Free chapter · Read without an account

Chapter 12

by Narrnarhh Bukar · BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

Narrnarhh Bukar

(Lady with the Amazing pen ✍️)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

012

Allah ya sa yana sauka tasha ya yi alwala tare da rama sallolin da ake bin sa,ya tsaya ya yi sallar Isha' sannan ya tari mashin ya nufo gida. Yunwa ce kaɗai yanzu take fatattakar 'yan hanjinsa. Ya iske Mairi na karatun Alqur'ani mai tsarki. Murmushi ya yi sannan ya samu wuri ya zauna,Yasir da Jalil na biye da shi.

''Washhh Allahna! Babu abinci gidan ne! Ji nake kamar na ci babu''

Murmushi Mairi ta yi,ta mayar da Al'qur'anin cikin jakar islamiyyarta sannan ta mike zuwa kicin, dawowa ta yi da plate da kofin ruwa. Sauran abincin da ya rage cikin kula ta zuba masa. Dambun tsaki ta yi,ya ji kayan lambu da zogale,ta zuba man gyaɗa da yaji sai ta ajiye masa plate ɗin a gabansa da kofin ruwa sannan ta koma gefe. Zuwa lokacin Yasir da Jalil sun yi bacci sai ta ɗauke su uwar ɗaka. Tas! Ya cinye abincin ya sha ruwa tare da hamdala,mai ya tuno sai ya tuntsire da dariya shi kaɗai.

''A'ahh! Baban Yasir lafiya kake dariya kai kaɗai!"

Girgiza mata kai kawai ya yi ba tare da ya bata amsa ba. Ba komai ya tuno ba sai dramar da aka yi ɗazu a waje da labarin da Saleh ya ba shi game da 'yar ƙuda(Talatu) a kan rashin iya girkinta. Gaskiya ko shi ba zai ɗauki kazanta da rashin iya girki ba. Tun wuri zai sallameta salamina-alamina,tun kan a kai lokacin da zuciya za ta rinjayeshi ya kasa adalci a tsakaninsu.

''Ɗaura mini ruwa wanka zafi nake ji,yau komin dare sai na yi '' ya yi maganar yana goge zufar da ta tsattsago a dandamalin goshinsa.

''To'' ta mike ta fita, lokacin ku san 10:02pm na dare agogon ɗakin ya nuna. Risho ta kunna tare da ɗaura ruwan,yana kashe sanyi ta kashe ta kai masa bayi. Cike da natsuwa ya yi wankan ya dawo falon. Bai isketa a nan ba. Zarcewa uwar ɗakan ya yi ya sameta har ta kwanta. Shiryawa ya yi cikin farar jallabiya ya kwanta. Daman da ƙishin ruwanta ya dawo,bai saurara mata sai da ya tabbatar da ya sauke gajiyarsa a kanta sannan komai ya lafa suka kwanta. Asubar fari suka yi wankan tsarki...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^

Airforce Base. Jikar Kaduna Nijeriya

A ɓangaren Sahura kukan Hamid ne ya tasheta daga baccin. Da ƙyar ta tashi zaune tana wawakekiyar hamma tare da miƙa. Tuno da maganar likita a kan yaye shi ya sa ta dakata daga ba shi nonon suka fito falon tana rirriga shi. Ajiye shi ta yi sannan ta nufi kicin ta ɗibo mishi abinci,ita ma ta sako ma kanta. Sai da ta fara ba shi ya ci kadan sannan ta ɗura mai maganin da aka ba shi a asibiti. Kuka sosai yake ya ƙi yin shiru. Ta yi lallashiin duniya amma ya ƙi yin shuru tamkar ana ƙara rura wutar kukan nasa ne. Goyasa ta yi ta fara kai-kawo a ɗakin. Cikinta sai sauti yake bayarwa tsabar yunwan da 'yan hanjinta suke ji. Ta rasa inda za ta saka ranta. Ga masassarar da take ji kaɗan-kaɗan. Tana rirriga shi a fili ta ce

''Anya Sahura! Anya za ki iya kuwa! Ga ciki! Ga goyo! Ga zazzaɓi! Ga baƙin cikin miji da na kishiya! Ni ɗiyar Gwaggwon Bugaje ina zan tsoma raina na ji sanyi!" Kamar ta kwarma ihu ko za ta samu sassaucin raɗaɗin da zuciyarta take yi. Da ƙyar ta samu ya yi bacci. A hankali ta kwantar da shi saman doguwar kujera sannan ta fara cin abinci. Loma uku ta yi ta ajiye abincin don ji ta yi ya sire mata. Tsaki ta ja sannan ta ɓalle maganin ta sha. Za ta kwanta ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofarta.

''Shigo!" Ta furta a zaunan,duk da bata san wace ce, bai wuce ƙawayenta.

''Assalamu Alaikum Mamam Hamid kuma matar malam daga ke babu ƙari" matar ta faɗa tana shigowa ɗakin,fuskarta shimfide da murmushi. Baƙa ce mai matsakaicin tsayi,tana da ɓulin hanci, ba za ta haura shekarun Sahura ba. Maman 'yar gayu dakakkiyar mace ce mai ɗauke da kyakkyawar sura.Martanin murmushin ta mayar mata tare da gyara zama ta ce

''Wa'alaikum salam! Maraba da zuwan Maman 'yar gayu!"

Turus! Maman 'yar gayu ta tsaya tana duban magungunqn da ke gaban Sahura. Ɗagowa ta yi ta ce

''Maman Hamid baki da lafiya ne?''

Murmushin ƙarfin hali Sahura ta yi sannan ta ce

''Dukanmu Maman 'yar gayu. Ɗazu muka dawo daga asibiti.''

''Wayyo! Tun yaushe Maman Hamid?" Ta faɗa tana zama kusa da ita fuskarta ɗauke da damuwa.

''Hmmm! Juna biyu ne da ni Maman 'yar gayu. Ɗazu likita yake sanar mana''

Waro ido Maman 'yar gayu ta yi da faɗin

''Ciki! Ikon Allah! Haka yayata take da ƙazamin goyo.Allah sarki Hamid ya sha ciki,shi ya sa ya rame ya fita hayyacinsa. Kin yaye shi ne?"

''Yau ɗin nan za mu yi yayen,don likita ya ce na yaye shi."

''Hakan shi ne daidai,ki samu alkama,waken suya,jar dawa da fara ki niƙo kina dama masa kunu. Kina zuba mishi madara a ciki. Nan da nan zai murmure. Ke kuma Allah ya sauke ki Allah''

Da ƙyar ta furta ''Ameen '' saboda aman da ya taso mata, cikin sauri ta nufi bayi tana kwarara amai babu ƙaƙƙautawa. Daga waje maman 'yar gayu take mata sannu. Bayan aman ya lafa ta wanke bakinta,sai ta tsaftace wurin ta fito.

''Allah sarki! Da malam ya sani ai da bai fita ba,tun da baku da lafiya ya kula da ku'' Maman 'yar gayu ta faɗa tana zama a ɗaya daga cikin kujerun. Murmushin da ya fi kuka ciwo Sahura ta saki tana faɗin

''Hmmmm! In ji mai ciwon haƙori. Kina maganar ya zauna damu. To ɗazu ya wuce Zamfara bayan ya san halin da muke ciki. Ya tafi wurin gantalalliyar matarsa mai zubin mayu''

''Zamfaraaaa! Yo kya ga laifinsa tun da ta mallakeshi,dole ya nuna azarɓaɓi. Ni na ga ƙoƙarinki da ba ki hanashi tafiya ba . Idan ni ce wallahi bazan bari ba. Ta ya ni da ɗanka ba mu da lafiya za ka tsallakemu ta tafi Zamfara!"

Hamma Sahura ta yi tana numshe ido ta ce

''Ki bar ni da su. Ban ga amfanin dakatar da shi ba tun da ya ɗau niyya. Wai kin san abin da ya ƙona mini rai ɗazu?"

Girgiza kai Maman 'yar gayu ta yi da faɗin ''A'a sai kin faɗa''

''Ganin a lokacin likita ya sanar da cikin jikina sai na ga kamar bai yi farin ciki ba, da muka dawo gida na tambaye ko ba ya murna da cikin ne. Buɗar bakinsa ya ce kwata-kwata hankalinsa yana Zamfara,bai san wani hali ya barsu ba,miye da miye''

''Jar uba! In ji kanawa! Lallai Malam daman haka yake. Ai a tunanina lafiya ta shafe komai. Madadin ya bari ko zuwa sati guda ne ya ga yanayin  jikinku sannan ya tafi. Hmmmm! Maza ai halinsu sai su. Allah dai ya kyauta ya baku lafiya''

''Ameen. Ɗan taimaka ki dama mini kunu a kicin ko zan iya sha''

Babu musu Maman 'yar gayu ta nufi kicin dama mata kunu. Maman 'yar gayu na daya daga kicin sabbin ƙawayen da Sahura ta yi a barikin. Halinsu ya zo ku san ɗaya,banbanci ɗaya ne.Maman 'yar gayu tana ta'amulli da wasu daga cikin mazan barikin a ɓoye,wanda babu wanda ya sani sai Allan da ya halicceta. Ba don ta rasa ci,sha da tufatarwa ba ne,kawai saboda kwaɗayi da ƙyale-ƙyalen duniya. Ɗaya daga cikin manyan sojojin da take ta'amulli da su ya saka aka tura mijinta Legas aiki, kasancewar mijinta Corporal ne,don shi da sauran manyan sojojin su ji daɗin sharholiyarsu da Ita. Suna sakar mata kuɗi amma bata nunawa saboda zargi,a wajen barikin suke haduwa bayan an aiko mata da wasika a kan inda za ta samesu. Sun mayar da ita tamkar matarsu ta sunna,idan mijin ya nemi a ba shi pass yana son zuwa wurin iyalinsa a hana shi. Sai lokacin da  Maman 'yar gayun ta buƙaci zuwanshi suke barinshi ya zo. Ba iya maman 'yar gayu take wannan ɓoyayyiyar harƙallar ba,har da wasu matan  musamman  waɗanda mazajensu ke da ƙaramin muƙami. Sun tsunduma cikin wannan harƙar,sun mayar da zina ba a bakin komai ba,da auransu suke aikatata saboda abin duniya. Wasu daga cikin manyan sojojin sun mayar da zina ga matan ƙananun sojoji ba komai ba. Wasunsu suna amfani da iko da son zuciya a kan wasu matan, musamman idan suka ƙyalla ido a kan macen suka ɗasa. Suna amfani da barazana ka matan idan suka ƙi ba su haɗin kai,amma irinsu Maman 'yar gayu da son ransu suke zinar,don su samu kuɗi su ɗaranma sauran matan barikin sa'a.

TUNATARWA

A kullum burin shaiɗan shi ne ya ga ya yi nasarar halakar da 'ya'yan Annabi Adam(A.S). Ya kaɗa gangarsa a kunnan wasu daga cikin matan aure,ya yi amfani da son duniyarsu ya jefasu a harkar zina da auransu. 'yar'uwa ki sani,zina babbar zunubi ce a cikin addinin musulunci da al’umma,tana raunata amana, keɓance iyali, kuma tana cutar da yara sannan bashi ce,komin daran daɗewa sai an biyata. Shi yasa Allah (S.W.T) ya faɗa a cikin Al'qur'ani mai girma "Kada ku kusanci zina,lallai ita mummunan aiki ce kuma hanya mara kyau'' (Suratul Isra'i 17:32). Annabin Rahma ya ce "Babu zunubin da yake jan bala'i bayan zalunci kamar zina da katse zumunci" (Ibn Majah). Ubangiji ya tsarkake zukatanmu,ya tsaremu daga faɗawa tarkon sheɗan,ya sa mufi karfin zukatanmu.*

Cikin labari

Bata ɗauki lokaci mai tsayi a kicin ɗin ta kammala dama kunun,ta zubo a kofi ta saka sugar sannan ta dawo falon. Sahura na kwance shame-shame a saman kujera. A ƙasa ta ajiya mata tare da faɗin

''Tashi ki ɗan sha Maman Hamid ko hanjinki zai warware.''

''Bari ya ɗan huce kaɗan'' Sahura ta bata amsa a hankali. Jikinta ya jiƙe sharfaf da zufa. Shiru ɗakin ya ɗauka sai can Sahura ta zauna tare da ɗaukar kunun tana kurɓa a hankali. Ta shanye kusan rabi sannan ta koma ta kwanta. Shiru ya sake ratsawa a tsakaninsu,can Maman 'yar gayu ta miƙe tana duban Sahura

''Maman Hamid zan koma block ɗinmu. Daman hira na zo mu yi. Allah ya ƙara afuwa''

''Ameen Maman 'yar gayu,jira ni zan je makaranta wurin malam Tsalha ba amsa kuɗi'' ta yi maganar ta a miƙewa da ƙyar tana yamutsa fuska.

''Ba kin ce Malam ya bar miki kuɗi ba?" Ta tambaya fuskarta shimmfiɗe da tsantsar mamaki. 'yar dariyar ƙarfin hali Sahura ta yi tana gyara rigarta

''Raba arne da mamaki wajibi ne,ai idan ya san wata bai san wata ba. Duk sati zan dinga zuwa ina amsar kuɗina,ba dai shi da kanshi ya ba ni dama ba. Hhhh''

''Ashe kema ana damawa da ke. Haka ni ma nake wa baban 'yar gayu. Je ki shirya ina jiranki har makarantar zan rakaki.''

''Yawwa. Bara na ɗauko mayafi'' ta yi maganar tana wucewa uwar ɗaki,babu jimawa ta fita ta ɗauki Hamid da ke bacci ta goyashi suka bar flat ɗin bayan ta kulle gidan. Har makarantar ta rakata sannan ta wuce. Da ƙyar ta yi nasarar amsar kuɗi wurin malam Tsalha,sai da ta haɗa mai da ƙaryayyaki kafin ya bata kuɗin. Domin Dauda Imamu ya fadɗa masa ya bar mata kuɗi ai,ko kwana ɗaya ba a yi ba har ta zo amsar kuɗi. Ba kuɗin da ta tambaya ta bata ba,rabinsu ya miƙa mata yana mita kamar shi ne mijin. Duk maganganun da yake mata ta yi biris da shi,burinta kawai ya miƙa mata kuɗin, tana amsa ta nufo gida. Bacci ta koma ita da Hamid...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^^^

Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya

A ɓangarensu Mairi hayaniyar jama'a ya sababba musu farkawa babu shiri daga bacci. Kallon junansu suka yi a yanayin bacci. Tamkar a cikin gidansu ake hayaniyar.

''Su waye ne haka da sassafe?" Dauda Imamu ya tambaya da muryar bacci.

''Ni ma ban sani ba,amma kamar muryar 'yar ƙuda nake ji haaaaaaaa...'' Hamma ta katse mata sauran maganar. Tsaki ya ja yana gyara kwanciya

''Za su da shi,ni na yi nawa''

Ita ma gyara kwamciyar ta yi don bacci bai isheta ba,kasaccnewar sun raya daran suna faranta wa junansu rai. Tamkar ana ƙara murɗa sautin hayaniyar ne.

''Baban Yasir ka taimaka ka je ka duba hayaniyar me ake,ba barinmu bacci za su yi ba''

Sarai ya jita amma ya ƙi koda motsi ne,shi ma karan kanshi hayaniyar ta dameshi,amma haushin ko ya je ba maraba da zantukansa za su yi ba ya sa bai da niyyar tashi. Sai da Mairi ta maimata masa sau uku kafin ya tashi zaune yana jan dogon tsaki.

''Ban san me yake shiga ƙwaƙwalwar wasu ba. Mts! Wallahi saboda sun hanamu bacci ne zan je,da ba don haka ba,babu inda ƙafata zata taka. Iskancin banza!" Ya yi maganar yana barin ɗakin. Murmushi Mairi ta yi tana gyara kwanciyarta,ta san halin kayanta. Ya fito kenan gabansa ya yi mummunan bugawa. A kiɗime ya furta ''Innalillahi wa inna ilahi raji'un!" Yana nufar gidan 'yar ƙuda inda mata da mazan layi suka yi cuncirindo tamkar ana raba zakka. Saleh ke aikin watsi da kayan 'yar ƙuda a waje yana sumbatu kamar zautacce. Duk kayan da ya fitar da su sai 'yar ƙuda ta mayar tana faɗin

''Idan ka ga nabar gidan nan sai na mutu aka zo fitar da gawata!"

An rasa cikin gungun mazan wanda zai dakatar da Saleh, matan sai ba 'yar ƙuda hakuri suke amma kamar da dutse suke. Lokacin da Dauda Imamu ya fito,daidai lokacin Saleh ya ɗauke fuskar 'yar ƙuda da zafafan maruka tare da shaƙo wuyanta. Kafin ya kai wurin tuni mazan suka yakice hannun Saleh a wuyan 'yar ƙuda. Sai fadin

''Sai kin bar mini gida ko na lahantaki! Wallahi na sakeki saki so babu adadi'' ana rirriƙeshi ya koma kamar zaki a wajen farauta. Tun da Saleh ya ɗauke 'yar ƙuda da zafafan maruka ta ɗauke wuta. Shaƙar wuyanta da ya yi ya sabbaba mitsi-mitsin idanunta firfitowa waje,ji take tamkar za ta sheƙa barzagu. Fizge hannunsa da mazan suka yi,sai ta zube wurin warwas kamar gawa. Hankali tashe wasu daga cikin matan suka ɗibo ruwa tare da yayyafa mata. Dogon numfashi ta sauke mai ƙarfi. A hankali ta tashi daga kwancen tana sauke tagwayen ajiyar zuciya kamar ta yi tseran gudu.

''Haba Saleh driba,idan ido ya rufe tunani ba zai gushe ba! Ina hankalinka da tunaninka suke da kake shirin illata matarka'' Wani daga cikin mazan ya faɗa.

''Karka sake haɗa ni da wannan mahaukaciyar malam,idan kai ne a matsayina wa ya san abin da za ka mata! Kasan gubar da nake kurɓa daga gareta ne! Wallahi idan da kai ne ƙila da yanzu ta bar duniyar! " Ya bashi amsa yana tsuke fuska. Hannun Saleh Dauda Imamu ya riƙo tare da nufar gidansa. Babu tirjiya Saleh ya bisa tamkar raƙumi da akala. Kai tsaye ya ɗauko tabarma sannan ya shimfiɗa suka zauna. Wa'azi mai ratsa jini da ɓargo Dauda Imamu ya yi masa. Sosai jikinsa ya yi sanya kamar ruwa ya cinyeshi. Sai da ya dawo cikin hayyacinshi sannan ya aiki Mairi ta kira 'yar ƙuda. Saleh ya so hanawa amma Dauda Imamu ya dakatar da shi. Ta jima 'yar ƙuda bata shigo gidan ba,har sun cira rai a kan zuwanta,sai can ta shigo gidan bagazan-bazagan kamar an korota,tana gaba yaran suna biye da ita. Wawan tsaki Saleh ya ja tare da faɗin...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.