Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Salis M Reza · INA MUKA DOSA?

INA MUKA DOSA?

S-Reza✍️

Please kuyi following wannan chanel ɗin nawa please, nasan zakuyi domin Allah, sabo ne mutanen ciki basu fi ɗari da wani abu ba, please duk masoyin s Reza ya daure ya shiga harma da maƙiyan domin suna da amfani 😅. Ni dai kawai a min kara a cika min wannan zaure, daga marubuta har makaranta ban ware kowa ba Pls.

GARGAƊI

Kuskure ne yin amfani da wani sashe daga cikin wannan littafin ba tare da izini ba. Haka zalika kuskure ne wani/wata ya ɗora min littafi a YouTube ba tare da izini ba. Muddin hakan ta faru to abun ba zai yi daɗi ba. Wannan gargaɗi ne ga masu ci da gumin wasu, da kuma masu satar fasaha.

JAN HANKALI

Kaman yadda muka saba a dukkanin littatafai na wannan karan ma haka ne. Babu posting ranar juma'a da kuma ranar Lahadi. Sannan in sha Allah wannan tafiyar ta haɗa muku abubuwan ban mamaki da kuma nishadi harda ilmantarwa duk a cikin wannan littafin. In sha Allah duk wanda ya karanta wannan labarin ba zaiji kunya ba domin zai samu abun da yake so 99 cikin 100. Muje zuwa cikin labarin Allah ya sa yadda muka fara lafiya yasa mu kammala shi lafiya, kuma Allah ya tsare ni da rubutu abun da ba zai amfani al'umma ba. Amin ya rabbil alamin.

Bismillahi Rahamanun Rahim

Page 1️⃣

MABUƊI

Likitan ya kalli ɗan ƙaramin yaron dake gabansa ya ce "Ina iyayen ku suke?" Yaron yayi shiru yana kallon likitan da shima yake kallon sa. A karo na biyu ya ƙara maimaita tambayar da yayiwa yaron yana cigaba da kallonsa. Cikin dakewar rai da nuna jarumta yaron ya ce "Daga ni har ita bamu da iyaye, nine ubanta ita kuma itace uwata, saboda haka kawai sanar mini da abun dake damun ta ko ma menene, bamu da kowa haka muke rayuwa tsawon lokaci masu yawa bata san kowa ba sai ni, haka nima ita na sani. Yaron ya ƙaras maganar fuskarsa a haɗe, kai ba ka rantse cewar cikin tashin hankali yake ba, domin kuwa cikin zuciyarsa wani irin harbawa take yi kamar zuciyarsa zata buɗe ta fito. Likitan ya sauke ajiyar zuciya yana mamakin iKon Allah jin wani sabon salo wai shine uba ita kuma uwa. A zahirin gaskiya wannan yaron yayi ƙarami da yi masa bayanin abun da ya samu yarinyar domin ba zai taɓa ganewa ba, to amma tunda har yace basu da kowa ai ya zama dole yayi masa bayani ta yadda zai gane. Likitan ya ce "Shekarar ka nawa? Yaron ya bashi amsa da cewar "Shekara sha biyar" likitan ya ce "Ita kuma yarinyar fa? Wannan karan sai da ya ɗago ya kalli likitan kafin ya basa amsa yana mai ƙara jin tsoron abun da ya sameta jin irin tambayar sa yake ta masa. "Shekara sha biyu". Wannan karan ma sai da likitan ya ƙara kallonsa sosai har sai da yaron ya tsargu ya ce "Likita ko mutuwa tayi? Yayi tambayar muryarsa na rawa. Likitan ya miƙe tsaye ya dawo kusa da yaron sannan ya fara magana cikin natsuwa yanda yasan yaron zai fahimta kuma zai gane. "Ƙanwarka ta samu cutar mantau (Mantuwa)dalilin buguwar da tayi a kai, yanzu haka ta manta da kowa da komai ciki kuwa harda kanta da ma dukkanin wanda yake tare da ita da kuma rayuwar da tayi a baya. Amma a kwai abu guda ɗaya da zai iya dawo da ita cikin tunaninta sai dai abun yana da sauƙi da kuma wahala, amma muddin aka yi abun koda a yau ne to tabbas zata dawo cikin hankalinta. Da saurin yaron ya mike tsaye shima ya ce "Ƙarya kake yi Sara ba zata taɓa mantawa dani ba ko meye zai sameta, wallhi karya ne, kai ɗin banza waye kai da zaka ce haka. Yaron na faɗa ya tashi da nufin barin office ɗin. Likitan da dama yasan abun da zai faru kenan, domin yaso ace da wani babba yayi wannan maganar ba wannan yaron ba. Riƙo yaron yayi ya dawo dashi baya, ganin yadda yaron yake kukan maza wato ga hawaye amma babu ihu. Shakka babu wannan yaron Namiji ne ko daga jin yadda yake magana cike da zuciya da jarumta. Ƙokarin ƙwace hannunsa yake amma likitan ya ƙi bashi damar hakan. Likitan ya ce "Kaga natsu sai muyi magana?" Ganin dai yaron yaki natsuwa ne yasa shi faɗin "Zo muje ɗakin da take sai ka ganewa idanunka. Yana faɗa ya sakar masa hannu. Yaron ya ce "Idan ma wani abu kukayi mata to wallhi ba zan yarda ba, ai saboda mugunta yasa tun shekaran jiya kuka hanani na ganta, shine yanzu zaku ce wai ta manta da ni saboda ku mugaye ne. Yaron yayi maganar da harshen larabci wanda likitan ya tsaya yana kallonsa, domin baya magana ɗaya biyu bai haɗa da larabci ba. Haka suna tafiya yana zagin likitan da labarci har suka ƙaraso cikin ɗakin da yarinyar ke zaune a karshen gadon ta cusa ƙanta cikin cinyoyenta kanta babu ko ɗan kwali. Sanye take da bakar rigar a baya sabuwa, gashin kanta duk sun zubo sun rufe mata gefe da gefen fuska. Da sauri yaron ya ƙaraso gurin yana kiran sunanta muryarsa cike da farin ciki ganinta zaune. Yana ƙarasowa gurin ya kai hannu ya taɓa bayanta wanda yasa tayi zumbur ta ɗago kanta tana kallonsa. Shi kuwa likitan daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallon su. Da sauri yarinyar ta ja da baya tana masa wani irin kallo irin na anga abun tsoro ko an gamu da abun cutarwa. Yaron bai damu ba ya fara ƙoƙarin hawa kan gadon yana faɗin "Sara kin samu lafiya ko? Nayi kewarki yau kwana biyu kenan sun hana ni na ganki sannu kinji. Ya faɗa yana ta ƙokarin ganin ya kai gare ta. Wani irin ƙara ta sake tana kare jikinta tana ƙara komawa baya, karshe ma ta sauka a kan gadon ta koma cen gefe guda tana ɓoye kanta. Yaron ya kalli jikinsa ya kalli likitan da yake ta kallonsu. Sai kuma ya ƙara dosar gurin da take yana cewa "Sara nine fa Ziyach ɗin ki, ko baki ganni bane, lafiya kike kuwa?. Ya faɗa yana ƙara dosar ta da saurinsa. Ai kuwa ta sake fasa wani irin ƙara da tasa Ziyach rufe kunnuwansa yana kallonta. Ganin haka yasa ya nufeta da ƙarfi ya riƙe ta yana magana yana hawaye, yayin da ita kuma take ta ihu kamar wanda kura ta kamata. Ganin yaƙi sakinta ne yasa ta sakar masa cizo tana barin gurin da gudu ta sake guri tana kare kanta. Ziyach ya kalli likitan cikin kuka yace "Me kukayi mata? Na ce me kuka yi mata da ta koma haka?" Yayi tambayar kamar wani babban mutum, kuma yana faɗa yana tunkaro likitan cike da zuciya. Sai da yazo har gaban likatan kafin ya aikata masa abun da yayi niyya likitan ya faɗa masa maganar da tasa Ziyach tsayawa yana kallonsa. Ya ce "A kwai magani wanda zai iya dawowa da ita cikin hankalinta ko a yanzu ne, kuma kaima zaka iya yi mata wannan maganin. Ziyach ya yi shiru kafin ya ce "Faɗa min ko menene shi muddin zata dawo cikin hankalinta zanyi wallhi zanyi ko menene, Sara ita kaɗai ce gareni bani da kowa sai ita. Ziyach ya ƙarasa yana kuka sosai kamar ransa zai fita. Likatan ya ce "Sex za'ayi da ita shine kaɗai zai iya dawowa da ita cikin tunaninta a cikin kankanin lokaci. Idan har a kwai aure tsakanin ku to ka Aureta domin sama mata lafiya. Idan kuwa babu aure to ka nemo mata wanda zaka aura mata domin ceto lafiyar ta. Muddin ba haka akayi ba, to ba zata taɓa dawowa cikin hankalinta nan kusa ba, domin irin wannan ciwon wasu ma dashi suke mutuwa, wasu kuma suna ɗaukar shekaru masu yawa. Har yanzu likitoci suna bincike akan samo maganin irin wannan ciwon wanda ba sai ta wannan hanyar ba, domin irin wannan lokacin da zai samu yara ƙanana da basu isa yin aure ba kamar dai ita wannan. Sosai likitan ya shiga Korowa Ziyach labarin da shi bai ma san yana yi ba. Hasali ma shi tuni tunanin sa ya faɗa izuwa abun da likitan ya ke cewa wai Sex, kuma wai Sara. Yarinyar da bata ma gama sanin kanta ba, yarinyar da gaba ɗaya ma nawa take, ƴar shekara sha biyu. Likitan ya katse masa tunani da faɗin "Karka damu ɗan saurayi ai ba wai dole bane, zaka iya zama da ita a haka amma fa ka sani a koda yaushe tsoron mutane take yi, kuma a haka zata cigaba da rayuwa, kuma ba zata iya zama a gurin da a kwai mutum ba, zata na yin rayuwa ne ita ɗaya, sannan wasu lokutan ma zata dinga yin abubuwa irin na mahaukata, muddin wani yaje kusa da ita to ba zata iya zama a gurin ba sai dai tai ta yin ihu tana kuka har sai an bar gurin da take, shi kansa Sex ɗin da za'ayi da ita sai dai a saka mata maganin barci ko kuma ayi mata na ƙarfi kuma na dole domin samun lafiyar ta. Sannan kuma mutumin da ya bige ita yarinyar ya fiya kuɗin aikin da a kai mata harda sauran chanji da za'a baku idan zaku tafi. To yanzu zaɓi ya rage naka ko ka sama mata magani ko dai ka barta a haka har lokacin da Allah yayi zata samu lafiya.

ASALIN LABARI

SAUDIYYA

Shiru palon yayi kamar babu wata halitta mai numfashi a ciki bayan jin abun da an kai awa guda ana tambayar ta shi babu amsa, sai gashi bayan furta kalmar kowa ya kasa magana. Kalma ce guda ɗaya tak amma abun da zata haifar ɗin zuciya ba zata iya jurewa ba. Sosai larabawan kowa ya kasa magana jin sabon al'amarin da ya ke tun kararosu a daidai wannan lokacin da basu zata ba kuma basu nufa ba. A ƙalla an kwashe mitoci sama da biyar babu wanda ya iya magana alama dai kowa ya rasa abun cewa ne, maganar ma ta maƙalewa kowa. Tabbas abun da ciwo kuma da zafi sosai ace ƴar da ka gama bata yarda da amincewa, wacce kake alfahari da ita a ko'ina, kuma wacce al'ummar dake zagaye daku suke yin kwatance da kyawawan halayen ta, amma wai yau ita ce ke sanar maku da cewar tana ɗauke da cikin wani namijin kuma ba da aure ba, cikin shege dai da kuke ji ana labarin sa a wasu guraren ashe kuma yana nan tafe, cikin shige fa, kuma wai ƴarsa, ƴar tasa ma wacce ya ɗora mata dukkanin yardar sa, bama shi ba, za'a iya rantsuwa da Allah akan yardar da mutanen unguwa suka yi mata ma yafi nasa. Sosai Abdul Aziz yake ta maimaita sunan wanda ƴar tasa ta ambata a matsayin wanda yayi mata cikin ya kasa cewa komai yana ta kallonta yadda ta sunkuyar da kai tana zubar da hawaye. Mai da kallonsa yayi ga matar tasa da itama tayi tagumi tana ta kallon ƴar tasu kaman yadda shima yayi, itama dai babu bakin magana. Su huɗu ne a palon, Abdul Aziz wanda ya kasance mahaifi a gare su, sai Khadijah wacce itace mahaifiyar su, sai Abdullahi wanda shine Babba ɗan shekara sha tara. Sai Laila wacce ke bi masa ƴar shekara goma sha shida. Su ɗin larabawa ne sosai gaba da baya mazauna ƙasar Saudiyya tun iyaye da kakanu. Sosai Aziz yake tsaye akan family ɗin nasa wajen tarbiyya kamar yadda ake kwatance da ƴaƴansa musumman ma ita Laila wacce kullum ba'a ko ganin fuskarta a waje tsabar alkunya da tsoron Allah, zuwa makaranta sai ta sa liƙaf da safar hannu da ta ƙafa, sannan bata magana da kowa a kan hanya idan ba gaisuwa ba. Idan aka ce yarda to haƙiƙa iyayen nata sun gama dan ƙawa gareta domin sun yarda da ita sosai fiye da tunanin mai tunani. Abun da yake ƙara ƙonawa Abdul Aziz rai bai wuce yadda yake mata kallon yarinya karama ba, yana mata kallon bata ma san komai a duniya ba, a she kallon kitse yakewa rogo, ashe recover kawai take musu. Gashi yanzu da bakinta ta furta kalmar amma wata zuciyar tasa tana ƙin yarda da cewar Laila bata da ciki a jikinta.

Abdul Aziz yayi ƙarfin halin magantuwa ganin kowa ya kasa magana "Tun yaushe hakan ke faruwa tsakanin ki da shi? Dama soyayya kuke yi ko kuma dole yayi miki?" Abdul Aziz ya faɗa yana kafe ta da ido, dukda cewar bai yarda ba, amma zai so jin ko dai fyaɗe yayi mata, ai kuwa da sai yasa an ɗaure ubansa da dukkanin danginsa har sai igiya tayi saura. Laila ta ja majina da karfi tana ɗago kanta ta sauke shi a fuskar mahaifin nata da gaba ɗaya tausayin sa ya gama cika mata ƙalbinta, dama tasan wannan ranar zata zo hakan yasa ta shirya mata sosai, dole ne ta cire kunya tayi bayani domin kuwa komai ya gama faruwa. Ta ce "Eh soyayya muke yi" Ta faɗa tana mayar da kanta ƙasa. Hakan ya tabbatar wa da Aziz cewar ba dole yayi mata ba kenan. Ita kuwa Laila tana ƙarasa maganar ta cigaba da kukan da Abdul Aziz ya rasa na meye take yi, shin na sanin tana ɗauke da cikin shege ne, ko kuma na tausayin iyayen nata da ta zubar musu da mutumci ko dai na tausayin kanta. Aziz ya ce "Kina sonsa shine yasa kika yarda kuka aikata zina da shi Laila!? Laila ina ilimin naki da hankalin naki yaje a lokacin da kika iya budewa Namiji jikin ki?" Aziz ya faɗa hawaye na zubowa daga idanunsa. Sai a lokacin Khadijah ta iya cewa "Tun yaushe kuke tare da shi Alpha ɗin? Kuma yasan da cewar kina ɗauke da cikin nasa?" Khadijah ta faɗa tana kallon ƴar tata. Ta ce "Eh ya sani. Laila ta amsa tana tattaro dukkanin ƙwarin guiwarta, tabbas tana jin kunya irin Kunyar da mutum zaiji kamar ƙasa ta tsage ya shige ciki, amma kuma ai komai ya faru, ba'a dawo da hannun agogo baya. A hankali Aziz ya ce "Tashi ki tafi" ya faɗa yana kawar da kai daga kallonta domin bai kuma san abun da zai sake cewa ba. A hankali ta fara ƙoƙarin tashi tana jin wani irin kunya mai sa mutum yaji kamar ya nitse cikin ƙarƙashin ƙasar da babu wanda zai sake ganin sa, jin kanta take kamar ba ita ba. Sai lokacin ma ta fara tunanin yadda zata kalli mutanen da suka santa, da kuma ƴan makarantar su da ƴan unguwa da kowa yake kwatance da ita, tana cikin wannan tunanin kuma tunanin mahaliccin ta ya faɗo mata, shin mai zata ce masa idan taje lahira. Sosai Laila ta dinga tunanin laifin da tayi har ta bar cikin palon ba tare da ta sani ba.

Aziz ya dawo da kallonsa ga Abdulhi cikin harshen su na gado ya ce "Waye shi Alpha ɗin a ina suka haɗu da ita?" Abdullahi ya ce "Abi ɗan makarantar su ne, kuma yaro ne qarami baya jin magana, babu wanda bai san shi a fannin rashin ji ba. Ya ce "Ɗan gidan waye? Abdullahi yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yace "Abi ban san mahaifinsa ba, amma zan iya tambaya yanzu. Aziz ya furta hazbunallahu wani'imal'wakil! Allahuma ajurni fi masibata!. Nan take Abdulhi ya ɗaga waya ya shiga kira. Minti ɗaya ya sauke wayar yana kallon mahaifin nasu da gaba ɗaya ya koma abun tausayi. Kafin Abdullahi yayi magana Aziz ya ce "Abdul da wani ido zan kalli mutane ace Laila tayi ciki?! Abdul ciki fa, irin na shege!. Aziz ya ƙarasa yana fashewa da kukan da bai samu yayi ba. Abdullahi ya karasa kusa da Mahaifin nasu ya kamosa yana basa baki. Ya ce "Abi yanzu ake faɗa min cewar wai Mahaifin yaron ya rasu daga shi sai ƙanwarsa guda ɗaya tare da mahaifiyarsu. Wai Mahaifin su ɗan Afrika ne neman kuɗi ya kawo shi nan Saudiyya har suka haɗu da ita mahaifiyar tasu. Aziz ya ce "Ina son ganin yaron yanzu. Yana faɗa ya miƙe tsaye yayi hanyar ɗakin da matar tasa ta shige tun dazu. Abdullahi ya bisa da kallo har ya daina hangosa. Ɗakin Laila ya kalla ya girgiza kafin ya kama hanyar waje yana jin kamar idan ya fita za'a fara nuna shi.

Tana shiga ɗaki ta kulle ƙofar ta samu bakin gado ta zauna tana cigaba da kuka da kuma tunanin yadda zata haɗa ido da mutanen duniya. Rigar jikinta ta ɗaga tana kallon cikin nata da babu wata alama ta ciki ko kaɗan, sai ta share hawayen fuskanta sannan ta shafa a cikin nata tana ƙara zurfin tunani. A fili ta furta "Astagfulrullah ya Allah! Tana ajiye kalmar wayarta ta hau ƙara da wani sauti mai sanyi wanda shi kaɗai ta sakawa. Wata waƙa ce ta larabawa mai sanyi wanda ake yabon masoyin gaskiya, ko baka jin yaran sai yanayin waƙar ta tafi da imaninka domin yadda sautin yake tashi mai taushi babu hayaniya. Kallon wayar tayi har ta tsinke bata ɗaga ba. Wani kiran ne ya sake shigowa wanda har lokacin idanunta na kan wayar tana sauraron baiticin farkon waƙar da take ji kamar da ita ake yi. Da sanyin jiki ta ɗaga. Kafin tayi magana ta tsinkawo muryar sa yana faɗin "Ina kika ajiye wayarki ina ta kira?" Ba tare da ta amsa masa ba ta ce "Su Abi sun gano komai Alpha!". Ta faɗa tana fashewa da sabon kuka. Cikin nuna damuwa da jin kukan nata ya ce "Sun gano me?" Ta ce "Cikin" Lokaci ɗaya ya saki murmushin da sai da ta jiyo sautin sa. ya ce "Ai na faɗa miki tun kafin su gano ga yadda za'ayi amma kin ce ba haka ba, Laila kina da taurin kai wallhi, yanzu ga abun da kike gudu ɗin ya tabbata, shi yasa ni tun farko banso har aka kai wannan matakin ba. Ta ce "Tsoro nake ji sosai wallhi, ban san kowa ba bayan Abi da Ummi sai ɗan uwana Abdullahi, idan na aikata abun da kace zan shiga damuwa. Shima ya ce "Nima bayan nawa dangin ban san kowa ba, amma saboda ina sonki nake jin zan iya yin komai domin kawai na rayu da ke. Ya faɗa da wata murya ta abun tausayi. Jin tayi shiru ya ce "Idan kin yarda a daren yau zan gama haɗa mana kaya mu tafi domin tsira da mutuncinki, domin Kinga yanzu babu wanda ya sani sai iyayenki, idan muka bar garin babu wanda zai ganki da cikin bare har kiji kunya, tun farko ma da kin yarda da su kansu iyayen naki ba zasu ji labarin ba wallhi, na baki minti goma kiyi tunani zan sake kiranki please kiyi nazari mai kyau, ki tuno da Kunyar mutanen gari da ta ƴan uwa. Amma fa ki sani ina tare dake har abada, domin ina sonki. Yana faɗa ya kashe wayar. Lalai tabi wayar da wani irin kallo tana ta ƙokarin auna maganganun nasa. Ta sani cewar Alpah yana sonta sosai, amma anya ta kyautu ta bar kowa nata ta bisa izuwa gurin da ba ta sani ba, to amma idan bata tafi ba yaya za'ayi ta iya haɗa ido da mutanen unguwa da ƙawaye, su kansu iyayen nata ma yanzu kunyarsu take yi. To amma guduwa ɗin itace mafita kuwa? Idan ta bisa ina zasu je?.

******

ALPHA

Ya gama shirya komai da zasu buƙata ba tare da mahaifiyarsu ta gane ba, hatta ƙanwarsa da kusan kullum suna tare bai bari ta gane takun nasa ba. Dama gaba ɗaya kadarorin su a hannunsa suke, wanda ba karamin dukiya mahaifinsu ya mutu ya bar musu ba, kasancewar sa babban ɗan kasuwa anan Saudiyya. Mahaifinsa mai suna Jamilu wanda ya rasu tun ƙanwar sa na shekaru goma. Yanzu haka mahaifiyarsu ta sake yin aure ta auri wani babban mai arziki a cikin garin na Saudiyya ta tare ita da ƙanwar sa mai suna Ummul kairi, a cikin gidan da suke kasancewar mutumin yana da wata matar. Mahaifiyarsu balarabiya ce, yayin da ma haifinsu ya kasance ɗan Nigeria kuma bahaushe. Yanzu haka suna zaune ne su uku a cikin gidan da shi Alpha ɗin sai Ummul kairi sai kuma ita mahaifiyar tasu da suke kira da Katii. Bayan kasuwanci da Alpha yake yi yana kuma koyarwa a ɗaya daga cikin manyan jami'o'in na Saudiyya wanda a cen ne suka haɗu da Laila wacce ta kasance ɗaya daga cikin daliban wannan makaranta. Kamewarta da natsuwarta ce taja hankalinsa har ya tunkareta, ya sha wahala sosai kafin ta sauraresa. Kasancewar sa mutum mai surutu da kuma jiji da kai, ga rashin girmama na gaba, ga shi an masa sheda da rashin taimakon mabuƙata, kaman yadda ake cewar halin mahaifiyarsa ya dauko. Hakan yasa koda suka fara soyayya da Laila sai ya zama tana ɓoyewa kowa domin abun kunya ne kamar ita mai natsuwa tana soyayya da irin sa. Cikin wata ɗaya Laila ta faɗa komar son Alpha dumu-dumu wanda bata ji bata gani, amma tana tsoron nuna shi a matsayin wanda take so, ba dan baida kyau ko wani abu ba, a'a kawai halinsa ne ba mai kyau ba, daga karshe kuma har dai wannan mummunan al'amarin ya afku s tsakanin su, kuma yazo da tangarda har aka samu juna biyu. Shi yaso kawai su gudu subar ƙasar Saudiyya sai suyi aure abun su tun ma kafin cikin ya baiyana amma ita kuma tana tsoro, babu yadda baiyi da ita ba amma taki. Yanzu haka yau ya kai letter jami'ar da ya fara koyarwa akan ya ajiye aiki, sannan yabi duk inda yake da hannun jari yayi musu bayani yadda za'ayi. Yanzu haka ya shigo gida ne domin yayi sallama da Katii da kuma Ummul Kairi domin a daren nan ne Laila zata gudo daga gidan nasu kamar yadda suka tsara.

Da sallama ya shigo gidan wanda kafin ma ta amsa masa tambayar ta ce "Alpha ɗazu nake samun labarin wai ka ajiye akin koyarwa me ya faru?" Ta tambaya tana kafe ɗan nata da ido. Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya samu guri ya zauna. Ummul Kairi ce ta ce "Ai na faɗa miki da gaske ne ajiye aikin nasa yayi ba gashi yana ta dariya ba. Alpha ya kalleta ya ce "Shifa munafuki kullum lamarinsa baya yake yayi, kuma Allah baya tare da shi a dukkanin lamarinsa" Alpha ya faɗa da sigar wasa yana kallon ta da ita kuma ta cuno baki gaba kamar zai taɓa bango ta ce "Ni dai ba munafika bace ai gaskiya na faɗa. Katii ce ta daka masa tsawa ganin zai sake buɗe baki yayi wata maganar ba tare da ya tanka maka ba. "Bana son zancen banza, yaya ina maka magana kana maiyar dani kamar abokiyar wasan ka, meye dalilin ajiye akin naka da kayi?" Ta ƙarasa tana cigaba da kallonsa. Alpha da har lokacin bai daina wannan murmushin nasa da yake tsawa mutane a rai muddin yayi irin saba. Ya ce "Haba Katii Kema har kin yarda na ajiye aiki haka kawai, to duka-duka ma yaushe na fara aikin da zan ajiye shi?" Ya tambaya yana ƙoƙarin mikewa. Ta ce "Alpha koma ka zauna" ai kuwa ya koma ya zauna yana kallonta. Ta ce "Ba wasa nake ba, har gida aka zo aka sanar min, kuma ga Kairi itama ta faɗa min, wai Alpha me kake shiryawa ne? Ya ce "Katii duk karya ne, munafukai ne kawai, kuma ni bamma san da maganar ba. Ta ce "Gobe zamu je makarantar tare sai na tabbatar idan kuwa gaskiya ne wallhi zan baka mamaki Alpha, ban san me kake son zama ba, kaine babba amma Gaba ɗaya kaƙi ka natsu guri ɗaya ko. Jin ta fara faɗan nata ne yasa Ya ce "Allah ya kaimu goben lafiya" yana faɗa ya shige ɗakin sa suka bisa da kallo. Kairii ta ce "Bashi da gaskiya wallhi. Katii ta ce "Allah ya kwimu goben kawai ina daidai da shi. Mahaifinsa ya rasu ya bar masu dukiya sosai, domin saboda dukiyar ce yasa Alpah yin abun da yaga dama, ko wannan aikin koyarwar sai da Katii tayi da gaske kafin ya fara, farko yayi tunanin mijin da Katii ta aura saboda dukiyar su yake santa, hakan yasa baya shiri da mutumin, ai kuwa yayi baƙe-baƙe akan dukkanin dukiyar su domin kuwa shi yake jan ragamar komai tare da wani aminin mahaifin nasu wanda shine babban yaron baban sa lokacin yana raye. Misalin ƙarfe goma ya gama fitowa daga gida bayan da ya tabbatar ya dauki komai. Yazo gurin da sukayi zasu haɗu da ita Laila ɗin ya zauna yana jiranta domin sunyi akan karya kirata, kuma karta ɗauko komai sai takardun makarantar ta da abun da tasan tana bukata.

*******

LAILA

Bayan kammala cin abincin dare Abdul Aziz ya kalleta ya ce "Da naso azo min da shi yaron amma yanzu na fasa zuwa gobe zaki kaimu har gidan su yaron. Lokaci ɗaya gabanta ya bada wani sauti mai karfi har saida ta dafe gurin. Ummi ta ce "Ba haka za'ayi ba, ni a nawa kawai ya fito ya aureta shine kawai mafita". Abi ya kalli matar tasa ya ce "Yaron da bashi da asali kuma ɗan iska mara kunya shine kike cewa wai na yarda ya auri ƴata? To bari kiji Wallhi sai munyi shari'a da shi akan wannan abun. Ummi ta ce "To yanzu mai ya rage, gashi baka aura masa ba ya mata ciki, kuma batun yin shari'a wallhi kanka zaka tozarta da kuma ita ƴar taka, abun da yafi kawai shine kayi hakuri a binne wannan abun a kira yaron kawai ayi musu aure domin kuwa yana sonta kaman yadda tace. Abi ya tashi fuu ya bar gurin ba tare da yayi wata maganar ba. Ummi ta kalli Lalia ta ce "Kin bamu kunya wallhi, kuma kinji abun da yace, ki shirya shiga kotu domin yin shari'a da shi a gaban ɗaruruwan mutane kina ɗauke da cikin shege. Ummi na faɗa ta bar gurin duk ranta a mugun ɓace. Lokaci ɗaya Laila ta ɗago tana kallon bayan uwar tata da har ta shige ɗaki. Ashe bata sani ba kallon ƙarshe tayi mata. Ya rage daga ita sai Abdullahi a palon. Ya ƙaraso kusa da ita ya ce "Karki damu in sha Allah ba zan bari Abi ya kai wannan maganar kotu ba, nasan abun ba zai miki daɗi ba, muma ba zai mana ba. Yana faɗa shima ya tashi ya bar palon. Shima tabi bayan sa da kallo tana masa kallon ƙarshe. Ta kwashe a ƙalla mintuna biyar kafin ta iya samun ƙarfik halin tashi ta shiga haɗa duk abun da tasa zata bukata. Ta samu takarda tayi dogon rubutu ta ajiye a fili yadda kana shiga zaka hangota. Dama ita bata da shamaki da fita daga gida domin yardar da a kayi mata. Amma yanzu tasan dole ne sai ta iya taku domin bata so a san da fitar tata....📝

Love all

One love

One house

Love my fans

By S-Reza ✍️

Ina muka dosa new

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.