Free chapter · Read without an account
Chapter 11
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
Narrnarhh Bukar
(Lady with the Amazing pen ✍️)
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
011
Wurin zaman marasa lafiya suka zauna suna fuskantar likitan. 'yan rubuce-rubuce ya yi ya ɗago yana dubansu ya ce
"Ina tayaka murna oga. Matarka na da juna biyu''
A razane suka dubi likitan. Sahura ta kasa haƙuri ta ce
''Likita watan ɗana takwas fa''
''Uhm! Sai me idan ɗanki watan shi takwas. It's happens ai. Ba ya fara tafiya ba kuma yana cin abinci?" Ya tambaya.
''Eh duka yana yi likita''
''Good! a shawarce ki yaye shi. Hormones ɗinki sun sauya daga mai shayarwa zuwa mai ciki,nonon da wuya ya yi masa amfani kamar da''
''To likita'' ta furta a sanyaye. Farinciki za ta yi ko baƙin ciki, wata zuciyar ta ce abin farinciki ne a gareki tun da za ki taddo Mairi a yara,ƙila ma ki wuceta idan Dauda Imamu ya mutu ki kwashi gado mai tsoka. Murmushi ta sakar wa kanta
''Mun gode likita. Za mu iya tafiya?'' Dauda Imamu ya tambaya fuskarsa babu yabo babu fallasa. Miƙa masa takarda likitan ya yi da faɗin
''Ka tafi ɗakin magunguna ka sayi waɗannan,za a faɗa maka yadda matarka da ɗanka za su sha. Allah ya inganta''
''Ameen '' ya furta yana mikewa da Hamid a kafaɗarsa,Sahura ta miƙe ita ma suka bar ofis ɗin. Ta lura da yanayin Dauda Imamu, kwata-kwata bata ga ya nuna farincikin a kan samuwar cikin ba,sai ka ce shi zai sha wahalar cikin da haihuwar ɗan. Taɓe baki ta yi suka ci gaba da tafiya har ɗakin magungunan,ya miƙa musu takarda suka fito da maganin,ya biya sai suka koma gida. Kai tsaye Dauda Imamu ya wuce da Hamid uwar ɗaka ya kwantar da shi ya dawo falon ya zauna. Kusa da shi Sahura ta dawo ta zauna tana dubansa, ta yi kundumbalar cewa
''Yaya Imamu na ga kamar baka yi farinciki da samuwar cikin ba''
A karon farko Dauda Imamu ya murmusa,ya juyo yana kallonta da murmushi kwance a fuskarsa
''Ta ya Ubangiji zai ba ni kyauta na ƙi gode masa,ai butulci kenan. A cikin Alqur'ani mai tsarki Ubangiji ya ambata Idan ku ka gode mini zan ƙara muku,idan kuma ku ka kafirce mini,to lallai ku sani azabata tana da raɗaɗi kin ga kuwa ta ya Allah ya ba ni kyauta na ki gode masa. Na yi farinciki sosai a raina''
Sanyi ta ji a ranta,ƙara samun wuri sai ta kuma cewa
''To na ga a ofishin likita fuskarka a ɗaure''
Wannan karon ma murmushin ya sake yi
''Abin da ya sa kika ga kamar ban nuna farinciki a ofishin likita ba, kwata-kwata hankalina na Zamfara, wata uku kenan ban san halin da suke ciki ba. Suna lafiya ne,ko kuma akasin haka. Burina bai wuce na ganni a Gusau. Ina ganin bayan azahar zan wuce tun da na ga kun samu sauƙi,bari ma na ɗauko kayana a ɗaki'' ya yi maganar yana miƙewa.
Tun lokacin da Dauda Imamu ya ambaci kalmar Zamfara fuskar Sahura ta sauya,farincikin da take ciki ya dusashe zuwa tsantsar tsagwaran zallar baƙin ciki, wato dai mai hali baya taɓa fasa halinsa. A gabanta ko kunya bai ji ba yake ambatar ya yi kewar kishiyarta. Tsabar ya raina wayonta saboda kishiyarta ne ya sa bai yi farinciki da cikin jikinta ba. Tauna leɓanta na ƙasa ta yi da ƙarfi idanunta na kallon hanyar ɗakin. Zuciyarta turiri take tamkar garwashin da ke cikin murhun gashin masara. A zuciye ta juyar da fuskarta tana sake tamke fuska. Dauda Imamu ko oho,bai ma san tana yi ba,don shi mutum ne mai faɗin anihin abin da ke cikin ransa,ko ya mutum daɗi ko kar ya yi masa daɗi bai damu ba,bai kawo a rai za ta ji haushi balle ya tauna maganarsa kafin ya furta ba. Bai jima a ɗakin ba ya fito da 'yar Ghana-must-go ɗinsa ƙarama ya ajiye a tsakiyar ɗakin. Hannu ya sa cikin aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mata tare da faɗin
''Ga shi idan kina da buƙatar sayen wani abu, kar ki yi wasa da shan maganinki da na Hamid. Idan kuɗi ya ƙare kuma kina da buƙatar wani abu ki tuntuɓi malam Tsalha cikin islamiyya zai baki kuɗin da kike buƙata in shaa Allah. Daga nan zan wuce Islamiyya bayan sallar Azahar sai na tafi, bazan dawo ta gida ba. Allah ya ƙara sauƙi ya sa kaffara ne''
Bayan ta amsa kudin cike da girmamawa, a sanyaye ta ce
''Na gode. Allah ya tsara hanya,a gaida mini da su Yasir da mamansu''
''Za su in shaa Allah '' ya furta fuskarsa ɗauke da murmushi. Ya ɗauki jakar shi ya bar flat ɗin.
''Mtssssss! Aikin bazan! Wallahi yadda ka ƙuntata zuciyata a yau sai na yi maka mafiyinshi. Ni Sahurar gwaggwan bugaje za ka kalla ka ce kana kewar kishiyata! Ni Sahura! Hmmmm! Zan shayar da kai giyar mamaki mara garwaye! Ba dai gwaggota ta ce nan da shekara huɗu ba! Mu zuba mu gani! Shege kan fasa ɗan halak sai yanka! Da kai da matarka da yaranka duka za ku dawo a ƙarkashin ikona! Sai na gasa muku tsakuwa a hannu! Sannan sai na tabbatar muku da yawon dare ba na akuya ba ne. Mtsssssss! ''
Zumbur ta mike zuwa uwar ɗaka ta kwanta kusa da Hamid. Yunwa ke ƙwaƙularta amma zuciyarta da gangar jikinta sun hanata tashi zuwa kicin da zuba abincin. Lokaci guda wahalallan bacci ya yi wuff da ita.
A ɓangaren Dauda Imamu kai tsaya ya wuce islamiyya. Babbar makaranta ce mai ɗakunan karatu guda shida da ɗakin malamai da ofishin shugaban makaranta. Malam Tsalha ne mataimakinsa. Kiran malam Tsalha ya sa a yi,bayan wani lokaci malam Tsalha ya shigo ofis ɗin da sallama a laɓɓansa. Musabaha suka yi sai ya zauna a saman kujerar da ke fuskantar ta Dauda Imamu,ya ɗora hannunsa na dama a saman taburin da ke tsakaninsu.
''Bayan Azahar zan wuce Zamfara wurin ɗayar iyalin tawa,kasan yau wata uku kenan rabona da Zamfara. Zan bar makarantar da masallacin a hannunka. Wata ɗaya nake son yi na dawo. In shaa Allah''
''Allah ya tsare hanya. Ya dawo da kai lafiya''
''Ameen Ameen. Yawwa na bar maman Hamid bata jin daɗi,duk da na bar mata kuɗi wadatattun,amma na ce mata idan tana da buƙatar wani abu ta zo ta sameka. Cikin kuɗin da ake ba mu,ka dauki kaɗan daga cikin nawa ka bata''
''To shikenan, In shaa Allah ''
Sun shiga tattaunawa wasu abubuwa game da islamiyya. Kasancewar sabuwar islamiyya ce da sojoji suka gina,yawanci fararen hula ne malam sai matan sojoji suke koyarwa. Dauda Imamu ne shugaban makarantar kuma limamin juma'a na katafaren masallacin da aka gina. Suna koyar da yaran sojoji da matansu. Uniform din makarantar kalar sararin samaniya da navy blue ne,Duk jumma'a bayan isha'i Dauda Imamu na wa'azi a masallacin,yayin da sojojin ke tsayawa bayan sallar Isha'i su saurara wa'azin. Dauda Imamu ya shigo da ƙafar dama barikin,domin tun zuwansa yake samun alkhairai a wurin manyan sojoji da ƙananu. Sun jima suna tattaunawa daga bisani suka wuce masallaci, lokacin an tashi 'yan islamiyya da yake asabar ne babu boko. Shi ya jagoranci sallar Azahar . Bayan sun idar ya saɓi jakarsa...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^^
Tudun Wada premier road Gusau, jihar Zamfara. Nijeriya
Ƙarfe 8:30pm na dare
A daidai wannan lokacin mai mashin ya sauke Dauda Imamu,bayan ya ba shi kuɗi yana ƙoƙarin shiga gida kunnuwansa suka farauto masa hayaniya,juyawan da zai idanunsa suka yi arba da abin da ya saka shi mamaki. Mata da mazan unguwa ne ciki da wajen gidan 'yar ƙuda. A ransa ya furta 'lafiya! Wannan hayaniya haka kamar ana faɗa' tsaki ya ja zai shiga gida ya ji muryar mace
''Idan ka isa Allah ya tsinan! Macuci azzalumi mara adalci!" 'Yar ƙuda ta faɗa tana biyo mijinta waje,magulmatan layi na biye suna bayar da haƙuri. Mijin bai tanka mata ba,bai kuma fasa tafiya ba. 'yar ƙuda wadda daga ita sai ɗaurin ƙirji a hasale ta jawosa. Yana juyowa ya ɗauketa da lafiyayyen mari. A tsawace ya fara magana
''Ke wace irin dabba ce mara hankali da lissafi! Na ƙyaleki na fito ban kuma tanka miki ba amma sai kin ƙule ni! Na ce a gidan Aina'u zan kwana ki yi duk abin da za ki yi!"
Tun da ya sauke mata yatsu biyar ta ɗauke wuta ɗif! Babu ƙarya marin ya shigeta. Tsabar yadda idanunta suka a rufe,jaraba da cinta,ta yi kukan kura ta damƙi hantsar wandansa daidai al'aurarsa. Lokaci guda wurin ya kaure da salati. Wani razanannan ƙara ya saki yana kai mata duka,amma ko gezau,kamar yana bugun dutse. Idanunta sun ƙafe tamkar ƙafaffiyar rijiya,bata da buri wanda ya wuce ta lahanta gabansa kowa ya huta. Cike da zafin nama Dauda Imamu da wasu mazan suka dirar mata. Da ƙyar suka cire hannunta a gabansa,zuwa lokacin ya galabaita matuƙa gaya. Fizge-fizge take tana faɗin
''Wallahi ku sakeni! Sai na illata shegiyar abar kowa ya rasa! Ku sakeni! Na ce ku sake ni!"
Ihu take tana jijjiga har ɗaurin zaninta ya fara kwancewa,ga yaranta a gefe suna rusa gurshiƙeƙen kuka. Tsoro da firgici sun gama sabauta su. A hasale Dauda Imamu ya dubeta
''Me ya shiga ƙwaƙwalwarki kike shirin illata mijin kuma uban 'ya'yanki! Ba ki tunanin tsaigumin layi da rayuwar 'ya'yanki a gaba! Yanzu idan mijinki ya nakasa wa zai je ya nemo muku abinci. Fisabilillah yanzu kin yi wa kanki da yaranki adalci?''
''Uban adalcin! Shi ya yi mini adalcin ne! Shi ba ka ce me ya sa bai yi mini adalci ba sai ni! Ta ya a ranar kwanana zai zo ya ce mini a ɗakin kishiyata zai kwana! Saboda tsabar ya raina hankalina wai bata da lafiya,alhalin ƙarya ne ko yau mun hadu a gidan biki da ita! Ni lokacin da nake rashin lafiya ya taɓa hakura da kwana gidanta ya zo gidana! Ƙannenta 'yan mata uku ne! Me ya sa ba zai aika a kirasu su kwana da ita ba! Gwara na illata mazantakar tasa kowa ya rasa!"
''Malam Ƙarya take! Ki je na sakeki saki biyu! Kuma a yau za ki bar mini gida ba sai gobe ba! Matsiyaciya mai ƙashin ala-tsini,tun da na aureki babu abin da na ajiye sai tarin takaici da talauci!''
Hakurin Dauda Imamu da mazan wurin suka shiga ba shi. 'yar kuɗa ko a jikinta,sai maimaita ba za ta bar gidan ba,ai gidan yaranta ne.(Na so ƙawarta Sahura na garin aka yi wannan bidirin. Na san haka kuma kuke tunani my Esteem fans. Da an yi shagali💃💃💃😂)
Jan hannunsa Dauda Imamu ya yi zuwa gidansa. Da sallama ya shigo gidan. Mairi da ke falo tare da su Yasir suna karatu suka amsa. Da gudu Jalil da Yasir suka fito jin muryar mahaifinsu,biyo bayansu ta yi fuskarta ɗauke da murmushi. Kafin ta gama fitowa ya karaso inda take
''Fito mana da tabarma''
''To'' ta ce sannan ta juya ta dauko tabarmar ba tare da ta fito ba ya amshi tabarmar ya shimfiɗa. Suka zauna. Jalil na saman cinyarsa ya fara magana cike da natsuwa.
''Saleh wani tsautsayi ya kai ka biye mata alhalin kai namiji ne. Ka san mata Ubangiji ya haliccesu a boƙare,duk yadda ka so miƙar da su sai dai su ɓalle.''
Ɗan gyara zama Saleh ya yi a hankali,don har yanzu zafi yake ji a gabansa. Sauke ajiyar zuciya ya yi sannan ce
''Malam duk abin da zan faɗa maka a kan Talatu ba za ka yarda ba, mai ɗaki shi ya san inda yake yi masa yoyo. Amma tun da an yi sara a kan gaɓa.
Yau zan amayar da ƙunshin baƙin cikin da ke cikin zuciyata.''
Ɗan numfasawa ya yi Dauda bai katse ba,ya ci gaba da cewa
''Malam! Talatu ce matata ta farko. Ban san mene ne daɗin aure ba sai yanzu da na auri Aina'u. Talatu ƙazama ce ta ajin farko, bata iya girki ba,bata iya magana ba,bata iya kula da yara ba,ga uwa-uba bata iya kwanciyar aure ba,haka take jinta sakaka tamkar tunkiya. A duk san da nake ɗakinta babu abin da nake ƙunsa sai kayan takaici da baƙin ciki. Ko ya ka ce ta gyara za ta nemi yi maka tujara. Ga tsananin kishi, har gida take samun amaryata ta yi mata zagin babban bargo. Kwanakin baya har ɗoyi gabanta ya...''
''Subhanallahi! Saleh ba a kai nan ba...''
A hasale Saleh ya katse shi da cewa
''Har an wuce wurin! Wallahi ba zan tsaya sai na kai bus stop. Ina so ka fahimci wace ce Talatu. Ina faɗa maka har ɗoyi gabanta ya fara kwanakin baya. Cikin lunama na faɗa mata ya kamata ta nemi magani kar ya zamar mata illata,don ta ɗauki maganar da muhimmanci na ce ba zan ƙara mu'amalar aure da ita ba sai ta nemi magani,amma sai ta sauya maganar ta yi ta surfa mini baƙaƙen maganganu. Bini-bini ta ce ai ba haka nake ma amaryata ba. To don girman Allah mai kyautata mini ta ya ba zan kyautata mata ba. Duk abubuwan da na lissafo maka babu ɗayanta Aina'u take yi. Ga iya girki,ga iya magana mai daɗi da taushi,ga tsafta,ga kwarkwasa da iya karairaya,ga uwa-uba sanin salon kwanciyar aure. Yanzu Malam in tambayeka idan kai ne za ka so kwana a gidan da ka san babu abin da za ka kurɓa sai maɗaci,alhalin ga inda za ka kurɓi zuma. Ka ga laifina don na yi ƙaryar ciwo zan kwana gidan Aina'u?"
Jinjina kai Dauda Imamu ya yi da fadin
''Ƙwarai kuwa! A gaskiya kai ne da rashin gaskiya a nan,duk munanan abubuwan da ka lissafo tana yi hakan bai baka tikitin zuwa gidan abokiyar zamanta alhalin ba ranar kwananta ba ne. Ka ji tsoron Allah Saleh ka sani manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce a ranar tashin alƙiyama,akwai magidancin da zai ta shi ɓarayinsa ɗaya a shanye. Kuma kasan dalilin da ya sa barayinsa ɗaya yake a shanye?" Ya tambaya yana dubansa a hasken lantarkin tsabar gidan. Girgiza kai ya yi sai Dauda Imamu ya ci gaba da cewa
''Wanda baya adalci a tsakanin matansa,ma'ana ya fifita ɗaya a kan ɗaya,yana kyautata wa ɗaya amma ɗayar ba ya kyautata mata. Irinsu Ubangiji ya tanadar musu azaba mai radaɗi. Shi ya sa Ubangiji ya faɗa cikin al'qur'ani mai tsarki Idan kun san ba za ku yi adalci ba,to ku auri ɗaya Tun da ka san ba za iya adalci a tsakaninsu ba,da tun farko mace ɗaya ka aura. A gaskiya Saleh ba zan ɓoye maka ba, ka nuna rashin adalci ƙarara a nan,duk da bata kyautata maka amma ai tana da hakki rataye a kanka. Yanzu dai ka yi haƙuri ka mayar da ita. Shi aure ɗan hakuri ne. Zo mu zauna ne zo mu saɓa. ''
Taɓe baki Saleh ya yi tare da miƙewa,fuskarsa bata nuna nadamar hukuncin da ya yanke ba ya ce
''Sai dai kar a kuma,gwara ta je gida ta ji yadda zawarcin yake,idan ya so daga baya ta gyaru na mayar da ita. Kazantar ne babban abin da ya fi ci mini tuwo a ƙwarya. Gobe zan zo na dauki yarana. Sai da safe malam kar na shiga haƙƙin iyalinka. Na gode.''
Bai jira amsar shi ba ya fice daga gidan. Shiru Dauda Imamu ya yi yana nazari. A gaskiya idan saboda abubuwan da Saleh ya fada ne zai yi rashin adalci,to babu ranar hakan. Ba Mairin ba,ba Sahura ba,dukkaninsu suna da tsafta da iya girki. Matsalar shi biyu ce da Sahura, rashin saninta a kan addini da yawo gidan maƙota,bayan waɗannan bata da makusa. Miƙewa ya yi da yaran zuwa falo. Allah ya sa yana sauka tasha ya yi alwala tare da rama sallolin da ake bin sa sannan ya hau mashin. Yunwa ce kaɗai yanzu take fatattakar 'yan hanjinsa. Ya iske Mairi na karanta Al'qur'ani mai tsarki. Murmushi ya yi sannan ya samu wuri ya zauna.
''Washhh Allahna! Babu abinci gidan ne! Ji nake kamar na ci...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️
***