Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Narrnarhh Bukar · BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

Narrnarhh Bukar

(Lady with the Amazing pen✍️)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

003

Wata bazawarar dariya matar ta shiga ƙyaƙyatawa kamar wata zautatta har tana ƙwalla. Galala Sahura ta tsaya tana kallonta. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita tare da rangaɗa guɗa

''Ayyiririiiii! Daɗi kasheni ni 'yar ƙuda! Na kuwa ji daɗi da Baban Yasir ya ƙara aure,ta ji yadda zuciyata ta soyu lokacin da ni ma aka ƙaro mini kishiya. Ai daman na faɗa sai Allah ya saka mini''

''Ban gane inda zancenki ya dosa ba baiwar Allah ''Sahura ta faɗa tana matsowa kusa da ita. Ɗan taɓe baki 'yar ƙuda ta yi sannan ta ce

''A lokacin da aka danƙaro mini kishiya ƙafarta bata tako zuwa gidana taya ni alhini balle dannar ƙirji. Da muka haɗu a gidan barka ta yi mursisi abinta. Ai Allah ba azzalumin bawa ba ne. Yanzu ga kishiya nan an ƙaro mata galleliya sabuwa fil a leda,ta ji yadda zuciyata ta ji''

Riƙe baki Sahura ta yi da faɗin ''Au Allah! Haka daman take! A fuska kamar ta annabi ashe mugun hali gareta! To gwara da kika sanar mini kin ga na ci maganin zama da 'yar ƙwal uba''

Washe baki 'yar ƙuda ta yi jin furucin Sahura,da alamu dai za a yi tafiyar da ita.

''Kar ki damu ƙawata mun zama ɗaya yanzu, zan sanar miki waɗansu sirrika da za su taimaka miki wajen zama da ita. Idan kin samu lokaci ki zo mu tattauna tun da tana zuwa makaranta, Baban Yasir ma haka. Gidana na kallon gidanku''

''Kar ki damu in shaa maka Allahu za ki ganni kuwa,yooo ni da nake neman hanya ruwa a jallo na samu a ɓagas 'yar uwa! Za ki ganni wallahi!. Sun tafi kai shegen ɗanta na goye mai idanu kamar na mujiya asibiti,ya addabemu da kuka.''

Taɓe baki 'yar ƙuda ta yi tana huro buɗaɗdun hancinta

''Kaɗan kika gani in dai Jalil ne. Kin ga! na yi tafiyata kar su iskemu tare su zargi wani abu. Bakinki alaikum idan kina son ƙawancanmu ya ɓulle'' ta yi maganar tana nufar waje. Sahura bata yi ƙasa a gwiwa ba ta rakata har ƙofar gidan tana mata godiya da alƙawarin kawo mata ziyara idan ta samu lokaci.  Bayan ta dawo cikin gidan farin ciki mara misaltuwa ya kewaye lungu da saƙon zuciyarta. A hankali ta zauna a saman tabarma tana sakar wa kanta murmushi akai-akai,da alamu dai ta zo da sa'a gidan Yaya Dauda Imamu, hancinta sun fara jiyo mata ƙamshin nasara. Ta jima tana tattaunawa da zuciyarta,da ta gaji da zaman ta koma cikin falon, har ta zauna sai kuma wata zuciyar ta umurci ta je ɗakin Mairi sake ganin ƙwaƙwaf. Zumbur ta miƙe har Yasir da ke wasa da mota ya ɗan dubeta sai kuma ya cigaba da wasansa yana gwarancinsa shi kaɗai. Tsaf ta natsu tana kallon yadda ɗakin ya tsaru ya yi kyau wanda ko a sakkwato mai irin kayan sai 'yar attajiri. Gadon katako ne fari 6by7 wanda sai 'yar wane da wance. Ga saitin samiru a bango ɗaya rairas. Cije laɓɓanta ta yi da ƙarfi wani abu mai kauri ya tsaya mata a daidai wuyanta.

''Yanzu duka waɗannan kayan Yaya Dauda Imamu ne ya yi ma 'yar ƙwal uban nan! To wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa. Ni ma dole a gwangwaje ɗakina da irin waɗannan koma su fi waɗannan,domin sawun giwa ya take na raƙumi. Hhhhhh! Cab! '' Ita kaɗai take maganar tana ƙara kallon ɗaki. Ta jima a ɗakin tana dube-dube wai ko za ta ga inda ta ɓoye asiri a wani wuri,don ita bata yadda da son da Dauda Imamu yake wa Mairi na gaskiya ba ne. Haka ta haƙura ta bar ɗakin kar su dawo su sameta ciki. Falo ta dawo abinta. Ganin har 10:30 na safe ya yi amma har yanzu ba su dawo ba. Ta nufi kicin don ɗora sanwa, a gidansu ana gama karin safe ake ɗora na rana kasancewar suna da yawa a gidan. Inda aka ajiye kayan abinci a cikin kicin ta nufa, ganin akwai komai baja-baja ta kunna risho tare da ɗora babbar tukunya mai cin loka guda na shinkafa. Tumaturin da ke wurin ta kwashi kusan rabi da tarugu da albasa sai ta fito da turmin waje ta fara daka. Lokaci bayan lokaci tana duba tukunyar a kicin. Yasir da ya gaji da wasan ya fito waje ya zauna saman tabarma. Ta yi nisa a girkin ƙofofin kunnuwanta suka tsinkayi sallamar Mairi da Dauda Imamu. Da gudu Yasir ya je garesu yana murna.

''Sannunku da zuwa'' Sahura ta faɗa tana miƙa hannu za ta ɗauki Jalil. Noƙewa ya yi jikin mahaifiyarshi yana shirin sakin wani sabon kuka.

''Ai tun da ya fara wannan kuka yake ƙyuiya har malaman asibiti bai bar su ba''

Murmushin da bai kai ciki ta yi tana satar kallon Dauda Imamu da ya shagala wasa da Yasir.

''Girki kika ɗaura ashe'' Mairi ta tambaya.

''Eh yaya Mairi,ai na ji shiru-shiru ba ku dawo ba,ga hantsi ya fara duban ludayi shi ya sa''

Murmushi Mairi ta yi tare da miƙa wa Dauda Imamu shi,abin mamaki da fara'ah ya mika hannunsa. Suka shige ciki,sai ta nufi kicin ɗin. Mamaki sosai ya cikata ganin aika-aikar da Sahura ta yi da kayan abinci. Duban Sahura ta yi

''Sahura ai kin cika abincin,ina za mu kai shinkafa loka guda? ''

Ɗan ɓata fuska Sahura ta yi don ba haka ta so ji daga bakinta ba.

''Yaya Mairi yi haƙuri kin san na saba da girkin gandu, na za ci girkin har dare ne ba sai an kuma yin wani ba irin na gidanmu.''

'yar dariya Mairi ta yi ''A'a! mene ne na ba ni haƙuri kamar kin mini laifi. Ba komai wallahi. Baban Yasir bai cika son abinci mai sanyi ba musamman  da daddare. Shi ya sa nake girki biyu a rana. Karin safe sai girkin dare da yake baya wuni gida sai yamma yake shigowa.''

''Ai shikenan zan kiyaye na gaba''

Daga haka suka ci gaba da aikin a tare har abinci ya kammala wanda a lokacin an kusa kiran sallar azahar. Cikin kuloli Mairi ta zuba abincin tare da kai su cikin falo ta bar Sahura a kicin. Plate ɗaya na shinkafa ta take sannan ta koma cikin falon. Bata tarar da Dauda Imamu ba sai Mairi tana shayar da Jalil. Zama ta yi har aka kira sallah sannan ta fita ɗauro alwala. Bata iske Mairi a falon ba ta wuce ɗakinta buga sallarta ta 'yar faki ba yawa sai lada. Koda ta idar bata fito ba ta yi kwanciyarta tun da cikinta ya dau lodi.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a gidan Dauda Imamu inda Sahura bata bar koda taku ɗaya wanda za a gane halayyarta ba. Cike da salo irin na hawainiya take komanta, sannan bata daina yi musu laɓe ba.A ɓangaren zamantakewarta da Dauda Imamu ba laifi yana kyautata mata daidai gwargwado. Bata ganin kyautatawan idan ta haɗa da yadda yake nuna tsantsar kulawa ga Mairi da yaranta,sai ta raina kanta,ƙiyayyar da ta ji akan ya sake linkuwa. Jalil kuma tun daga ranar ya fara mata ƙyuiya, baya yadda da ita kwata-kwata.A cikin satin ta samu damar zuwa gidan 'yar ƙuda,inda ta samu sabbin darussa waɗanda tamkar muggan makamai ne da za ta yi amfani da su wurin kai abokiyar zamanta ƙasa warwas!. Da zarar Mairi ta tafi makaranta sai ta kulle gidan ta nufi gidan 'yar ƙuda a can suke kafa majalisa su yi ta ƙulla makirci kala-kala ga abokan zamansu. Burinsu ɗaya,tafiyarsu ɗaya sannan BAHAGON TUNANINSU iri ɗaya ne a kan abokan zamansu. Sun zama tamkar ɗan juma da ɗan jummai. 'yar ƙuda irin makiran matan nan ne masu tsananin kishi, ba su da lokacin kula da yaransu balle mazajensu sai zafin kishi da mitar magana,wanda dalilin haka ne ya sabbaba wa mijinta ƙaro mata kishiya duk da ba a gida ɗaya suke ba amma bata tsira daga sharrinta ba. Abu mafi muni daga cin halayyar 'yar ƙuda shi ne kyakkyawan ƙawancen da ta ƙulla da ƙazanta tare da rashin iya girki. Bambancinta da Sahura abu biyu ne: ita Sahura ta iya girki sannan tana da tsafta sosai. Mugun hali ne dai ya zo irin ɗaya.

A gefe guda Dauda Imamu yana koyarwansa da sayar da hatsinsa. Wani abu da ke ci mishi tuwo a kwarya shi ne ƙarancin addinin da Sahura ke fama da shi. Ya yi matuƙar mamaki a daren da ya kwana ɗakinta,inda ya yi mata 'yan wasu tambayoyi waɗanda suka shafi addininta, sai ya ji ɗif! Tamkar an ɗauke ruwan sama,ta kasa ba shi amsa sai inda-inda take. Ganin 'yan tambayoyin addini ma ta kasa amsawa,sai ya tambayeta yadda ake addu'ar saduwa da iyali da wankan janaban. Tirƙashi! Yau ake yinta wai tsohuwa ta ga ranar mutuwarta. Tamkar ruwa ya cinyeta haka ta yi shiru tare da duƙar da kanta saboda kunya. Ya kwankwanɗi madarar mamakin da bai taɓa kwankwaɗa ba, a ce 'yar gidan kawunsa ta kasa amsa tambayoyi masu sauƙi da suka shafi addininta. Ɗiyar malami mai tsanani a kan mayar da hankali wurin karatu. Ta ya hakan ta faru? Ganin babu mai ba shi amsa,sai kawai ya koya mata yadda ake wankan tsarki da sauran abubuwan da suka shafi ma'aurata.Daga bisani suka canja channel. Washegari ya samu Mairi a kan ta fara koyar da ita abubuwa mahimmai da suka jiɓanci addini kafin ya sakata islamiya,don wannan abin kunya ne mai girma gare shi,a ce matarsa ko farillan alwala bata sani ba. Bayan fitar Dauda Imamu Mairi ta tuntuɓi Sahura maganar koyarwan. Shafa ma idanunta toka ta yi tana mazurai a kan ba wani Dauda Imamu ya ce ta koya mata karatu, karya take. Abinka da mai sanyin hali fita daga har karta ta yi,sannankoda Dauda Imamu ya dawo bata sanar masa abin da ya faru ba gudun cece-kuce.

Cikin ikon Allah a cikin wata biyu da zuwan Sahura gidan ta samu juna biyu, ta yi murna sosai wanda misaltawa ɓata lokaci ne. Da yake tun da ta zo gidan bata ga baƙonta ba ga kuma ɗan massasara da ke yawan kawo mata ziyara musamman da yamma, sai Dauda Imamu ya kai ta asibiti inda a nan aka tabbatar masa da juna biyu gareta na sati uku. Ya yi murna da samuwar cikin haka Mairi lokacin da ya sanar mata. Sahura ta ci gaba da renon cikinta inda take samun kula sosai   musamman wurin Mairi,duk fitar da za ta yi sai ta dawo mata da kayan maƙulashe wanda ta san masu ciki na so. Dauda Imamu ma wani lokacin yana kawo mata. A gefe guɗa ƙawancenta da 'yar ƙuda sai ƙara ƙarfi yake. Haƙiƙa Sahura ta yi nasarar saye zukatan Mairi da Dauda Imamu da kyawawan halayyarta da take nuna musu. Ga hakuri da kawaici, duk abin da za su yi idan bai shafeta ba bata saka musu baki koda kuwa a ranta tana son hakan. Duk da cikin da ke jikinta bata fasa aikin gidan ba,Mairi ta kwaɓe ta a kan ta bari amma ina neman gindin zama take da iya ƙarfinta,haka Mairi ta hakura sai dai suna komai a tare kamar yaya da ƙanwa.

Kwanci tashi babu wuya wurin Ubangijin halittu, cikin Sahura ya shiga watan haihuwarsa, da yake tana zuwa asibiti awo duk da ba kowa yake zuwa a unguwar ba amma Dauda Imamu ya kafe tare da tirjewa a kan zuwanta asibitin duba tafiyarta da ɗan da ke cikin. A ɓangaren Mairi kuma ta yaye Jalil amma har yanzu babu ciki,hakan ma take so ,a cewarta gwara ta huta. A ranar wata asabar Sahura ta tashi da matsanancin ciwon baya,Allah ya ƙaddara shigowan Dauda Imamu kenan ya ga halin da take ciki, bai yi wata-wata ba ya fita da kiran mai 'yar ƙumbula, cikin ƙanƙanin suka wuce da ita asibiti, ta daɗe tana naƙuda daga bisani Allah ya sauketa lafiya,ta haifo zankaɗedan Jariri mai dogon hanci irin nata. Da yake Mairi ta taho da kayan haihuwa,ana haifar yaron wata malamar asibiti ta fito daga ɗakin ta amsa kayan. Da kusan mintuna ashirin aka fito da jaririn cikin kayan sanyi masu kyau. Mairi da ke ƙofar ɗakin ta yi saurin amsarshi cike da murna. Kallon ƙauna take yi masa murmushi kwance a fuskarta,sai ta miƙa ma Dauda Imamu inda a nan ya yi masa kuɗuba da kiran sallah. Ya tauna dabino ya ɗiba kadan ya lakata masa a baki da ruwan zam-zam. Unguzoma ta sanar musu sun yi mata allurar bacci zuwa nan da awa ɗaya zata farka. Ɗakin da aka kwantar da ita ta yi musu jagora kasancewar a ɗakin haihuwa akwai ƙofar da ake fita da masu haihuwa zuwa ɗakunan hutu. Sun sameta tana bacci. Barin Yasir Mairi ta yi hannun Dauda Imamu, sai ta goya Jalil ta bar asibitin zuwa giɗa haɗo ma Sahura abin da za ta ci,Babur ta hau ya kaita har unguwarsu cikin ƙanƙanin lokaci. Ruwan zafi ta dafa sai ta juye a flask sannan ta hado da madara da biredin da suka rage ta nufo asibtin,har ta kulle gidan za ta tari mai babur 'yar ƙuda ta fito daga gidanta,a tsaitsaya Mairi ta sanar mata da haihuwar sannan ta hau babur ya wuce da ita fatanta kar Sahura ta farka babu wani abu mai ruwa da zai warware mata 'yan hanji. 'yar ƙuda komawa gidan ta yi ta sauya shiga. Tsaftattun kaya ta saka sai ta kai yaranta biyu gidan maƙotanta sannan ta nufi asibitin. Mairi bata cika mintuna goma  da zama ba Sahura ta farka,sai faman ɗaura na mujiyarta take a allon fuskokinsi. Jaririn Dauda Imamu ya mika mata

''Ya jikin naki?" Ya tambaya bayan ta amshi yaron

A hankali da furta ''Da sauƙi''

Miƙo mata kofin shayi Mairi ta yi tana mata sannu.

''Assalamu Alaikum'' 'yar ƙuda ta yi sallamar tana shigowa ciki,ta cancaɗa ado kamar mai zuwa biki. Har yaranta sun laƙanceta, bata kwalliya ko saka sutura mai kyau sai idan za ta unguwa. Kujerar da ke kusa da gadon ta zauna tana mata sannu. A hankali Sahura ta ɗaga mata kai. Yaron na tsotson nono ita kuma tana kurɓar shayin a hankali kamar an yi mata dole. Malaman asibiti biyu suka shigo suna tambayar ya jikin nata ko akwai inda yake mata ciwo. Sanar musu ta yi bata jin ciwon komai sai cikin kaɗan da ƙasanta. Jin komai lafiya lau ɗaya daga cikin  malaman ta dubi Dauda Imamu tare da sanar masa za su iya komawa gida amma kafin nan ga wasu sunan magani da ta rubuta za ta  din ga sha ya siya. Mikewa ya yi ya bar ɗakin zuwa kemis da ke wajen asibiti,koda ya dawo har Sahura ta kammala shan shayin sun haɗa kayansu. Sake fitawa ya yi ya nemi 'yar ƙumbula,sai suka dawo gida

'yan barka suka shiga zuwa ganin jariri da yake yanzu Sahura tana shiga gidaje. A washegari Dauda Imamu ya yi tafiya zuwa Sakkwato faɗin haihuwa. Kwanansa biyu daga bisani ya dawo tare da ƙanwarta Sahura autarsu da ƙanwar mahaifiyarta, lokacin  saura kwana huɗu suna. Danƙareran rago ya siyo mata,a ranar suna jaririn ya ci sunan HAMID DAUDA ƊAHIRU IMAMU. 'yan layi sun yi kara sosai don babu masaka tsinke a gidan. Washegari aka soye rago,Inna Rahane ta kasa ragon kowa ya ɗauki nashi, ɗayan washegarin su kuma suka koma Sakkwato. Sun bar Mairi ta yi wa Sahura wankan jego tun da ta iya. Da safe bayan sun kammala karyawa ya yi gyaran murya don akwai maganar da ke guntse cikin bakinsa ta farinciki yana so ya furza musu su ma.

''Akwai magana mai muhimmanci da nake so na sanar muku. Daman  wani abun alkhairi kuma cigaba ya same ni a wancan satin,ganin ana hada-hadar suna ya sa na bari sai bayan suna sai na sanar muku da abin farin ciki''

Hamdala kowannansu ya yi,sai Dauda Imamu ya ɗan numfasa sannan ya ɗora

''An aiƙo mini saƙo daga Kaduna a kan...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol