Free chapter · Read without an account
Chapter 24
Yau tunda aka tashi ake ta hada hada a gidan, ko ina banda shaiki ba abinda yake yi, masu decor sun yi tun da wuri, ga manyan banner guda biyu da aka ajiye a gefen, da akayi decor me ɗauke da picturen Leena da rubutu ajikin "Double Celebration for Leena! Congratulations on Your Secondary School Graduation & Qur'anic Completion" yanda gidan yake kelli da yadda akayi mata decor sai ka rantse auren ta akeyi. Niswa da ta fito zata kaiwa Hajiya breakfast kallo ɗaya tayi wa compound ɗin ta ɗauke kai, tana sallama Hajiya ta fito tayi shiga na Alfarma na gani na faɗa tana amsa sallaman, Niswa ta gaishe ta Hajiya ta amsa tana cewa "Ni da tun ɗazu nake jiran ku, na ɗauka ai ba yanzu zaku gama ba, shine naje sashin su Leena dan na karya" Niswa bata ce mata komai ba ta je ta ajiye mata akan dinning ta nufi kofa da niyyar fita Hajiya tace "toh ya nagan ki haka? Ku ba zaku bane ?" "Eh" kawai tace wa Hajiya ta fita Hajiya tace ji mugun hali duk uwar ta su ta cusa musu. Jidda da ta gagara ɗauke ido akan Leena sabar wani kyaun ta da ya fito tsantsa cikin Alkebban dake jikin ta, Jiddah tace "SubhanAllah! Wallahi gwara ma da kika ce baki son wani makeup hakan ma kin fi kyau" Murmushi Leena kawai tayi. Ammi na kallon Jidda tace "zaku tafi yanzu ko? Idan yaso ma biyo ku abaya zuwa ɗan anjima" Jidda tace"Toh barin ma driver magana ya karasa ya ɗauke ta anan" sai ga Hajiya ta shigo da sallama duk suka amsa Jidda ta gashe da Hajiya sannan ta wuce dan kiran driver. Bayan driver ya karasa har kusa da kofar su Leena zai ɗauke ta, horn yayi, hakan yasa Jidda na kallon Leena tace "muje, ya karaso" Leena sai duk take jin wani iri haka nan, sun fita Jiddah zata buɗe mata kofar baya ta shiga suka ji Murya Mummy na ihu "Kai, Kai, kai tsaya nan" ta karasa da ɗan saurin ta kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai tana kallon kallon mai tukin motar tace "ina da aika da zaka je min a can kubau yanzu" Jidda suka haɗa ido da Leena suna ganin ikon Allah jin inda Mummy ta aike sa, Driver ya tsunkuyar da kansa kasa yace "Toh, Hajiya" Jidda na kallon Mummy tace "Mama bari ya ajiye mu kafin ya tafi, tunda mu ba wani wajan ba ne" Mummy ta hayyako mata kamar zata dake ta tace "Sannu Me gidan, nace sannu ko? Ashe motar gidan ku ne ko kuma ke kika ajiye drivern da zan basa umarni kice sai dai yayi naki farko" Driver ya koma mota ya tada sannan ya koma can part ɗin Mummy yana gudun yanzu sai ta iya sa a kore sa, Jidda tana kallon Mummy da mugun mamaki, ita tun lokacin da Leena ta ɓata Sultan ya basu labarin Mummyn taji ta tsane ta, Mummy tace "Saina tsole Miki wannan idon naki da kika zuba min" Jidda ta kama hannun Leena suka shiga ciki, Hajiya ta mike tana kallon su tace "Ku kuma me ya haɗa ku da wancan matar?" Jidda kana ganin ta kasan ranta ya mugun ɓaci tace "Wallahi matar nan taci sa'an yau mutane na na mutunci suna kusa ne, kuma ina ganin girman ta ne, amma da wallahi sai tayi nadama rashin kirkin da ta min, ba ranan da zan shigo gidan nan bata min kallon kaskanci ba" ta zauna rai bace Ammi na kallon Leena tace "me ya haɗa ku?" Leena tace "ta hana driver ne kaimu wai zata aike sa" Ammi tayi shiru Hajiya tace "Lallai matan nan abinda take yi yanzu kuma ya fara yawa" Hajiya zata kira Daddy Ammi ta hana ta Jiddah ta ɗauki yawa ta kira Sadeeq bayan sun gama wayan ta kashe tace "zata ga kuwa mota nagani na faɗa ba ta tsaya tana wa mutane wulakanci akan wannan karamar motar ba" Ammi tace "dan Allah Jidda kiyi hakuri" ba'a ɗau lokaci ba sai ga Sadeeq ya karasa har compound ɗin ya shigo da motar yayi parking, ido ya kurawa bannern Leena sai gashi sun fito Jidda ta buɗe mata backseat ta shiga ita kuma ta zauna a gaba Leena tace "Good morning" yace "sun Miki magana?" tace "Eh, Thank you" be sake cewa komai ba ya tada motar suka kama hanyar fita sai sannan Leena taga decon da kyau sake baki tayi ganin bannern tace "Anty Jidda yaushe kuma akayi banner?" Jidda na Murmushi tace "Ya Sadeeq ne Nima da safe yake faɗa min shine masu decor suka je suka karba" Leena tayi shiru sai ta daga kai ta mirror suka haɗa ido tace "Thank you and may almighty reward you" a takaice yace "the pleasure is mine"
Ana gudanar da bikin yaye ɗalibai abun ba'a cewa komai sai Ma shaa Allah, pictures da Leena tayi ta shiga sending ma Muhammad, Leena ita ce zakaran kwajin gani kamar yadda ta saba a baya lokacin da zata karɓa prize dinta ita da Daddy suka fita tare Leena couldn't help but cry.
Leena zata gun su Ammi ta bar friends ɗinta a wajan da aka tanadar domin su, kamar ance ta kalli mutumin dake gaban ta kallon sa tayi taga yana tsaye ya zuba mata idanu She whispered Malik Areej, ta ɗauke kai zata wuce yace "Congratulations Leena, You're a prodigious talent, and it's inspiring to see" sai sannan ta kalle sa murmushi ɗauke a fuskan sa tace "Thank you, I do appreciate" daga haka ta koma inda su Ammi suke ta kalli Zahra dake mata Murmushi ta ɗauke kanta tayi kamar bata ganta ba, Zahra tayi hugging ɗin ta tace "Haba Leena, fushi zakiyi da Ni?" Leena tace "Sai yanzu zaki zo" Zahra na Murmushi tace "kin manta ranan last paper ɗin mu banda lafiya? Toh, ai har yanzu Ban gama warware wa ba beside nine ma ya kamata nayi fushi ko sau ɗaya baki taɓa zuwa in duba Ni ba" Leena tace "Wallahi na ɗauka ai kin warware ne" Ammi dake kallon su tace "toh kenan sai kiyi fushin Zahra, tunda bata san ta kira ki ba" Leena na kallon Ammi kamar zata yi kuka tace "Haba Ammi" Zahra dariya kawai tayi. Bayan sun koma. gida mutane suka dinga shigowa duk da de unguwar su ba wai unguwan da makwabci zai shiga ma makwabci bane amma idan Ammi taji wani abu takan shiga tace bari ta sauke hakkin makwabtaka, hakan yasa duk da ba wai tayi gayya bane anajin cewa Leena ce sai zuwa ake sai ka ɗauka Ammi ba ƴar Niger bace, waje ya kawatu na ban mamaki, Jidda tasa Leena ta sake wanka ta chanza kaya, sai ka rantse bikin ta akeyi, waya kare a kunnen ta tana waya da Muhammad Ammi ta shigo da niyar sanar da ita ta fito ta gaishe da ƴan unguwan su Babaajo da Nyaama na das sai ga Zahra ta shigo da gold a hannu tace ki "ki ɗan hakura da Wayan nan idan kin gama kyau sai ki kira shi ku yi tayi, Ni dai yanzu ba zan saka Miki gold ɗin nan" Ammi na kallon ta tace "Gold kuma? Gokd ɗin waye" Jidda tace "Au, be faɗa muku ba halan? Yayan ta Rayyan ne yace na kai mata tayi amfani da shi" Ammi tayi shiru tana kallon Leena da ta sauke idon ta kasa. abinci Chefs suka shigo da su ana raba wa mutane Kujeran da Leena ke zaune gefen ta Zahra ce, bayan anyi walima suka fara hotuna Jiddah ta kama hannun Leena tana tafiya da ita tace wa Ammi "bari yanzu zata dawo" haka nan Leena taji tsinkewan zuciya ita de tana bin Jiddah taga ba zata iya ba tace "Meya faru ne Anty Jidda?" sai da suka isa bakin gate Jidda ta sake ta tana gyara mata fuskanta ta buɗe gate ɗin su tana kallon Leena da murmushi a fuskan ta tace "toh Leena ki ɗan sake fuskan mana? Ko haka zaki fita?" Leena ta ɗan sake fuska Jiddah ta karasa fita amma hannun ta na rike dana Leena ta jawo ta waje kallon motar dake parke kofar gidan tayi and she saw him kallon sa take yi and froze, looking like a statue, she couldn't believe what she was seeing, was it really him? Yana murmushi ya karasa har inda take yasan tayi mamakin ganin sa ne yace "Yes, it's your baby, babe. I wanted to surprise you, so I decided to attend your graduation" Leena taji hawaye ya cika idon ta It wasn't until she saw him that she had realized just how much she missed him yana lekan fuskan ta yace "Baby! Kuka kuma? toh ko in koma ne?" Bata san sanda ta harare sa ba murmushi yayi yace "Congratulations on your secondary school and Qur'anic graduations, baby. You're incredibly talented more than anyone can imagine. I hope our babies will be just like you.'' ta ɗan kalli inda Jiddah take taga hankalin ta na kan waya sai sannan ta kalle shi tace "Thank you, I do appreciate, I can't hide" yace "shiitttt, don't stress yourself for me please" gani tayi yayi wa Jiddah maganan da ido sannan Jidda ta karaso inda suke tana kallon Leena tana murmushi ta zaga ta bayan ta to her surprise taga Jiddah ta rufe mata ido kuma sannan tana janta ji tayi son saya kuma ta gagara magana. Motar da ke gaban su aka yaye wa rigar motar da aka lulluɓe wani sabowar dalleliyar Bugatti Veyron ne ya bayyana gashi anyi decor ɗin jikin motar da Flowers and balloon sai sheki yake yi Muhammad ya cewa Jidda "take off your hand, Ma" Jidda ta cire tana murmushi, She stared at the car, then at her Muhammad, her expression a mix of surprise and confusion. Turning to Jidda, she seemed to ask silently, 'What's going on?" Jiddah ta mata alama da hannu i don't know, too. ta kuma juyawa side ɗin Muhammad keyn motar yake mika mata girgiza kai ta fara masa bata son tayi believing abinda ranta ke saka mata ya maso kusa da kunnan ta yace "Be Miki bane baby? toh ko a chanza Miki ne?" tace "Toh me zan yi da shi? Ka bari, wallahi Nagode, amma Ni yanzu me zan yi da mota?" jin shirun sa yasa ta ɗaga kai tana kallon sa gani tayi kamar ranshi ya ɓaci da hakan da tayi bata san sanya ta fashe da kuka ta karasa jikin motar tana kallo ba, Jidda a ranta take mamakin iko na Ubangiji, kamar ba ɗazu bane Mummy ta wulakan ta su akan mota.
Gaba ɗaya gidan da wanda suka zo suka ji labarin kyautar da Muhammad ya mata kowa yana jinjina kokarin sa lokacin har an shigar da motar cikin gida, Mummy ji tayi kamar ta ɗaura hannu aka ta dinga zunduma ihu haka take ji, hatta su Nisreen sai da ta basu tsoro gashi ko kallon ta sukayi sai ta fara sauke musu masifan dake cinta. Bayan Magrib, Rayyan suka shigo gidan tare ya masa sallama ya koma sashin su, gaba ɗaya ji yayi zuciyarsa ya masa nauyi Allah yana sani saboda Daddy yace su tafi sallah tare ne har ya iya haɗa hanya da Muhammad. A car park inda aka masa shinfiɗi ya zauna, yana jiran Leena ta fito dama suna zaune aka kira sallah Daddy yace ya bi Rayyan, bata ɗauki lokaci ba sai ga Leena ta fito tun daga nesa yake kallon ta, kanta a kasa ta karasa inda yake tace "bari na ɗan karbo sako a waje" yana kallon ta yace "Go ahead baby" ta tashi ta fita waje Sultan ta gani tsaye kallon cikin motar tayi taga Sadeeq, tace "Uncle Sultan shine baka zo ba ko?" yace "Haba little girl, ba gashi yanzu na zo ba?" ta koma side ɗin Sadeeq da ko sau ɗaya be kalle su ba tace "Uncle ina wuni" sai sannan ya kalle ta, ya gagara bata amsa sai gƴaɗa masa kai da tayi zata tafi ta jiyo Muryan sa "Har ya tafi kenan?" ta sauke kanta tace "Aa" ta koma gefen Sadeeq ciro abu yayi a bayar Motan ya mika mata taki karɓa tace "Menene kuma?" Yace"karɓa mana" tace "bayan duk abinda Mami da Amty Jiddah sukayi kuma sai ka sake bani, Allah Nagode" zai kama hannun ta ya danna mata tayi sauri ta karɓa ita gani take kamar zata takura mutane ne idan ta karɓa godiya ta musu ta wuce cikin gida.
Muhammad yace "kila idan na koma ba zaki sake gani na ba sai gobe bikin mu" Leena de taki ce masa komai ita mamakin yadda Muhammad yake son ta kawai take yi satan kallon sa tayi taga ashe ita yake kallo ta rufe fuskanta da hannayen ta tace "toh ka daina kallo na mana" yace "Ai wani abun ma baby sai an kawo min ke gida na, daga safe har dare kallon ki zan na yi"
Wajan pass 9pm Leena na kallon Ammi tace "Toh Ammi ke sai kina hawan motar mana, Ni me zanyi da shi, ji yadda kullum Mummy sai ta mana gori akan mota, ɗazu ta gama mana wulakanci akan mota sai kuma yanzu taga ikon Allah ai" Ammi tayi dariya tace "a wani garin kika taɓa ganin anyi haka? Ai mota taki ne Leena, so kike a kaiki Abuja babu motar ya ce an sayar?"
Bayan wasu kwana ki, bikin Leena sauran sati ɗaya kenan, amma har sannan Leena na zuwa makarantar koyan abinci, wanda kusan kullum sai ta haɗu da Malik saboda a unguwar yake da zama shi da iyayen sa kuma sukan gaisa amma kuma baya yarda ya mata ko wani yare sai larabci tunda ya fahimci tana ji, ta fito daga sashin su tana sanye da Hijab har kasa da nikab a fuskar ta zata fita taga Mummy da kawarta zasu fita Mummy tace "Eh wallahi, ai yarinyar yawo ta fara baki ganin ta ne a social media? Duk ta makalewa manyan gari shiyasa fah aka bata motar, ke kin taɓa gani an bawa budurwa mota kyauta, kema kinsa ba haka kawai za su bata ba" Fatima ta rike haɓa tace "Gashi ba karamin Mota bane wallahi! Chap lalle idon ta ya buɗe, Allah yasa ta iya zaman aure" Leena ko kallon su bata yi ba ta fita abinda and boiling inside her, taji ta sane Mummy with passion, ada takan bi umurnin Amminta ta gaishe ta amma yanzu ta daina tunda aka bata mota ta kara sanarta kuma duk wanda yazo gidan sai sun yi wannan maganar inda sabo ta saba ji amma ai kalmar da zafi sosai, anan bakin tutu ta hau taxi..
Hint the star at the corner please, ko baku son kuna motivating ɗina