Free chapter · Read without an account

Chapter 2

by Salis M Reza · A BAR WA RAI!

ABARWA RAI

°S-Reza ✍️

                      Chapter 2

Har bakin katangar ya ƙarasa ya na shiga duba wa ko zai iya samun ƙaramar hanyar da zai iya kamawa ya haura amma babu dama. Haka ya dinga zaga wa har ya zagayo ta gaban get ɗin, ya tsaya daga nesa yana jin gabansa na faɗuwa kar Emeka ya hango shi. Haka ya sunkuya ya na tafiya a duƙe kamar ɓarawo har ya ƙaraso bakin get ɗin. Nan ya tsaya ya na sauke ajiyar zuciya.  Kama bakin get ɗin yayi ya leƙa sai ya hango ƙofar ɗakin Emeka a buɗe amma baya gurin. Hakan yasa ya kama bakin get ɗin kenan ya ga hasken fitila ta haske masa ido, hakan yasa yayi saurin sakin get ɗin sai gashi a ƙasa tim ya faɗo, kuma bai tsaya ta zafin da yaji ba dalilin jin muryar Emeka ɗin da yayi ya na nufowa gurin da sauri domin ganin waye. Da gudu yasha kwanar makarantar yana jin yadda bayansa ke masa zafi. Bai tsaya a nan kusa ba domin yasa zai iya bin bayansa. Sai da yayi nisa kafin ya samu guri ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya. Bayansa ya dafe ya na haki sai kuma ya riƙe ƙirjinsa ya na jin takaicin kansa. Take zuciyar sa ta shiga aiyano masa suffar Haura da ya gani yau, ya na yin ƙirjinta da yaja hankalinsa yanzu gashi baiyi komai ba yasa kansa a matsla, alhalin yana da matarsa ta Sunnah a gida halak ɗin sa da zai iya yin komai da ita. Take ya shiga tsinewa zuciyarsa da ta raya masa wannan masifar da bai ma kai gayi ba kenan. Haka ya kama hanyar gida a ƙafa yana tafiya ya na tunanin tsawon lokacin da Haura take manne masa akan tana sonsa, kullum idan har tana da class ɗin sa haka zata dinga masa abubuwan da dole hankalinsa ya kai gareta, wasu lokutan har ofis ɗin sa take binsa, tun baya biye mata har ya fara yarda yana ɗan taɓa ta idan sun keɓe ko ya shafa ta. Daga fara mata haka kuma ta sake samun dama sosai domin ita har zuciyarta sonsa takeyi, shi kuma hakan da take masa yasa sheɗan ƙawata masa ita har yake aiyana yadda zai ji daɗi Idan ya samu burin ransa a kanta, gata yarinya ƙarana mai kyau ga tsafta, kuma daga gani yar manyan mutane ce, domin kullum cikin shigar kaya masu ɗan banzan kyau da nauyin kuɗi take.

Saida Habib yayi doguwar tafiya kafin ya tare mai ɗan sahu ya ƙarasa da shi gida. Yana shiga gidan yaga wutar palon a kashe hakan yasa yaji daɗi domin yasan Nadiya tayi barci kenan. Yana zuwa tsakiyar palon yaga haske ya karaɗe palon hakan yasa ya tsaya ya na juyowa ya sauke idonsa akan nata da tayi tsaye tana binsa da wani irin kallon tuhuma. Duk yadda Habib ya kai da ya ɓoye halin da yake ciki sai ya ƙasa domin ba zai taɓa iya samun kwanciyar hankali ba muddin bai san halin da Haura ke ciki ba. Yana tsaye yana kallon Nadiya amma ya fara tunanin yanzu idan ta mutu za'a zarge shi ne ko yaya, to an sanshi da ita ne ko wani yaga  lokacin da suka rage a school ɗin, lokaci ɗaya ya tuno da Emeka yasan dole ne sai an zarge shi, hakan yasa bai san lokacin da ya furta "Innalillahi wa inna'ilaihi rajiun ba" Nadiya da fitar sautin salatin nasa ya sake haifar mata da wani irin tsoro da fargaba ta ce "Beb daga ina kake? Wai me yake faruwa da kaine?" Ta ƙarasa tana sakin kuka domin iya abun da tasan zata iya yi kenan a halin yanzu, gashi ba yaro ba bare ta zane shi ya faɗa mata wacce irin masifa ya tabo musu haka da ya kasa samun natsuwa. Sai a lokacin ya kula da cewar ashe fa a gida yake kuma a gaban Nadiya. Jin kukan da take yi ne yasa ya ƙaraso kusa da ita ya rungumeta da karfi yana jin ina ma shima zai iya yin kukan kaman yadda takeyi, sai yake jin ita ai kuka mara dalili takeyi shine ya dace yayi kuka mai dalili. Ta na jiran taji ya fara lallashinta kuma ya faɗa mata matsalar sa amma sai ta lura kamar ma hankalinsa baya tare da ita, sai ma wani irin matsa da yake mata kamar ya manta da cewar mutum ce kuma mace a jikinsa, macen ma mai juna biyu. Ƙarar da tayi ce tasa yayi saurin sakinta yana ja da baya yana kuma kafeta da ido. Sosai tsoro ya sake baiyana a fuskarta ta na furta Innalillahi a ƙasan maƙoshin ta domin lamarin nasa ya fi ƙarfin tunaninta. Juyawa yayi ya nufi cikin daki sai idonta ya sauka akan bayan wandonsa da ya faɗi ɗazu ya kwashi jar ƙasa. Binsa tayi da kallo har ya ɓacewa ganinta. Gaba ɗaya ta rikice to ko dai faɗa yaje yayi ne. Bata san lokacin da ta zauna daɓas a tsakiyar palon ba tana sake rushewa da kuka. Kusan minti ashirin tana kuka amma kamar babu kowa a gidan, haka dole ta tashi ta shiga cikin dakin da yake ta sameshi kwance, yana jin shigarta ya yi saurin lumshe ido kamar mai barci. Toilet ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta dawo ɗakin ta hau kan gadon ta kwanta ta juyo tana kwallonsa. Kasancewar a kwai hasken wuta yasa ta kafe shi da ita, tana kallon yadda yake buɗe idon yana rufe wa kamar munafuki. Ta ce "Beb nasam ba barci kake ba, dan Allah ka faɗa min me yake faruwa, me ya kawo ƙasa a bayan wandonka a cikin wannan daren?" Ai da sauri ya mike tsaye ya duba wandon nasa sai ga nan alamun kasan. Hakan yasa ya cire wandon ya na faɗin "Faduwa nayi, kuma ki kwantar da hankalinki komai lafiya" ya faɗa yana shigewa Toilet ba tare da yasan mai zaiyi a ciki ba sai dan kawai ya gujewa tambayoyin wannan ƴar jaridar da ya samu yau. Yana shiga toilet ya sake haɗe kansa da bango yana ta tunanin yanzu gobe haka za'a je school a samu gawarta. Sai lokacin ma ya tuna bai duba gobe karfe nawa yake da class ba. Tuno da haka yasa ya fito da sauri kamar ma harda gudu ya hada a ganin Nadiya. Sai lokacin ya tuna da cewar ya bar wayar tasa a cikin ofis ɗin sa, sai ma lokacin wani tinani ya fado masa, anya kuwa a ofis ɗin ya bar wayar tasa. Take gabansa ya bada wani rass da ya tuna cewar tabbas da wayar a jikinsa ya zame wandonsa lokacin da yake ƙoƙarin yin abun. Da karfi ya furta "Na shiga uku na lalace" ya furta yana dafe koshi. Nadiya ta tashi zaune tana kwallonsa. Da sauri ya karasa gurin da laptop dinsa take June a jikin chaji. Ya buɗe ta hannunsa na rawa ya kunna. Tana daga gurin da take tana kallon yadda hannayensa ke rawa sun kasa bashi haɗin kai akan abun da zaiyi. Yana dubawa yaga yau class ɗin sa na yamma ne kawai babu na safe. Sai ya rufe laptop ɗin yana kuma jin ai dole ne ma gobe yaje school da wuri kafin kowa yaje, to amma idan kuma aka kama shi fa, to amma idan bai je ya ɗauke wayarsa daga gurin bafa har aka zo aka gani. Sai kawai ya bari akan gobe yaje da wuri ko iya wayar ya dauke koda kuwa mutuwa tayi. Yana kashe laptop ɗin ya juyo sai ya ga Nadiya zaune tana kwallonsa tana hawaye. Shi wallahi har mantawa ma yake yi da tana dakin.

Danne abun da yakeyi yayi ya hau kan gadon ya rumgumota jikinsa ya ce "Please I'm sorry, matsala ce ake so sai an dora min ita a makaranta wacce ban san da ita ba, hakan yasa gaba ɗaya na kasa natsuwa" ya ƙarasa yana jin shi da kansa ƙaryar bata samu gurin zama a bakinsa ba bare kuma zuciyar Nadiya da ya sani da saurin gane gaskiya ko ƙaryar da zai mata. Yana ji tace "Hum" daga haka kuma bata sake cewa kuma bai, kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba domin bai son yin wata maganar kuma. Daga haka ta kwanta sai dai ta kasa barci tana ta hasaso abubuwan da zasu iya firgita mata miji kamar haka, amma duk tunanin da tayi sai ta kasa yarda, harda tunanin ko dai ciki yayiwa wata amma tasan ba halinsa bane. Sai kusan ɗaya yaji alamun barci ya ɗauketa hakan yasa ya ɗan leƙa fuskarta yaga da gaske barci takeyi. Sai ya tashi zaune yaci gaba da zaman jiran wayewar gobe. A kunnensa a kayi kiran sallah sai a lokacin ya tuna da ko magriba da isha bai samu yayi ba. Ya shiga toilet ya ɗauro alaula ya tada sallar magriba bayan ya idar yayi Isha. Ita kanta sallar yana yi ne yana tunani domin bai yi ta a cikin natsuwa ba. Sallar asuba ma a cikin ɗakin yabi jam'i duk da kuwa yasan illar yin hakan, yasan irin asarar da mutum ke yi idan ya rasa jam'i salla musamman salar asuba da Manzon Allah saw yake cewa "Tabbas munafuki baya iya tashi domin yin sallar asuba a jam'i, duk wanda ka ga yana iya tashi ya je masallaci domin yin sallar asuba to tabbas ba munafiki bane. Amma dukda wannan sanin haka ya danne har aka idar da sallar tare da shi. Daidai lokacin Nadiya ta farka tana furta addu'ar tashi daga barci wato "Alhamdu lillahil lazi ayana ba'adama amatana wa'ilaihin nushur. Ta bishi da kallo ganin yana salla a gida domin bata saba ganin haka ba. A cikin wannan satin ne ma yake makara har sai an tada salla zata tashe shi kuma haka zai yi alaula cikin sauri ya tafi, kasancewar taga baya barci da wuri, to idan ya dawo ne kuma zai ta barci har sai tayi da gaske zai tashi ya shirya ya tafi makaranta. Haka take ta fama kwana biyun nan. Ta ce "Beb salla a gida kuma kamar Mace?" Ta faɗa tana sauka daga kan gadon cikin muryar barci. Ya ce "Bana jin dadi ne" ya faɗa yana fita daga dakin ya dawo Palo.

Haka ya kishingiɗa a kan kujera mai ɗaukar mutum uku yana ta alla-alla gari ya ƙarasa wayewa. Yana zaune har shida da rabi lokacin gari yayi haske sai ga Nadiya ta fito bata ce masa komai ba ta shiga kichin. Sai lokacin taga kwanukan abincin sa da baici ta dawo dasu. Na safe ma sai almajirai ta bawa, haka na rana ma da taga bai dawo ba. Wannan kuwa shi zata ɗumama sai ta haɗa musu shayi tunda suna da bredi koda ƙwai huɗu ne sai ta soya musu. Tunda Allah yasa yau ya tashi da wuri itama bari ta haɗa komai da wuri sai ta kai masa kar ya sake fita barci komai ba. Bata fito daga kichin ɗin ba saida ta soya ƙwai guda huɗu ta hado ruwan zafi. Ta kawo dainintebul ta ajiye, sannan ta koma ta zubo jalof ɗin taliyar da waken da ta ɗumama a flet ɗaya ta ajiye. Ta kwaso kayan shayi harda biride ta ajiye duk tana yi tana satar kallon ganin hankalinsa baya gareta. Saida ta haɗa masa shayin kafin ta ƙarsa gurin da yake tana kiran sa. Firgigit ya dawo hankalinsa yana kallonta. Ta ce "Breakfast na gama ka tashi kaci da wuri kafin ka fita" ta ƙarasa tana barin gurin. Ya kalli a gogon palon mai irgen biyar-biyar sai yaga ya bashi karfe bakwai harda minti biyar ga kuma ɗan ƙaramin tsinken ya kusa hawa kan ɗaya number mai nuni da cewar da minti goma ya kusa. Ya kalli Nadiya ya ce "Bari na shirya nazo" ya shige daki yana jin shi har ma ya manta da batun abinci, baya ko iya tunawa da shi bare kuma yaci. Ko minti biyar bata ce yayi ba ya fito cikin shigar ƙananan kaya, yau ko samun damar gyara ma gashin bai samu ba, ta kalleshi ganin ya nufo gurin da take zaune tana jiransa. Tun kallon farko da tayi masa ta gane baya cikin haiyacinsa har yanzu, domin ba haka ya saba fita ba. Ya sunkuya ya ɗauki kofin shayin gabanta ya kurɓa sai ya ajiye. Sai ta kalli wanda ta haɗa masa a kusa da shi, ko bai ga wannan ɗin bane oho. Tayi tunanin zama zaiyi sai taji yace "Thank you Beb I'm okay, sai na dawo" yana faɗa kuma ya ja mata hanci ya bar gidan yana sauri. Har ya fita ta ƙaranin get ɗin sai ya tuna da bai ɗauki motar ba. Haka ya dawo ya tada motar ya fita daga gidan. Kamar kar ya dawo ya rufe get ɗin amma haka ya fito ya rufe yana kama hanyar school. Sosai yake gudu yana addu'ar Allah yasa shine mutum na farko da zai fara shiga cikin makarantar duk da kuwa yasan bashi da class ɗin safe. Amma sai me zai faru tun daga nesa ya hango get ɗin makarantar a wangale ga kuma dalibai har sun fara shiga. Ya kalli agogon motar ya bashi karfe bakwai da rabi harda minti ɗaya. Gabansa ne ya shiga bada wani irin sauti mai kamar ana dakan sakwara, dukda safiya ce sai ya ji kamar zufa ce ke ƙoƙarin karyo masa, musamman da yazo kusa da get ɗin yaga kamar mutanene a tsaitsaye ana kallon wani abu, wanda zuciyarsa ta raya masa cewar gawar Aisha Adam ce aka gani shine kowa ya tsaya kallo...📝

Muje zuwa a kwai ƙura a gaba.

S Reza...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.