda na aurar da yarana biyu shekarar daya wuce shi ya musu komai, ga kamalu nan ya turashi qasar waje karatu daya dawo ya bashi aiki kinga kuwa komai kika min bazan damu ba dan mahaifinku Allah ya jikan rai mutumin arziki ne ...
Ranar sury a gidan ta wuni harta abinci ita tamusu fried rice da plantain ga tsaraba da dama ta taho musu dashi
Cike da addu'o'i,da godiya mama ta raka ta
Ranar kuwa kamal yazo ya tarar da abinda sury tayi yaji dadin haka amma yana tunanin ko dai daga gida aka sa tazo ta bada hakuri
Zuwanshi Abuja ya je gidansu dan yimata godiya da Kuma saqon mama data aiko mata duk dayana tunanin irin tarbarta na rashin mutunci data saba zata masa amma mey!
Sai yaga sabanin haka datazo cikin kwalliya tazo gashi maimakon waje datake ajiyeshi yau har falon baqi tasa aka shigo dashi bayan an kawo masa Abubuwa na motsa baki
Koda tazo sallama ta masa tare da ya hanya, mamaki ya hanashi amsawa daga baya ya tattara nistsuwarsa ya amsa mata
Hira ta fara jansa dashi tana tambayarsa su mama da mutanen gida
Ranar abin mamaki shida basu taba hirar minti biyarba amma yau har kusan minti talatin kafin tace masa zata shiga ciki koda ya bata saqon mama abin mamaki sai gashi ta amsa harda godiya ...
Daga ranar suka saita Kansu duk da tana ja masa aji amma yanzu ya fahimci tanasonshi koda kuwa kadan ne ......
54
NI. DA. MUBEEN
Zaman mu da mubeen zama ne na amana,shaquwa,yarda,da Kuma aminci ,
Ni da mubeen Mun kasance tamkar wasu masoya kusan komai da za ace masoya nayi munayi tun daga,cin abinci tare,wasa,irinsu ball,basket ball,game na waya ko tv, hide and seek,da sauransu Kai abin gwanin sha'awa hakan nan nasan duk wani farin ciki nashi,damuwarsa, baqin cikin sa,dariyarsa,kukansa,nasan 95%na halinsa da yanayinsa,haka shima,
Nikam na Dade da kamuwa da soyayyar mijina ina son mubeen sosai bana son abinda zai bata masa rai kullum cikin Neman yadda zan jawo hankalin shi nake amma ban iya ba domin zaman shi a qasar waje yasa shi ya zama mutun mai tsananin riqo da alkawari soyayyar Simran ta rufe mai ido duk da cewa ya dena wasu abubuwa akanta amma har yanzu nasan yana sonta (riqo da alkawari halayene da musulunci ya koyar damu amma gaskiya musulmanmu yanzu qalilan ke da halin nan Munyi watsi dashi ta yadda wani lokaci zakaga kafirai musamman turawa sunfi riqe alkawari, Allah ka yafemu gaba daya ka Kuma gyara mana halayenmu zuwa na kwarai amin)
Har yanzu fargaba na bai wuce simran ba wani lokaci idan yamin wani abu sai na dauka ya fara sona ne amma daga baya sai na ganshi rungume da hoton simran wannan abin na bata min rai duk lokacin dana ga hotunan simran a dakinshi sai naji kamar inje in qona su kowa ya huta amma bani da hali
Mubeen ya maidani very social yanzu inka kalleni baza Kace Maimunatu Telar Mata bace yarinyar da koda yaushe take Neman na kanta dan tallafawa Iyayenta
Bani da matsala na kudi domin duk wata matsalata mubeen ya dauke duk wata yana turawa Khalil kudi ni banma Sani ba saidai wata rana danaje gida Baba kemin godiya ashe cewa yayi kar Khalil ya gayamin sosai naji dadin haka dan bayan Khalil duk wata yana yiwa iyayena alkhairi ...
Bani da abinda zan saka masa dashi saidai addu'a kullum ina cikin yi masa, yanzu ko turancina ya banbanta dana da dan takanas muke da ranar turanci, aranar completely yaran English zamuyi tun ina kwabawa yana gyara min har na dan saba average yanzu I can communicate in English very well all thanks to my husband mubeen wadda ko word na gaya ba daidai ba zai gyaramin daga baya Kuma yayita min dariyar yanayin da na fada ...
Ganin ya sauya min rayuwata in his own way nima nace na gwada nawa sa'ar ta inda na introducing mana axumin litinin da alhamis dama ni tun ina gida inada kokarin yi, duk randa mukayi azumi tare zamu shirya kayan bude baki inko ranar bai dawo da wuri ba to a waje zamuje muci ko ya siyo mana muci a gida .
Abu na biyu dana kawo mana shine musaffa na alqur'ani tare (musaffa: wani yanayi ne na karatun Qur'ani da mutum biyu ko fiye zasuyi ta yadda idan wannan ya karanta sai wannan ya karanta,ana iyayi aya daddaya ko biyu biyu ko fiye koma ayi shi shafi shafi irin wannan yana qara kaifin hadda sosai)
Munayin musaffa na na izub biyar duk Daren alhamis wayewar Jumu'ah saboda falalar dake cikin Daren, wannan yasa duk Daren nan bamu cika kwantawa da wuri ba saboda bayan Mun gama zamuyi sallah nafila tare saidai duk min dadewa da mukayi bayasa mubeen ya kwana tare dani haka zaija jikinsa ya koma dakinsa wannan na tayar min da hankali saidai ba yadda na iya ...
Yanzu babbar matsalata shine Hajiya duk da tun rasuwar Dad bata sake tada zancen auren mubeen da yusra ba saidai fa har wayau bata daukeni da wata matsayi ba hasalima tana min kallon nice sanadin kashe mijinta na Kuma jawo musu fitina tsakaninsu kafin ya rasu ranar danaje gaishesu ta gayamin maganganu nayi Kuka sosai mom ce ta bani hakuri tare da min nasiha tace watarana Hajiya zata kalleni da mutinci
Yanzu mubeen duk karshen sati yake zuwa bauchi nikuma sai karshen wata yake tafiya dani kwatakwata idan baya gidan bana jin dadi na dinga kewarsa kenan
Har lokacin dasu mom suka kare takaba Hajiya bata kulani idan naje wajenta ma cewa zatayi inbar mata wuri Inko naqi ita saita tashi a wurin hakan baisa na dena zuwa gaisheta ba haka kullum ina tura mata saqon gaisuwa saidai bata taba mayarwa ba ....
Haka rayuwa ta kasance tsakaninmu nida mijina muna zaune lafiya cikin kula da juna duk sanda nazo bauchi sai Anty Fatima tasani a gaba ta gyara ni bata San ba amfanin gyaranba dan duk Abubuwan data ke bani insha idan na tafi dashi Abuja haka nake jibge shi bana amfani dasu iyakaci
Hadi irinsu kwakwa,aya,Zuma, kankana,da sauran fruits su kadai nake amfani dasu,
Yanzu na yi fresh na dan qara kiba,baqi na har shining yake ...
Wasawasa saura wata biyu ayi bikinsu Sury inajin last zuwana bauchi nakejin wai Hajcy, Ammi,matar uncle Muhammad da Anty Ramlah ne Zasu je hado lefe nanda sati biyu masu zuwa abin ka da masu shi wai har qasashe biyar zasuje nikam nace ko a qasarmu ma ai Zasu samu yadda sukeso amma kasan idan akwai naira toh fa everybody went for the best. ...
04-04 ....
Happy birthday to you, happy birthday to you my tailor, happy birthday to you !!!!
Bude ido na nayi nace bhayya stop joking yaushe muka shiga sabuwar shekara amma wai har April ya shigo, hancina ya ja yace crazy larki dayake bakya aikin albashi dole ki mance lissafin kwanan wata ai
Nima hancinsa na ja nace pagal larka koba albashiba ni mai lissafin kwanan wata ne saboda inada baqo mai zuwan wata wata
I see watan nan idan yazo kice mai I won't be there to welcome him dan na gaji da danna miki ciki da mara,bazan Kuma ba
Haba bhayya nidin Kuma
Yes mana now get up sleepy head today is our day har ya tashi zai fita na riqe mai hannu
Yace what now tailor ..
Tashi nayi ba shiri na rungumeshi nace Happy birthday mera bhai,mera jaan,mera pyaar,mera sab kuch,aur mera dosti,
Janye jikinshi yayi as usual dan na lura kwannan nan bayason muna hada jiki,
I'm impressed tailor gaskiya zan bada ke kiyi wani indian soap opera tunda kin koyi yaren
Ba matsala ai indai Kaine co star din ....
Jana yayi mukayi waje yana we have cake to work on ...
After the cake has been done muna kitchen muna icing din cake din na dangwali abin na shafa masa a fiska ...
Tailor you .....
Dariya nayi nace abin ma ya karbe kafa kaga yadda kayi kyau kuwa ...
Clean it tailor
No
I said clean it now
No
Idan na irga uku baki goge min ba kinsan sauran ai
One
Two....
Ok ok zan goge amma ka rufe idonka
Ba musu ya rufe
Fiskarshi na sa hannu na jawo na daga kafafuna saboda ya fini tsayi mai makon na goge da hannuna sai na fara lashewa tas na lashe kafin nace open your eyes
Cike da mamakin abinda nayi yake kallon idona yafi Minti biyu muna kallon kallo kafin ya cakuleni crazy larki .....
Later that day
Mun Riga Mun shirya komai cake din Mun saka M&M da Kuma 2033 wato shekarana da nashi yayi kyau sosai
Na samu messages da calls daga wurin 'yan uwana Babana as usual addu'a yamin wadda ya kashe min jiki dan ranar dana zo duniya ranar mahaifiyata ta koma ...
Ina zaune gaban mirror naji wayana na kara ma dauka mubeen ne
Tailor will you take a year to come downstairs ne ...
Ganinan zuwa shine abinda nace ..
A hankali nake takawa cikin tafiya mai jan hankali tunda yaji qaran takalmina ya dago ido bai sauke ba har na sauka na qarasa wajen daya tsaya
Kallona yake tun daga sama har kasa na kasa gane shin mamakin shigan danayi ne ko kuwa sha'awa ce
Murya a sarqe yace tailor how did you have this dress
Nace what kana mamakine nasa irin kayan simran
Nop I mean it look the same fa
Nayi dariya ka manta ni tela ce ni na dinka
Wow amazing tailor gaskiya you are genius you made this dress exactly like the one Simu wored on her 21st birthday kai amazing
Jin sunan simran a bakinshi na bata rai yace kya huwa tailor why the sad face
Na qaqaro Murmushi nace na tuna da mamana ne
Ya dafa kafadana yace Allah ya jikanta tailor addu'a zamu mata 20years kenan data bar duniya Alhamdulillah ma tabar mai mata addu'a so cheer up now, na goge hawayen daya gangaromin nace na gode bhayya ...
Birthday dinmu was memorable to me domin naji dadin every moment I spent with mubeen
Kyautar sarqar gold yamin ni kuwa na bashi jumper dana dinka mai
Lokacin daya gwada like seriously tailor yaushe kikayi dinki ban Sani ba, dama kin iya dinkin maza ne
Do you like it na tambayeshi
It's good tailor bansan kin riqe measurement dina ba kikamin dinki that suits me perfectly gaskiya ya kamata na baki queen of tailors
Dariya nayi nace inzaka karbi king of tailor ba
Kai rabani ko scissors ban iya riqewa ba muka sa dariya gaba daya
I'm glad you liked it na koyi dinkin maxa a wurin yaya KB saidai bana yi bayan babana ba wadda nayiwa dinkin maza saikai ..
Ya shafa fiskata I appreciated it tailor.....
.......bayan kwana biyu yau Alhamis da yamma muka fita shopping saboda akwai matar abokinshi data haihu zamuje musu barka ...
Muna fitowa daga shagon mukaci karo da wani abokinshi wadda sukayi karatu a India tare ...
OMG who I'm I seeing MMA Muhammad mubeen Aliyu na Simran bada kanka a sare ..
SYM Sadiq Yusuf Michika ....
.suka rungume juna
Kai mubeen kayi wuyar gani na Dade ina nemanka amma ban sameka ba
Har yanzu baka bar halinka ba tun yaushe na ke kasar nan Kace ka nemeni see you
Sorry dan uwa kasan Abubuwan ne sai a hankali idan mutum na aiki wa turawa sai hakuri dansu aikin kawai suke so ba wasa
Naji Mustafah nacemin kana aiki a Florida shege mutumina kana jin dadi fah
Wani jin dadi aiki ba Hutu yanzu ma daka ganni haka rasuwa aka mana nashigo kasar
Eyya ya hakuri
Alhamdulillah yau sati kenan next week zan koma ..
Kai mutumina wace damsel ka dauko haka ko itace madam din dan ancemin kayi aure ..
Mubeen ya kaimai duka yace Dalla chan sister nane
Perfect wallahi ina zuwa
Ya tako wajen danake sannu qanwarmu, dama naji duk hiransu nace sannu yaya ya hakuri Alhamdulillah yace gaskiya sister kin burgeni ga kyau ga shiga ta kamala,
Nace na gode
Ganin yana jana da hira har yana tambayan contact yasa mubeen ya jawoshi gefe yace kai Sadiq an fa mata miji ka dauke idonka akanta
Ina ba a daura auren ba kagani I can try my luck dan wallahi sis dinka ta tafi dani,beautiful, gentle, modest,virtuous perfect ideal wife kawai
Mubeen da kalaman Sadiq sun birkitashi ya ce like I said back off ya Ciro card dinshi yasamai a aljihu yace call me
Cike da mamaki Sadiq ya bishi da kallo dan idan abindaya gani gaskiya ne toh fa mubeen kishi yake but why bayace sistanshi bane but.......
Koda ya ja mota hanyar gida muka nufa nace bhayya gida Kuma zamuje bai kulani ba
Koda motar ya tsaya zan fita yace stop
Wato kika biye sadiq kuna hira ko harda wani tambayar number ashe dabanyi magana ba haka zaki bashi ko ..
Na juyo na kalleshi da idanuwana da sukayi jaa nace ee nayi hira dashi din bacewa kayi ni qanwarka bace Dan haka abokin yayana ai yaya nane
Ban jira amsarsa ba na fita
Ranar dukkanmu Munyi fishi da juna amma kafin sallar Maghreb Mun shirya....
Zaune muke kan sallaya muna musaffa amma ko izub daya bamu yiba mubeen ya fara sarewa dan sai tsallake aya yake daga gani bacci ya keji ...
Ba haka bane ayarfa
Hakane
Allah bashi bane fa
Shine
Barinyi ayar kaji
Na bude baki zan fara karantawa ya hada bakin mu for the first time after several months of marriage mubeen yana kissing dina
It was a very deep kiss full of passion munfi Minti biyar muna kissing daga karshe ma hijabina ya cire ban hana shiba ya cigaba da abinda yake har wuyana nidai gaba daya na miqa wuya dan ya rikitani sosai ...
Wayar aljihunsa ne ya fara qara dakyar ya cire bakinshi daga baki na yana maida numfashi ya Ciro wayar yana dauka ya tashi ya fita jiki ba kwari...
Tunda ya fita daga dakin nake Murmushi na kasa ma tashi a wurin ga sakonninsa da basu bar jikina ba ga Kuma murnar koba komai ya nuna min na fara samun matsayi a wurinshi ....
Ina cikin haka naji fitar motarshi
Tashi nayi na dau wayata na kira baby na sanar da ita
Baby tace to wallahi karki bari wannan ya wuce haka kisake rikitashi sosai kiyi wanka ki shirya cikin fitinannun kaya fa angel kinji I'm happy for you dama nasan bhayya has feelings for you, yanzu kafin ya dawo kije ki shirya gobe zanzo inyi jinya
Ba jinya ba cuta
Tasa dariya ta kashe wayar
Nima dariyar nayi
Toilet na shiga nayi wanka sosai na sake wankan turare kafin na fito, shafe shafen danayi ba a magana
Nayi kwalliya sosai na dauko wata rigar bacci wadda da ita da babu duk daya nasa har zan fita haka Kuma naji wani iri na dauko hijab na daura akai
Dakin shi naje na zauna ina jiranshi Ganin hotunan simran a dakin naji hankalina ya tashi
Na ce la'ananniya Allah ya karbi addu'o'ina yanzu mijina ni yakeso na tashi kamar an fisgeni na fara cire hotunan
A takaice duk wani hoto na simran dake dakin na tattarasu haka duk wani gift ko wani abu danasan ya ta'allaka da simran tattarasu nayi waje dasu naje na qona
Dana dawo naji sanyi a raina chan Kuma na dauko laptop dinshi nayiwa hotunanta permanent delete ...
Ina zaune har sha daya saura naji shigowar motarsa nanfa naji tsoro ya shigeni farat daya amma na danne chan na tuna da wani magani da hajcy ta bani tace inyi amfani dashi Daren farko lokacin bikinmu nace barinje nasha ...
Oh khuda yazanyi kenan why did I even kiss her what is wrong with me now how could I face her ....
Chan yace barinje kawai na shiga dakina na kwanta tomorrow ,zanyi kamar ba abinda ya faru idan tayi maganan zance mata bansan zanceba gaskiya I won't let this happen ever again
Mubeen you are such a fool Allah...
A haka dai yake ta dibiyadibiya har ya shigo dakinsa
Tukunna bai lura babu hoton simran ba saidaya zauna akan gado zai cire takalmi ya gani
What ina hoton Simu, ya fara dube dube baiga komai ba
Sauran dasuke album ya duba suma babu
Hankalin shi ya tashi ya dauko laptop dinshi ya bude ya duba nan ma babu
T...ai..lo..r.............
Ina shirin hada maganin naji ihunshi harga Allah na dauka wani abu ya sameshi dan haka kota hijabi banyiba na fita da gudu ....
Ina shigo wa naga ya birkita dakin cikin tashin hankali nace bhayya lafiya ..
Ya dago rinannun idanuwansa yace tailor ina hotunan simran
A hankali nace bhayya since we are going to start a new life shiyasa na qona su
What you burnt them!
How dare you tailor,
Shaqoni yayi yace tell me what made you burn them ....
Bhayya plz ....
Ya jefar dani na buge kaina
Yace oh you think I kissed you that gave you the impression cewa ina sonki ko
I don't love you I never love you and I will never love you...
Kina hauka ne I kept memories for more than 4 years kizo ki destroying min su
How dare you ....
Ki Sani I only love Simran Malhotra and will always love her
If you have any problem with it deal with it you can leave dama ba wai ni na kawoki ba
Ya buga hannunsa a bango har wurin ya fara jini
Ina kwance Inda ya jefani ina shesheqa dan hawaye yaki zuwa
Yazo ya dagani yace leave my presence dan zan iya kashe ki anan ..
Bhayya......ka...
Wani mari ya shara min yace don't dare open your filthy mouth in my presence now leave my room
Leave my house
You are nothing but a tailor baki da matsayin dazan hada makwanci dake, trying to seduce me with stupid dress,
Da qarfi ya jani wannan karan ya bude kofa ya jefani yace leave my life I don't want to ever see your face again coz I hate you ....
Ya banko kofar dakinsa ya rufe...