Free chapter 路 Read without an account

PAGE 23

by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO

GANIN IDO 馃馃

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

     OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671

FREE-BOOK

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel 蓷inmu na tafe in sha Allahu zamu ri茩a yi muku posting gaba 蓷aya free books 蓷inmu wa蓷anda babu algus....

PAGE 23

  A hankali Hajiya ta taka ta mi茩awa 蓷aya daga cin ba茩in nata babyn kawai ta juya cike da jin 蓳acin rai ta koma gefenta.

Ni kuma tsaye kawai nake tare da sadda kaina 茩asa, a irin yanda na ji na muzanta da ace lokacin da ne da yanzu na fara kuka, amma kuma tunawa da irin garga蓷in da Haula ta yi mini sai yasa na dake kawai na ha蓷e raina ina jiran in ga 茩arshen gudun ruwanta.

茒orawa ta yi da fa蓷in.

"Kuma ana ta aiki ke shafaffa da mai kullum da kinzo ki yi wani sharar gulma sai ki kama ki koma gida, da 茩arfe biyu ki bar en wahalar ki su ci gaba da yi miki wahala ko? To wallahi tun da ba zane kika fi su ba, dole ki ri茩a tsayawa har dare sannan ki tafi kinji umarnina daga.... "

Hannun Hairiyyah ma茩ale dana Emraan suka shigo cikin Parlourn, hakan yasa Ziza saurin ha蓷iye sauran maganar ta tana mai fuskantar Emraan da murmushi ta ce.

"Emraan! Ga su Safinar ku gaisa."

Shima 蓷in ita yake kallo da mamaki sai kuma ya kalleni ya kalli mutanen da ke 蓷akin ya sake mayar da kallonsa gare ta ya ce.

"And what's going on here na Ji Kamar kina Ihu Ziza?"

Waskewa tayi tana wani murmushi ta ce.

"No! Ni wai? Ba komai.."

Kallona Hairi ta yi ta ce.

"Pretty, miye kike a nan? Kin kambala mini gyaran 蓷akin ne?"

Ban san dani take magana ba, domin ban sanni da wani suna wai shi Pretty ba, amma kuma jin ta ambaci kin kambala mini gyaran 蓷akin ne yasa na 蓷ago na kalle ta ina mai jinjina kaina alamar eh.

"To miyasa kika tsaya a nan?"

Kallon Aunty Ziza na yi na ce.

"Aunty Ziza ce ke magana dani..."

"No... You can go ai, shikenan."

Kallona ya yi cike da kulawa yace.

"And why are you sad?..."

Ganin yanda na yi masa wani kallon yasa ya girgiza kansa ya ce.

"I mean.... Miyasa kike cikin damuwa?"

Muryar Hairi na ji tana fa蓷in.

"And da fushin nan bakya yin kyau pretty. Je abinki Kawai...Ya Emraan kasan wani lokacin rayuwar farin ciki wani lokacin kuma akasin haka."

Tamkar an kwance mayunwacin Zaki daga sar茩a, haka na saka 茩afa kamar walkiya na fice daga 蓷akin.

Gaisawa ya yi da ba茩in da suka dawo tamkar hoto a zaune suna kallon mu tun蓷azu tana ta tijara tamkar ba mai haihuwa ba. Bayan sun gama yi masa barka ya juya ya koma still ri茩e da hannun Hairi, daman saboda ya gaisa da ba茩in ne yasa ta kira shi a waya ya zo.

Suna fitowa ya kalli Hairiyyar yana murmushi ya ce.

"And why did you give her the name?"

"huh! Kana nufin wai Beenafah?"

Jinjina kansa ya yi ba tare da yayi magana.

Itama dai jinjina kan nata ta yi sannan ta 蓷an 蓷age shoulder tare da ware hannayenta ta ce.

"Nothing, kawai dai she deserves to be call pretty,because ita 蓷in mai kyau ce da gaske, and beside...Aunty Labiba ta bani labarinta tana da kirki sosai kamar dai sauran ma'aikatan gidan nan."

"And wai ita kowa sai ta bashi labarin wannan yarinyar ne? Miye yasa haka?"

Dariya Hairi ta fashe da ita tana jinjina kanta ta ce.

"Tun ina UK ake bani labarin Beenafah har na dawo, Aunty Nadee ma naji jiya tana ta mata mita wai ita bata san miye yake damun Aunty Labiba ba wanda bata da wani zance saina mai aiki, shi ne fa Aunty Labibar tana dariya tace wallahi babu abinda yake tsakanin su sai alheri, kawai dai yarinyar ta burgeta ne da kuma darajar Biba..."

"Biba....kina nufin Yarinyar Inna Ramatu?"

"Eh, ita fa. Wai ita ce ta kawo mata ita."

Jinjina kai ya yi sannan ya kalle ta ya ce.

"Ki koma Aminiya, ina da wasu ba茩in da dole zan yi attending na su."

A nan ta tsaya tana 蓷aga mishi hannu ta ce.

"OK amini, Bye."

Ni kuwa, A 蓷aki na samu Haula ita ka蓷ai tana bubbu蓷e 蓷inkuna masu kyau na Leshi.

Kallona ta yi ta ce.

"Sai yanzu? Kinga kayanmu in ji Hajiya, yanzu Lawan ya kawo su."

Murmushi kawai na yi amma ba don ina jin da蓷i ba,domin na ji haushin abin da Aunty Ziza ta mini ba ka蓷an ba.

"Miye kuma? Na san dai Hairiyyah ba ta da matsala..."

Ina kallonta na ce.

"Itama '拼ar Hajiya ce?"

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Auta Jaja manya kenan, 蓷iyarta ce, ita ce auta. Ga ta蓳ara ga kirki ga kuma shagwa蓳a. Suna matu茩ar matu茩ar ji da ita sosai musamman Ya Emraan cewa yake ita ce babbar 茩awarsa Aminiyar sa, kinga yanda take damu? Kamar wa su abokan wasanta,musamman Munira, haka za ta kiramu 蓷akin ta muyita fira, sai taga dare ya yi sosai ta ce wallahi babu inda zamu sai mun gyara mata 蓷akinta zamu fito......"

"Wannan matar ta jiya fa da ta ce in zo in goge ruwa ya zube?"

"Au! Mummy Na'ima kike nufi wai? Matar Baba Ustazu ce shi ne 茩anin Alhaji marigayin gidannan."

Wucewa na yi na shige na yo alwala na zo na tayar da Sallah.

                            ****

Haka muka yi ta aiki wanda dolena na dinga tsayawa sai Magrib sannan in koma gida domin sai da ta 茩ara jaddadawa Su Munira amma bana tunanin su Hajiya sun san da wannan.

Gidan ya cika sosai, mutane babu kalar da babu da masu kirki da marasa kirki, wata idan ta saka ki aiki tamkar ta samu Engine ba bu abunda ya dame ta. Wannan dalilin ne yasa dole bazan iya zuwa bukin gidansu Yaya Ashiru ba domin rana 蓷aya ake yi dana Aunty Ziza.

Daren da nake yowa yasa bana samun ganawa da Yaya Ashiru, sannan shi ma Ya Jafaru ya canza mini sosai wanda har abin ya fara damuna. Ko wayarsa na ce ya ara mini sai yace mini bata da caji ko kuma yace wani abokinsa ya ara.

Bayan na fa蓷awa Ammie cewa ba zan samu zuwa gidan su Yaya Ashiru ba, shi ne ta ce ita dole sai ta tafi ita da Bahrain, ni kuma hakan yasa dole ba zan iya barinta ta hau 茩arfe taje wani wurin ba tare da ni ba, hakan yasa na ce mata yau daga zaran naje sunan duk yanda zan yi zuwa 茩arfe biyar ta jirani zan dawo mu tafi.

Koda na je gidan ya ilahiy! Ya cika ma茩il ana ta hidima, wai bahaushe yace masu abu da abun su, 蓷an fari a wurin Emraan Attahiru Araam. Su kansu mutanen gidan shaida ne akan yanda Hajiya take tsananin 茩aunar Emraan,da kuma aka zo aka haifo mata jika daga tsatsonshi sai taji 茩aunar da take yiwa jairirin har ta zarce misali, sannan kuma uwa uba ga shi Muhammad.

Su Aunty Labiba da yaransu, dangin Aunty Ziza da kuma dangin Hajiya sun taru sai farin ciki suke suna taya murna. Tunda nake da su, yau ne rana ta farko da na ta蓳a tu蓳e kayana nayi wanka a gidan muka shirya a tare cikin 蓷inkin da aka yi mana mai kyau.

Muna nan dai a 蓷akinmu sai zuba uwar fira wanda sai idan za'a yi wani abinne muke ta shi mu fita. Ni daman yau na yi al茩awari na kuma ro茩e su alfarma na cewa dan Allah kada su ce na shiga cikin gidan nan domin ba zan shiga ba In Sha Allahu har na koma gida.

Ina nan ma sai ga Adeel ya shigo nemana, nan muka lalace dani da shi yana ta bani labari ina dariya.

Sai da hu蓷u tayi na yi sallah sannan  na kamkanta kayana, duk wani abin da Haula ta kawo mini da sunan nawa ne na tattara gudan kaya na ce musu na wuce gida. Munira sai tsiya take mini wai sai ta fa蓷awa Aunty Ziza tace na wuce tun ba'a gama bukin sunan 蓷an gold ba.

Hijabi na Sanyo na hawo mashin daga can zuwa gida, ina zuwa na cire na sanya gyalen Lace 蓷in na 茩ara gyara fuskata wacce ba komai sai farar powder da lipstick muka fito mu hu蓷u da niyyan zuwa mu hau Napep har da Farisa da tace tana zuwa.

Wani irin girgiza Zuciyar Ya Jafaru tayi a lokacin da idanuwansa suka yi tozali dani. Tunda nake bai ta蓳a ganina da gyale ba sai yau, sannan kuma gashi daman na 蓷an 茩ara samun gogewa a abubuwa da dama ba kamar da ba.

Take yaji duk wani 蓳acin randa na sanya masa ya gafarta mini.

Baki kamar gonar auduga ya kalleni wanda da alama ya manta cewa har da Ammie muke yace.

"Masha Allahu! Beenafah 茩arshen kyau kenan...da an ce Beenafah to an kai 茩arshen magana. Ammie bukin ne aka fito? To Allah ya tsare...."

Ina murmushi na ce.

"Na yi kyau dai kenan ko Ya Jafaru?"

"Haba!...."

A hankali muka ga mota ta iso ta parker inda muke tsaye kowa 蓷auke da mamaki a fuskarsa.

Wani irin mugun ha蓷e rai Ya Jafaru yayi ganin Yaya Ashiru ya fito a hankali daga motar yana murmushi ya ce.

"Ammie ina wuni?"

Itama da murmushin ta ce.

"Lafiya lau Ashiru. Ya hidima kuma? Allah yasa alheri?"

"Amin Ammie. Daman cewa na yi bari na zo na tafi daku tunda baku san wuri ba kada kuje kuyi ta wahala."

"Amma Ashiru baka 蓷aurawa kanka wata wahala ba? Ai da ka bar shi munzo a Napep.."

Hannu ya mi茩awa Ya Jafaru yana murmushi yayin da Ya Jafarun ya gimtse sosai suka gaisa.

茦ofar motar ya bu蓷e wanda Bahrain har ya jima ciki tunda ya bu蓷e ya fito ya shige ciki yace mana.

" Ku shiga Ammie mu tafi yamma na 茩ara yi. "

Cikin motar Ammie tashiga, sannan Farisa, sai kuma ni da na kasa ce masa komai sai murmushi nake na shiga sannan ya rufe.

Ya Jafaru dake tsaye ji yayi wani ba茩in ciki ya taso ya tokare masa ma茩ogwaro...wata zuciyar na ingiza shi akan ya shiga motar shima ya bimu, wata kuma zuciyar na ce masa a'a Jafaru! Kai dai yi zaman ka, kana nan zaune zaka ga sun dawo.

Da haka na yi ta 蓷aga mishi hannu har muka wuce. Bakin bishiya ya kama ya zauna yana jin a zuciyar shi ba zai iya 蓷agawa ko'ina ba sai idan ya ga mun dawo.

Shi wallahi a yanzu yama rasa wane kalar tunani ya kamata ya yi. Ko Makaho ya lalaba tsakanin Beenafah da Ashirun nan yasan cewa Ashiru sonta yake... Wata irin zabura ya yi da 茩arfi ya furta.

"Kai! Inaaaa! Wallahi tallahi wannan 茦arya ce ma."

Daga haka ya sake komawa ya zauna yana mai 蓷ora hannayensa akan gwiwoyinsa ya buga wani uban tagumi yana tunani.

Duk irin labarin da take bashi akan Ashiru bai ta蓳a hasko abin ta haka ba, tun ranar farko da Ashiru ya zo suka tsaya suna wannan firar tun a ranar ya tsinci kansa cikin matsanin ba茩in cikin da har bacci sai da ya hana shi. Ya hana mai walwala, babu abin da yake gani da ji idan ba firar su ba ta ranar.

Ya kasa zuwa makaranta, tun ranar Kawunsa ke kiran sa amma ya kasa 蓷agawa domin bai ga ta tafiya yabar gari ba domin wallahi ba zai ta蓳a yarda ya yi sake ayi mishi sakkiya ba.

To amma kuma ina mafita? Mafita 蓷aya ce mafitar da bai san ya ma zai iya fuskantar ta ba a yanzu amma kuma dole ya yi wani abu idan ba haka ba wallahi yana nan tsaye yana kallon ruwa kwa蓷o zai masa 茩afa.

                            ****

Yaya Ashiru bai tsaya ko'ina damu ba sai 茩ofar gidansu inda muka tarar mutane da yawa sai kai kawo ake masha Allah ana ta hidima.

Cikin farin ciki da wani alfahari yake nunawa duk wanda muka ha蓷u da shi ni yana fa蓷in ga Beenafah su gaisa.

茦ofar Umma aka yi mana shimfi蓷a muka zauna wanda ni sam na kasa ganewa, domin mutane sai watsewa suke a hankali suna barinmu a zaune. Ummar ce ta fito daga cikin 蓷aki ta zauna a gefena, fuska cike da murmushi ta ce mana.

"Hajiya! Sannu da zuwa."

"Yauwa Maman Ashiru sannu, ya gida ya bayan rabuwa kuma?"

Umma ta ce.

"Alhamdulillah! Sai godiya. Ya kuma jiki?"

"Jiki Alhamdulillah! Sai godiyar ubangiji. Ana ta hidima ashe? Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya."

"To amin amin ya Allah. Mun gode sosai Allah ya saka da alheri..."

Muryar Ashiru muka ji yana ta 茩wala kiran Ayya amma kuma babu ita babu labarinta. Da kanshi ya dinga kiran mutanen gidan muna gaisawa, sai wani kallona suke tamkar sunga wata sabuwar halitta har sai da naji har cikin raina na tsargu.

Abinci aka kawo mana da ruwa wanda gaba蓷ayanmu babu wanda ya ta蓳a sai Bahrain ne ma ya 蓷auki lemu 蓷a蓷a蓷aya da shi da Farisa suka fasa suna sha.

Kallon Ammie na yi ganin kowa ya kama wata sabgar domin har Umma an kira ta wani wuri, ganin hakan yasa murya a 茩asa-茩asa na ce.

"Ammie ta shi mu tafi gida."

Gya蓷a kanta ta yi sai muka mi茩e a tare muna kiran zamu tafi. Fitowa Yaya Ashiru ya yi daga can cikin wani 蓷akin da ya shiga tun蓷azu ya ce mu shigo mu gaisa da Ayya.

茒akin cinjim yake da mutane wanda ashe har Amaryar tana ciki. Nan muka sake shiga wani babin gaishe-gaishe,daga can 茩uryar 蓷aki 茩arshen gado Ayya take yi mana magana ciki-ciki kamar ba ita ce ta ta蓳a zuwa gidanmu tana surutu tamkar an kunna redio FM ba.

Dubu uku Ammie ta mi茩awa Ayya tace a sai wa Amarya tsintsiya Allah yasa albarka ya bada zaman lafiya.

Har waje wasu daga cikin su suka rakomu suna mana godiya yayin da wasu kuma suke ta baya-baya damu.

Da kanshi ya sake 蓷aukarmu ya maishe mu har 茩ofar gida wanda har lokacin ashe Ya Jafaru yana nan inda muka bar shi yana zaune.

Yana ganin mun fito motar ya zo yana mai kar蓳ar ledar da take hannuna ya ce.

"Sai yanzu?"

Murmushi na yi na ce.

"Mun da蓷e ne Ya Jafaru?"

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Gaskiya dai kam."

Gida Ammie ta shige tabarni ina magana da Ya Jafaru wanda bamu ankare ba muka ji horn 蓷in Ya Ashiru.

Juyawa na yi na koma gefen driver na tsaya jikin window na ce.

"Yaya Ashiru mun gode sosai."

Jinjina kan shi yayi da murmushi ya ce.

"Ba komai Beenafah ai ni ke da godiya, na gode sosai. Sai na dawo.."

"Yaushe kenan?"

"Uhm! Ni ko gobe kika ce na dawo zan dawo...beside yau an riga an gama komai kinga na zama free."

"Eyyah ni kuma Kaga Alhamis da juma'a ne ka蓷ai nake gida domin sauran ranaku ina makaranta."

"To yanzu sai Alhamis kenan?"

Gya蓷a kaina na yi na ce.

"Eh, zai fi."

"To Allah ya kaimu."

"Amin, sai anjima na gode."

Idon Ya Jafaru 茩yar a kaina koda na juyo, gashi ya wani ha蓷e rai sosai kamar ba shi ne yanzu yake mini murmushi ba.

"Beenafah!"

"Na am"

Na amsa ina kallon shi kamar yanda shi ma ni yake kallo ya ce.

"Wane ne wannan a wurin ki?"

"Uhmmm! Wai Yaya Ashiru kake nufi?"

"Eh"

Ya bani amsa kai tsaye.

"Yaya na mana, wanda ya taimaka mana."

"Bayan wannan dalilin fa Beenafah?"

Ba tare da sanin inda maganar sa ta dosa ba na ce.

"Ba wani dalili."

"Kin tabbata Beenafah?"

Gya蓷a kaina na yi na ce.

"Na tabbata."

Cikin jin wani irin sanyin da ya jima bai ji irin sa a zuciyarsa ba ya lumshe idanunsa a hankali sannan ya bu蓷e su a kaina yana mai kwantar da murya sosai cikin yanayinda ban ta蓳a jin muryar sa a haka ba yace.

"Bani da wani za蓳i Beenafah, ya zama dole gobe in tafi Zaria, Kawu har ya yi fushi sosai akan rashin zuwana...."

"To wai ni abinda ya hana ka tafiyar ne ya bani mamaki Ya Jafaru..."

Wani guntun Murmushin ya saki yana girgiza kansa ya ce.

"Ko na fa蓷a miki dalilina yanzu ba za ki fahimta ba Beenafah... Zo.. Zo mu zauna a nan."

Ya 茩arashe maganar yana mai samun bakin bishiya ya zauna nima ya nuna mini gefen sa yace in zauna.

Wani irin rikitaccen kallo ne ya bini da shi har sai da na ji zuciyata ta tsinke domin a tunanina wani laifin na aikata masa.

" Beenafah ki yi mini al茩awarin cewa daga gidan aikin ki sai Islamiyyar ki ka蓷ai za ki ri茩a bai wa muhimmanci, duk wani mutum ko waye shi ba za ki tsaya kina 蓳ata lokacinki wurin tsayawa magana da shi ba..."

"Haba! Ka sanni ai Ya Jafaru, ni bani da wannan rayuwar, ko mazan da suke ajinmu a islamiyya babu wanda nake magana da shi in dai ba ta kama ba. Sannan gidan aikina ma su kansu suna da doka,babu wacce ta isa ta tsaya da namiji suna fira koda a wajen gidan ne."

Cikin jinda蓷in fahimtar sa da nayi yasa shi sakin murmushi ya ce.

"To na gode Beenafah, zan ri茩a kira da wayar Mama sai ta baki muyi magana a duk sanda na tashi, kema kuma idan kina so ki yi magana dani za ki iya 蓷aukar wayar ki yi mini plashing kai tsaye kinji ko."

"In sha Allahu Lauyanmu na gobe, Allah ya taimaka ya bada sa'ar abinda aka je nema.."

"Amin. To amma ke baki da wani al茩awarin da kike so na ri茩e miki ne Beenafah??"

Cikin seconds na 蓷an wawwara ido nayi nazarin maganar sannan na jinjina kaina ina murmushi na ce.

"Al茩awari 蓷aya Ya Jafaru, kada ka biyewa abokan banza, kamar yanda Ammie ke yawan gaya mini, abokan banza sune babban jigon da ke taka rawa wurin ta蓳ar蓳arewar tarbiyyar yaro duk yanda kuwa ya samu training a gida. ka mayarda hankali akan karatunka kamar yanda kake fa蓷a mini nima."

Wani abu yake ji yana 茩ara girmama a zuciyarsa fiye da yadda yake tunani musamman wannan firar da mukayi, ta tsaya a cikin ranshi tare da sake haska mi shi wata sabuwar hanyar da bai san tana existing ba a cikin duniyar sa.

Muna nan zaune muna ta fira har sai da aka fara kiran Magrib sannan ya ce na tashi na shiga gida.

Washegari koda na fito na shiga gidan wai har yayi sammako ya wuce zuwa Zaria. Fatan alheri na yi musu sannan na sa kai na wuce.

Ko bayan da aka gama sunan Muhammad (Abeer) sai da muka kwashe tsawon sati muna aiki sosai sannan daga baya muka samu sassauci bayan mutanen da suka zo kowa ya watse sai en tsirarrun da suka rage ne ba su tafi ba.

Maimakon Aunty Ziza ta canja daga halin da take nuna mini tunda Hajiya ta yi magana, ko 蓷aya ba ta sauya ba wanda sai ma 茩aro sabbin wula茩ancin da ta 茩ir茩iro, hatta kofi idan za ta sha ruwa sai ta saka an kirani na zo na 蓷auko mata. Ni kuma abin da bata gane ba, ko ka蓷an yanzu na daina shakkarta tunda na gano abin ta bana arziki bane, duk tayi abu don ta 蓳ata mini rai ko ka蓷an hakan baya damuna wanda ita shi ne abinda yake 茩ara 茩onata dangane da ni, aiki kuwa, idan za ta kwana tana saka ni aiki bana ta蓳a nuna mata komai, kuma ita ko a gaban waye bata shakkar yi mini haka idan ka cire Aunty Labiba da Emraan. Wa蓷an nan mutum biyun sune ka蓷ai idan suna a wuri bata nuna alamun musgunawa a gare ni.

Yauma ina zaune bakin kitchen tare da Haula sai gashi ta kira Haula a waya wai in zo tana nemana. Tashi na yi kai tsaye na shige na ce mata gani.

Flask ta nuna mini tana fa蓷in.

"茒auki ki dafo mini ruwan zafi ki kawo ina jiran ki yanzu."

茒auka na yi ina fa蓷in to,babban kitchen na dawo na bu蓷e wata babbar tukunyar ruwan zafi ina ta wani mitsitstsika ido akan haya茩i su Munira sunata mini dariya na cika flask 蓷in na 蓷auka naje na kai mata na ce ga shi.

Wani kallon sama 茩asa ta mini ta ce.

"kina nufin yanzun nan har kin dafo ruwa?"

Girgiza kaina na yi kai tsaye na ce.

"A'a, a Kitchen na 蓷ebo wurin su Inna Kuluwa..."

"Did I asked you to go there and fetch?? Cewa na yi kije ki kunna wuta ki 蓷ora ki dafasu su tafasa sannan ki juye ki kawo mini."

茒auka na yi kurum na fice naje waje na juyesu a bakin famfo cikin wani bucket duk su Munira suna zaune suna kallona fuskokinsu cike da alamar tambaya.

Kitchen 蓷in ciki na koma naje na kunna Gas kamar yanda Haula ta koya mini na 蓷ora tukunya na tsaya nan jikin 茩ofa har sai da ruwan suka tafasa na juye na kashe sannan na fito naje na kai mata.

"茒auki Abeer kije ki cire masa diaper ki kawo mini shi."

Ta 茩arashe maganar tana mai nuna mini toilet.

茒aukar shi na yi na je toilet 蓷in na tsabta ce shi tas cikin lokaci na dawo na mi茩a mata shi. Wai ita 茩ila a tunaninta zan rikice ne na ce bansan yanda akeyi ba,don ta samu damar ci mini mutunci son ranta. Bata san cewa In Sha Allahu ko ita bata fini sanin yanda ake kulawa da jariri ba, domin lokacin da Ammie ta haifi Sajjad, ni ce na dawo uwar sa ta dalilin halin da Ammie ta tsinci kanta a ciki wanda hatta wanka, bacci, da cin abincinsa duk ni ce, sai da ya bar duniyar sannan na daina kulawa da shi. Saboda haka ni kula da yaro sam baya bani wahala, kuma zan iya jure 茩iriniyar yaro ko yaya yake ko.

Yana da fa Nannynsa ta musamman da aka kawo mata ita kwana uku da suka wuce. Amma don neman fitina ita dole sai ta san yanda ta nemi hanyar musguna mini.

"茒auko ga cup can Ki ha蓷a mini Tea Ki zauna ki fifita mini har sai ya sha iska sannan."

Ina zaune a 茩asa ina fifita mata na ji sautin muryar ta tana fa蓷in.

"Wai har ke Hairi za ta dinga wani zuzutawa! Ina abin zuzutawa a nan? Mai aiki ana biyan ta har wani abin burgewa ke gareta? Hmm! Wai Pretty! Pretty na inda take ke kam sai dai Pretto..."

Tamkar tana magana da iska haka na yi mata kamar ban san dani take ba. Ina nan zaune Haula ta shigo mata da Lunch cikin wani babban tray mai 蓷auke da dishes sun kai kala biyar ta ajiye mata a gefe tana fa蓷in ga abincin ta nan, kallona tayi ta yi mini murmushi nima kuma sai na mayar mata.. Aiko ina wuta ta ka 蓷ani, kawai ta hau bakinta tana fa蓷in wai na raina ta ina kallonta ina yi mata dariya, ita sai na nuna mata abinda na gani a jikinta da yake sakani dariya.

Maimakon in ji tsoro in daina, yanda take 蓷in sai ya 茩ara sakani dariya wanda har bansan lokacin da wata dariyar ta sake su蓳uce mini ba.

Aikuwa jiki na rawa ta mi茩e ta nufo inda nake, kallonta nake da mamaki ina jira inga shin dukana za ta yi ko kuma me. Ganin ta juyo gareni yasa Haula sakin dariyarta a hankali tana yi tana toshe baki wanda shi ne abu na uku da ya sake bani dariya.

Ficewa tayi fuu! Sai inda Hajiya tana wani huci ta ce.

"Hajiya! Shin ina so in san wani abu. Waccan '拼ar aikin bata san matsayina ba ne a gidannan ko kuwa?"

Ajiye remote 蓷inda ke hannunta Hajiyar ta yi sannan ta kalle ta ta ce.

"Ziza wacce mai aiki kike nufi?"

"Marar kunyar yarinyar da Aunty Labiba ta kawo mana."

"Beenafah kike nufi?"

Da sauri ta gya蓷a kanta ta ce.

"Eh, ita. Hajiya dariya fa ta dinga mini, sai ta kalleni ta tuntsire da dariya..."

Hankali kwance Hajiya ta girgiza kanta ta ce.

"Ba dai Beenafah ba Ziza, ko Munira da nasan tana iya aikata makamancin haka ba za ta yi miki dariya ba ballantana Beenafah da ba ruwanta...."

"Wallahi Haji..."

"Ziza! Samu wuri ki zauna mu yi magana."

Ha蓷iye sauran maganar ta tayi tare da samun kujera wacce ke fecing Hajiyar ta zauna tana kallonta.

"Ki daina shigewa gaban yarinyar nan Ziza, Hairiyyah ta fa蓷a mini irin abin da kika mata ranar wanda Munira ce ta fa蓷a mata kuma hakan sam bai kamata ba,ko ni ranar a gabana ki ka dinga yi mata kuma kin san ni bana son haka, ni da na ajiye su ban uzurra musu ba kema banga dalilin da zai sa ki ri茩a uzurra musu ba. Tunda kika yi aure gidan nan ban sanki da haka ba, saboda haka dan Allah ki bari, idan ma akan kuskuren da Emraan ya yi ne kema kin san ya fa蓷a ne kawai, domin kinfi kowa sanin wane ne mijin ki, ko 蓷aura mishi ita aka yi a 茩afa ba zai ja ta ba. Ki kama girmanki ki daina shiga harkar yaran nan bana son hakan. Ban hana ki saka su aiki ba, duk abin da kike so suyi miki dole za su yi shi ko basa so domin matsayinki da na su Nadeeyah duk 蓷aya ne a gidan nan, to amma ki tsaya matsayin ki dan Allah."

Murya a raunane ta kalli Hajiyar ta ce.

" Ki yi ha茩uri Hajiya."

Jinjina kanta ta yi ta ce.

" Ba komai. Kina iya tafiya."

Fitowa tayi jiki sanyaye ta dawo 蓷akin wanda har a lokacin ina nan inda ta barni ina fifita mata shayinta. Wani kallon ta yi mini a yatsine ta ce.

"Ki ha蓷a da kofin ki wuce da shi ki bani wuri."

Cikin sauri na fito ri茩e da Tea cup 蓷in na cikawa rigata iska. 茒aki na dawo wurin su Munira. Sai da na shanye lafiyayyen Shayi na wanda ya ji komai yayi zam sannan muka dawo muna cin abinci ina 茩ara ba su labarin abin da ya faru sai dariya muke har muka kambala na ta shi na ha蓷a kayana na yi gida.

Koda na koma na tarar da Ya Ashiru cikin gida zaune da shi da Ammie suna fira.

茒aki na shige na ajiye kayan na fito muka gaisa da shi.

A nan gaban Ammie ya ciro waya a kwalinta ya ajiye yana fa蓷in.

"Ammie Waya ce na kawo muku domin zan koma Kano gobe,kuma ina so idan na koma in ri茩a ji daga gareku kada a maimaita er gidan jiya."

茒an Jim tayi sannan ta ce.

"Waya Ashiru? Kuma Wayar ma irin wannan babba haka?"

茒an 茩ara sadda kan shi ya yi 茩asa yana fa蓷in.

"Ba komai Ammie... Ai ba wani abu bane, kunfi 茩arfin haka a wurina."

Daga haka ya mi茩e yana mana sallama ya wuce waje. A hankali cikin jin ba da蓷i a raina na biyo bayan shi har bakin Mashin 蓷inda ya saba zuwa da shi muka tsaya, muryata a sanyaye ba tare da sanin mi nake ji ba na ce.

" Yanzu Yaya Ashiru idan ka tafi sai yaushe kenan?"

Murmushi ya yi ya ce.

"Ban sani ba Beenafah, amma dai ni na san ba zan iya jure nisa dake ba, tabbas dole zan dawo..."

"Allah ya kai ka lafiya yasa a dawo lafiya.."

"Amin. Ina Layina da na baki?"

Zaro idona na yi ina mai jin wani irin ba da蓷i a raina na ce.

"Yana Wayar Ya Jafaru kuma ya tafi Zaria."

Wani murmushin gefen baki ya yi yana kallona ya ce.

"Wane ne wannan Ya Jafarun? Ku en uwa ne?"

"Eh to, haka zan ce dai, su 蓷in ma茩otanmu ne, ga gidan su nan..."

Na fa蓷a ina mai nuna mai gidan su sannan na ce.

"Tun da muka dawo unguwar nan da su muka fara ha蓷uwa, kuma suna da kirki sosai, hakan yasa sai muka zama kamar en uwa."

Jinjina kansa ya yi yana wani kalar murmushi ya ce.

"OK. Ba damuwa, akwai layi a ciki na yi mata caji na yi komai, zan ri茩a kiran ku ina jin halin da kuke ciki."

"To Allah ya tsare hanya, ina gaida su Ayya."

Daga haka ya haye Mashin 蓷insa yana yi yana kallon gidan su Jafaru tare da tariyo duk abinda ya ri茩a yi masa a cikin 茩wa茩walwarsa. Tun ranar da ya fara zuwa gidan tun daren ranar ya cire Layin ya yasar daga wayarsa, domin duk ya kira ce masa ake a kashe take har yau kuwa.

Ni dai ina nan a tsaye har sai da ya 蓳acewa ganina sannan na koma cikin gida.

Cike da zumu蓷i na ja wayar na bu蓷eta,Infinix ce touching screen mai kyau sabuwa dal da ita.

Kunnawa na yi ina ta latsawa cike da farin ciki. En ajinmu a islamiyya kawai nake tunawa su Hafsa wa蓷anda mafi yawancinsu suna da Waya, sai kuma su Munira. Camera na shiga na fara Selfie ina yi ina dariya kamar wata ta蓳a蓳蓳iya.

"Beenafah!"

Waigowa na yi na kalli Ammie jin ta kira Sunana na ce.

"Na'am."

"kina ganin kar蓳ar wayar nan ya yi Beenafah?"

茒an jim na yi sannan na kalle ta fuska cike da neman 茩arin bayani na ce.

"mi kika gani Ammie?"

"Ba komai, kawai dai wani abu nake dubawa..."

"Ammie fa kinji cewa ya yi so yake ya ri茩a ji idan muna lafiya."

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta jinjina kanta ta ce.

"Haka ne kuma. Allah ubangiji yasa mu dace."

"Amin. Tashi na yi na shirya tsab cike da zumu蓷i na fito da jakar Islamiyyata na 蓷auko wayar na saka a jaka domin tafiya da ita.

Ammie dake fitowa daga 蓷aki ne ta kalleni ta ce.

" Beenafah ina wayar nan take?"

Kallon jakata na yi sai kuma na kalle ta na ce.

"Gata nan a Jakata."

"Ciro ta ki ajiye a 蓷aki, daga Islamiyya har gidan aikin ki ban amince kije da ita ba."

A hankali na juya na shige 蓷akin na ajiye ta akan Katifa na fito na wuce.

Da dare bayan na yi sallar Isha Ya Hamza na shigowa na 蓷auko wayar na nuna masa sannan na ce ya saka mini numbern Ya Jafaru.

Jujjuya wayar ya yi a hannunsa ya jinjina kai yana 茩ara kallon wayar ya ce.

"Iyyeh! Infinix! Lallai yarinya kice kin Faso garin..."

Cike da jin ya wani fasa mini kai na fashe da dariya na ce.

"Yaya Ashiru ne ya siyo mini ita."

"Gaskiya ya yi 茩o茩ari..."

"Yi sauri ka saka mini Numbern Ya Jafaru dan Allah na kira shi kada kaje ka rigani fa蓷a masa nasan halinka."

鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.