Free chapter · Read without an account
3
CHAPTER THREE
Zaune Hadiza take akan kujera ta baza tarin test scripts na ɗalibai a gabanta tana marking. Waƙar Omah Lay mai take 'Uderstand' yana tashi a wayarta. Tana marking tana bibiyar waƙar, waƙa yana sakata nishaɗi. Shi yasa ko aiki take za ka ga ta kunna music. Waƙoƙin da ta ke ji kuwa ba ga India ba, ba ga Turawa ko Mawaƙan Kudancin Nigeria ba har Waƙoƙin da irin su Shata da Ɗanƙwairo tana sauraro duk yadda ya zo mata.
Kwanƙwasa ƙofarta aka yi, Abba ya kira asalin sunan "Hadiza".
Caɓ! tunda ta ji ya kirata da Hadiza to fa akwai ƙura. Wataƙila faɗa suka yi da Umma. Ai kuwa ta chanki dai-dai, dan kuwa lokacin da Abban ya shigo ɗakin ya zauna a bakin gadonta ƙaran Umman nata ya kawo.
Ajiye jan biron hannunta ta yi ta buɗe kunnuwanta da kyau tana sauraron bayanin Abban nata.
"Fisabilillahi, Ina daɗi a wannan abin. A ce ba za ka yiwa mahaifiyarka ɗinki ba, saboda duk sadda ka mata a baya sai ta kushe"
Hadiza ta ce "Ba daɗi kam, Abba"
"Azumi za a shiga, ya kamata tun kafin Azumi ta ɗinka kayan nan ta kai mata. Azumin bara haka na yita magana har satin Sallah bata ɗinka kayan nan ba. ƙarshe ina ke kika yi ɗinkin kika kai mata ana gobe Sallah. To wannan karan ba zan zuba mata ido ba, ki sameta ki mata magana ta ɗinka kayan nan ta kai kafin a fara Azumi"
Yana gama faɗin haka ya miƙe ya fita daga ɗakin. Sai a lokacin Hadiza ta iya shaƙar numfashi mai kyau dan tun da ya fara magana ta sha jinin jikinta. Iyayenta ba su cika faɗa ba kuma tun tasowarta duk faɗan da za su yi ma baya wuce akan maganar Hajiya ne wato mahaifiyar Umma.
Ita yanzu da Abba ya ce ta yiwa Umma magana me za ta ce?.
Shiru za ta yi da bakinta ai sun san yadda suke shiryawa idan sun yi faɗa. Idan ta saka baki a ciki ma ita za ta ji kunya, balle ma Hajiya da Umman kowa yana da nasa laifin. Ita Hajiya ko yaushe Umma tai mata ɗinki haka za ta yita kushe kayan tana cewa ɗinkin bai yi ba kuma fa za ta saka. Infact ita Hadiza ta san yadda Hajiya ke nacewa kayan da Umma ta ɗinka, sai ta ce sun fi sake mata, amma ba za ta taɓa faɗa a gaban Umman ba. Itama Umman ta san Hajiya ba da gaske take ba amma sai ta yi ta fushi.
Da dare da wuri ta ɗauko abincinta daga kitchen ta kawo ɗaki. Tana cikin cin abinci bayan ta gama sallar Isha Umma ta ƙwala mata kira daga falo.
Kai! Ta faɗa tana miƙewa ta ƙarisa suɗe hannunta kamin ta fita.
"Umma, gani" ta faɗa tana kallon Iyayen nata da suka zauna nesa da juna.
"ki je ki kawowa Abbanku abinci"
ta ɗan saci kallon Abba da hankalinsa ke kan TV sannan ta wuce Kitchen ta ɗauko tray ɗin abincin ta zo ta ɗaura a centre table ta jawo teburin kusa da Abba. Ta je ta ɗauko ruwan wanke hannu ta kawo. Za ta tafi Umma ta ce "Ki tsaya ki zuba masa". Kenan har yanzu ba su shirya ba. Ta zo za ta fara zuba masa Abba ya dakar da ita ya ce "bar shi" ya buɗe abincin da kansa.
Da ta juya za ta tafi sai Abba ya kirata "Hajiya"
"Na'am" Hadiza ta faɗa da sauri dan gaba ɗaya a takure take, tension dake falon kaɗai ya isa ya tada gobara.
"Kin faɗi saƙon dana baki?"
"A...Zan faɗa, na manta ne"
"To gashi na tuna miki"
Hadiza ta haɗiyi yawu da ƙyar ta kalli saitin Umma da ta ke danna wayarta da alama dai yau ba tare za su ci abinci ba.
Ta juya za ta tafi Abba ya sake cewa "Ba za ki faɗi saƙon bane?"
Hadiza ta ji kamar ta nitse. Wai ya za su sakata a gaba ne. Ga shi ita kaɗai ne a gidan, ƙaninta Bashir yana Boarding School.
Ta ɗan matso gaban Umma ta ce "Umma, wai in ji Abba in tuna miki ɗinkin Hajiya dan Allah a kai mata da wuri"
Umma ta jefeta da wani kallo ta ce "ki je ba ruwanki" ai ko jiran dogon bayani ba ta yi ba ta yi ɗakinta a ɗari.
Tana shiga ɗakin kuwa ta sa sakata sannan ta saka wayarta a flight mode. Ai Wallahi duk kiran da za su mata ba za ta fito daga ɗakin nan ba sai da safe, haka kawai za su ɗaga mata hankali, su je can su sasanta kansu ba za a sata a tsakiya ba, ita ba Alƙali ba ce.
Ko abincinta ba bata iya ƙarisa cinsa ta daɗi ba, ta tura kwanukan gefe ta hau gado dan wanke-wanke ma sai da safe kawai za ta yi.
Wani Hausa novel ta fara karantawa a wayarta mai suna CHEF ZEEY: Love in the Kitchen, wanda Marubuciya Azizat Hamza ta rubuta. Ai kuwa ba a jima ba Umma ta fara kiran sunanta wai ta zo ta tattara kwanuka. Ta ja bargonta ta rufe fiskarta ta fara baccin ƙarya.
Washegari da safe Hadiza tana cikin wanke-wanke bayan ta ɗaura ruwan shayi a wuta saboda ta ga Bredin da Abba ya siyo jiya da dare a saman fridge sai ga Umma ta shigo kitchen ɗin. Ta ɗan risina kaɗan ta gaisheta. Umma ta amsa a daƙile.
"kin saka citta a ruwan?"
"Na saka komai"
"Akwai sauran ƙwai ne?"
"guda biyu ya rage"
" ki soya muku kawai, ina Azumi"
Hadiza ta girgiza kai tana mamakin wannan Azumin Larabar da aka ɗauka ana zaune lafiya. Umma tare take haɗa Sitta Shawwal da biyan bashi dan haka dai ba Azumin bashi bane.
"Shi kullum sai ya riƙa nuna shi ya fi son Hajiya a kaina. Ni bana ƙoƙarina ne? Da na ce ba zan mata ɗinki ba ai sai ya ce ki ɗinka mata ko a kai mata kayan haka ta bawa duk wanda za su mata yadda take so. Idan da zan faɗa masa yadda take kushe kayan da yake matan, ai shi kansa ba zai ji daɗin sake siya mata kaya ba"
Hadiza dai shiru ta yi tana jinta. Duk da dai akwai laifin Hajiya amma maganarta na farko gaskiya ne, tabbas Abba ya fita damuwa da Hajiya duk da kuwa Hajiyar kullum cikin kushe shi take. Amma bai taɓa gazawa ba wajen kyautata mata da kuma mutuntata kamar uwar data haife shi.
Bayan fitan Umma daga kitchen ɗin a gurguje ta ƙarisa haɗa musu breakfast ta je ta fara shiryawa. Lokacin da ta fito ta samu Abba a falo yana karyawa. Itama zama ta yi a falon ta fara cin nata abincin. Ta riga shi gamawa ta ɗau jakarta da key ɗin machine za ta fita sai ta fara jin ƙaran takun keke a ƙaramin store da Umma ke ɗinki.
Hadiza ta yi murmushi ta leƙa ɗakin ta yiwa Umma Sallama. Atamfar da ta ga Umman na ɗinkawa ne ya sa ta fahimci Azumin rantsuwa take yi dan ta rantse a baya ba za ta sake yiwa Hajiya ɗinki ba.
***
Daf Maghriba Abba ya shigo gida ɗauke da ledan fruits. Hadiza ce ta karɓa dan tana kallo a falo ya shigo.
"Ki saka mata Kankanan a fridge tunda akwai wuta zai ɗan yi sanyi zuwa anjima" Hadiza ta ce 'to' tana murmushi.
Shikenan fa an shirya. Sun wani kama sun ɗaga mata hankali daga jiya zuwa yau.
Da ta saka fruits ɗin a fridge sai ta ɓalli Ayaba ɗaya ta fara ci tana duba wayarta tana kallo. Chatting take da Deej da take mata ƙorafin kwana biyu ba ta zo mata ba.
Deej akwai son kai, ita yaushe rabon da ta zo gidansu. Tun wani zazzaɓi da ta yi da Deej ta zo ta gaisheta bata sake takowa ƙofar gidansu ba. Shi yasa Umma take ce mata bata da zuciya.
Reply ta mata da cewa idan Yara sun yi hutu za ta zo mata.
Bayan Isha kuwa da Abba ya dawo sai ga shi Umma da kanta ta kawo masa abinci. Ya tambayeta an sha ruwa lafiya? ta washe baki ta ce Alhamdulillahi, Kankanan da ya kawo mata da zaƙi.
Kai! Aure bai yi ba. Hadiza ta faɗa a ranta tana dariyansu. Shikenan fa sun manta fushin da suke da junansu.
Tana gefe ta naɗe ƙafarta akan kujera tana faman gwagwuyar ƙashi su kuma sai taɗi suke har da dariya.
Deep down! Tana addu'ar Allah ya sa ta samun farin ciki da zaman lafiya idan ta yi aure kamar na iyayenta.
Bayan an gama cin abinci ta kwashe kwanuka ta je kitchen ta fara wanke-wanke. Tana cikin yi NEPA da tsiya suka ɗauke wuta, ta kunna torchlight ɗin wayarta ta ƙarisa aikin da shi. Lokacin da ta gama wanke-wanken ta fito falo su Umma sun shige ɗakinsu.
Ta yi dariya a ƙasan ranta, wato an killace a ɗaki za a je a yi soyayya tunda an gama faɗa.
Ƙofar fita ta duba ta ga Abba ya riga ya rufe dan haka itama ta wuce nata ɗakin. Akwai ɗan zafi dan haka wani ficilar rigan baccinta ta saka ta kwanta. Ta jawo wayarta ta shiga Facebook ta hau shafinta mai suna CHAKWAKIYAR HADIZA ta fara rubuta labarin yau wanda tsakure ne daga faɗan da su Umma suka yi da kuma shiryawansu. Kan ka ce me har an fara yi mata Comment rututu.
Tana Level two a Jami'a ta buɗe shafin Chakwakwiyar Hadiza a Facebook. Lokacin hackers sun ƙwace mata asalin account ɗinta, ta yi- ta yi ta dawo da Account ɗin amma bai yiwu ba saboda bata ɗaura masa gmail a kai ba. Wannan ya sa ta buɗe wani Facebook account ɗin ta saka masa suna Chakwakiyar Hadiza maimakon Hadiza Zango da take amfani da shi a tsohon account ɗin. A wajen take zuba duk wani surutunta. A hankali kuma sai kawai shafin ya fara girma yana ta samun followers. A Level 4 sai Deej ta ce ta buɗe Instagram da sunan. Yanzu haka tana da Followers dubu shatakwas (18k) a Facebook, a Instagram kuma dubu huɗu (4k). Chakwakwiyar Hadiza, dandali ne na hira, na bada labarai, na bayar da shawarwari, da kuma ƙarfafawa mata gwiwa.
Da a ce ba aikin koyarwa take ba da babu abin da zai hanata zama 'yar Jarida ta yi aiki a gidan Rediyo ko Talabijin.
***
Ranan Asabat da safe Hadiza ta samu Abba a ɗaki ta ce masa za ta je Asibiti bada jini.
"Hajiya, har ya kai wata huɗun ne?"
"A farkon Azumi zai cika wata huɗu shi yasa kawai zan je yanzu"
"To barin sa kaya in kai ki ko?
"Abba, Khadija za ta zo mu tafi tare"
"Tooo, Allah ya sa a yi lafiya a kuma gama lafiya"
Hadiza ta amsa da Amin.
Bayan kaman minti shabiyar su ka ji horn ɗin motar Deej. Ta yi sallama ta shigo gidan. Umma na kan Keke tana ɗinki suka gaisa sama-sama. Abba ma ya fito da shirinsa zai fita Kasuwa. Ya tambayi Deej ya aiki ta ce masa lafiya.
Sai da Hadiza ta sake ɓata musu lokaci kafin nan suka fito. Suka yiwa Umma sallama suka wuce Asibiti.
A cikin mota Deej ke tambayarta kamar last donation da ta yi bai kai wata huɗu ba. Hadiza ta ce "just two weeks ya rage kuma za a shiga Azumi shi yasa"
"Gaskiya ina ganin ƙoƙarinki. Wallahi Sis ba zan iya abinda kike ba. Duk bayan wata huɗu sai kin je an soka miki ƙatuwar allurar nan, caɓ!"
Hadiza ta sa dariya ta ce "ai na saba, 4 years kenan fa"
Khadija dai Likita ce amma ɗan banzan tsoron allura gareta har gobe, Hadiza kuwa babu ruwanta.
Ta fara bada jini ne lokacin suna final year da wata 'yar ajinsu ta yi jinya aka zo ana neman jini Blood Group O Negative (O-) sai ta yiwa Abba magana akan za ta je ta bayar tunda itama kalar jininta kenan. Abba ya ce mata babu matsala in za ta iya. Shi da kansa ya kaita aka mata screening aka ɗau jini leda ɗaya suka dawo gida. Umma tana ta tsoro, sai ta ga ko daɗewa ba su yi ba har sun dawo. Ranan wuni ta yi tana yiwa Hadiza hidimar abubuwan da za ta ci. Ita kuwa Hadiza ban da ɗan jiri-jiri da ta ji bayan an ɗau jinin da kuma ciwon kai ba abinda ya sameta, amma ganin Umma ta damu sai ta langwaɓe jiki tana ta raki wai ita a dole jininta ya ragu. Sai da aka yi sati kuwa ana kawo mata kayan daɗi. Daga lokacin bata sake bada jini ba, sai a ƙarshen shekaran aka kirata daga Asibitin ana neman irin jininta emergency idan za ta iya bayarwa, bata ko ji tsoro ba duk da zafin ƙatuwar allurar cire jinin da ta ji ranan farko. Ta je ta sake bayar da jininta, daga lokacin kuma a karan kanta sai ta ƙudiri anniyar donating jininta sau uku a shekara. Da ta gayawa Abba ya ce Allah yasa hakan ya zamo silar shigarta Aljannah. Umma ne da farko ta so gardama ganin ita macece amma da ta ga Hadizan ko a jikinta sai ta haƙura.
Alhamdulillahi yanzu kam Hadiza ko tsoron zuwa ba ta ji. Akwai lokacin da ita kaɗai ma ta je aka cire jinin da ta ɗan huta ta hau Keke ta dawo gida. Abba da ya dawo ya ji labari sai da ya mata faɗa sosai.
Suna isowa cikin Asibitin Deej da maganar Dr Tafida ke cinta ta ce da Hadiza ko za su fara zuwa office ɗin Yaya Khalil su gaishe shi?.
"Kin san Allah ba ki da lafiya, Deej. Ina ruwana da shi da zan je na gaishe shi. Ya san da zamana ne da zan je in bata lokacina ina masa bayanin ko ni wacece"
"Haba, Deeza. Allah ya san ki. Waye bai san Hadizan Hajiya ba a kaf Danginmu"
"To zage ni" Hadiza ta faɗa tana hararanta.
"Allah, ba jimawa za mu yi ba. Ya ce yau Saturday zai shigo, kin ga ga ma can Motarsa" Khadija ta faɗa tana nuna mata wata mota ɗan nesa da inda suka yi parking.
"Ke ni babu inda zan je, ki kai ni Lab na yi abinda ya kawoni ko kuma yanzun nan mu ɓata da ke"
Khadija ta ce " Yi haƙuri ranki shi daɗe zan raka ki"
Suka fito daga mota suka nufi Lab.
Ɗaukan jininta aka yi za a yi screening, lokacin da suka zauna zaman jiran result ɗin gwajin kafin a zo a ɗau jinin sai aka kira wayar Deej. Ta bawa Hadiza haƙuri ta ce bari ta je office ɗinsu ana nemanta. Hadiza ta ce ba komai.
Bayan an kawo result ɗin test babu matsalar komai sai aka ce ta zo ta kwanta.
"Kin ci abinci?" wanda zai cire jinin ya tambayeta.
Hadiza ta ce "Ni fa customer ɗinku ce, ko ban ci abinci ba ai na saba"
Mutumin ya ce "Idan kika faɗi mana a nan kuwa ba mai ɗaga ki"
Hadiza ta yi dariya ta ce kar ya damu ba za ta faɗi ba.
Haka dai suna ɗan taɗi har aka sa mata allurar aka fara ɗaukan jinin. Banda rufe ido da ta yi lokacin da allurar ta shiga ƙatuwar jijiyarta saboda zafi, bata sake jin komai ba, ta saba.
Lokacin da aka gama cire jinin Hadiza zama ta yi ta riƙe kanta dan ta gaji da kwanciyar da ta ke, tana ɗan jin jiri shi yasa ba za ta iya tafiya a lokacin ba.
Mutumin da ya cire jinin ya fara tsokalarta yana cewa ya dai Customer da raki haka. Ta ce masa jiran 'yar'uwarta take.
Ganin ta kira Deej bata ɗaga ba sai ta ce bari kawai ta je office ɗin nasu ta dubata ƙila bata kusa da wayar ne ko aiki ya riƙeta.
Kamar dai a Paediatry unit suke yanzu. Ta tashi ta ɗau jakarta bayan ta dena jin jirin ta nufi can.
***
Daga ɗan nesa ya hangota tana yiwa wani magana a reception. Ganinta sanye da kayan gida ba scrubs ko Lab coat sai ya yi tunanin ko yau ba shift ɗinta bane. Kwana ya yi ya nufo inda take tsaye kafin ya ƙariso aka kira wayarta, yadda ta ɗau wayar tana magana sai ya ga kamar ba Dr Khadijan bace. Amma kuma kaman ya san fiskar. Ƙarisawa ya yi ya kira sunanta hoping dai ba idanunsa bane suka fara tafiya duk dai glasses ɗinsa na aiki ne ba na yawo ba.
"Nana" ya kira sunanta hoping ita ɗin ce.
A hankali ta juyo wanda hakan ya bashi damar kallon fiskarta sosai. Still waya ta ke bata masa magana ba.
Ba Dr Khadija ba ce, amma kuma suna kama sosai.
"Sorry, ba Nana ba ne" abinda ta faɗa kenan ta juya ta bar shi tsaye har lokacin waya take.
Girgiza kai ya yi ya juya zai tafi yana tunanin ko dai kama ce take da Nanan ko kuma dai ɗaya daga cikin 'yar'uwarsu ce da bata san shi ba. Yana cikin tafiya sai ƙwaƙwalwarsa ta haɗa masa 1+1 na inda ya san fiskar.
Juyawa ya yi da sauri amma tuni ta wuce.
Tabbas ita ce.
Ita ce ya gani kwanaki tana gudu da machine...
#BestHausanovel2025
©MarubuciyaAzizatHamza2025