Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by Narrnarhh Bukar · BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

Narrnarhh Bukar

(Lady with the Amazing pen ✍️)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

004

Da safe  bayan sun kammala karyawa ya yi gyaran murya don akwai maganar da ke guntse a bakinsa ta farinciki yana so ya furza musu su ma.

''Alhamdulillah taro ya tashi lafiya. Daman akwai wani abun alkhairi da ya same ni wancan satin,ganin ana hada-hadar suna ya sa na bari sai bayan suna sai na sanar muku da abin farin cikin''

Hamdala kowannansu ya yi,sai Dauda Imamu ya ce

''An aiƙo mini saƙo daga Kaduna a kan ana roƙon na zo na koyar tare da limancin jumma'a a sabon masallacin da ke cikin barikin sojojin sama na cikin jihar Kaduna. Ba a daɗe da gama ginin islamiyyar da masallacin ba. Ta hanyar abokina wanda muka kammala sakandare tare sakon ya iso gare ni''

''Alhamdulillahi khasiran! Wannan kuwa abin farinciki ne sosai a garemu. Allah ya ci gaba da buɗa maka hanyoyin samun dubban nasarori.'' Mairi ta faɗa cike da murna. Da ''Ameen'' suka amsa.

''Na yi murna sosai da wannan abin farincikin. Hamid ya buɗe hanyar samun nasarori garemu...''

''Auzubillah! Sahura! Kin san girman saɓon da kika yi yanzu kuwa!" Dauda Imamu ya faɗa yana katse mata sauran furucin da bata ƙarasa faɗi ba. To ita me furucinta ya yi da za a haɗa shi da saɓo. Narai-narai da idanu ta yi tana duban Dauda Imamu ta ce

''Yaya Imamu me furucina ya yi? ''

''Au ba ma ki san saɓo kika yi ba yanzun ! Ta ya za ki ce sanadin Hamid hanyar nasara ta buɗe. Wa ya ce miki saboda wani ne Ubangiji ke ikonsa a kan bayi. Ana saura kwana huɗu ki haihu saƙon ya iso gare ni. Sai da na  bincika sahihancin saƙon da kusan kwana uku kika haihu. Yanzu a nan ina alaƙar haihuwar Hamid da wannan saƙon? Ki dinga auna magana kafin ki furta?"

''To Yaya Imamu zan kiyaye. In shaa maka Allahu..''

''Ba in shaa maka Allahu ake cewa ba, in shaa Allah ake faɗa''

''To''. Sahura ta faɗa a sanyaye zuciyarta na ƙuna saboda tozarcin da ya yi mata gaban kishiyarta. Ya rasa inda zai jizgata sai gaban kishiyarta 'Akwai ranar ƙin dillanci. Mu je zuwa! Za ku sha mamakina ne! Da Sahurar gwaggwan bugaje kuke taɗin' ta faɗa a ranta. Zama Dauda Imamu ya gyara sai ya ci gaba da cewa

'' Gobe zan yi tafiya zuwa Sakkwato sanar da su Inna da Kawu maganar aikin, idan na dawo zan tafi Kaduna. Zan je na ga komai da idanuna, idan komai na wurin ya kwanta mini ciki har da tsarinsu,to a tafiya ta biyu zan ɗauki ɗaya daga cikinku mu je can, daga baya ta dawo sai 'yar'uwarta ita ma ta je. Sadiƙu zai riƙa aiko da kuɗin cefane. Sannan idan kuna da buƙatar wani abu ku sanar mishi. Kamar yadda kuke zamanku lafiya don Allah kar don bana nan ku sauya hali. Ban da shiga maƙwabta da zuwa suna na sake jaddadawa. Musamman ga ke Sahura da har yanzu baki gama sanin kan unguwar ba'' ya ƙarashe maganar yana dubanta. Jinjina masa kai ta yi a ranta tana faɗin 'Sai dai kar a kuma, shiga maƙwabta na nawa. Da sahurar gwaggwan bugaje kake zancen'

Fita Dauda Imamu ya yi daga gidan zuwa kantinsa da ke kasuwa. Mairi ta wuce ɗakinta ko mintuna goma bai cika ba ta fito sanye cikin hijabi mai zip a baya. Ta goya Jalil ta riƙo hannun Yasir.

"Maman Hamid zan je gaishe da 'yar'ajinmu. An kwantar da ita a asibitin Yariman Bakura. Ban samu zuwa tare da 'yan'aji ba saboda ranar sunan Hamid ne. "

"A dawo lafiya! Ki yi mata sannu da jiki" Sahura da faɗa tana ciro wa Hamid nono. "To" Mairi ta ce sannan ta nufi hanyar waje. Watar uwar harara Sahura ta bi bayanta da shi tana taɓe baki. Sai da ta tabbatar ta bar gidan sannan ta ja tsaki mai tsayi tana faɗin

"Kallonku kawai nake yi! Duk cin fuskar da kuke mini sai na yi muku wanda ya fi shi! Shiga maƙota yanzu na saka ƙafa. Haka kurum! A hanaka shiga jama'a saboda munafunci. To ba zan yarda ba!''

Mayar da nonon ta yi cikin riga sannan ta wuce ɗaki ta goya Hamid sai ta zuri mayafi ta fito tana bambami ita kaɗai. Kulle ƙofar falon ta yi sannan ta fito ta kulle ƙofar waje. Sai ta wuce gidan 'yar ƙuda. Ta tarar da gidan kaca-kaca. Kayan wanki a gefe guda wasu an tsumasu cikin ruwa,wasu kuma an matse su amma suna ajiye, ga baho cike da kayan wanke-wanke ƙuda sai cin kasuwarsu suke ciki hankali kwance. Ga sumumun warin da ke tasowa daga kwatar da ke tsakiyar gidan. Toshe hanci Sahura ta yi tana tsallake kwatan sai ta shige ɗakin 'yar ƙuda,a ranta tana mamakin ƙazantar 'yar ƙuda. Ita dai bata taso gidansu ta ga ana ƙazanta ba. Gwaggwon Bugaje mahaifiyarta ƙarshe ce a tsafta, duk sati sai ta yi kwalemar ɗakinta haka sauran matan ubanta dukkaninsu suna da tsafta daidai gwargwado. Da zancen zucinta ta shige cikin ɗakin laɓɓanta ɗauke da sallama.

''Salamu alekun''

''Wa'alaikum salam. Maman Hamid! ke da kike jego me ya fito da ke?''  'yar ƙuda ta furta cike da mamaki tana dubanta.

Zama Sahura ta yi a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin tana sake jin ƙyanƙyamin ɗakin ba tare da ta bata amsa ba. 'yan matan Kaduna sai bidirinsu suke a saman kujerun.

''Ina na ga ta zama 'yar ƙuda! Dole na zo na tsaigunta miki da dumu-duminsa'' Sahura ta faɗa bakinta kamar gonar audiga tana ciro Hamid da ke ɗan mutsu-mutsu a baya. 'yar ƙuda da jin haka ta tashi daga saman kujerar da take ta dawo kusa da kujerarta.

''Yawwa aminiya tsaigunta mini! Ji nake kamar na antaya cikin zuciyarki na karanto da kaina! Hala a kan Maman Jalil ne?" 'yar ƙuda ta tambaya tana amsar Hamid daga hannunta. 'yar dariya Sahura ta yi bayan ta miƙa mata shi ta ce

''Ko kusa 'yar ƙuda. Baban Hamid ne ya samu aikin koyarwa a barikin sojojin sama da ke cikin jihar Kaduna''

''Da gaske Aminiya?!" 'Yar ƙuda ta tambaya fuskarta ɗauke da murmushi.

''Wallahi kuwa. Yau ɗin nan yake sanar mana ni da 'yar iyayi"

''Kai amma na tayaki murna. Da ke zai je hala. Garin 'yan boko kuma wayayyu ƙila ma ki koyi turanci a can''

''Ban san takamaiman da wacce zai je ba. Amma na yi imani da mai sama Mairi ba za ta taɓa taka ƙafarta zuwa Kaduna ba,in dai ina numfashi a doron duniya.'' Sahura ta faɗa cike da fariya. Dariya 'yar ƙuda ta yi tare da faɗin

''Wannan rantsuwa haka maman Hamid. Kar Imamu ya ce ta ita zai je fa"

Harara Sahura ta wurga mata tare da cije gefan leɓanta na ƙasa kaɗan. Tsabar bala'i miƙewa ta yi ta shiga jujjuya yatsanta manuniya na hagun tana faɗin

''Wallahi! Wallahi! Wallahi! Rantsuwar musulmi uku ce ko? Idan na bar Mairi ta je Kaduna tsinuwar Allah ta tabbata a kaina. Kin san Allah! Hah! Hah! Haaaa! Da alama baki gama sanin halina ba! Ba dai zan yi yawon arba'in ba. To magana ta ƙare kuma za ki ce na sanar miki''

''Sai da ke 'yar ƙunan baƙin wake. Duk da ban gama sanin halinki ba amma idanunki kaɗai sun shaida za ki iya komai a kan cikar burinki.''

Amsar Hamid Sahura ta yi sai ta koma  mazauninta,a nan 'yar ƙuda take sanar mata  faɗan da suka yi ita da ƙanwar kishiyarta a kan kwanan miji. Har gida 'yar ƙuda ta yi ma kishiyarta takakka ta so mata zagin  soso da sabulu amma ta haɗu daa daidai da ita. Da yake lokacin ƙanwar kishiyarta na nan kuma masifaffiya ce har ma ta zarceta a faɗa. Sai ta tsoma baki tana tare ma 'yar'uwarta, nan faɗa ya kaure a tsakaninsu har maƙotan kishiyar suka zo bayar da haƙuri. Da yake mijin driban mota ne mai tafiya zuwa garuruwa. A ranar da ya dace ya kwana gidan 'yar ƙuda ya manta ya kwana gidan kishiyar,sai hakan ya ƙona mata rai duk da ya rama mata kwanan kuma ya bata haƙuri amma sai da ta yi mata takakka,sai dai ta haɗu da daidai ta ita,domin ƙanwar bata rage mata koda kuwa farcen susa ba ne. Da ƙarshe ita ya ba rashin gaskiya sai hakan ya ƙara ƙona mata zuciya. Sahura da jin wannan labari ta shiga zuga 'yar ƙuda a kan kar ta kuskura ta yarda da wannan iskanci, ba wani ya manta,da sananshi ya yi hakan saboda ya ga kishiyar ta fi ta tsafta da iya kwalliya. Cikin hikima Sahura ta yi maganar, hannunka mai sanda take mata a kan rashin tsaftarta saboda ta gyara. Kamar Sahura ta sani 'yar ƙuda ta ce mata haka ne,don ƙanwar kishiyarta sai da ta goranta mata a kan ƙazama ce wai taya miji ba zai manta ɗakinta ba. Nan Sahura ta rikiɗa zuwa mallamar tsafta tana ba wa 'yar ƙuda darussa a kan tsaftar jiki da na muhalli. Kamar da gaske haka 'yar ƙuda ta shiga jinjina kai tamkar ƙadangaruwa. Bayan sun gama tattaunawar sai Sahura ta yi azamar barin gidan kar kishiyarta ta dawo ta tarar bata nan.

Ta fito daga gidan kenan idanunta suka yi arangama da Dauda Imamu tsaye a barandar gidan ya sarƙafe hannunsa yana kallon ƙasa kamar mai nazari. Miyau mai kauri ta haɗiye muƙut! Sannan ta ci gaba da tafiya kamar wacce take tsoron ƙwai ya fashe mata a ciki. Tana isowa wurin ta yi ƙarfin halin cewa

''Sannu da zuwa yaya Imamu. Daman 'yar ƙuda ce ta ari...''

''Ban tambayeki ba! Buɗe mini ƙofa!" Ya faɗa yana katse mata hanzari a tsawace.

Mukullin tasa ta buɗe ƙofar ƙirjinta na dukan uku-uku. Bai kulata ba ya shiga ciki,jiki a sanyaye ta bi bayansa,yau dai dubunta ta cika. Ko awa ɗaya ba a yi da faɗa mata a kan shiga maƙota ba amma ta shige. Suna isa falon ya jiyo idanunsa duk sun kaɗa saboda ɓacin rai ya ce

''Wani kashedi na yi miki ɗazu?" Ya tambaya yana kallon ƙwayar idonta. Da sauri Sahura ta yi ƙasa da idanunta sabon firgici da tsoro suna sake lulluɓeta.

''Da ke nake!" Ya furta a matuƙar tsawace wanda hakan ya sabbaba mata firgici ita da Hamid da ke goye. Ta yunƙura za ta ba shi amsa Mairi ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama. Amsawa Dauda Imamu ya yi a ɗaure,Sahura kuma ta duƙar da

kanta tana jin zafi a zuciyarta. Tambaya Dauda Imamu ya sake yi mata. Cike da inda-inda Sahura ta fara magana tana jijjiga goyonta

''Daman Daman Yaya Imamu ka ce ne Mu daina shiga gidan gidan maƙota. Kuma ni wallahi tallahi na rantse maka da Allah kaya na...''

''Rufe mini baki! Ke har kin yi taurin kan da zan kafa doka ki ƙetare! Kina wankan jego amma kin iya fita gulma!Na maimata yau da safe a kan bana son kuna shiga gidan maƙota amma kika yi biris da zantukana,kika yi tafiyarki! Saboda kin raina ni! Babu abin da ke cikin ƙwaƙwalwarki sai yawon bin gidajen maƙota gulma da tsaigumi. To wannan ya zamanto na farko kuma na ƙarshe idan har kina son zama da ni a gidan nan lafiya! Kar ki kuskura ƙarfarki ta sake taka gidan wata idan ba barka ko rasuwa aka yi ba! Idan kuma kin ce ba haka ba, to zan fito miki da aihinin launina. Haka kika ga Mairi tana yi ne. Na ga alamar zaman gidan ne kika gaji da shi,da zarar na dawo daga Kaduna zan saka ki islamiya.'' Daga haka ya wuce ɗakin Mairi ya bar Sahura tsaye ƙiƙan tana zubar hawaye. Mairi tun da ta yi sallamar ta ga yanayin yadda ya amsa mata bata sake cewa komai ba ta ja hannun Yasir suka shiga ciki ta shimfiɗar da Jalil da ke bacci. Koda Dauda Imamu ya shigo ciki wani littafi ya ɗauka ya bar gidan ba tare da ya dubi Sahura da ke tsaye wuri guda ba. Takaicin duniya ya gama lulluɓeta, a kan abin da bai taka kara ya karya ba yake mata sababi a kunnuwan kishiyarta. Tun da ta zo gidan bata taɓa jin ya yi mummunar furuci ga Mairi ba sai ita,duk wani kashi idan ya tashi ita yake yaɓama wa. Matar so bata laifi sai ita. A gaskiya haƙurinta ya ƙare ko a gidan mijinta na farko bata fuskanci wulaƙanci irin haka ba,hasalima ita take murza kambun ikonta son rai,sai abin da ta ce shi tsohon mijinta yake kuma cikin hanzari da rawar jiki amma ta zo nan ana mata cin fuska da iya shege kala-kala. Da sake kam!

Fuuuu! Ta wuce ɗakinta ta sauke Hamid da ke baccin lokacin a saman sabon gadon da Dauda Imamu ya saka a yi mata kafin haihuwarta. Bai kai na Mairi ba amma shi ma yana da kyau sosai. Gefe guda ta koma tana huci ita kaɗe. Ƙwaƙwalwarta na sake tafiyo mata kalaman Dauda Imamu

''Rufe mini baki! Ke har kin yi taurin kan da zan kafa doka ki ƙetare! Kina wankan jego amma kin iya fita gulma! Na maimata yau da safe a kan bana son kuna shiga gidan maƙota amma kika yi biris da zantukana,kika yi tafiyarki! Saboda kin raina ni! Babu abin da ke cikin ƙwaƙwalwarki sai yawo bin gidajen maƙota gulma da tsaigumi. To wannan ya zamanto na farko kuma na ƙarshe idan har kina son zama da ni a gidan nan lafiya! Kar ki kuskura ƙarfarki ta sake taka gidan wata idan ba barka ko rasuwa aka yi ba! Idan kuma kin ce ba haka ba, zan fito miki da aihinin launina. Haka kika ga Mairi tana yi ne!  Na ga alamar zaman gidan ne kika gaji da shi,da zarar na dawo daga Kaduna zan saka ki islamiya.''

Cije laɓɓanta ta yi da matuƙar ƙarfin wanda hakan ɗabi'arta ce idan abu ya ɓata mata rai. 'Idan ka san wata ai bai san wata! Islamiyyar ba zan je ba tun da ban ta so na gani a ɗakin gwaggwota ba! Duk faɗan Baba haka nan ya gaji ya ƙyalemu! Don haka kaima haka za ka barni!  Aikin ɓur in ji tusa! Da Sahurar gwaggwan bugaje kake da kai da makirar matarka annamimiya! Duk zan yi maganinku! Zan shayar da ku giyar mamakin da ba ku taɓa sha ba da hannuna. Mtsss!' ta faɗa a ranta, zuciyarta na ƙara mata ƙuna.  

Wani cur Sahura ta yi a ɗaki,daman ba sallah take balle ta fito yin alwala,ta kan ji muryar Mairi da yaranta, kwallar da naman sunan yake ciki ta ɗauko ta tasa a gaba tana mishi cin yunwa. Ta ci sosai daga bisani ta mayar da kwallar ƙarƙashin gado. Sai yamma Mairi ta leƙo ɗakin ta sanar mata ta kai mata ruwan wanka. Sai da ta mulla ta mulle sannan ta je bayin, Mairi ta biyota a baya ta taimaka mata ta yi wankan ta yi ma Hamid shi ma wanka. Da daddare bayan Dauda Imamu ya kammala cin abin ya aiki Mairi ta kira Sahura. Hannunta riƙe da Hamid ta fito kallon,a sanyaye take tafiyar kamar marainiya. Bayan ta Zauna ta dubi Dauda Imamu ta ce

''Yaya Imamu ga ni"

Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya fara magana

''Ki shirya zuwa gobe zan wuce da ke Sakkwato ki yi wankan a can. Na ga alama a nan yawanki kawai za ki  yi  madadin wankan jegon. Duk kayan da kika san kina buƙata to ki tattara su a daren yau,gobe tare za mu tafi In shaa Allah''

Wani irin farinciki mara misaltuwa ya mamaye zuciyarta,wannan gwaggwaɓar damace mai girman gaske a gareta,damar ta za ta sauya komai ya koma a tafin hannunta. Kamar yadda ta juya tsohon mijin haka take fatan juya Dauda Imamu da makirar matarsa mai zubin mayu...

''Kin yi shiru! Tafiyar dole ki yi ta! Don ba zan bar gari ki ci gaba da wasa ƙafarki kina bin gidajen unguwa gulma ba. Da mutuncina da ƙimata a unguwar nan ba zan bari ki yi silar zubewansu ba. ''

''To to Yaya Allah ya kai mu goben lami lafiya" bata jira amsarsa ba ta miƙe,har za ta wuce ta ji muryarsa

''Kawo Hamid kar ya takura miki wurin haɗa kayan'' Babu musu ta miƙa masa shi sannan ta wuce cikin ɗakin. Ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga zaɓar kayan da za ta tafi da su da na Hamid. Tana 'yan waƙe-waƙenta,ta rasa inda za tsoma ranta don farinciki. Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala komai har  da namanta na kwalla sai da ta juye shi cikin leda. Sai da ta kammala komai sannan ta dawo falon ta ɗauki Hamid lokacin kusan 9:30pm na dare,sai ta shimfiɗar da shi saman gado ita ma ta bi lafiyar gadon. Jim! Kaɗan da kwanciyarta kunnuwanta suka farauto mata muryar Mairi da Dauda Imamu. A hankali ta cire nonon daga bakin Hamid ta gyara rigar sannan ta miƙe. Saɗaf! Saɗaf! Ta shiga takawa tana ɗage dudduginta sama har ta isa ƙofar ɗakin Mairi. Isarta ke ta wuya ƙofofin kunnuwanta suka tsinkayi furucin da ya kusa zautar da ƙwaƙwalwarta da sauya farincikin da take ciki zuwa baƙin ciki. A ranta ta furta 'Kutumar...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.