Free chapter · Read without an account
BABI NA GOMA SHA TAKWAS
BA NI DA IKO...
©Fareeda Abdallah
***
Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.
In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.
18)
Karɓan kuɗin siyayyar kayan ɗakin Zainab da aka yi a hannunta ba ƙaramin daɗaɗa mata zuciya yayi ba. Dama tun farko ta karɓi kuɗin ne da nufin idan an kwana biyu Malam ya huce, za ta nunar mishi da illar da ke tattare da ace ita ce ta jagoranci siyayyar kayan, kuma ba tare da amincewar uwar ƴa ba. A yanzu da aka yi haka sai ta ce a ranta
"Ta fi nono fari."
Zancen anko ma da a farko tayi niyyar ɗauko ma Amarya da ƙawayenta bayan sun zaɓi ɗaya daga cikin ƙyallayen atamfofin da ta kawo musu, ta buƙaci duk wacce take so ta kawo ɗaya bisa uku na kuɗi kafin ta siyo, ko da taga suna neman yi mata yawo da hankali bayan ita kuma tsabar kuɗinta za ta narka ta siyo sai kawai ta ce musu ta fasa ɗauko ankon, su siya a kasuwa ranar alhamis.
"Haba Anty, don girman Allah kiyi haƙuri. Ni da kaina zan haɗa miki kuɗaɗenki gaba ɗaya idan kika saro zannuwan, wannan alƙawari na ɗauka miki."
Zainab tayi maganar a marairaice.
Binta tayi dariya kawai, kamar baza ta tanka ba sai kuma ta ce
"Kiyi haƙuri Zee, Wallahi da gaske na fasa ɗauko Ankon. Ba kuma don ba kuɗi ba, haka kawai tunda suka ƙi bada Deposit na ji hankalina bai kwanta da al'amarin ba. Kin ga kuwa an ce ka bar abinda kake kokwanto zuwa wanda ba ka kokwanto."
Suka yi dariya gaba ɗaya.
Zainab ta karkace za ta cigaba da mata magiya ta katse ta da cewa
"Ina zuwa, bari ki ga tanadin da na fara yi miki."
Cikin ɗakinta ta shige, can sai ga ta fito da leda mai zane-zane a hannunta.
A kan kujera ta zazzage kayan da ke cikin ledar, ta fara ɗaɗɗaga kayan ɗaya bayan ɗaya. Kayan turawa ne na gwanjo, amma fa masu kyau sosai grade 1, in ba sani akai ba ma baza a taɓa cewa gwanjo bane.
"Tunda na ji Malam ya ce baza ki zauna a gidan Gandu ba na ce to bari in miki ƴan tanade-tanade a matsayina na ƙaramar uwa."
Suka sake yin dariya a karo na biyu.
"Tabbas Kunya ado ne a gurin ɗiya mace. Amma tsakaninki da mijinki ko za ki nuna kunyar to fa lallai cikin salo da wayewa za ki nuna. Ire-iren waɗannan kayan da kike gani idan mace tayi kwalliya da su a cikin gidanta ga mijinta kaɗai ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa take yi ba.
Kuskuren da mafiyawancin yara matan ƙauyen nan ke yi shi ne sai su dinga saka ƙananun kaya da sunan kwalliya ga miji, amma sai su dinga yawo da kayan a gaban surukansu, ba tare da wani jin kunya ba.
Shi yasa surukan suyi ta yamaɗiɗi da su suna cewa ai yaran yanzu ba su da kunya, idan aka sami iyaye marasa haƙuri kuwa kai tsaye suke umartan mijin ya hana matarsa saka ire-iren kayan, ko kuma su su kwaɓa mata ta daina irin wannan shigar kar ta lalata musu tarbiyar ƙananun ƴaƴansu. Amma kinga ke tunda gidanki ke kaɗai ce, za ki iya yin kwalliyarki daga ke sai mijinki. Idan kika ji sallamar baƙi za su shigo ki saka babban hijabi."
"Allah ya saka miki da alkhairi Anty."
Zainab ta faɗa cikin farin ciki, ɗaya bayan ɗaya take ɗaga kayan, bakinta kamar zai yage don fara'a.
"Wallahi Anty Kamar kina duba... Satin da ya wuce fa yake faɗa min yana so yasa kayan turawa a akwati Innarsa ta ce bazai janyo musu abin magana ba..."
"Abin magana kuma? Wani irin abin magana?"
Binta ta katse ta da mamaki a fuskarta.
"Cewa tayi fa wai kar masu ganin kayan akwati suyi ta cewa ɗan gidan Liman guda da zuba kayan ƴan iska a kayan aure."
Binta ta ƙyalƙyale da dariya.
"Gaskiya har yanzu da sauranmu a ƙauyennan. To Wallahi a Kaduna akwati guda wasu masu kuɗin ma akwatuna biyu suke shaƙe cikinsu da kayan turawa. Kin san su birni ba ruwansu, daga mazansu har matansu, musamman matan, sun saka ma zuciyarsu da namiji yaga mace a waje ta matse ta tsuke tana juya mazaunai gara suyi a gida mazan su kallah..."
Sai kuma ta katse maganar tayi saurin dafe baki
"Oh! Kin ga mu bar wannan maganar ma, tunda dai har yanzu baki shiga daga ciki ba..."
A kunyace Zainab ta ce
"Kai Aunty..."
"A'ah kai Aunty ko gaskiya?"
Binta ta katse ta tana dariya.
Sai kuma ta zauna a kusa da Zainab ɗin, ta rage murya sosai ta fara warware mata zare da abawa na rayuwar aure, da yadda ake tarairayar miji cikin nutsuwa ba da hauka ba. Abinda ta san da wuya idan Ramatu za ta iya zama ta warware ma Zainab ɗin.
A ƙarshen duk maganganunta ne ta rufe da cewa
"Shi dai zaman aure da kike ji da gani manyan makamai biyar da za ki riƙe ki haura tudun mun tsira cikin sauƙi su ne: Gaskiya, Jin tsoron Allah, Haƙuri, riƙon Amana, sai kuma uzuri ga abokin zama. Idan kika riƙe waɗannan in sha Allahu ko za ki wahala a cikin aure tabbas wahalarki za ta zo da sauƙi. Domin abubuwa da yawa da za'ayi don a cusguna miki a baƙanta miki sai Allah ya sassauta abin a idanunki da kunnuwanki, sai ki kalle shi a ba komai bane. Idan kuwa aka nufo ki da wani babban cutarwa daga miji, danginsa, iyayensa, abokansa, ko ƙawayenki kina daga zaune Allah zai tare miki wannan cutarwar."
Shiru Zainab tayi, ta dafe kumatu da hannu bibiyu tana kallon Binta. A zuciyarta take tunani ita kuwa Binta wace irin macece haka mai saka alkhairi da sharri? A bayan duk irin cutarwar da Innarsu ke mata, a bayan duk irin fitsarar da suke mata, bayan duk irin zaluntar ƴarta da suke yi, yanzu ta zaunar da ita tana tsage mata gaskiyar da ko mahaifiyarta bata taɓa faɗa mata ba tunda maganar aurenta ya taso...
"Ki yafe min don Allah Anty Binta."
Ta katse tunaninta da faɗin haka cikin rawar murya.
"Yafiya kuma?"
Binta ta tambayeta da mamaki.
"Kinyi min wani abu ne ban sani ba?"
Ta sake tambayarta a karo na biyu.
Ta sa babban yatsarta ta ɗauke hawayen da suka taru a kwarmin idanunta.
"Gani nayi duk yadda nake yi miki raini a wasu lokuta, da yadda nake cin zalin Humaira idan na sami dama duk da haka baki ƙullace ni ba, kika zaunar da ni kina faɗa min hanyoyin da zan bi in gudanar da rayuwar aurena cikin sauƙi. Don Allah ki ce kin yafe min..."
"Wallahi Allah kenan ko? Ban taɓa riƙe ɗaya daga cikinku a zuciyata ba. Ni kin san ma ba ni da rufi, duk sadda kuka yi min abinda bai gamshe ni ba zan lallasa yarinya ne kai tsaye."
Ta ƙarasa maganar tana dariya.
Ita ma Zainab dariyar tayi, bayan ta tuna wani gigitaccen mari da Bintan ta taɓa yi mata wani lokaci can baya da ya wuce. Kawai don ta aike ta ita kuma ta ce baza ta je ba, bayan haka kuma sai ta tsaya tana mata ƙunƙunai. Ai kuwa ƙaƙƙarfan marin da Binta ta sakar mata saboda tsabanin azaba bata san sadda ta saki fitsari ba.
Ta sake yin dariya a karo na biyu. Ta buɗe baki za tayi magana sai jin muryar Humaira suka yi tana sallama a ƙofar ɗakin, ta dawo daga yini, gidan Kawun Bala.
Dalilin da yasa suka bar hirar da suke yi kenan, suka mayar da hankalinsu kan Humaira, suna yaba ƙunshin da aka yi mata a yinin da ta je, baƙin ƙunshin da aka saka ma taki ya yi kyau sosai a fararen ƙananun ƙafafunta.
******
"Innanmu unguwa za ki je?"
Zakiyya ta tambayeta, tana kallon Ramatu ganin yadda ta sha kwalliya, a daidai lokacin kuma Ladan ya kwaɗa kiran sallar magriba a babban masallacin unguwar.
"Laaa.. Inna zan biki."
Hadiza da ta kasance auta ta faɗi haka, lokaci ɗaya ta tsame hannunta daga cikin kwanon tuwon da take ci ta fara suɗewa.
Sauran yaran ma da basu yi magana ba duk bin ta suka yi da idanu, sun buɗe kunne suna jiran ta faɗa musu unguwar da za ta je.
Lokaci ɗaya Ramatu ta tamke fuska, duk yanayin da ta shiga na farin cikin kyawun da tayi, ga sabbin kaya ta saka, ga uban humra ta bulbula a jikinta tana baza ƙamshi nan da nan ranta ya ɓaci saboda kalaman yaran. Ta kalli Zakiyya ta hurga mata harara
"Wani irin iskanci ne haka? Babu damar mutum yayi kwalliya sai za shi unguwa...?"
"To Innarmu kwalliyar ce fa ba yi kike yi ba sai za ki unguwa, unguwar ma ta masu ƙarari, kin ga kuwa ai dole mu tambaya idan kika yi kwalliya."
Ta ƙarasa maganar tana murguɗa ma Ramatu baki kamar ba uwarta ba.
Da masifaffen fushi ta buɗe baki za ta antaya ma Zakiyya bamagujiyar zagi, sai ga Zainab ta shiga ɗakin da sallama, Kawai sai ta huce haushin a kanta.
"Yanzu Zainab duk irin tanadin da nake yi a kanki ni za ki wulaƙanta ko? Ni ce za ki zaɓi maƙiyiyata a kaina ko?"
Sai kuma tayi raɓa-raɓa da fuska kamar za tayi kuka don takaici, sannan ta cigaba da cewa
"Tun yaushe nake aiken Zakiyya ta kira min ke a ɗakin wancan munafukar kina cewa baza ki zo ba?"
"Ni kika aiko a kira ni Inna? Ni?"
Zainab ta tambayeta da mamaki.
Kafin ta amsa Zainab ta cigaba da magana
"To na rantse da Allah babu yarinyar da ta zo tace kina kirana."
Sai kuma ta juya kan Zakiyya a fusace ta fara mata titsiye
"Ke Zakiyya don ubanki da yaushe kika zo kika faɗa min saƙon kiran Inna?"
Da yake kusan kullum Zakiyya cikin haushin Zainab take, nan da nan ta hayayyaƙo mata kamar ita ce babba
"Ah ni fa Zainab kar ki wani ce ban zo ba. Atoh! Kuma Wallahi ba dai ubana ba..."
A fusace Zainab ta ɗaga hannu za ta mauje ta Ramatu tayi saurin tarewa tana sallallami.
"Shi kenan! Shi kenan! Ni kam na ga ta kaina na shiga uku!! Binta ta raba ni da mijina yanzu kuma ta juyo za ta farraƙa min kan ƴaƴa. Inna lillahi..."
Sai kawai ta duƙe a gurin tana matsar ƙwallah da sakin numfarfashi sama-sama.
Sai kuma jikin Zainab yayi sanyi, dama tana lure da Innar tasu tun a wancan daren da ta jiyo abinda ya fi ƙarfin kunnuwanta a turakar Malam, yanzu da zaran wani abin tashin hankali ya faru da ita sai ta dinga jan numfashi sama-sama. Tsoronta Allah tsoronta ace wani ciwon ne zai kama Innarsu. Da sanyin murya ta ce
"Kiyi haƙuri Inna, Zakiyya ce ba ta da kunya, kina ganin irin rashin kunyar da take min, amma in Allah ya yarda bazan sake biye mata ba. Sannan kuma na faɗa miki ki daina damun kanki da zancen Binta. Ke kinsan ko haukacewa nayi babu yadda za'ayi in zaɓi maƙiyiyarki a kanki. Allah ya baki haƙuri."
Tana gama faɗin haka bata jira cewarsu ba ta shige ɗaki da sauri, idanunta ciccike da hawaye.
Duk zuciyarta babu daɗi, sabida ire-iren munanan maganganun da ako yaushe Innarsu ke faɗa a kan Binta, bayan kuma a zahirin gaskiya ita sai a yanzu da ta cire son zuciya ta gane sam ba haka Binta take ba.
Da yake ta yi alwalar sallar magrib tun a ɓangaren Binta, kawai sai ta watsar da tunanin komai ta shimfiɗa sallaya ta kabbarta sallah.
******
Baki buɗe ya bi ta da kallo, kamar bazaiyi magana ba, sai kuma ya karkace kai da murmushi a fuskarsa ya ce
"Ramatu? Wai ke ce haka?"
Ga mamakin Malam kawai sai yaga ta sunne kai, a kunyace. Ai kuwa mai zaiyi ba dariya ba? Ya kuwa buɗe babbar muryarsa ya dinga ƙyaƙyatawa yana kallonta yana nuna ta da yatsarsa manuniya har sai da Ramatu ta ji babu daɗi.
Ai kuwa ta ɗaure fuska tamau, daga ƙarshe ma a fusace ta miƙe za ta bar turakar da hanzari ya riƙo ta. Da ƙyar ya iya tsagaita dariyar da yake yi, idanunsa cike da hawaye.
Ya zaunar da ita a gefensa yana sake ƙare mata kallo.
"Kuma fa Wallahi kin yi kyau ba kaɗan ba Ramatu."
Ya faɗa da zallar gaskiyarsa.
Duk da yadda zuciyarta ba daɗi saboda dariyar da yaita mata da farko, haka ta daure tayi murmushi.
"Amma don Allah me yasa kika daina yin kwalliya?"
A bazata tambayarsa ya sauka a kunnuwanta.
Ta daɗe cikin shiru, a zuciyarta take laluben amsar da za ta bashi. Can sai ta ce cikin sanyin murya.
"Ina yin kwalliya fa Malam, kawai dai ba ka lura ne."
"Ki dinga yin kwalliya irin wannan. Kina yin kyau, da ba kya kwalliyar nan sai tsufa ya sauka miki gaba ɗaya. Amma yau ji yadda kika yi kyau, har wani ƙoƙon nono kika sa don gayu Ramatu."
Ya ƙarasa maganar yana taɓo na shanunta da kallo ɗaya yai ma ƙirjinta ya gane ta saka bireziya, saboda idan bata saka ba duk da nonuwan a cike suke, suna sauka ƙasa ne har gurin cikinta.
Tsam tayi da rai tana tunanin yaushe ma rabon da ta saka rigar nono? ita da kanta ta kasa tunawa. Yau ma da ta saka Yaya Luba ce ta bata kyautar guda uku a kwalemar kayan da tayi mata, ta kuma jaddada mata lallai duk sadda tayi kwalliya ta tabbatar ta saka nonuwanta a cikin rigarsu, idan ba haka ba kuwa kwalliyarta baza ta taɓa fita yadda ake so ba.
"Ki daina barin nonuwanki na sauka har ciki shirim kamar ƙaramin bokitin penti..."
"Ku ji Yaya Luba da wani zance."
Ta katse ta
"Duk saukarsu dai ai ƴaƴansa ne suka janye nonon suka kwanta har ciki."
"Ko shi da kanshi ya shanye nonon bai zama hujjar da za ki bar ɗaya daga cikin abubuwa ukun da ke fara jan hankalin namiji zuwa mace a wulaƙance ba."
Yaya Luba ta amsa mata.
Kamar wasa kuwa tayi amfani da shawarar ta saka, ga mamakinta kuwa sai gashi har Malam yayi magana a kai. Ajiyar zuciya ta ja ta sauke, a sanyaye ta sake shayar da shi mamaki ta hanyar cewa
"In zuba maka abincin ne?"
"Zuba min kaɗan."
Ya amsa yana jifanta da murmushi. Duk da bai jin yunwa, haka kawai sai ya kasa tankwaɓe ƙoƙarinta na sabon tarairayar da ta tsiro mishi da ita a daren.
Ya ci tuwon tana jan shi sama-sama da hirar bikin Zainab shi kuma yana amsa mata, har ya cinye wanda ta zuba mishi gaba ɗaya."
Wani abu da ya lura a daren shi ne kamar kaffa-kaffa take yi don kar ta ɓata mishi rai, shi kuma sai ya taya ma ƙoƙarinta. Har suka kwanta lafiya ƙalau, kamar dai ba ita ce Ramatunnan da tunda ya ƙaro aure duk sadda ya nufi gabas ita sai ta nufi yamma ba.
******
Kwanci tashi asarar mai rai, kuma ko me aka saka ma lokaci lallai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba. Sai ga bikin Zainab ya zo, har ana jibi ɗaurin aure. Kuma a wannan ranar ne bisa jagorancin Yaya Luba suka tafi Kaduna, can da yamma suka iso gidan niƙi-niƙi da kayan ɗakin Zainab.
Kayan da kallo ɗaya za ayi musu a gane sun fi karfin kuɗaɗen da Malam ya bayar. Gudumuwar Yaya Luba da ƴaƴanta gaba ɗaya a cikin kuɗin kayan ta zuba, bayan ta faɗa ma Ramatu ga abinda suka haɗa na gudummuwa.
Duk yadda Safiya taso tayi uwa tayi makarɓiya a gurin sayen kayan kicin da tun farko ita Ramatu ta damƙa ma kuɗin hakan ya gagara samuwa. Luba ta tare gaba da baya, ta ci burin ta samu rabonta, amma abin ya gagara. Yaya Luba ta kankane komai ta hana ta rawar hantsi.
Ai kuwa Yaya Luba ta sha zagi da tsinuwa a zuciyarta. Daga baya ma da gagara dannewa guri ta nema ta zauna, ta fake da ciwon kai. Har aka ƙarasa siyayyar bata motsa ba. Suna komawa gida da motar siyayyar da suka yi ta tattare ƴaƴanta ko abinci bata tsaya ta ci ba ta wuce gida.
"Toh faa! Ita kuma Safiya me aka mata?"
Ramatu ta tambayi Sakina ƙanwarta da har da ita aka je siyayyar.
"Ohon mata. Tun a Kaduna na ga tana ta wani ciccin magani ba'a yi mata komai ba. Yaya Luba ce ma naji tana tambayarta me ya faru, ta ce kanta ke ciwo. Ni da na fi ta iya duniya kuwa banza na ba ajiyarta na cigaba da harkokina."
"Allah ya kyauta."
"Amin."
Ramatu suna hira da ƴan'uwanta a can ƙuryar ɗaki sai ga Binta ta shiga da sallama a bakinta. Akan idanun Binta biyu daga cikin ƴan'uwan Ramatu da ita kanta suka haɗa idanu da juna suka yi gyatsine, sai kawai ta murmusa, kamar bata gani ba.
Manyan kwalaye guda biyu da ke riƙe a hannuwanta ta ajiye sannu a hankali a tsakar ɗakin. Ta duƙa a ladabce ta gaishe su cikin jam'i.
Yaya Luba da tsiraru daga cikinsu suka amsa a mutunce. Da yake Binta ta san duk cikin ƴan'uwan Ramatu Yaya Luba ce kaɗai ba ta da gutsuri tsoma, don haka ta matsa da kwalayen kusa da ita tana cewa
"Yaya ga tawa gudumuwar ba yawa. Ayi haƙuri, Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya."
"Ah ma sha Allahu!"
Lallai ƙaramar uwa ta fito."
Yaya Luba tayi maganar da dariya tana buɗe ɗaya daga cikin kwalayen.
"Allah ya saka da alkhairi Binta. Ubangiji Allah ya ƙara buɗi. Ramatu kun gani?"
Ta ƙarasa maganar tana nuna musu set ɗaya na kular da ta ciro.
"Lallai, an gode."
Ramatu ta faɗa a taƙaice.
Jikin Binta sanyi ƙalau ta ja ƙafafunta ta fice daga ɗakin. Tun kafin tayi nisa ta fara jin muryar Ramatu tana gatsa mata baƙa.
"Aikin banza da wofi. Ko rantsuwa nayi ba kaffara na tabbata waɗannan kulolin da kuɗin Malam ta siya. Mun san komai fa..."