Free chapter 路 Read without an account
PAGE 21
馃挮馃挮RASHIN SANI 馃挮馃挮
STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).
Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.
Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.
PAGE 21.
Wasa wasa, yanzu su Aimana sun tafi 400 level, karatu ya mika sosai, a yayinda Kamal kuma sun kammala, sun karbi certificate nasu, sun kuma samu licence na yin aiki a ko ina.
Nura yana nan har yanzu, ya kasa rabuwa da Aimana, duk kuwa da tarin abubuwan ban haushin da take masa, yace dai yana nan zai ci gaba da jarabawa, idan Aimana rabonsa ce, zai aureta, idan kuma ba matarsa bace shikenan.
A gefe daya kuma ga Junior, duk da bai fito fili ya fadi kudurinsa ba, amma ba wanda bai fahimcesa ba, musamman ma uwar gayya Aimana, ta dai zuba masa ido tayi tana son ganin iya inda wasan nasa zai tsaya, ga kawayenta kuma da suka mato akan yayan nata, duk tana hankalce dasu.
Kamal ya samu aiki a wani private hospital mai kyau, kuma ba laifi suna da salary mai kyau, a take har ya dan fara warwarewa, alamun manyantaka duk sun fara bayyana, ya kara zama wani hadadden gaye, dama Kamal akwai son kwalliya da kwalisa, yanzu da yake samun yan canji sai abun ya karu, ya danyi wa gidansu kwaskwarima, ya gyara dakinsa, har mashin ya saya mai kyau.
Yanzun kusan watansa bakwai da fara aiki, hankalinsa kwance, Aimana ta kosa Kamal ya bayyana mata soyayyarsa, amma har zuwa yanzu yaki fada mata sirrin zuciyarsa, akwai lokacinda ta tambaye sa yaushe zaiyi aure, sai ce mata yayi sai bayan ta gama makaranta ta fara aiki, a lokacin wani sanyi taji har kasan ranta, wato Kamal zai jirata har sai ta gama school, ai kuwa itama zata kula masa da kanta da zuciyarta, ba wanda zata bawa kofa komin kankantarsa kuwa.
Mama kuwa tana tsaye ba dare ba rana akan yaranta, addu'a take musu kullum na Allah ya zaba musu abunda yafi alkhairi a rayuwarsu duniya da lahira,. musamman ma Aimana da take cikin cakwakiyar soyayya.
Haka dai rayuwa take ta gangarawa, kwanci tashi kwanakinmu nata karewa ba tare da mun ankara ba, mutuwa tana ta dada kusanto mu, amma wasu a yanzu suke ta kokarin share fagen zama a cikin duniyar, ba su ko tunanin me suka tara da zai taya su kwanciyar kabari, basu tunanin wannan daren farko da zasuyi a karkashin kasa, inda ba haske ba shimfida, ba iskar shaka, babu wadataccen filin kwanciya da zaka juya, inda ka kwanta dinnan dai shikenan, ba batun na gaji in juya, hmm akwai babban aiki a gabanmu, mu dage da istigfari, da aikin alkhairi da kuma nisantar abunda zai kaimu ga halaka, Allah yasa mu dace, ya bamu kyakkyawan karshe, Ameen.
A cikin wannan kalubale da Aimana take ciki na soyayya, Allah ya kaddari ta kammala karatunta, kuma Alhamdulillahi an samu abunda ake nema,da first class ta fita.
Murna a wurin ahalinta kam ai ba'a magana, Abdul ma ya kammala nasa karatun last two years, dayake shi course nashi na shekaru hudu ne.
A wannan lokacinne kuma Allah ya azurta uncle Hashim da samun haihuwa tun bayan aurensa, shekara hudu kenan, inda matarsa ta haifi tagwayen yanmata, suka ci sunan Dada da kuma mahaifyarsa Inna, wato Fatima da Asiya wanda ake jiransu, Hanan da Janan, sunzo gida dangi duk sunga yara, watansu biyu suka koma.
Kudi sun kara zauna ma uncle Hashim, kamfanin sa na sarrafa shinkafa wanda ya bar aikin a hannun yayyensa kafin ya tafi, ya dade da kammala har an zuba ma'aikata, ba karamin alkhairi yake samu ba a wurin, kasancewar Junior shine babban da a kaf family yasa uncle Hashim yace a barmasa ragamar company, yanzu haka shine MD na kanfanin, Munnir kuma yana aiki da wani babban ma'aikata na gwanmati, idan ka gansu shar dasu, suna juya duniyar yanda suke so, don basu da wata matsala dai a yanzu.
Lokacinda aka musu maganar aure, Junior dai cewa yayi a bashi lokaci, shi kuwa Munnir Aina'u kawar Aimana yake nema, tun wani zuwanda sukayi wurin Aimana a hutu, nan ya kyalkara ido ya ganta, yace kuwa shi yaga mata, Aimana ta shige masa gaba ta daidaita komai, yanzu haka soyayyar su suke sha ba kama hannun yaro, don har manya sun shiga maganar.
Nura dai har yanzu yana nan yana jiran Aimana, an matsa masa a gida da maganar aure, saidai yace musu, wacce yake nema tana makaranta, amma da zaran ta gama za'ayi, haka aka hakura aka zuba masa ido.
Nana ma yanxu haka yaranta uku, bayan Aryan ta haifi Raniya, da Ra'eesa, Amal ma yaranta biyu, Ibrahim Khalil, da kuma Hafiz takwaran Abba kenan, Farida ne dai Allah bai bata haihuwa ba tukun har yanzu.
~~~~~~~~
Likkafa taci gaba a bangaren Kamal, don a cikin wannan shekaru uku, Alhamdulillahi za'a ce, kudi sun zauna masa, don yanzu haka yana aiki ne da Federal Medical Centre Gusau (FMCG), kuma yana zuwa visiting doctor a wasu hospitals din, ya gyara gidansu kamar ba shi ba, ya saida mashin dinsa ya sayi karamar mota, yanmata kuwa ko ta ina ribibinsa sukeyi, saidai shi basa ma gabansa, su Hamida ma sunyi aure last year, yanzu haka Hamida ta kusa haihuwa, Humaida ce dai take da karamin ciki.
Dr Aimana kuwa tana nan, tace bazata yi aiki yanzu ba, sai ta huta tukun daga stress na makaranta, saidai tana zuwa a matsayin visiting doctor a wani private hospital da yake bayan layinsu duk randa tayi ra'ayi, kuma mutane sosai suke son ganinta, saboda akwai iya bi da patients dinta, idan tasa ranar zuwa takan sanar dasu, dama suna da list na masu son ganinta, sai a musu booking.
Watansu shida da gama makaranta, Daddy ya nema mata aiki Gusau General Hospital, ta fara zuwa aikinta lafiya lau, har yanzu dai driver Daddy ya bata, so bata da Matalan abun hawa.
Ba wanda ya taba mata maganar aure, saboda dududu yanzu Aimana tayi 22 years, kawai dai ta gama makaranta da wuri ne, shiyasa ake kiranta da young doctor, ko a wurin aiki kuwa, don idan ka kalleta sai ka raina mata, wasu kan ma sai suce bazata duba su ba tayi karama, basu san abunda yake kan yawa gareshi ba, amma ga wadanda take dubawa suna yaba kokarin ta, don wasu sai randa take call, suke zuwa asibitin.
Ganin har yanzu da sauranta yasa ba wanda ya mata maganar aure, Mama ce ma kadai take tuntubarta lokaci lokaci, don Nura ma yanzu kam ya yunkuro da gaske, yace mata an matsa masa a gida da maganar aure, shikuma ita yake jira.
A wannan karon Aimana bata boye masa komai ba, ta fada masa gaskiya ita tana da wanda zuciyar ta take so, yayi hakuri, Allah ya bashi wanda ta fita.
Koda jin haka, sai ga Nura durkushe a kan gwiwarsa yana rokon Aimana, "Don Allah Aimana kiyi hakuri ki so ni ko dan kadanne, zuciyata bazata iya rabuwa da taki ba, kinsan yanda nakejin sonki a raina kuwa Aimana, idan kika guje ni zuciyata bugawa zatayi, don Allah ki taimaki rayuwata Aimana, ki aureni, zan baki dukkan wani kulawa da farincikin, sai kinfi ko wace mace a gidan miji, zan sallama miki kaina da rayuwata sai yanda kikayi dani, don Allah ki taimakeni Aimana".
Kuka Aimana takeyi bilhakki, idan tace Nura bai bata tausayi ba tayi karya, amma ya zatayi, ce masa tayi...
"Kayi hakuri Nura ka tashi".
Tashi yayi ya tsaya a gabanta, da ka kallesa zaka tabbatar yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali, mahaifinsa wata biyu kacal ya bashi ya fidda mata, ko ya aura masa koma wacece, shi kuwa babu wacce yake so a duniyar nan idan ba Aimana ba, sai gashi tana fada masa wata maganar da zai iya tarwatsa masa zuciya.
Kallonsa Aimana tayi cike da tausayawa sannan ta share wani guntun hawayen da ya zubo mata, tace...
"Kayi hakuri Nura, nasan yadda kakeji a zuciyar ka, tunda nima hakan nakeji watakila ma har ya zarce naka, nayi dakon soyayyarsa na tsayin shekaru da bansan adadinsu ba, na so shi tun bansan menene soyayyar ba, kaf rayuwata da soyayyar sa na rayu, kaga kuwa abunda nakeji ma yafi kai wanda kakeji, idan na aureka ni da kai bazamu taba farinciki ba, kai kana so na, ni ina son wanin ka, zaman mu bazai taba dadi ba, don na san har abada bazan taba iya baka zuciyata ba, gangar jikina kawai zaka aura, don haka kayi hakuri, lets pray for the best, zan tayaka da addu'a, Allah zai baka wacce ta fini insha'Allah, kuma zakayi farinciki a gaba, bi'izinllahi".
Tana gama fadin haka tayi cikin gida da gudu, tana share kwallar da yake ta zuba daga idonta, dakinta ta shige a guje ta fada kan katifarta tana sakin wani irin kukan tausayin kanta da kuma Nura, sabida ita kanta har yanzu ta kasa gane inda Kamal ya sa gaba, ta hakura ta bashi dukkan lokacinda ya kamata, amma har yanzu ya kasa confessing mata soyayyarsa.
Mama da taga wucewarta a wannan yanayi, yasa ta bi bayanta, bayan kamar minti goma shabiyar, samunta tayi tana kwance har lokacin tana goge hawayenta, zama tayi a gefen katifar sannan ta kira sunan Aimana.
Sai yanzu Aimana tasan da shigowar Mama dakin, tashi tayi taje ta kwanta a kafar Mama, ita kuma ta fara shafa mata gashin kanta alamar rarrashi, saida taga Aimana ta dan dawo nitsuwarta tukun sannan ta tambaye ta abinda yake faruwa.
Aimana tana daga kwancen ta fara magana, dayake Aimana bata boyewa Mama komai, kusan ma itace abokiyar shawararta, anan ta fada mata yanda sukayi da Nura.
"Amma nake ga Aimana bai kamata ki sallami Nura ba, yaron yana da hankali da sanin ya kamata, yanzu da kika sallame sa wa kika kama, ko shi Kamal din da kike yi dominsa ya fada miki yana sonki ne, ko ya shirya aure, kar kiga an zuba miki ido, kiyi yanda kike so, zuwa yanzu ya kamata ki tsayar da miji, me kike nema, me ya rage miki yanzu, kin gama karatu har kina aiki, aure kawai ta rage kiyi Aimana".
"Shikenan Mama, zan fadawa Kamal ya fito kawai idan ya shirya, amma Mama maganar Nura a barta, kusan shekara hudu nake bata masa lokaci, gara na fada masa gaskiya kawai, ko ya nemi wata, ya daina bata lokacinsa a kaina".
"Kul karma ki fara, shi Kamal din ya taba fada miki yana sonki da bakinsa ne da zakice ya fito?, kar ki yadda, kar kuma inji wani abu makamancin wannan bari na fada miki, Allah bai hanaki masoya ba, amma kin zauna bata lokacinki akan wani Kamal, idan har son naki yake me ya hanashi bayyana miki har yanzu, to kar ki yadda inji kinje masa da wata maganar, na gaya miki kenan".
"To Mama ya zanyi, ni ina zansa raina, wallahi Mama Kamal ne kadai a zuciyata".
"Addu'a, addu'a Aimana ita zakiyi, duk wanda kikaji yace ya zanyi to tabbas ya mance da addu'a, ki daure ki rika tashi da dare kina kai kukanki wurin Ubangiji, sannan ki nemi zabi daga gareshi, insha'Allah bazaki taba danasani ba".
"Shikenan Mama, zan kokarta, ki tayani da addu'a Mama, Allah ya shige mini gaba".
"Ai inayi Aimana, saidai in kara, kuma kema ki dage, bacci bai ganki ba a yanzu".
Haka Mama tayi ta rarrashinta, tare da bata shawarwari cikin hikima irin ta uwa, tare da nuna mata muhimmacin addu'a ga bawa, koda baida wani damuwa kuwa, bare kuma yana dashi.
Bayan kwana biyu da wannan al'amarin kuma, sai ga Junior ma ya fito da nashi batun.
Wata ranar Friday yazo ya dauketa suka tafi wani park, sukayi ordern abinci, don har yanzu suna fita yawon shakatawa, saidai ba kamar da ba, dayake yanzu kowa na da abun yi, sai ya zamana ba koda yaushe suke da lokaci ba.
Bayan an kawo musu, abinci, har sun kusa cinyewa, Junior ya kalli Aimana with a serious look, sannan yace, "Aimana akwai abinda nake son fada miki da dadewa, saidai na bari ne har zuwa lokacinda ya dace, kuma a yanzu nake ga lokacin yazo, don haka yau zan fada miki".
Dukanda kirjinta yakeyi ne ya tsananta, kar dai ya kasance abunda take gudu ne yake shirin faruwa, amma sai ta daure tace, "Ina jinka Yayana".
Kallonta yayi da kyau sannan yace, "Aimana, wato na dade ina jin wani abu a zuciyata game dake, ban tashi fahimtar komai ba sai daga baya, Aimana na fahimci ina tsananin sonki, da na dauka so nake miki irin na kanwa, amma daga baya na fahimci wannan ya wuce soyayya irinta Yaya da kanwa, Aimana ina sonki, ina sonki, ina sonki, da fatan wannan Yayan zai samu soyayyar kanwarsa", ya karashe maganar cike da wani irin murmushi.
Gabadaya Aimana ta shiga cikin wani yanayi, ta rasa ma me ya kamata tayi ko ta fada, she is totally speechless, kallonsa kawai take da wani irin yanayi, duk da ta dade da fahimtar sa, amma yau da ya furta mata saida taji wani abu daban.
"Kinyi shiru Aimana baki ce komai ba".
"Ka kaini gida", haka kawai ta sami kanta da furtawa, don a yanzu bata san me takeyi ba, ko me zatayi.
"Shikenan muje", daga haka outing nasu na ranar ya kare.
Koda ta koma gida, ta samu Mama ta fada mata abunda ya faru, tausarta tayi tace mata taje taci gaba da neman zabin Allah, kar ta saka damuwar komai a ranta, ta kwantar mata da hankali sosai, kuma anyi sa'a, bata wani daga hankalinta ba, taci gaba da sabgoginta, saidai sosai Junior yake matsa mata da waya, yana tambayar ko ya samu karbuwa, daga karshe ce masa kawai tayi Allah ya zaba musu abunda yafi alkhairi, shikenan aka samu sauki ta nan.
Aimana harkokin gabanta taci gaba da yi, watarana a weekend suna zaune da Kamal suna hira, yace mata, "ki shirya Dr Aimana, akwai inda nakeson ki raka ni next week Saturday idan ba abunda zakiya in Allah ya kaimu.
"To my doctor, ina zamuje haka?".
"It's a surprise, sai munje zaki gani, I want to show you something".
"Okay then, Allah ya kaimu, har na zaku Saturday din yayi ma, I can't wait, don Allah ka dan fada min mana".
"No, idan na fada miki kuma ai ya zama ba suprise ba kenan".
"Shikenan, Allah ya kaimu"
"Ameen, our special doctor", hira sukayi kadan suka rabu.
Ranar Friday kuwa, da misalin karfe hudu suka fita a motar Kamal, wata unguwa sukaje, daga ganin unguwar kasan mazauna wurin talakawa ne sosai, a kofar wani gida suka tsaya, sannan suka fito daga motar, karewa unguwar kallo Aimana tayi, a take tausayin masu rayuwa a wurin ya kamata.
Tayi nisa a tunani har bata san abunda yake faruwa a inda take tsaye ba saida taji Kamal ya kwala mata kira da karfi, kafin ta dawo duniyar su, tana juyowa kuwa tayi arba da wata kyakkyawar budurwa a gabanta, ta sha adonta na daidai talaka, ba laifi bata kai Aimana kyau ba, amma kuma itama ba mummuna bace, don idan ta goge itama ba karamin kyau zatayi ba.
Kalmarda taji Kamal ya fada mata ne yasa taji duk wani lantarkin jikinta ya daina aiki, zuciyarta kamar ta tsaya, wani irin yanayi Aimana ta shiga da ta kasa tantance a wani duniyar take, ta tabbata suman wucin gadi tayi a wurin, wani irin shock ya shigeta lokaci daya, tana tsaye ne a wurin amma gabadaya batasan me yake faruwa ba.......
ALHAMDULILLAHI, A NAN MUKA ZO KARSHEN RASHIN SANI BOOK 1, IN SHA ALLAH GOBE ZAMU DAURA BOOK TWO. PAKA PAKA BA BATA LOKACI.
NA GODE DA ADDU'O'INKU, INA MUKU FATAN ALKHAIRI.
MA'ASSALAM