Free chapter · Read without an account

BABI NA GOMA SHA HUƊU

by Fareeda Abdallah · BA NI DA IKO...

BA NI DA IKO...

©Fareeda Abdallah

***

Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.

In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.

14)

Saukar ƙaƙƙarfan mari a kumatunta yasa maimakon ƙarashen maganar da take yi ya fito, sai ihun kuka ne ya zama ƙarashen. Kafin ta dawo hayyacinta ta gane wa ya mare ta aka sake gaura mata mari a ɗaya ɓangaren kumatunta.

Ramatu da take kwance akan ledar tsakar ɗaki tana ƙailula ihun kukan Zakiyya ne ya farkar da ita. Ta fito a gigice daga ita sai ɗaurin ƙirji, gefen bakinta dagaje-dagaje da miyaun barci.

Ta iso gurin a daidai lokacin da Binta ke ce ma Zakiyya da ta zube a ƙasa tana burgima da ihun kuka saboda azaba.

"Na ga alama kame kaina da nake yi a gidannan ba na shiga harkarku yasa raini ya fara shiga tsakanina da ke Zakiyya, ni sa'arki ce da zan tambaye ki dalilin marar min ƴa za ki tsaya kina min rashin kunya?"

"Marinta kika yi?"

Ramatu ta tambaya a haukace.

"Au marinta kika yi saboda ke azzaluma ce? Ai kuwa na rantse da Allah a jikinki zan rama mata."

Cikin zafin rai Ramatu ta ɗaga hannu za ta tsinka ma Binta mari sai ta ji saukar muryar Malam cikin tsawa yana cewa

"Kul! Kul!! Ahir ɗinki Ramatu! Wallahi duk ranar da kika yi gangancin kai hannunki jikin Binta zamanki ya ƙare a cikin gidannan. Tunda ba zamanki take yi ba..."

"Ahayye nanaye..."

Ramatu ta yi shewa tana tafa hannuwa.

"Eh lallai! Na yarda Goro na sa zawo. Ah tabbas sai yau na ƙara yarda Binta ta wanke ta baka ka shanye Malam. To ai ni baza ka burge ni ba, sai Binta ta sa ka yi min saki uku nan take, shi ne zan ƙara tabbatarwa lallai Binta ta gama da kai."

Bai ce mata komai ba, sai kama hannun Binta yayi, ita kuma tana riƙe da Humaira suka wuce zuwa ɗakinta.

"Aikin ɓur inji tusa! Zancen banza da na wofi. Ai Wallahi Binta duk baƙin cikinki na zame ma Malam ɗuwaiwai dole ya zauna da ni. In anyi duniya don Manzo SAW sai dai ki fita ki barni a gidannan."

'Ba Amin ba.'

Malam ya amsa a zuci.

Ta durƙusa ta kamo Zakiyya da tayi jiƙa jikinta sharkaf da ruwan wankan da ta zubar saboda burgima, tana share mata hawaye ta cigaba da yada ma Binta habaici cikin ɗaga murya.

"Taso mu je ƴar Inna... Baƙin cikinku take yi ta ganku ku shida rigis, ita kuwa sai ƴar guda ɗaya da aka gama ƙaryar namiji za'a haifa, aka gama yaudarar ubanku da cinye mishi tattalin arziki, a ƙarshe kuma sai ga shi macen dai da ba'a so ita aka haifa. Haihuwar ma da ta zo da rashin sa'a da mummunar asara, ai Wallahi kaɗan ma kuka gani, in Allah ya yarda ƴar nan da ake wulaƙanta mu ana gwada mana iyakarmu a kanta sai ta zame muku sila ta masifa da bala'in da baku taɓa zato ba."

"Ba Amin ba."

Binta ta amsa cikin ɗaga murya, hankalinta a tashe.

Har ta yi shiru, sai kuma ta kasa dannar zuciyarta ta sake cewa

"Da yaddar Allah bazan ga bala'i da masifa ba, sai dai ki gani a kanki da zuri'arki."

"Haba Binta."

Malam ya katse ta.

"Ke ma kina so ki zama ita kenan...?"

"To kai baka ji irin mummunar addu'ar da take ma Humaira bane?"

Ta katse shi cikin rawar murya.

"Da yaddar Allah Humaira za ta kasance ƴar albarka, abar alfahari ga kowa. Ba ita da ƴaƴanta kaɗai ba, in sha Allah mutanen ƙauyennan ma sai sun ci albarkacin Humaira."

"In sha Allahu."

Malam ya sake jaddada maganarta.

*******

"Kun dai ga kumatun Zakiyya ko?"

Ramatu ta faɗa tana nuna musu kuncin Zakiyya dama da hagu, har yanzu da aka ɗauki awoyi uku da faruwar al'amarin zanen yatsun Binta basu washe daga fuskarta ba.

"To wannan zanen yatsun ba na komai bane sai na mari, marin ma ba na kowa bace sai na Binta."

Aikuwa da sauri yaran gaba ɗaya suka ɗaga idanu suna kallon Innarsu. Idanunsu a warwaje, Zainab da zancen ya dake ta saboda abu ne da bai taɓa faruwa ba har sai da ta dafe ƙirji da hannu bibiyu.

Ramatu ta kallesu ɗaya bayan ɗaya, ta ga yadda suka ba ta hankulansu ɗari bisa ɗari, daman abinda take so kenan. Sai ta cigaba da basu labarin abinda ya faru cikin kururutawa da kambawa, kaso goma sha biyar gaskiya kaso tamanin da biyar ƙarya.

"Ƙwarai da gaske. Ku fa in banda Allah ya kiyaye ma ai da sai dai ku dawo gidannan ku tarar Babanku ya sake ni. Saki uku rigis!! Hmmmm!"

Ta ja wani nannauyan numfashi mai cike da takaici.

"Ai ni ina ganin ta kaina a gidannan. Tunda nake a rayuwata ina jin labarin asirai kala-kala Wallahi ban taɓa jin labarin irin mugun asirin da Binta tayi ma Malam ba.

Ta mallake shi tsaf! Baya ji ba ya gani sai Binta da ƴarta da duk wani abu da take so a gidannan. Ta raba ni da mijina, ku kuma ta raba ku da ubanku. Idan ba haka ba taya ma za'a ce ƙaramar sallah guda Malam yayi muku kaya kala ɗai-ɗai, ita kuma da ƴarta yayi musu kala shida shida?"

Ta tuno musu da labarin ƙaramar sallah da aka yi watanni biyu da suka wuce.

"Ku tuna dai irin caɗa-caɗan bulawusoshin da ƴarta tai ta sakawa. Mu kuwa tunda ya jefe mu da ƴar atamfar nan guda uku kunga ya ƙara mana tsinke? Ca nake ko kuɗin ɗinkin kayan da ke Zainab kika matsa aka kai gidan yarinyar nan Masrura saboda iya ɗinkinta ni na biya? To bari ku ji abinda ni ma sai kwanannan na sani, ɗinkunan Binta na sallah gaba ɗaya gurin Mustapha telan ƴan gayu aka kai. Kun san duk garin Kasuwar Magani mata sunyi ittifaki in dai kina so kiga an fitar miki da ɗinki tsaf kamar a Kaduna aka yi to lallai sai gurin Mustapha, daga shi kuma a ƙauyen nan sai gurin yaronnan Zahraddini, kun san ƙanin Mustaphan ne, kuma rainonsa ne a fagen ɗinki. Itama Masrura ƙanwar Mustaphan ce, shi yasa ɗinkunansu yake fita daban da na sauran telolin garinnan.

Safiya da take bani labari ta ce kuɗin ɗinkunan Binta guda uku kacal dubu goma sha huɗu haka Malam ya falle ya biya, saboda tsabar zalunci kuɗin atamfofin da ya mana gaba ɗaya ita shi ne kuɗin ɗinkunanta."

Tayi ƙwafa mai ƙarfi, sannan ta cigaba da zuga ƴaƴan tana ƙara hure musu kunne akan Binta da ƴarta Humaira.

"Duk inda kuka samu dama ku ci uban shegiyar ƴar nan tata da ja kamar jan ƙosai. Abinda jan nata ma mun san har da man bature ake ƙara mata. Ita ma Bintan na baku dama ku dinga mata rashin mutunci iri-iri. Ko kuna ganin akwai wata girmamawa ce da ta rage tsakaninku da wacce ta shiga ta fita ta raba ku da mahaifinku?"

"Babu Inna."

Suka amsa gaba ɗaya.

"Yauwa, kar ku wani ji tsoro... Ko da ta dake ku ai za ku rama akan ƴarta. Ke kuma Zainab da ke Zakiyya nan gaba kaɗan ma idan kuka ƙara girma ai Wallahi Binta tana yi muku wani gani-gani ku haɗa kai kuyi mata ribiti (Duka), ina daga gefe idan na ga za ta fi ƙarfinku har zan sa hannu mu ragargaji bakin banza a banza."

Sai da ta tabbatar tayi musu famfo iya famfo, sannan ta sallame su.

Yaran gaba ɗaya idan aka cire Zainab sun tashi ne a gaban Innarsu da burin fara ƙuntata ma rayuwar Humaira, a ko wace ƙanƙanin kafa da suka sami dama.

******

Sanannen abu ne a mafiyawancin ƙauyuka shekaru sha biyar sha shida in dai yarinya ta sami miji za su aurar da ita. Idan aka samu yarinya mai gaɓa-gaɓan jiki ma ko bata kai sha biyar ba, aka yi sa'a tana da farin jinin samari, tsaf! Suke aurar da yarinya babu ruwansu da wani abinda zai je ya zo.

A yanzu Zainab shekarunta goma sha Shida, Cikin sa'a kuma Allah ya kawo mata samari masu yawa, ai kuwa babu ɓata lokaci Malam ya bata damar fitar da wanda take so a cikinsu.

Auwal ta fitar, Ɗaya daga cikin ƴaƴan Alhaji Baballe, babban ɗan kasuwa a ƙauyen Kasuwar Magani, yaro ne mai hankali da nutsuwa, ga kuma Nasibi da Allah yayi mishi a cikin sana'arsa. Bayan gudanar da al'adar kawo kuɗin gaisuwa da kayan sa rana Malam ya tsayar da ranar aurenta watanni biyu masu zuwa.

Da yake makarantar boko ga ƴa mace ba wani abu ne da wasu daga cikin ƴan ƙauyen suka ɗauka da muhimmanci ba tun bikin bai matso kusa ba Zainab ta daina zuwa makarantar Day da Binta ce ta dage sai da Malam ya saka su ita da Zakiyya bayan sun gama primary, duk da dai Ramatu ba ta so a dole ta haƙura. Domin Malam ya yi mata jan ido, ya nuna mata lallai fa shi ne mai gida.

******

"Accanamu anaikum"

Humaira tayi sallama a ƙofar ɗakin Ramatu, da tsamin bakinta da hausa bai gama fita ba. Kallo ɗaya za'a yi mata a gane a tsorace take, hannunta riƙe da wani ɗan ƙaramin farin leda mai kyau.

Dawowarsu kenan daga Kaduna ita da mamanta. Duk da yanayin tsoron da ke cikin idanunta ta yi wani irin kyau mai ɗaukar ido. Yalwataccen gashin kanta anyi mata sabon kitson kalaba, ya sauka har kafaɗunta, an kame bakin ko wane kitso da bit manya masu kyau, an cire mata rigar jikinta saboda ta sha iska. Tana sanye da vest baƙi, da ɗan gajeren wandon jeans.

"Waye a nan?"

Ramatu ta tambaya cikin tsawa, duk da kuwa ta gane mai magana.

"Ni ce. Humaila."

Yarinyar ta amsa da sauri.

"Mamy na ce ta aikoni gulin Anty Dainab, ta ce wai ta duba watannan kyallan idan tunyi kyau ta kawo musu anko..."

"Dallah malama idan baza ki shigo ba ki koma. Kin ishi mutane da wani bakinki cwai-cwai kamar aku."

Zakiyya ta faɗa mata cikin tsawa.

Da sauri ta buɗe labulen ɗakin ta shiga ciki tana zazzare ido.

"Inna ina kwana."

Ta durƙusa har ƙasa ta gaida Inna.

Ranƙwashi mai ƙarfi Hadiza da ke zaune a bakin ƙofa ta sakar ma Humaira a kai

"Don uwarki ba ki da hankali ne za ki shigo ma mutane ɗaki ba sallama?"

A gigice Humaira ta buɗe baki za ta fasa ihun kuka, cikin sauri Zakiyya ta nuno mata almakashin da ke hannunta wanda take zuwa koyon ɗinki da shi ta ce

"Kina buɗe wannan tsattsaman bakin naki na rantse sai na yanke miki kunne. Haɗiye kukan nan!"

A tsorace tasa hannu biyu ta damƙe bakinta don hana ihun fita, duk da haka sai da wasu zafafan hawaye suka fara zubowa daga idanunta.

Sai ga Zainab ta fito daga cikin ɗaki tana tafe tinƙis-tinƙis irinna ƴanmata masu tasawa.

"Don Allah ku rage takura ma yarinyar nan..."

"Ki ƙyale su, an saki yarinya sakaka tana iskancin da taga dama ba dole su gyara mata zama ba?"

Ramatu tayi saurin katse Zainab, lokaci ɗaya tana aika ma Humaira Harara kamar idanunta za su faɗo.

"Uhmmm! Inna kenan. Zo nan kin ji Humaira."

A ɗarare ta ƙarasa gurin Zainab ɗin, duk da ita ma wasu lokutan tana cin ƙaniyarta amma ba kamar su Zakiyya da ƙarara suke nuna mata sun tsane ta ba.

"Yi haƙuri. Share hawayenki."

Zainab ta faɗa mata a tausashe, lokaci ɗaya kuma tana taya ta share hawayen da suka ɓata fuskarta.

"Me mamanki ta ce ki faɗa min? Ina saƙon da ta baki ki kawo?"

Can bakin ƙofa ta hangi ledar da ta zo da shi, jikinta na rawa ta je ta ɗauko ta miƙa ma Zainab ɗin, sannan ta sake faɗa mata abinda Mamanta ta ce.

Ko da Zainab ta ciro ƙyallayen da ke cikin ledar, ƙyallen atamfofi masu kyau ne guda uku, da ƙyallayen material guda biyu.

"Kai gaskiya duka sunyi kyau. Ki ce mata na gode, wai zan nuna ma Murja da Sadiya, wanda suka zaɓa sai ta ɗauko mana shi."

Da ɓacin rai a muryar Ramatu ta ce

"Ke ma dai Zainab na rasa gane irin wannan shisshigi da cusa kai da kike ma Binta tunda bikinnan ya matso. Yanzu duk kyawawan atamfofin da ake kawo su kasuwa ranar alhamis ku rasa wanda za ku zaɓa ki fitar da Anko sai Binta ta zaɓo muku daga Kaduna?"

"Ke ma dai kya faɗa Inna. Ni idan nayi magana cewa take na rainata."

Zakiyya ita ma ta tofa albarkacin bakinta.

Ita dai Humaira sum-sum ta fice daga ɗakin, hannunta ɗaya na kanta tana sosa inda aka ranƙwasheta da har lokacin yake mata raɗaɗi.

"Hmmm! Ke baza ki gane bane Inna. Amma dai bari inyi miki gwari-gwari."

Zainab ta faɗa da murmushi a fuskarta, bayan ta tabbatar Humaira ta yi nisa da ɗakinsu.

Sai kuma ta je ta zauna kusa da Ramatu. Da murya ƙasa-ƙasa ta cigaba da magana

"Ke dai Inna kin san in za mu faɗa ma kanmu gaskiya mun san duk gidannan Binta ta fi mu wayewa, da sanin kayayyakin ƴan gayu. Wannan dalilin yasa nake so in samu mu daidaita da ita ko don ta tilasta ma Baba yi min kayayyakin ɗaki masu kyau da tsada. Ni fa Wallahi da za ki amince ma Inna har kayan kicin da za ki siya min da ita kika ba kuɗin ta siyo min..."

"Wannan ne kuma baki isa ba."

Ramatu ta katse ta a fusace

"Kin ci ƙarya, kin kwana da yunwa yarinya. Ni da kuɗina? Ke har kin isa ki ce min ga abinda zanyi? Bintan banza, wayewarta na banza da wofi. Ashe ma na zama sakarya kenan idan har sai na ba kishiya kuɗin siyayyar kayan auren ƴar da na haifa a cikina, ni miye amfanina da tarin ƴan'uwa mata da ƙawaye da Allah ya bani. Kin ga mu bar ma wannan zancen banzan. Kar ki sake min irin wannan maganar, ba na so."

Tura baki Zainab tayi, ta miƙe ba tare da ta sake cewa komai ba ta wuce cikin ɗaki, gaf da za ta shige ne ta ja tsaki mai ƙarfi.

Da mamaki Zakiyya ta ce

"Lalalala! Inna kina jin abinda tayi? Tsaki fa tai miki..."

"Na rantse da Allah idan baki fita daga harka ta ba sai na miki matsiyacin duka a yammacin nan. Ni sa'arki ce? Ina ruwanki da ni?"

Zainab da ta juyo a fusace tayi maganar tana nuna Zakiyya da yatsarta manuniya.

"Ƙyale ta Zakiyya, rabu da ita. Kin san ta kusa aure, gani take yanzu ita daidai take da ni. Kuɗin siyayya ne dai bazan ba Binta ba, ni da Safiya za muje muyi mata siyayyar kayan ƙauyawa. In yaso bayan buki ta zubar da abinda muka danka mata a ɗaki."

Fuuu Zainab ta shige ɗaki kamar za ta tashi sama.

******

Da tausayi a fuskar Binta take share ma Humaira hawayen da suke ta zuba a idanunta bayan ta gama ba ta labarin ranƙwashin da Hadiza tayi mata a ɗakin Ramatu.

Bayan ta gama share mata hawayen ne ta ɗauko man zafi ta shafa mata a gurin ranƙwashin da tace yana mata zafi, ta ɗauko paracemol na ruwa ta bata. Sannan ta buɗe mata ɗaya daga cikin ledar Cizi da ta siyo mata jakarshi a kaduna.

"Kiyi haƙuri kin ji Mamana? Ki ƙyale su, Allah yana tare da masu haƙuri. Mai haƙuri yana dafa dutse har yasha romonsa, kuma mai haƙuri yana cimma rabo. Ki ƙara haƙuri da ƴan'uwanki, wata rana sai labari. Kin ji ko Mamana?"

"To Mamy."

Ta amsa a hankali, duk da wasu maganganun sunyi ma ƙwaƙwalwarta girma, matsayinta na yarinya ƴar shekara uku.

Tana gama cin Cizin tayi barci, a hankali Binta ta kwantar da ita akan dadduma kusa da ita. Ta ƙura ma yarinyar ido, zuciyarta cike da tunanin yadda yarinya ƙarama ta ratso ta cikin wannan mummunan ƙaddara da bata san ranar da zai zo ƙarshe ba.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.