Free chapter 路 Read without an account

07

by JamilaUmarJanafty 路 RA'AYI NE KO BURI?

**RA'AYI NE KO BURI..?*

Wattpad:jamilaumar351

Mallakar:Janafty馃挅

7

Alhaji Sa"ed Jada mainasara Shine asalin sunan Mahaifin Abdulmutaddif wanda ya kasance haifaffan garin Dawakin Tofa ne Dake Jahar kanon Dabo koda mai kazo anfika.

Mahaifinsa Alhaji Jada dan boko ne Na Bugawa ajarida kafin  Rasuwarsa sai da ya taka matsayin Shugaban Hukumar Inec na jahar kano Gabadaya yana da matar Aure Daya Hajiya Asiya wacce ta kasance itama yar dawakin Tofan ne iyayensu Sunyi zaman makota da juna shiyasa Suka hadasu aure,koda Alhaji jada ya kasnce abun alfaharin garinsu na Dawakin Tofa Saboda Shine kadai wanda yayi karatun Boko agarin ya samu Aikin gwannati mai girma Asiya primarya kadai tagama aka yi musu aure Lokacin agarin yake zaune da ita,agidanshi Daya gida irin na zamani lokaci yana aiki ahukumar Inec din ne kafin ya zama Shugaban Wajen.

Shekara daya Asiya tayi agarin Dawakin tofa Alhaji Jada yazo ya Dauketa suka koma cikin kano Da zama,har ya sakata a makaranta tundaga matakin Jss har tazo ta zana Neco kuma taci sai ya saka a wata makarantar Jinya wato School of Hygen Kano,Tacigaba da karatunta zuwa lokacn har ta haifi Danta na fari wanda yaci sunan Ahmed sai da yakai Shekara goma Kana Allah ya Dauki Ranshi Iyayenshi sun koka da rashinshi Sosai Asiya kamar zata zautu,Daga baya suka fauwalama Allah komai.

Bayan rasuwar Ahmed da Shekara daya ne Asiya ta samu Sa"ed wanda sanadiyar haihuwarshi aka cire mata mahaifa sakamakon jini ya yanke mata kuma tayi Duguwar Naguda sai da ta kwana uku batasan Inda kanta ke mata ciwo ba C.S aka mata aka ciro yaron kuma acire mata Mahaifa,sai datafi Sati acikin asibitin Mallam Aminu kano,Da"aka sallameta Dawakin Tofa ya wuce da ita chan akayi sunan Sa'ed Sai da suka Shafe wajen wata biyu Sa'ed yayi yawo kana suka koma kano Saboda gabatowar jarabawarsu Daga makarantarsu.

Asiya ta shiga damuwa lokacin Da Alhaji jada ya sanar da ita an ciremata mahaifa tayi kuka kamar me, tana fargaban in Allah ya kara karban Ran Sa"ed shikenan ita da Haihuwa har Abada Shiyayayi ta kokarin lallashinta har ta cire damuwar komai acikin ranta ta cigaba da kula da sa'ed dinta yana da Shekara Daya aduniya ta kamallah karatunta ba dadewa Alhaji jada ya sama mata aiki awani private Asibiti tana Zuwa,Ranar datake da Aikin kwana sai ta barmai Sa"ed tatafi sai da safe take dawowa, Ranar Datake da morning kuma Sai ta tafi dashi Lokacin Tashi nayi su Dawo gida tare ko kuma in ya tashi Daga wajen aiki ya biya ya Daukota Asiya ba karamin alfahari take da mijinta ba domin ya zama sanyin Indanuwanta,Ita da iyayenta da dansu,Dama mahaifiyarsa ta rasu tunkafin Aurensu,bayan Rasuwar Ahmed kuma Shima Mahaifinshi Allah ya karbi Rayuwarsa.

Rayuwa tana ta tafiya Tare da karewar kwanakinmu Aduniya Lokaci Daya kuma Asiya da Alhaji jada suna kula Da dansu Sa"ed,har ya gama secondary School yafada ABU zaria yana karatan Quantity Survey,Lokacin kuma tuni Asiya wato Har Alhaji jada yakaita makka da sauke Farali kana kuma ya sama mata wani aiki takoma Aminu kano da aiki tabar private,Sa'ed na Aji biyu a matakin Jami"a Alhaji jada ya samu mukamin shugaban Hukumar zabe na Jahar Kano,ya gida katon gidansu suka koma Tarauni,da zama zuwa wannan lokacin kowani jin Dadin Rayuwa Allah ya basu.

Watarana Alhaji jada,ya je Jigawa domin hallatar wani taro sai hanya ta biyo Dashi ta rugar Hardo Inda Wasu Fulanni ke zaune Gashi yayi Dare sakamakon anyi Ruwa sosai Lokacin Damina ne,yaso ya tsaya ya kwana sai yaya tunanin shima gobe karfe 7 na safe yana da meeting ,Shiyasa wajen karfe 8 ya kamo hanya Daidai Wajen Rugar Motarsa ta tsaya Gashi Daji ne wajen koda ya fito ya Duba gaban mota sai ya fahimta Ruwan motar ne ya kare gashi ba ruwa acikin Motan,Hankalinsa ya tashi ya fara Tunanin ina zai samu Ruwa Hango Wuta yayi Daga nesa inda Rugar Hardo take sai ya rufe motar nashi ya Fito da wayarsa ya kunna ya nufi Rugar da Sauri.

Daidaikun Gidaje ne awajen Rigar farko ya fara Doka sallama Baffa Abdulmutaddif Da matarsa Bintalo da ya"yansu guda biyu Fatima da Amina suna cikin Dakin Rugarsu sun Hura wuta Saboda dakin ya Dauki Dumi Saboda ruwan da akayi,karatu yake musu suka tsikayi sallama da farko sun Tsorata baffa ne bai Tsorata ba,yace su kwantar da hankalinsu bari ya Fita ya gani Sandarshi ya dauka ya Fita tare da fitilansa yana Fita yaci karo da Alhaji Jada Daidai Lokacin kuma Awakai da Shanayen Dake Garkensu suka Fara Kuka fitowar Baffa ganin kamalan Alhaji Jada ne da kuma kayan da jikinsa yasa yaji ya natsu Dashi,Nan suka gaisa yamai bayanin Taimakon Dayake nema Baffa baiyi kasa agwiwa ba ya koma cikin Gida ya saka Bintalo ta Dibomai Ruwa cikin Wata kwarya ya fita dashi tare suka karisa har wajen mota dashi ya mikamai ruwa ya zubama motar ammh kuma koda ya gwada Kunnata taki Tashi ganin yadda hankalin Alhaji Jada yatashi yafara Tambayan Baffa ko yasan wani hotel da zai samu ya kwana kafin gobe baffa yace Da kwai Nisa Domin Sai ya shiga Garin Jigawa ammh in ba damuwa yazo su karisa gidansa ya kwana in gari ya waye sai ya tafi yaji Dadi sosai da karaamcin wannan Tsohon batareda ya sanshi ba.

Wani Daki Baffa ya Sauke Alhaji jada bayan yayi mai Shinmfida bisa gadon Ganye,Yasa bintalo ta damai Fura mai kyau da Nono yasha yana ta godiya fatima da Amina suma suka zo suka gaisheshi ya amsa yana tambayasu sunayensu suka gayamai Lokaci daya yake tambayansu matakin karatunsu Fatima ce Babba ita tabashi amsa basa karatun Boko sai dai na Arabiya ta Sauke Qur"anin wajen Baffa nake Karatun Sauran Littafai cike da mamaki Ahaji jada ke kallon fatima yana mamakin kananun Shekarunta Domin a kiyasi bazata wuce 14 ba Amina ya tambaya Kanta na kasa take fadamai bata Sauke ba ammh izifinta talatin Abun yamai dadi Sosai Yakuma yakara yabawa da tsarin Tarbiyan baffa,Tare suka kwana a cikin Dakin Sun Raba Dare suna Hira Lokaci Daya Alhaji jada yaji Baffa yagama Kwantamai arai nan ya kwashe Tarihinsa duka ya bashi Shima Baffa ya bashi nashi ya jinjina ma basirarsa da iliminsa gashi dai Bafulatani ne,Ammh yasan Addininsa sosai kuma masanin mganin gargajiya Duk Rugar shine likitansu yagama aunawa inda Baffa Abdulmutaddif yayi karatun Boko da ba karamin Mai ilimi za"ayi ba shine ma Dalilin Daya sanya ake Kiranshi Baffa hardo Yana da arzikin garken Dabbobi kama Daga awakai da shanaye wadanda Baisan iyakarsu ba.

Washegari Tun Safe bayan Baffa ya matsama Alhaji jada ya tsaya ya karya sai ya Shiga garkensa ya tsatsan mai Nono da manshanu Shiya rakashi har Bakin titi ya samu Mota ya shiga Zuwa kano,bayan ya bar motarsa anan da cewar in ya isa kano sai turo bakaninkensa yazo ya Dauka,Dama tun adaren Jiya wayarsa ta mutu ba chaji Suka rabu da Baffa kamar karsu Rabu koda ya isa gida hankalin Asiya yagama tashi tasha kuka ta kuma kira Sa"ed dake Makaranta ta tayarmai da hankali Saboda tayi ta kiran wayarsa bata samu ba,nan yake bata labarin duk Abunda ya faru tana ta yaba girkin su baffa hardo da matarsa harda dawainiya yammah nayi sai ga sa"ed ya diro gidan Ganin Abbansa yasa hankalinsa ya kwanta.

Bakaninkensa ya Tura yamai kwatancen Wajen da motar ta tsaya da kuma kwatacen Rugarsu Baffa yaje har chan ya sanar dashi Alhaji Jada ya aikosa baffa ya rakashi har wajen Mota ya dubata ya gyarata sai gata tatashi,Shima basu barshi ba sai da suka bashi Sakon Nono dayawa Sukace yakaima Ahaji jada haka yakawo musu da abun arziki niiki Niki Tunda ga lokacin zumunci mai karfi ya Kulla tsakaninsa da baffa hardo har Asiya sai da ya dauketa sukaje taga iyalan Baffa hardo,basu rufe Shekara tare ba Alhaji Jada ya nuna Sha"awar kiwo nan da nan kuwa Baffa ya waremai Shanaye Guda biyu Duka mata sai Awakai kyauta Alhaji jada kasa mgana ma yayi Saboda farin ciki kafin wata Hudu duka sun Haihuwa zuwa arufe Shekara kuma Sun Fara tara garke.

Tun lokacin da Alhaji jada yaga fatima ya ji ta kwantamai acikin Ranshi Saboda natsuwarta Sai yayima sa"ed Sha"awarta har ya furtama Asiya itama kuma tayi Na"am da mganar,Basu sanar da Sa"ed ba sai Alhaji jada ya samu Baffa Hardo suka tattauna baiyi Gaddama ba yace yabama sa"ed din Auren Fatima domin Dama Bazata wuce 15 ba zai aurar da ita,Duk ko Sau Daya Alhaji Jada yataba zuwa da Sa"ed din Rugar Saboda Makaranta.

Abun yama Allaji jada dadi Sosai Lokacin kuma dama sa"ed na gabda kamallah Bautar kasarshi ne,Lokacin da ya tareshi da mganar Abunyazomai abazata ammh sakamakon shi yaro ne mai Biyayyah sai bai yima iyayensa gardama ba ya amince yaje yakara ganin Fatima Duk da baya kinta Saboda Fatima yarinya ce mai kyau ga kunya ammh aganinsa bata dace da rayuwarsa ba Sakamakon shi Mutum ne mai son Rayuwar Wayewa da ilimi agidan Auransa gashi kuma Fatima ko Aji bata taba zuwa ba,Sai ya bar ransa ko bayan sun yi aure da fatima ya zama dole shima ya auro Ra"ayinsa itama fatima anata bangaren Sa"ed yamata saboda Saukin halinsa Kana kuma darajan iyayensa da Kuma Martaba mganar baffa hardo yasa ta amince..

Ba"a dauki lokaci ba aka Daura musu aure fatima ta tare agidan iyayen Mijinta Dake kano,Tabar Innarta Bintalo da kanwarta Amina Duk da fatima yarinyace lokacin Tana da shekaru 15 aduniya ammh tana da hankali ga kunyar fulani da kawaici,Sai dai Duhun kai da rashin Wayewa na wanda yatashi acikin Rugga da kuma rashin Makarantar Boko,Ammh Karatun Addini ya taimaketa kusan Itace zata gado Baffa hardo ariko da Ilimin Addini.

Zamansu kadahan Kadahan Ita da sa"ed baya Muzguna mata yana kula da ita Daidai gwargwardo,Uwa uba kuma yadda su Asiya wacce suke kira goggo da Alhaji jada ke ji da ita itacema ke jin kunyarsu,Kafin ta rufe wata biyu ta chanza tayi kiba kamar ba ita ba, watansu uku da aure Alhaji jada ya samama Sa"ed aiki a hukumar costome Tashi daya akayi posting Dinshi Zuwa parthcourt,ya tattara ya ya bar fatima agida wajen iyayensa.

Yana tafiya tafara ciwo Sai Amai da Zazzabi Tunkafin Su tafi Asibiti Goggo Asiya ta gano Laluran Fatima tayi ta murna Tare suka tafi Asibitin murtala aka Dubata aka tabbattar da Shigar ciki wata biyu acikin Fatima,Duk da har Lokacin Goggo Asiya bata ijiye aiki ba tana cigaba da aikin Asibitinta,Alhaji jada yafi kowa murna Shi ya kira Sa"ed ya sanar Dashi wanda ya jinjina ma Ikon Allah Domin kwata kwata baifi Sau uku Ya kebence da fatima ba Shima Saboda kar Allah ya kamashi da laifin Hakkinta Dake kansa ne,gani yake tayi karama kamar bazata iya Daukansa ba sai gashi Har da shigar ciki lalle ba"a ma Allah Shisshigi.

Labari har chan Rugar Hardo suma sunyi Murna ammh basu zo ba kuma basu kira waya ba saboda kunya Sai da Amina da Alhaji jada ya aika Direba ya daukota saboda Fatimar taji Dadi,Kulawa ta musamman suke bata daga bangaren Sa"ed kuwa taga gata Kullum cikin kiranta yake awayar Goggo,yana zuwa hutu gida ya taho mata waya ya koyamata yadda zatayi amfani da ita kafin ya koma Saboda tsausayin ta dayake ji har sai da yama goggo Asiya maganar Yana ganin kamar zalunci ne in har aka bari fatima ta haihu da kanta dakuwa tamai ta ce sai yahanata ta haihu da kanta din.

Cikin Fatima na da wata takwas yayi girma kamar cikin yan Biyu Goggo Asiya kemata awo agida,Ta kara zama wata iri Saboda ciki ga Sa"ed baya zama in yazo kwana daya 2 ya koma Amina ce da goggo Asiya ke kula da ita cikin wannan Halin Sakon Rasuwar baffa hardo ta iskesu Macijiya mesa ce ta sareshi Adaji Cikin lokaci kankani yace gagarinku nan,sai dai gawarsa aka kawoma bintalo,Alhaji jada yaji Mutuwar nan sosai Fatima kuwa Harda kwanciya asibiti Sunsha kuka sosai Chan ta koma Sai da akayi sati biyu kana Sa"ed ya Daukota suka koma gida.

Alhaji jada shiya cigaba da kula da bintalo da Amina,har zuwa lokacin Da Edd Din Fatima ya cika har ya wuce da Sati uku ammh Haihuwa Shuru Ashe tun Sati Biyu dasuka wuce Takejin ciwon mara da ciwon baya ammh kunya ta hanata ta Fada tafi Tafi hartafara ganin Zubar wani Farin Abu mai yauki ammh kuma ta kassa magana saboda kunya sai da Ranar Goggo Asiya ta lura da In tatashi awaje sai ya jike shine ta bita ta dubata sai da ra Razana ganin Halin Data ke ciki Ko Waya batama Alhaji jada ba ta dauketa suka tafi asibitin Suna zuwa kafin akarbesu sunsha Fada sosai ana fadin kamar goggo Asiya Batasan Aikinta ba zata Zauna yarinya na nakuda Fiye da sati Biyu ba wanda ya sani kuka kawai take tana Tsausayin Fatima,Shuru Shuru haihu bata zo ba,sau uku ana sakamata ruwan naguda nan ma shuru fatima tagama galabaita alokacin,Alhaji jada ne ya kira sa"ed ya fadamai,halin da fatima take ciki, wanda Goggo Ta Kirashi ta gayamai,ya shiga rudani sosai haka kuma ya saka direba yaje ya taho dasu Bintalo koda suka zo fatima tagama galabaita Nan da nan Alhaji jada ya saka hannu aka shiga da ita Tiyata anyi Nasaran yimata aiki an cire kyakyawan D'anta jajir Dashi,wanda kusan Rabin fatima ya debo,,sai ya surka dana sa"ed,wanda ya iso Asibitin ba dadewa aka fito da jaririn Suna murna ganinsa sai kuma labari mara dadi Washegari da likitoci suka sanar dasu sakamakon dogon nagudan da fatima tayi yasa ta kamu da yoyon fitsari Saboda tsausayinta sai da sa"ed ya zubar mata da kwallah nan asibitin mallam Aminu kano suka riketa ta cigaba da zama ana kula da ita gefe daya kuma tana shayar da danta wanda ALHAJI Jada yama baffanta Takwara wato ABDULMUTADDIF SA"ED MAI NASARA

Fatima tana bala"in son Mutaddif gashi kuma tasha wuya,lokacin Haihuwarsa,Shiyasa har gobe yake da babban matsayi cikin zuciyarta Sai da ta shafe wata Shida tana jnya asibitin Mallam Aminu kano kafin ta warke Aka sallamota bayan an kafamata Dokokin banda aiki ko motsi mai karfi har na tsawon Wata hudu,Dama goggo Asiya ne ke zaune da ita Dawowarta gida Ba dadewa akayi Auren Amina da yaron maigarin Ringim wanda tunkafin Rasuwar baffa hardo yabada ita Fatima bata samu zuwa bikin ba Saboda yanayinta Sai dai ta aika da gudummuwarta wacce Sa"ed ya bata Alhaji Jada kuma yayi komai da uba keyi.

Bayan wata hudu suka koma asibiti akace ba mtsala zata iya Cigaba da aikinta Lokacin ne kuma sa"ed yamata mgana Shiga makaranta ammh Fatima taki tace Bazata shiga wata makaranta ba,gwara ta zauna ta kula da d'anta goggo Asiya ta mara mata baya ba yadda ya iya hakanan ya Kyaleta taciga da bama Mutaddif kulawa wanda takeji dashi kamar tsoka Daya amiya sai da ya shekara kana yatafi dasu porthcourt suka cigaba da zaman bayan taje har ringim Taga yar"uwanta wacce ta bari da tsohon Ciki.

Bata samu zuwa haihuwar Amina na fari ba, sai ana Biyu lokaci Tuni mutaddif yayi wayau ba inda baya zuwa har an sakashi a makaranta fatima tana gani Duk Duniya bata da sanyin idanuwa irin Mutaddif wanda take ma alkunya da BAFFIJO saboda Sunan Baffa ne,Bangaren Sa"ed kuma yaji ya kamu da son fatima shiyasa ya dake tayi ilimi ammh taki tace na arabi ya isheta,tsakani ga Allah bata da wani wayewa don ma wai goggo Asiya na nuna mata wasu abubuwa,Abdulmutaddif nada shekara 12 aduniya yana aji Shida a primary school Allah yayima Alhaji jada rasuwa sakamakon hatsarin Mota daga dawakin Tofa zuwa kano Mutuwar Data girgiza Zukata dadama kama daga ilayansa zuwa mutanen dawakin Tofa..

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.