Free chapter 路 Read without an account

PAGE 37

by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO

GANIN IDO 馃馃

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671

FREE-BOOK

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel 蓷inmu na tafe in sha Allahu zamu ri茩a yi muku posting gaba 蓷aya free books 蓷inmu wa蓷anda babu algus....

PAGE 37

"Na cutar da 蓷an da ya yarda dani Alhaji Ustaz, na jefa rayuwar sa cikin hatsari da wahala..."

Nan ta zayyane masa duk abin da ya faru bata 蓳oye masa komai ba har abin da ya faru ranar da aka kawo Beenafah. Bayan ta kambala fa蓷a masa ta kalle shi da wata irin damuwa ta ce.

"Alhaji Ustaz! Kai 蓷an uwan mijina ne,tsawon shekarun nan, tun Alhaji na raye da ma bayan 茩asa ta rufe idonsa, daidai da rana 蓷aya ba ka ta蓳a nuna min wani hali na musgunawa ko kuma cutarwa ba......"

A gigice ya mi茩e yana mai jin wata iriyar zufa na keto masa ta ko'ina ya 蓷aga mata hannu ya ce.

"Ke.. Ke! Hajiya Batula dan Allah dakata! Yanzu kina nufin daga ke har Margayi babu wanda ya ta蓳a fa蓷awa yaron nan cewa mahaifiyarsa da ta haife sa ta rasu ba? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

"Wallahi sharrin shai蓷an ne..."

"Sharrin ki dai Hajiya Batula! Sharrin ki dai... Kuma duk abin da ya faru na 蓳oye masa wannan maganar da kuka yi tabbas makircin ki ne..."

Share hawayenta ta yi ta shiga gya蓷a kanta kamar wata mai motsin 茩wa茩walwa tana fa蓷in.

"Wallahi ba laifinsa ba ne, duk ni ce na shirya hakan, don ya mutu kuma ba zan masa 茩azafi ba. Ni ce nan na shirya hakan na rokesa akan kar mu fa蓷a masa gaskiya don kada ya wayi gari ya yi kukan maraici ko ya ri茩a jin idan ya yi wani laifin na yi masa hukunci kada ya ri茩a jin cewa don ba ni na haife sa ba ne....wallahi a farko lafiya 茩alau nake zaune da shi a raina, ban ta蓳a cutar da shi ba, wannan ne kawai kuma na yi ne saboda.... "

" Kaicon ki Hajiya Batula! Wallahi Kaicon ki! Kinci amanar wannan yaron, kin ci amanar mijinki da ya yarda dake sannan muma kin ci amanar mu kin zubar mana da mutunci....sannan kin san wani abu? Wannan abun da kika aikata zai 蓷auka cewar duk da saka hannunmu hakan ta faru don kawai mu gaje dukiyarsa..."

" Na yarda, na kuma amsa laifina amma don Allah Alhaji Ustaz ka taimakeni wurin shawo kansa da basa ha茩uri...gaba蓷aya su Emraan sun guje ni kuma na san sun tsaneni akan wannan kuskuren da na aikata... Wallahi tallahy bana iya bacci. Zuciyata ciwo take, na rasa ina zan saka kaina. Ka taimakeni wurin daidaita wannan abun... "

Cikin wani irin jin sabuwar tsanarta a zafafe ya nuna mata 茩ofa yana fa蓷in.

" Ta shi ki fice mini daga gida! Ta shi na ce.. "

Cikin tausayawa matar sa Mummy Na'imatu ta saukar da murya ta ce.

" Haba Alhaji! Ka yi ha茩uri mana.. "

" Ke! Babu ruwan ki a cikin wannan maganar... Ta je can ta samu en uwanta ta fa蓷a musu.... Su san yanda za su yi da ita. Ai tasan da cewa akwai irin wannan ranar kul ba da蓷e kul ba jima, idan ma nan gidan duniya asirin nata bai tonu ba to akwai gobe al茩iyama inda wani wayonka ko basirar ka ba za su amfana maka komai ba....saboda haka taje can ta 茩ara ta..."

Cike da magiya ta ha蓷e hannayenta ta ce.

" Don Allah ka yi ha茩uri ka rufamin asiri kamar yanda Allah ya rufa maka ka taimaka min wurin ba shi hak'uri da shawo kan '拼a' 拼ana, wallahi tallahi idan har dangina suka ji wannan musamman Alhaji 茒an-Ladi akwai matsala..."

"Ba dole ki shiga matsala ba Hajiya Batula! Idan baki san halacci ba ai su sun sani tunda ya 蓷auke su da muhimmanci da daraja babu abin da suka nema suka rasa na rayuwa...amma ke da yake baki san girman amana ba ga shi son zuciya ya kai ki ya baro ki...."

茒an tsahirtawa ya yi da maganar sannan ya girgiza kan shi cike da takai ci da ba茩in cikin tuna yanda aka yi ta wahala aka yi ta fa蓷i tashi wurin neman masa aure da magani, ya ce.

" Kai duniya! Wallahi Hajiya Batula kin ci amana. Ko ka蓷an ba ki da imani ba ki da zuciyar musulunci! Kuma zaluncin da kika yi wa wannan yaron ki saurari sakamakon ki daga wurin Allah domin girman ha茩茩in sa ba zai bar ki ba..."

Cikin jin wani irin sabon tsoron da ya ta so ya lullu蓳e zuciyar ta yasa ta sake fashewa da kuka tana fa蓷in.

" Wallahi na tuba! Na tuba Alhaji Ustaz... "

Girgiza kansa ya yi ya ce.

" A'a kam! Ba ki tuba ba, domin ba don Allah ya jefa wannan yarinyar ta jiyo bakin zaren ba har ta yi namijin 茩o茩arin taimaka masa ba da yanzu yana nan a yanda yake ba ki yi tunanin daina cutar da shi ba... "

Daga haka ya wuce kai tsaye ya shige 蓷akin sa ya barta nan tana ta kiran sunan sa cike da kuka tana ro茩onsa.

Mummy Na'imatu ta kalla a rauna ne ta ce.

" Dan Allah Hajiya Na'imatu ki taimaka mini akan wannan maganar. Alhaji Ustaz shi ka蓷ai ne wanda zai iya taka min na samu na shawo kan wannan matsalar...."

"In sha Allahu zan masa magana. Ki kwantar da hankalinki komai zai dawo ya wuce."

Daga haka ta mi茩e taje 蓷akin nasa wurin ba shi ha茩uri 茩arshe haka ya kore ta itama yana mai balbaleta da masifa.

Wasa-wasa sai da ta share kusan kwana uku sannan da 茩yar Hajiya Na'imatu ta samu ta shawo kansa ya amince cewa zai yi magana da Mohaan da kuma su Emraan 蓷in. Amma dai ta shirya ta koma gida domin baya ma son yana ganinta a kusa da shi.

********

Gefen Daddy kuwa. Bayan anyi nasarar ce to shi zuwa asibiti sai da ya kwana 蓷aya sannan ya farfa蓷o daga nan aka samu aka kira Mummy, sai gashi ta iso asibitin a gigice. Ganin yanda ya yi wani sha蓳e-sha蓳e akan gadon yasa ta 茩ara gigicewa tana fa蓷in.

"Miye ya faru haka Alhaji?"

A hankali ya yun茩ura ya mi茩e zaune yana mai jin wani sabon zugin a kwankwason sa ya kalle ta a wahalce ya ce.

"Wallahi Ado ne ya kirani akan zancen Mulaifa, shi ne fa na ratse gefen hanya na fito domin yin magana da shi, ashe akwai wa su yaran banza a nan gefena da suka tsaya kamar motar su ce ta lallace suka shamma ce ni suka bugeni suka kar蓳e mukullin motar da wayoyina da komai suka gudu.... "

Wata irin zabura ta yi a gigice ta bugi 茩irji tana gwalo ido kamar na mota ta ce.

" Wace Motar kake magana Alhaji???"

"Wannan dai motar ta wa wacce Alhaji Mansur Anka ya siya min..."

A gigice ta 蓷ora hannu a kai tana fa蓷in.

"Wayyo Allah mun shiga uku mun lalace!!!"

"Haba Mummy dan Allah miye haka? Tun da har ba su yi masa komai ba ya samu ya tsira da ransa ai sai mu godewa Allah."

Cewar Husaina tana mai saukar mata da hannun da ta 蓷ora a kai.

Girgiza kai ta yi cike da kuka tana kallon Husainar ta ce.

"Husaina kin san ko motar miliyan nawa ce? Wannan mummunan labari da mi ya yi kama? Akan me zai tsaya gefen hanya inda yake da ji ba kowa ya ce wai zai yi waya in ban da dai shafewar basira.."

"Mummy 茩addara ce! Wallahi babu wanda ya isa ya kauce wa abin da Allah ya rubuta masa. Na san cewa dole rashi bashi ba da蓷i to amma abu mafi muhimmanci shi ne yana raye cikin 茩oshin lafiya. Allah da ya bashi shi zai 茩ara ba shi wata ta inda bai yi tsammani ba.."

"Haba Husaina! Wannan masifar ta yi mana yawa wallahi..."

"Mummy ki yi ha茩uri sai mu yi ta gayawa Allah shi ne zai yi mana mafita."

Daga haka ta juya ta kalli Daddy ta ce.

"Daddy ya jikin?"

Amsawa ya yi da.

"Jiki Alhamdulillahi Husaina..wallahi sai kin gansu, kamar mutanen kirki."

"Allah sarki! Wannan duk jarabawa ce. Allah ya mayar da alheri ya baka lafiya."

"Amin. Kin kira Aysha kin sanar mata halin da nake ciki.."

Wani irin mugun tsaki Mummy ta doka sannan ta ce.

"Wai kai ba za ka daina zancen Ayshar nan ba? Yarinyar da kana cikin halin jimami da damuwa ta saka 茩afa ta wuce ta barka shi ne har kake zancen ta..."

Girgiza kai Husaina ta yi jin irin zancen da Mummyn ke yi na takaici daga nan ta zauna gefen Daddy tana fa蓷in.

" Zan sanar mata, na fi son sai an sallame ka mun koma gida ina tsoro kada hankalinta ya tashi. Amma dai Yaya Hafiz yana kan hanyar zuwa In Sha Allahu... In zubo maka abincin?"

"Eh. Mi kuka zo da shi?"

"white Rice ce da stew, sai kuma tuwo daban."

"OK to, zuba min shinkafar Amma kar ki sa da yawa ka蓷an ya isa."

Ta shi ta yi ta zuba masa kamar yanda ya ce ta zuba mi shi nama sosai sannan ta tsiyaya mishi lemun 5alive a glass cup ta zauna a gefen shi ta mi茩a mishi tana fa蓷in.

"Humaida na makaranta, ka manta baka tambayeta ba.."

"Haka ne. Amma ba mantawa na yi ba nasan yanzu tana makaranta ne..."

Fira suka shiga yi sosai a hankali yana bata labarin abin da ya faru tiryan-tiryan yayin da Mummy ke gefe zuciyarta kamar za ta fashe tsabar ba茩in cikin motar da ya bari aka sace, sai kuka take kamar wacce aka yi wa mutuwa.

Bayan Hafiz ya iso 蓷in ne ya je ya ga likita ya biya ku蓷in magani sannan aka ba su sallama suka tafi gida.

Tun da abin nan ya faru tsawon sati 蓷aya Daddy bai san abin da yake masa da蓷i a rai ba. Daman ga matsalar Ammie da ta ce wai ta aurar da Beenafah ta gudu. To shin wai tun farko ma wacce haukar ce tace mishi ya kore ta daga gidansa? Kwata-kwata bai yi tsammanin cewa za ta iya yin tunani irin wannan ba, domin ya 蓷auka cewa har yanzu ciwon hauka yana damunta wanda ba ta iya fahimtar komai. Ashe yana nan zaune ya sake baki ta gama aiwatar da gaban kanta. Saboda haka, idan har bai yi saurin 蓷aukar mata mataki ba, to tabbas ya san za ta iya aikata masa wata muguntar. Shi yasa yake ta neman ta ruwa a jallo domin ta riga Malam masallaci.

Yana zaune da dare kamar wasa Ado ya kira ya sanar da shi cewa aikinsa ya kambala. Take ya ji kaso sittin cikin 蓷ari na matsalolinsa ya tafi. Ba 蓳ata lokaci ya tura masa miliyan goma rabin ku蓷in da suka yi zai ba shi akan zai turo masa da address 蓷inda ya 蓳oye su Ammie a nan Gusau a yanzu. Idan ya zo ya bashi su sai ya cika masa cikon ku蓷i su zama 20M kamar yan da suka yi.

Bayan ya gama zayyanewa Mummy ta fashe da wata irin dariyar nasara ta ce.

"Alhaji, ina so a wannan karon Mulaifa ta shiga haukar da tafi ta baya muni da hatsari. Dole mu salwantar da su da labarin su matu茩ar dai ka na so mu ci gaba da dawwama a cikin wannan daular arzikin har jikokinmu...."

"Ai tun farko ke ce ki ka ja mana duk wannan da 茩aramin tunanin ki. Da ace suna nan a tare damu da yanzu duk haka ba ta faru ba."

Wani irin hura hanci ta yi sannan ta jinjina kai ta ce.

"To ai yanzu za'a yi mai kankat gobe idan Allah ya kai mu na rai....ba茩in cikin da Mulaifa ta dasa min na hana auren Ameer da Beenafah dole itama ta 蓷an蓷ana ku蓷arta.."

Haka suka gama firarrakinsu sannan daga 茩arshe suka je suka kwanta da zimmar idan gari ya waye su wuce Zamfara.

*******

Muna isa da kansa ya bu蓷e min 茩ofa sannan ya kalleni a hankali yace na yi addu'a kafin na sauko da 茩afata.

Bayan na yi yaja hannuna muka shiga cikin gidan,gidan ya cunawa gidan su Hajiyarsa da gidan da muka baro a Abuja nesa ba kusa ba. Duniya ce mai zaman kanta.

Duk inda muka ratsa ni dai biye nake ina rayawa a raina cewa wai ni Beenafah ni ce a nan? Allah mai girma! Mai kuma juya al'amarin bawan sa a duk yanda ya so.

Bayan mun gama ratsa wurare sai ga mu a wani katafaren 蓷akin bacci tangameme mai 蓷auke da duk wasu abubuwan bu茩ata na more rayuwa.

Kallona ya yi a hankali ya ce.

"ki yi wanka ki huta. Akwai kayan ki a nan, komai da komai..."

Ya 茩arashe maganar yana mai nuna min wani closets da ke gefena.

Jinjina masa kai na na yi sannan ya saka kai ya wuce. Wata 茩ofar na nufa na bu蓷e ta sai ga shi na kuwa canka daidai domin nan ne bathroom 蓷in.

Hmm! Wato ba gidan ba, ba 蓷akin ba, hatta bathroom 蓷in wani 茩amshin yake fitarwa na musamman kamar wani 蓷akin bacci. Komai ga shi nan gwanin burgewa.

Wanka na yi domin a gajiye nake sosai,bayan na fito na zo jikin vanity mirror na tsaya na shafe jikina da mayuka da turaruka masu da蓷in 茩amshi sannan na je closet 蓷in na 蓷auki wata rigar roba doguwa marar nauyi na saka, sai da na saka na gane ashe bakin Knee 蓷ina ta tsaya ba ta sauka 茩asa ba. Har na yi nufin canza wa sai kuma na ga wani hijab har 茩asa da hular shi mai kyau na saka na zo inda naga an 蓷an zagaye an saka dimlight da sallayah na gabatar da sallar Asuba sannan na je kai tsaye na kwanta idona har wani ya ji suke min a lokacin tsabar yanda na gaji.

Shi kuwa, wani 蓷akin ya bu蓷e ya shiga ya yi wanka  ya fito ya yi sallah

Sannan ya 蓷auko wayarsa ya kunna ta ya shiga karanta texts 蓷in su Labiba a natse wanda suka kashe masa jiki gaba蓷aya ya kasa wani kata蓳us.

Bayan ya kambala duba sa茩on ya sake kashe wayar sannan ya janyo wata computer 茩arama ya fara aiki a cikinta na tsawon lokaci wanda yana yi  yana tunawa da ni.

Har na gama baccin na na tashi bai dawo 蓷akin ba a lokacin har misalin sha 蓷aya na safe.

Bayan na tashi na cire hijab 蓷in na koma jikin faskaceciyar windown na tsaya ina hango manyan-manyan gine-gine gwanin burgewa.

A hankali na ji takunsa a bayana domin ko ban waigo ba nasan cewa tabbas shi kai 蓷ai ne wanda zai iya shigowa nan direct. A hankali na waigo na gansa Sanye cikin wata casual white shirt da black trouser.

"Ina kwana?"

Abin da na iya furta masa kenan tare da yin 茩asa da kaina domin wani irin nauyinsa ne ke 蓷awainiya da ni a duk lokacin da muka yi ido biyu da shi.

Murmushi ya sakar min tare da 茩arasowa ya rungumoni a jikin sa muna facing windown a tare a hankali ya ce.

"Ban ta蓳a tunanin cewa rayuwa zata bani irin wannan damar ba Beenafah...wannan gidan da kike gani, shi ne duniyata wacce babu kowa a cikinta sai ni da masu aikina...amma a yau.. Sai gaki a ciki a matsayin matata wace ta zamo tsani ta kuma bani hope 蓷in rayuwa a karo na biyu... And from now on... Every sunrise, every night, every heartbeat and every dream.... Will begin and end with only you beside me.. "

Lumshe idanuwana na yi a hankali ina 茩ara saukar da kaina akan 茩irjinsa...tabbas ina jin wani sabon abu na da蓷a wanzuwa a hankali cikin zuciyata game da wannan mijin nawa da na aura saboda ceto rayuwar shi. A duk lokacin da ya furta kalmar godiya a gareni ko kuma kalaman 茩warara gwiwar da ya samu saboda ni, sai in ji gaba蓷aya na shiga wani yanayin farin ciki tare da jin nutsuwa a cikin ruhi da sassan jikina.

Mun jima a tsaye kowa na jin sabon abu na masa tartsatsi a cikin 茩irji sannan daga 茩arshe a hankali ya juyo ni ina fuskantar sa ya ce.

"Kin yi wanka?"

Jinjina masa kai na kawai na yi ina 茩ara yin kasa da kaina.

Da Kansa ya bu蓷e ya 蓷auko min wata Abaya ba茩a da gyalen ta ya bani ya ce.

"ki shirya mu fita waje."

Wani tsil-tsil na yi da ido ina kalle-kalle ganin yanda ya ja tunga ya tsaya yana kallona, to nufinsa in saka kayan a gabansa ko me?

"Ya dai?"

茦ara 茩asa da idona na yi domin ina da bu茩atar undies, maimakon ya yi avoiding 蓷ina kamar yanda ya saba, sai bai yi hakan ba. Ganin yan da na tsaya yasa ya sake Kallona ya ce.

"Do you need something?"

"am! Da..daman ina son undies before na saka wannan 蓷in..."

Bu蓷ewa ya yi ya 蓷auko sabon pant da bra Sannan ya 蓷auko skirt ya mi茩o min.. 'Wayyo Allah na!' Abin da na furta kenan jin yanda zuciyata ta yi wani tsalle har ban san lokacin da na sauke kaina a 茩asa ba tare da ma茩ale hannuna.

" Beenafah!"

Ya furta sunana cikin wata irin muryarda ta 茩ara hautsina wani abu a cikin 茩irjina. Maimakon ya 茩yale ni sai wani janyoni ya yi jikin sa yana fa蓷in.

"Why are you Shy? Huh! Kin manta cewa ni 蓷in mijin ki ne kuma ke 蓷in matata ce?......Ohh common dear! Ke fa kika yi min al茩awarin zamu haifi yara ma su yawa...Ba haka ba ne kenan?"

Fuskar sa ya kawo saitin tawa wanda har muna iya jiyo numfashin juna dani da shi ya 茩ara saukar da murya yana fa蓷in.

"Ki amsa min, ba haka ba ne kenan?"

Ba shiri na runtse idanuna a raina ina fa蓷in 'Innalillahi!.....Ya Allahu! Wannan mutumin ya gama dani a yau. Miyasa ba zai ji kunyata kamar yanda na ke ji game da shi ba.'

Jin saukar la蓳蓳ansa akan nawa shi ya dawo dani daga duniyar da na shiga, a daburce jiki na rawa na shiga neman zamewa amma kuma hakan bai hana shi aikata abin ya fara ba sai ma 茩ara saukar da hannun sa da ya yi zuwa waist 蓷ina giving him more access to my lips...hankalinsa kwance ya shiga kissing 蓷ina gently har zuwa wuyana wanda Shi kanshi na lura yanayin jikin shi ya 蓷an sauya yana shaking a hankali da alama shima karon sa na farko kenan.

Saukar 蓷umin hawayena akan fuskarsa yasa ya janye bakin nasa still da idanuwansa da suka canja launi ya kalleni yana jinjina kansa muryarsa  cikin wani irin yanayi ya ce.

"Na yi laifi ne Beenafah? Har da kuka haka. To ki yi ha茩uri, amma bana son kina jin kunya because now... we are one."

Yana gama fa蓷ar haka, ya saka yatsa ya goge min idona sannan ya ja hannuna ya kai ni gaban kayan ya ce na 蓷auki size 蓷ina na saka.

Jiki a sanyaye na mi茩a hannu na 蓷auko wasu, kafin ya yi wani yun茩uri na shige can ciki ta yanda ba ya iya hango ni na tsaya na saka a gaggauce, 茩irjina ne ya buga tuna cewa to ai rigar tana kan gadon kuma dole sai na fito zan iya sakawa, sannan a inda nake 蓳oye only inners ne a ciki.

Ganin da gaske ba zan fito wa ba yasa ya mi茩a hannu ya 蓷auko rigar ya mi茩o mini yana fa蓷in.

"kar蓳i!"

Bayan na saka na fito na je jikin mirror na na蓷a veil 蓷in sannan na matso inda yake wanda har yanzu 茩irjina bai daina 蓷agawa. bai ko kalleni ba kamar yanda nima ban kalle sa ba yaja hannuna muka fita inda ma'aikatan gidan ya shiga introducing 蓷ina a wurin su. Bayan ya gama mu ka je dining room muka yi break fast. Muna kambalawa ya je ya shirya muka fita, ban san a ina muke ba sai da na ganni a asibiti inda aka 蓷ibi jininmu da ni da shi aka tafi wurin gwaji.

Ina nan zaune wani kyakkyawan office ina kallon drama a TV duk da dai cewa kallon kawai nake amma abin da ya yi min 蓷azu ya yi matu茩ar tsaya min a zuciyata ba ka蓷an ba. Kwata-kwata ban sa rai da tsammanin cewa haka yake ba. Amma an ce baki shi kan yanka wuya. Sai yanxu na yi nadamar furta masa cewa wai zamu haifi yara. kaiii Beenafah! Hmm! In dai ciwon baki ne ai gobe sai in 茩ara yi. Hannu na kai akan bakina a hankali ina shafa la蓳蓳ana lokaci 蓷aya ina jin kamar yanzu ne abin ya faru a tsakaninmu. Har yanzu ban daina jin abin a 茩wa茩walwata ba domin ya shigeni ba ka蓷an ba. 'Wuya na fa!' na fa蓷a ina mai 茩ara kai hannuna inda ya sumbata a wuyana tare da  lumshe idona. Wallahi na ji kunya, na ji kunya sosai kamar 茩asa ta tsage in shige ciki haka na ji....jin an turo 茩ofar yasa na yi saurin shiga taitayina tare da saukar da kaina a 茩asa. Waya ya mi茩o min kurum ya juya ya fice.

Wayar na kai kunnena ganin tana kan kira na ce.

"Hallo Ammie..."

"Na am Beenafah. Da fatan kun isa lafiya?"

Cike da mamaki na ce.

"Daman kin san cewa zamu zo nan kenan?"

"Eh mana, ya sanar mana. Yanzu ma shi ne ya kirani ya ce kina son Magana dani."

"Allah sarki! Ina Bahrain?"

"Hmm! Bahrain yana makaranta, an kai shi tun jiya. Yanzu ni ka 蓷ai ce a gidan nan sai masu aiki, amma dai Hamza ya dawo nan da zama..."

Wata irin dariya na yi ta jindadi na ce.

"Ammie Yaya Hamza fa kika ce? Dan Allah ina yake?"

"sun fita tare da Dr. Zai kar蓳o min sa茩o..."

"To ina su Yaya Jafaru?"

"Jafaru yana makaranta. Su Fakiha suna Gusau.."

Fira muka sha sosai inda a nan ne ta bani labarin yanda suka yi da Uncle Isma'il da yanda tace ayi da ku蓷in. Duk yanda ta wani zage tana shaidamin irin halin da Aunty Hassana ta shiga ni wallahi ko ka蓷an bata bani tausayi ba sam. Yan da nake jin tsanarta a zuciyata duk abun da zai same ta ba zan iya tausaya mata ba. Daman masallaci takai ku蓷in tace ayi wa Abbie addu'a da yafi bai wa Aunty Hassana da ta yi. Bayan mun kambala kamar an ce na shiga gidan lambobi kawai naga numbern aunty Labiba. Ai ko jiki na rawa na kirata muka sha firarmu da ita kamar wani abu mai faru ba harda ta tsayawa ta yi ta 茩ara bani  shawarwari. Haka nake ganin rayuwarta kamar ta Aunty Aysha da Mummy Sameera wurin bai wa mutum shawarwari akan zamantakewa da sauran wasu al'amuran rayuwa.

Bayan na kambala ina nan zaune ina kallon TVn sai ga shi ya shigo. Hannu kawai ya mi茩omin alamar in zo mu tafi, ganin hakan yasa na mi茩a masa hannun don kada ya ce zai min wani abu idan na yi masa gardama.

********

Gefen su Daddy kuwa, washe gari da sassafe suka shiryo daga shi sai ita bayan sun bar Humaida a wurin Husaina da Biba.

Sun shiga mota kenan driver ya tayar sai ga shi an ce Daddy ya yi ba茩i a bakin gate.

Cike da mamaki ya ce.

"Ba茩i da sassafen nan? Je kace su shigo..."

Daga haka ya waiga gun Mummy ya ce.

"Bari in je in ji su waye ke nemana."

Wasu mutane ne su hu蓷u shirye cikin shigar suit ba茩a茩e suka shigo tare da bashi hannu su ka gaisa sannan 蓷aya daga ciki ya ce masa cikin harshen turanci.

"Daga hukumar cibiyar kasuwanci ta 茩asa muke, mun zo ne domin isar da wannan muhimmin sa茩on gareka...."

Hannu 蓷aya daga cikin su ya tura a aljihu ya ciro envelope ya mi茩awa daddy Sannan suka yi masa sallama suka fi ce.

Hannu na rawa ya bu蓷e envelope 蓷in ya ciro sa茩on takardar da ke ciki ya fara karantawa cikin harshen turanci kamar haka:

HUKUMAR KULA DA HARKOKIN KASUWANCI TA 茦ASA (FEDERAL BUSINESS COMMISSION)

Office: Plot 48, Commercial Avenue, Garki II, Abuja, Nigeria.

Zuwa ga:

Alhaji Mudassir Wazeer.

Katamfe Extension, Abuja.

Nigeria.

Subject matter: Sanarwar Rufe Dukkan Harkokin Kasuwancin Marigayi Dr. Bello Wazeer Na 蓷an Lokaci.

Wannan takarda ce daga Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci ta 茦asa (FBC).Dukkan kadarori,kamfanonan kasuwanci da suka kasance 茩ar茩ashin sunan Marigayi Dr. Bello Wazeer:

Bayan 茩arar da aka shigar da sunanka da kuma bin 茩a鈥檌dar da ke cikin Dokar Kula da Dukiyar Masu Kasuwanci.  Sashi na 12, sakin layi na (b), Hukumar ta yanke hukuncin cewa: dukkan ayyuka, kasuwanci, asusun ku蓷i, da mu鈥檃malolin da suka danganci sunan marigayi Dr. Bello Wazeer an dakatar da su na wucin gadi. Wanda ba za a sake bu蓷e kasuwancin ba, saka ku蓷i ko cirewa, canja sunan wani abu ko sauya masa fasali ko ci gaba da gudanar da kowanne daga cikin wa蓷annan kasuwanci ba har sai an samu rubutacciyar amincewa tare da sa hannun matarsa da 鈥檡a鈥檡ansa biyu na cikinsa wanda sai hukumar ta tabbatar da sahihancinsu.

Wannan mataki na nufin tabbatar da gaskiya, adalci, da bin 茩a鈥檌dojin doka wajen tafiyar da kadarorin marigayin. Idan kuma aka yi yunkurin bu蓷e ko yin amfani da dukiyar kasuwancin ba tare da izinin hukuma ba, hakan zai zama an karya doka kuma zai jawo hukunci daga sashen shari鈥檃 na hukumar mai tsanani. Kuma kai ma za a rufe komai naka tun daga kan asusun banki, gidaje, motoci ba za ka sake amfani da komai ba har sai an gama binciken da ya kamata.

Ana ro茩on ha蓷in kai da fahimtarka domin gudanar da wannan tsari cikin lumana.

Sign by:

Barr. (Mr.) Edward Jonathan.

Daraktan Sashen Doka da Bin 茩a'idoji na Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci ta 茦asa (FBC)

Hannu ya saka ya dafe kai tare da 茩wallara wani irin gigitaccen ihu yana fa蓷in.

"Wayyo na shiga uku sau uku! asiri na ya tonu ni Mudassiru....Ku nemomin Mulaifa... Dan Allah jama'a ku nemomin Mulaifa ta saka hannu ita da yaranta."

A gigice Mummy ta 蓳alle murfin motar ta fito amma kafin ta 茩araso har ya fa蓷i 茩asa ya suma.

         鉁嶏笍  OUM-AMEER  鉁嶏笍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.