Free chapter 路 Read without an account
PAGE 21
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671
FREE-BOOK
PAGE 21
Yau tun da na shigo babban gate na tarar da yawan motocin da ke harabar wurin sun 茩aru fiye da yan da na sansu.
A kitchen na tarar da su Munira suna ta faman darzazar aiki. Bayan mun gaisa fuskata 蓷auke da mamaki na ce.
"Muni buki ake a gidan ne?"
Girgiza kai ta yi ta ce.
"Za dai ayi, kwana biyar mai zuwa...."
Dariya ta koma yi 茩asasa tana kallona ta ci gaba da cewa.
"Mutuniyarki ce ta haihu, jiya bayan kin tafi suka iso daga 茩asar waje."
Tsaki na ja ina 蓷an yi mata hararar wasa na ce.
"mts! To miye abun dariya a nan kuma? Allah ya raya. Mi aka samu?"
Sai kuma na dawo murmushi ina mai bin su da ido ina jiran amsar su.
Haula ce ta jinjina kai ta ce.
"茒a namiji aka samu, Wallahi baki ganshi ba, barakallah kamar Ya Emraan."
Jinjina kai na na yi na ce.
"Masha Allah! Allah ya raya....Bari kiga bawa yaje ya yi aikinsa da wuri ya huta. Tashi muje Hajiya Muni."
Tare muka shige muka bar su nan suna ta aikin ha蓷a breakfast. Duk da cewa ba茩i sun cika gidan,nan take mukayi komai muka kambala kuma muka dawo kitchen ana ta kai kawo wurin kai musu abincin kari.
Muna tsaye na ce musu bari na shiga na gaishe da Hajiya domin ban ganta ba a 蓷a zu.
Munira ce tace.
"Ko 蓷a zu ba ki shiga inda zaki ganta ba ne... Duba.. Idan kika shiga ta wannan 茩ofar."
Ta fa蓷a tana mai nuna mini wata 茩ofar wacce ni dai ban ta蓳a ganin an bu蓷e ta ba, ta ce.
"Da kin shiga akwai 茩ofofi guda biyu, sai ki shiga ta hannun daman ki."
Mi茩ewa na yi na shige ba tare da jin komai ba, nan take ko sai gani cikin wani parlourn wanda ban ta蓳a sani da shi ba, kuma gashi duk a cikin rufi 蓷aya. Ikon Allah!
Ina shiga na du茩a 茩asa na gaishe su ita da wasu ba茩in da na tarar,bayan sun amsa Hajiya ta kalle ni 蓷auke da murmushin samun sabon Grand Son a fuskarta ta ce.
"Beenafah kinga masu haihuwa sun dawo ko? Aziza an haihu na samu Muhammad 蓷ina."
Ni ma murmushin na yi na ce.
"Allah sarki! Allah ya raya..."
"Amin. Su Haulatu sun kai ki kin yi mata barka kuwa?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"A'a, yanzu dai nake batun tafiya."
"To gaskiya kam, ya kamata ki je ki ga Mummaduna."
Mi茩ewa na yi na fito ina wani rarraba ido na cewa Haula.
"Hajiya fa ta tambayeni wai na yiwa Aunty Ziza barka, na ce a'a, shi ne ta ce ya kamata na je....muje dan Allah ku rakani."
"Jiya koda muka je kin tafi saboda haka yanzu aiki muke, kin dai ji yanzu Hajiya ta kirani a waya.."
"Haba mana dan Allah! Muni.."
"Sai dai fa idan za ki jira in wani abu ya shigar damu kije ki yi mata,amma yanzu da ta gan mu bata tunanin aikinda muke za ta 茩ara tula mana wani.... Mts! Sai da fa akace ta koma gidanta amma matar nan ta kafe wai ita sai an yi suna."
Cewar Munira tana mai sauke ruwan zafi daga wuta tana yi tana 茩ara yin mita.
Tsaye na yi shiruuuu! Ina nazari wanda a gaskiya ba zan bari har zuwa wani lokaci ba, tunda har Hajiya ta kada bakinta ta yi mini magana. Da haka na taka na shige ciki kai tsaye na yi nocking,sai da na yi kusan minti uku sannan na ji an ce mini in shiga.
Gabana ne ya yanke ya fa蓷i ganinta zaune tare da Mijinta jiki da jiki yana rungume da jaririn a hannun sa. Cike da mamaki ta yi mini wani kallon ta ce.
"Lafiya?"
Dur茩usawa na yi daga can gefen kujerar farko, murya a sanyaye ganin irin wula茩antaccen kallon da take jifana da shi, na ce.
"Daman Hajiya ce ta ce in zo in miki barka. Allah ya raya.."
"To na gode."
Ina shirin Mi茩ewa na ji tana fa蓷in.
"Ba Za ki 蓷auki babyn ba...."
Kasa matsawa na yi kusa da su akan irin wani kallon da take yi mini ta 茩asan ido wanda ba shiri na mi茩e na juya ina fa蓷in.
"Na gan shi, Allah ya raya."
Da gudu na yo waje kamar zan kifa yayin da na ji wani sabon tsoron ta ya 茩ara cika mini zuciyata. Tunani ne ya juye zuwa wani bigire na daban. Komai ta yi shi cike da taku ba tare da ya gane ba. Domin tunda na shiga ya kalleni sau 蓷aya bai sake kallon inda nake ba har na fito, yana jin kalamanta kamar da gaske a baki amma zuciyarta ba haka bane.
Ina fitowa, Emraan 蓷in ya kalli Ziza ya na murmushi ya girgiza kai ya ce.
"Ni wallahi yanayin yanda yarinyar nan ke baya-baya da mutane ne yake bani dariya. Magana ma can ciki kamar wacce akace za'a cinye Namanta 蓷anye..."
"Ashe su Mummy Na'ima suna hanyar zuwa? ta yi mini waya 蓷a zu."
Ta yi saurin tare numfashinsa da wata maganar don bata so ma yaci gaba da yi mata zancen banza.
Saman jikinta ya 蓷aura jaririn ya mi茩e yana fa蓷in.
"Allah ya kawo su lafiya. Hairiyyah ma haka tace mini yau za ta taso... To amma mutanen Kebbi fa?"
Wani kallon ta mi shi sannan ta ce.
"Mutanen Kebbi baga su Mummy Raliya nan ba! Tun jiya fa suka iso..Su Aunty Darajja ne suka ce sai gobe. Sannan su Daddy Ashraf ma ai tun jiya suka iso kuma ka gan su."
Murmushi ya yi ya ce.
"Eyyah! Sorry, wallahi ban lura ba kin san jiya abubuwa sun yi yawa,kuma ba wanda ya sanar mini, amma su Daddy Ashraf kam jiya muna masallaci har aka gama sallar Isha....Bari yanzu na je na gaishe da su Mummy Raliya 蓷in."
Ya 茩arashe maganar yana mai nufar 茩ofa.
Ita kuma sai wani hararenshi take 茩asa-茩asa wanda ita kanta bata san dalili ba.
Ni kuma, a parlour na ci karo da su Aunty Labiba,cikin farin ciki na 蓷auki Hanan sama ina fa蓷in.
"Hanan Oyoyo!"
Da murmushi Aunty Labiba ta ce.
"Beenafah. Halan wurin ganin Babyna kika je?"
Gya蓷a kaina na yi ina murmushi na ce.
"Eyh, na ganshi kyakkyawa ne, Allah ya raya."
"Amin...ga Aunty Nadeeyah ki gaishe ta."
Ta yi maganar tana mai kallon wata kyakkyawar mata dake gefen ta 蓷auke da yarinya a kafa蓷arta wacce tayi bacci,da alama za ta yi shekara biyu zuwa uku.
Du茩awa na yi na ce.
"Ina kwana!"
Da murmushinta ta ce.
"Lafiya, sannun ki?...."
Ihun Munira na ji a bayana da gudu tazo wurin wacce aka ce in gaishe ta ta rungumeta ta ce.
"Oyoyo.. Wayyo Allah Aunty Nadeenmu ta zo..."
Janyewa tayi tana dariya ta ce.
"Dan Allah 茩yaleni kada ki tada mini da yarinya.. Ai tun jinya na zo ina gidan Aunty Labiba abina..."
"Allah sarki! Kai Aunty Nadee! Ina su Dija?"
"Sun shiga Sashen Hajiya Yanzu."
"Tau yayi, sannu da zuwa.."
Harara Aunty Labiba ta maka mata ta ce.
"Wato kin ga uwar 蓷akin ki ni kin share ni ko..?"
"Innalillahi! Aunty Labiba sannu da zuwa ina kwana..."
Fitowar Ya Emraan ita ce ta katse mana moment 蓷in, wanda a tare suka koma cikin 蓷akin Aunty Ziza mu kuma muka wuce waje bayan Munira ta ajiye abin da ya kawo ta.
Zaune nake a bakin famfo ina wanke kayan miya amma kuma abinda Ziza ta yi mini ne ya tsaya a tunanina. Ina cikin tunani naji murya Munira a kaina ta na fa蓷in.
"Wannan ita ce Aunty Nadeeyah, daga Aunty Labiba sai ita. A Kaduna take aure itama.....ita wannan 蓷in ta ma fi Aunty Labiba sanyi da sau茩in kai..."
Wani kallon kin ma rainawa kanki wayau na yi mata sannan na girgiza kaina na ce.
"Wannan zancen banza ne, domin wallahi ko mi za ki ce nasan ba za ta kai Aunty Labiba ba..."
Muna nan bakin famfon muna ta gardama sai ga Aunty Nadeeyah ta zo da kanta. Duk ma'aikatan da ke wurin da sauri suka zube kan 茩afafunsu suna ta famar mi茩a gaisuwa.
Bayan sun gama gaisheta ta mi茩owa Munira takarda tana fa蓷in.
" Kin san fa ke wani lokacin kin cika shiririta Munira, Hajiya ta yi ta kiran wayarki amma ba ki 蓷aga ba."
Da sauri ta ce.
"Eyyah, tana can kan Window..."
"Yi maza ga Sule can ya kaiki ki amso wannan kayan kasuwa, na ga Haula aiki ya yi musu yawa. Ga ba茩i da yawa suna hanya."
"Tau Yanzu kuwa.."
茒aki ta koma bayan Aunty Nadeeyar ta wuce ta 蓷auko hijabinta wanda ni already da hijabina a jikina ta kalle ni ta ce.
"Ta shi muje mu dawo."
Girgiza kaina na yi na ce.
"A'a. Kije dai ki dawo... Kalli fa yawan kayan miyan nan? Ki je kafin ki dawo na kambala.."
Tsuke fuska ta yi ta ce.
"Kinga ke matsalar ki ko? Koda sun zo sun ga bamu 茩arasa ba ai dole su yi shi da kansu..."
"Ni dai A'a... Kin san da wuri nake wucewa domin makarant..."
Munira wani lokacin haka nake ganinta kamar tana da motsin 茩wa茩walwa, ina kan magana ta janyo ni daga inda nake zaune ta shiga kabta rantsuwa akan cewa dole sai na rakata,hakan yasa na bita muka tafi ina ta tunzuro bakina.
Kasuwar Tudun Wada ce muka taho, duk inda muka tsaya iyaka ta mi茩a a duba a zubo mana kaya, wanda duk zuwan da muke ni dai ban ta蓳a ganin sun bayar da ku蓷i ba, iyaka a kar蓳o kaya wasu-wasu ne kawai suke bada ku蓷i da alama 茩ila daga can sama suke tura musu da ku蓷insu.
Muna tsaye ana tuttula cabbage a kwali wanda shi ne abu na 茩arshe kawai na ga mutum ya bayyana a gabana. Yanda ya tsura mini ido yana kallona nima haka na zuba mishi nawa idon yayin da zuciyata ta shiga bugawa da 茩arfi, 茩wa茩walwata ta shiga hasko mini hoton fuskar sa a ranar da muka rabu na 茩arshe yana 蓷aga mini hannu.
Cikin tsananin shock muryar shi har tana har蓷ewa ya ce.
"BB.. Beenafah!!!"
Rungume shi na yi cike da ru蓷anin 茩wa茩walwa na ce.
"Yaya Ashiru!!!... "
Da 茩arfin tsiya Munira ta janyo ni baya tana zaro ido waje ta ce.
"Ke! Kin haukace ne? Wannan baligin za ki runguma?"
Ha蓳a na rawa na shiga nuna shi da yatsa yayinda idona ya cika da ruwan hawaye na ce.
"Shi 蓷in Yaya na ne..."
Hannuna ya sake raruma ganin abin tamkar a mafarkin sa ya ce.
"Be.. Be.. Beenafah dan Allah ke ce? Ke ce Beenafah? Da gaske ke ce ko? Dan Allah ki fa蓷amin gaskiya cewa ke 蓷in ce ba aljana ba ce Beenafah.."
Da wani irin sabon 蓳acin rai Munira ta 茩wace mini hannuna tana mai yi mai wani irin kallo ta ce.
"Wai malam kana da hankali kuwa? Garjeje da kai za ka wani kamata ka ri茩e ta. Ka fa蓷a mata duk abin da za ka fa蓷a mata da fatar baki mana. Mts!"
Tamkar wasu kuramen da basa gane komai sai yaren junansu haka muka 茩urawa juna ido musamman shi da yake ganin kamar ba ni ba, domin na yi matu茩ar canja masa ta fuska da yanayin jiki gaba 蓷aya. Idanunsa cike da hawaye ya ce.
" Dan Allah ki fa蓷a mini cewa da gaske ke ce Beenafah ba mafarki na ke ba..."
Jinjina kaina nayi domin ba shi tabbaci na ce.
"Wallahi ni ce Beenafah a gaske Yaya Ashiru ba mafarki kake ba...."
"To ina kika shiga tsawon lokaci? Rana, dare, sanyi, zafi, damana da iska, wa蓷annan duk ba su hana mini neman ki ba, ina kika shiga haka?"
Hannayena na saka na share hawayena ina girgiza kaina na ce.
"Gida Muka canza Yaya Ashiru, a ranar da muka dawo daga asibiti muka canja gida.."
"To ina wayarda na baki? Laifin me tayi da kika kashe ta kika hana mini jin labarin ku?"
"Wallahi tallahi ba kashe wayar nan na yi ba Yaya Ashiru, Bahrain ne ya danna ta ta shiga wani wuri sai layin ya rufe,."
"To amma Beenafah ai inda kin cire Layin kin kunna wayar za ki ga number ta ta fito gidan kira ko ba suna...."
Ji na yi Munira taja hannuna tana fa蓷in.
"Dan Allah ki wuce muje hakanan, wallahi Hajiya bata son irin wannan, idan ta ji za ta yi fa蓷a..."
Da 茩arfi ya zo ya fisge hannuna rai a 蓳ace ya kalli Munira ya ce.
"Ke dan Allah Malama ki saketa, kuma ki rufewa mutane wannan bakin naki. Kin san abin da yake tsakanina da ita ne da har zaki zo ki wani tsaya a gabana kina nema ki tunzurani.."
"Ka yi ha茩uri Yaya Ashiru, don bata san ka bane kaima kuma baka santa ba..."
Wata uwar hararar ya maka mata sannan ya dawo da kallon sa gareni ya ce.
"Naga tana neman ita dole sai ta rabani dake... Wai har da wani cewa Hajiya ba ta son haka, a'a ba Hajiya ba wallahi makawuya..."
Zaro Ido na yi ina mai dafe 茩irji na ce.
"Dan Allah ka daina Yaya Ashiru ka yi ha茩uri..."
Wani irin uban tsaki Munira ta buga tare da galla mishi wata uwar harara sannan taje ta kar蓳i sauran kayan ta saka a booth ta shiga mota ta zauna.
Kallon shi na yi cikin jin wani irin sabon yana yi, domin yanda ya ga na canza masa shi ma haka naga ya canza mini sosai kamar ba shi ba, ya 茩ara 茩iba ya yi kyau. Na ce.
"Yaya Ashiru ni ma na yi ta neman ka, duk inda Napep za ta bi ta wuce sai na yi ta kallonta da saka ran cewa kai ne a cikinta, amma kuma wayam haka zan ga ba kai 蓷in ba ne.."
"Allah sarki! Yanzu ki fa蓷a mini ina ne gidanku, domin wa蓷annan maganganun duk ba za su yiyu a nan ba,...."
Horn 蓷in Oga Sule shine ya ja hankalina na kalli inda motar take sannan da sauri na ce.
"To ka bani numbernka zan kira ka da wayar Ya Jafaru idan na koma gida...Yanzu sauri muke an aikemu."
"To bari na bi ku a baya mana, sai in cim miki a gidan.."
Da sauri na girgiza kaina ina 蓷an zaro ido na ce.
"A'a. Can 蓷in ba gidanmu ba ne, gidan da nake aiki ne, ka bani numbern zan kira ka idan na koma gida."
Lalabe ya fara ko zai ji biro amma kuma tunda ba'a kasuwa yake ba yasan ba zai samu ba,hakan yasa cike da hanzari ya ciro wayarsa daga aljihu ya sake zare simcard 蓷aya ya bani ya ce idan naje na saka zai kira ni zuwa yamma, ko kuma duk sanda na saka simcard 蓷in in duba zanga numbern Umma sai in kira.
Daga haka muka rabu, wanda har bakin motar ya zo ya bu蓷e mini na shiga yana ta 蓷aga mini hannu har sai da na daina ganin sa.
Daga ni har Munira babu wanda ya yi magana har muka shiga gidan na wuce 蓷aki na kwanta shiru ina ta tunani.
Wani irin jim茩e Simcard 蓷in na yi a cikin hannuna tamkar wadda akace za'a 茩wace mata shi.
Sai da muka kambala cin abinci, ina batun tafiya gida Munira ta kalle ni ta ce.
"Waye shi 蓷in?"
Kallonta na yi, ina mai jin ba da蓷i akan abin da ya faru 蓷a zu na ce.
"Ki yi ha茩uri."
茒an murmusawa ta yi tare da jinjina kanta ta ce.
"Ba komai."
Daga haka na yi musu sallama na tashi na wuce.
****
Da gudu ya juya ya koma gida jiki na rawa ya taradda su Ayya cikin tsananin 蓷oki da murna ya ce.
"Ayya! Alhamdulillahi Rabbil Alameen! Allah yau ya bayyanar mini da Beenafah... Wallahi na ganta Ayya... Umma! A kasuwar Tudun Wada na ganta tana siyayya...."
Ido Ayya ta zaro waje tare da saka hannaye ta dafe 茩irjinta ta ce.
"Na shiga ukuna ni Ayyatu ya sake gamo da wannan hatsabibiyar a karo na biyu bayan mun shafe tsawon lokaci muna wahalar nema masa magani.."
Jiki na rawa ya matso gaban Ayya ya ce.
"Wallahi tallahi da gaske nake, ba Aljana ba ce mutum ce. Yanzu haka na bata Layina na ce idan ta saka ta kira Umma...Ayya wai kinga Beenafah yanda ta canza?"
Cikin gatse ta ce mishi.
"Ban ganta ba sai kai..."
Jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce.
"In Sha Allahu kuwa zan kai k..."
Mi茩ewa ta yi da sauri tana fa蓷in.
"Allah ubangiji ya tsareni nikam, ai wallahi an yi 蓷aya ba za a koma ba."
Daga haka ta shige 蓷aki ta bar shi nan tare da sauran mutanenda suka yi shiru suna sauraren su tare da Umma.
A hankali Umma ta kalle shi ta ce.
"Shin yanzu ina kayan Jallof 蓷inda kace a bari kaje ka siyo?"
Dariya ya fara yana wani sosa bayan kan shi ya ce.
"Umma! wallahi ni nama ru蓷e, kwata-kwata na manta da cewa siyayya na je. Amma bari na koma yanzu-yanzu na siyo..."
Har ya kai 茩ofa sai kuma ya dawo ya kalli Umma ya ce.
"Umma dan Allah ki ajiye wayarki a kusa, Beenafah za ta kira in sha Allahu..."
Cike da tuhuma Umma ta ce.
"Ka tabbata Beenafah ka gani Ashiru?"
"Wallahi na rantse da Allah ita ce Umma, bari ai dai za ku gani."
****
Ni kuma, Ina zuwa gida na fa蓷a jikin Ammie ina fa蓷in.
"Ammie wallahy yau na ga Yaya Ashiru a kasuwar Tudun Wada..."
Zaro ido Ammie ta yi tace.
"Da gaske Beenafah?"
"Wallahi kuwa Ammie. Kawai ban lura ba muna cikin siyayya kawai naga mutum gabana.... Kinga ma wani Layin ya bani ya ce in sa a waya zai kirani, ko kuma in kira lambar Umma akwaita a ciki.."
Na 茩arashe maganar ina mai warwaro simcard 蓷in daga cikin hular kaina na nuna mata.
"Alhamdulillah! Ha茩i茩a komai nisan dare gari zai waye. Ni ma ina so in gansa da iyayen shi in 茩ara musu godiya..."
"Sosai kuwa Ammie. Bari na je idan Ya Jafaru nan ya ara mini wayarsa in saka in kirashi....shin yaushe ma ya ce zai wuce makarantar?"
Tana janyo ledar abincin da na ajiye ta ce.
"Gobe fa zai tafi. Baki sani ba daman?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"Na sani. Kawai dai na manta ne tsabar ru蓷ewa wallahi... Bari naje na ji idan yana nan."
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍