Free chapter · Read without an account
BABI NA GOMA SHA TARA
BA NI DA IKO...
©Fareeda Abdallah
***
Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.
In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.
19)
"Ki ji tsoron Allah Ramatu."
Yaya Luba ta katse ta da ɓacin rai a fuskarta.
"Zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya."
Ta sake faɗa, tun kafin Ramatu da ta cukwuikwuiye fuska ta bata amsa.
"Ah ba fa wani zato a wannan maganar Yaya Luba. Gaskiya ce na faɗa, abu ne da ya sha faruwa a kunne na ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba."
Tayi ƙwafa mai ƙarfi.
"In dai wannan sumumu kasau ɗin ce ke har ma kya yi mamaki idan na ce ga abinda ta yi? Ai sharrin Binta ya wuce duk yadda kike tsammani..."
Tsam! Yaya Luba ta miƙe daga zaunen da take. Hijabinta da ke rataye a ƙofar Ramatu ta ɗauka ta saka a jikinta.
"Allah ya kyauta, ni kin ga tafiyata. Amma dai tabbas ina ƙara gargaɗinki akan ire-iren waɗannan maganganun da kike yi marasa amfani masu zubar da mutuncinki a cikin mutane. Ita dai Binta idan za mu cire ma kanmu son zuciya za mu san lallai ta yi abin a yaba mata. Kishiyoyi nawa ne idan sha'ani ya kama abokan zamansu ko tsinke ba sa iya bayarwa? Ai Binta ko da kuɗin Balarabe tayi wannan siyayyar ta kai jarumar mace a gurina. Amma tunda ke bata burge ki ba, kina iya haɗa kulolin guri ɗaya ki ba Sakina ta miƙa mata ɗakinta da cewar ba kya so..."
"Allah ya baki haƙuri Yaya Luba, abin duk bai kai haka ba."
Rahane da suke ɗaki ɗaya da Ramatu tayi saurin faɗa tana ɗan dariyar yaƙe.
Wani kallo ta aika musu kawai saboda takaici, ta kama hanyar fita daga ɗakin bayan ta yi tsaki ƙasa-ƙasa, ta kasa ce musu komai don baƙin cikin halayensu na rashin faɗa ma junansu gaskiya.
"Yaya Luba tafiya za kiyi?"
Sakina ta tambayeta da sauri.
A niyyarta yadda ta miƙen tafiyarta gida za tayi, amma wani tunani da tayi yasa ta cewa
"A'a! Ɗakin Binta zan je in bata haƙuri, domin na tabbata kunnuwanta sun kwashe mata mugayen kalaman da Ramatu tayi a kanta tun kafin tayi nisa."
"Gaskiya ya kamata a bata haƙuri. Barin zo in raka ki."
Da sauri Sakina ta miƙe ta bi bayan Yaya Luba zuwa ɗakin Binta.
Ko da suka shiga, sun tarar da ita ne tana sallah. A kan kujerarta kuma ga Ankon ɗinkin Shadda nan da aka yi aiki mai bala'in kyau a ajiye.
Ɗinkin Doguwar rigar da alamun ta Binta ce, ga ta nan an warware karin gugar da aka yi, da alamun an ɗaga rigar an duba ɗinki da aikin da aka cancaɗa ne tun daga wuyan rigar har ƙasan rigar. Sai kuma wata doguwar rigar shadda ƴar ƙarama daidai Humaira, ita ma anyi mata aiki mai masifar kyau irinta babbar rigar.
A gefe guda kuma ga malum-malum itama ta sha aikin wuta, sai dai ba'a warwareta ba, a goge take tsaf, ga alamun riga da wando ƴar cikin babban rigar nan ajiye a ƙasan babban rigar. A hannun kujera kuma an ajiye hular dara mai kyau, wacce ta shiga sosai da aikin da ke jikin shaddar.
Da sauri Sakina ta sake kallon Binta, ko da taga ta yi sujada sai tayi saurin ɗaga ɗinkunan tana kallo ɗaya bayan ɗaya. Ta kallah, ta ƙara kallah, sai kawai ta kama haɓa alamun mamaki. A zuciyarta take ƙiyasta tsadar shaddar, da tsadar aikin da ke jikin shaddar, ta jinjina kai. Ta kalli Yaya Luba da take kallonta ita ma, ta nuna mata rigar da baki, irin tsegumin nan, sai taga Yaya Luba ta gallah mata harara ta zaro mata ido.
Ai kuwa da sauri ta aje rigar, a daidai lokacin kuma Binta ta sallame sallar da take yi. Ta juyo da fara'a a fuskarta tana kallonsu. Da girmamawa sosai a muryarta ta gaishe su.
Bayan sun amsa, Yaya Luba ce ta fara mata magana a tausashe.
"Binta mun zo ne mu baki haƙuri akan abinda ya faru ɗazu, don Allah kiyi haƙuri. Kin dai san halin mutuniyar taki, don haka nake roƙon ki ƙara cin maganin zama da ita. Don Allah ko me za tai miki ki taimaka mana har a gama taronnan lafiya ba tare da kin biye mata ba, don girman Allah kiyi mana wannan alfarmar."
"Laaa... Wallahi babu komai Yaya Luba."
Binta ta yi maganar har lokacin murmushin fuskarta bai ɓace ba.
"In Allah ya yarda ni kam daga ɓangarena babu abinda zai faru. Allah ya sanya alkhairi, Allah yasa taro ya tashi lafiya."
"Amin ya Allah."
Sakina da Yaya Luba suka amsa.
Har sun miƙe za su tafi Binta ta dakatar da su. Cikin ɗakinta ta shiga, ledar saƙon da Maman Fati ta ba direba ya kai mata ɗazu ta kwance, akwai cincin mai yawa da ta saka aka yi mata, shi ta ɗiba musu a faranti ta kai musu.
"Allah yayi albarka Binta. Mun gode, bari mu je da farantin idan mun gama zan aiko miki da shi."
"Amin ya rabbi. To Yaya, na gode."
Har sun kusa fita daga ɗakin Binta ta ce
"Yaya idan akwai aiki don Allah ko ban fito ba ki aiko min."
"To Binta. Sai na aiko."
Suka fice daga ɗakin.
Suna hanya Yaya Luba sai yaba halayen Binta take yi, ita dai Sakina sai uhm da uhm wai uwar gulma ta yi cikin shege. Duk ta ƙosa su isa ɗakin Ramatu, ta samu keɓewa da ita don tattauna wata muhimmiyar magana.
*******
Ya ɗaga shaddar, ya juya, ya sake juyata, duk da ba wani sanin tsadar shaddodi yayi ba wannan ko daga kallonta a ido ya san za tayi tsada. Sai ya mayar da idanunsa kan Binta, jikinsa a sanyaye ya ce
"Yanzu Binta duk wannan galleliyar shaddar tawa ce?"
Sai da tai masa fari da idanu sannan ta amsa da
"Ƙwarai kuwa Abban Humaira. Ta ka ce, ga hula, ga kuma takalma nan a gabanka. Gudumuwata ne a gare ka, kayi haƙuri babu yawa..."
"Wannan ne kike cewa ba yawa?"
Ya tambayeta.
"Mai yawan kenan Binta. Na gode Na gode. Allah yayi miki albarka." Duk da dai nima na sayi yadin da zan saka ranar ɗaurin aure, In sha Allahu wannan shaddar zan saka a ranar."
"Ka ga shi kenan sai muyi anko. Dama na ɗinka mana ne ni da kai da Humaira. Ita kuma Innarsu Zainab sai na siya mata Kuloli seti biyu na ba ta gudumuwa..."
"Munafuka algunguma. Matsiyatan kulolin da kika bani su ne har kike da bakin shelantawa kin bani kula?"
Ramatu da isarta ƙofar ɗakin kenan saɗarar ƙarshe na maganar Binta ya shiga kunnenta kawai sai ta faɗa ɗakin a haukace tana faɗin haka.
Kallo ɗaya Binta tayi mata ta gane a matuƙar fusace take. Kawai sai ta sauke kanta ƙasa, ta fara tattare kayan da nufin ta shige da shi ɗakin barcin Malam.
Tana fara tafiya Ramatu ta janyo ta baya da ƙarfi, aikuwa ta tafi taga-taga za ta faɗi Allah ya taimaketa ta faɗa kan kujerar kusa da Malam.
Da sauri Malam ya miƙe tsaye, hankalinshi a tashe ya ce
"Ramatu? Kin yi hauka ne? Miye haka kike yi?"
Yai mata tambayoyin da fushi a muryarsa.
Gajiya ce ba ƴar kaɗan ba a jikinshi. Tun safe da ya fita bai dawo gidan ba sai yanzu, ya yini a gona yana aiki. Ko da ya shigo cikin gari yana son dawowa gida amma bai dawo ba saboda ya san gidan cike yake da dangin Ramatu.
Haka yai ta rara gefe a masallaci har sai da duhu ya shigo, shi ne fa ya lallaɓa ya shigo gidan. Wanka kawai yayi ya ci abinci, sun fara hira kenan Binta tana nuna mishi kaya sai ga ta ta shigo tana neman ɗaga musu hankali.
"Hmmm! Ga doki har doki amma ƙafar na sakaina."
Tayi maganar tana nuna shi da hannunta daga sama har ƙasa.
"Jibe ka dai Malam. Babu wanda zai kalleka a haka cikakken mutum ya ce za ka iya karkata ɓangaren mace ɗaya ka bar ɗaya, don tsananin zalunci da son zuciya irin na shaiɗaniyar da ka auro."
Ta ja dogon tsaki kamar bakinta zai taɓa ƙasa.
"Ai sai ki je kiyi tayi Binta, daɗin abin gida biyu ne, bayan duniya akwai lahira. Za mu haɗu a inda tsafi da muggan asiranki baza su taɓa yin tasiri ba."
Ta ɗan tsahirta ta mayar da numfashi
"Zuwa nayi in karɓi tawa shaddar cin bikin da ka ɗinka muku kai da ita da figigiyar ƴarta, ni da ƴaƴana kuma ko oho!"
Da mamaki yake kallonta, duk da ransa yayi mugun ɓaci da irin cin mutuncin da tayi masa sam bai nuna mata ba.
"Waye yace miki ni na ɗinka mana shaddar cin biki?"
"Au!"
Tayi gyatsine
"Har ma sai an faɗa min? Haba Malam! Wani dare ne jemage bai gani ba...?"
Da sauri ya katse ta.
"Tambaya ɗaya nayi miki, idan kuma baza ki amsa ba don girman Allah ki fice min daga nan tun kafin rayukanmu su ɓaci. Wa ya faɗa miki ni na ɗinka mana shaddar cin biki?"
"Da idona na gani."
Ta amsa tana wulƙita idanu.
"Inda ba ƙasa ma ai nan ake gardamar kokuwa. Ga zahiran nan na gani a kusa da kai."
Ta faɗa tana nuna kayan da ke hannun Binta da yatsarta manuniya.
"Ƙaramin sani ƙuƙumi... Ko ki yarda ko kar ki yarda zan faɗa miki magana ta ƙarshe akan kayannan da kika gani. Wallahi, Tallahi, kwabona babu a cikin siyayyar kayannan nawa da na Binta da ƴarta da kike magana a kai. Kamar yadda na faɗa muku ba ni da kuɗin da zanyi muku sabbin ɗinkuna da sunan cin biki, tunda dai Allah yasa sallah bata daɗe da wucewa ba ku da ƴaƴanku ku saka kayan sallarku ku ci bikin da su. Waɗannan kayan da kike gani Binta ce ta ɗinka mana. Kuma Wallahi ban san ta ɗinka ba sai yanzu da take nuna min kamar yadda kika gani. Ina fatan kin fahimce ni?"
Ya ƙarasa maganar yana sassauta muryarsa.
"Ban fahimce ka ba. Kuma bazan taɓa fahimtarka ba Malam in dai da wannan shaiɗaniyar a cikin gidannan."
Ta amsa tana karkaɗa jiki kamar mai shirin yin dambe.
Zuwa yanzu duk yadda Malam yake danne ɓacin ransa ya riga ya kai ƙololuwa, a fusace ya ce
"To shi kenan. Kar Allah yasa ki fahimceni Ramatu. Ni nayi mana Ankon Shadda da Binta da ƴarta. Ki ɗauki duk matakin da kike ganin kin isa ki ɗauka."
Kwaɓa-kwaɓa tayi da fuska za ta saka kuka.
"Haka ma za ka ce Malam..?"
Hannu ya ɗaga mata alamar dakatarwa. Da salon umarni a muryarsa ya ce
"Fita ki bani guri."
Idanu ta zazzaro
"Kora ta..."
"Ramatu Wallahi idan baki fita ba zan ɗauki mummunan mataki a kanki."
Tayi ƙwafa mai ƙarfi, ta girgiza kai, ta fita a fusace.
Yaraf! Ya zauna a kan kujera. Hannu biyu yasa ya dafe kanshi da yake mishi mugun ciwo kamar ana buga mishi guduma.
"Kayi haƙuri Abban Humaira."
Binta ta faɗa a tausashe.
Kayan ta kwashe ta kai cikin ɗaki kamar yadda tayi niyya da farko. Can kuma sai ta fito, kai tsaye gurinsa ta nufa ta zare hannayensa da yayi tagumi.
"Zo muje ciki ka ga wani abu."
Tana riƙe da hannunsa ta taimaka mishi ya miƙe tsaye, kamar makaho da ƴar jagora ta ja hannunshi suka shige ɗakin barcinsa. Mintuna biyu tsakani, babu abinda ke tashi a cikin ɗakin sai dariyarsu.
*******
Tsayuwar Yaya Luba, Hajiya, da ɗaiɗaiku daga cikin ƴan'uwan Ramatu ne yasa har aka yi bikin Zainab lafiya aka watse taron biki lafiya. Amma a ɓangaren Safiya ƙawar Ramatu, da ƴan'uwan Ramatu su Sakina, Rahane, Salaha, su so sukayi a wannan biki Ramatu ta zage dantse ta ci Uban Binta la'ada waje.
Ba don komai ba sai don ganin yadda komai na abincin bikin mutanen Malam, da nama da lemu duk Binta ya damƙa ma. Abu na biyu shi ne yadda Binta ta dinga shiga tana fita a cikin kwanaki biyu na bikin da wasu zafafan atamfofi da leshika da shadda. Ashe Shaddar da Ramatu take ta tayar da jijiyar wuya akai ba komai bane a kan sauran kayan da tayi tanadi don ta ci biki. Ko Zainab da take amarya bata sa kaya masu darajar da Binta tasa ba, balle kuma Ramatu da ba a ko maganarta, duk tattalin arzikinta ta kwashe tas ta yi ma Zainab siyayya.
Gudummuwar da ƴan'uwanta suka bata kuma da ƙyar ta iya cirewa ta sayi atamfofi kala biyu, su ma masu matsakaitan kuɗi. Don a ganinta ɓarnar kuɗi ne mace ta cire maƙudan kuɗaɗe ta sayi atamfa ko leshi, balle wata shaddah da ko an siya idan ana so ta fito da kyau sai an sake kashe kuɗin aikin wuta.
Sama sama dai aka lallaɓa aka gama taron biki lafiya, sai fatan Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba.
******* *******
Tatbikutta'alim islamiyya academy Kasuwan magani, sabuwar makaranta ce da take tashe a cikin garin Kasuwar Magani. Abin burgewar shi ne tashenta bai tsaya a baki kaɗai ba, akwai zaƙwaƙuran malamai da suka san yadda ake koyarwa.
Duk daƙiƙancin yaro da rashin ƙoƙarinsa in dai aka kaishi makarantar to in sha Allahu sannu a hankali ƙwaƙwalwar yaro zai fara buɗewa.
Wannan dalilin yasa burin ko wane uba ko uwa su kai ƴaƴansu wannan makaranta. In dai suna so ɗansu ko ƴarsu ta taso da karatu.
Ko da Humaira ta isa shiga makaranta, Binta ta ce ma Malam nan makarantar take so ya saka Humaira, kai tsaye ya ce mata ba shi da kuɗi. Ko da yana da kuɗin ma tsakani da Allah bazai iya jure biya mata kuɗin makarantar da ya kusa ninka na ƴaƴanshi biyar da suke makarantar gwamnati ba.
Ba tare da damuwar komai ba Binta ta je da kanta tayi ma Humaira register da duk wani abu da ake buƙata na wannan makaranta. Ranar Litini na zagayowa Humaira ta fara zuwa makaranta cikin tsananin sa'a da farin jini.
Tsarin makarantar shi ne, daga ranar litini zuwa ranar alhamis tun safe idan suka tafi ba'a komawa gida sai ƙarfe shida na yamma. Ko wane yaro sai dai a kai mishi abinci da abinsha. Ko kuma tun safe iyaye su haɗa ma yaro duk abincin da zai nema har zuwa yamma.
Binta da himma, musamman ta samu dauwamammen almajiri wanda kullum zai dinga zuwa gidanta da rana yana ɗauka ma Humaira abinci ya kai mata makaranta. Idan aka tashi kuma da yake makarantar yana daf da gidan Kawu Bala ne. Yaran gidan kullum su ke jelar ɗauko Humaira daga makaranta su mayar da ita gida.
Shekaru biyu da suka biyo baya lokacin Humaira tana ƴar shekara biyar da rabi. Saboda tsananin ƙoƙari da hazaƙarta har ta shiga primary 2. A makarantar gaba ɗaya ta yi fice saboda ƙoƙari da tsananin wayon ta, kowa Humaira... Ba yara ba manya, ba ɗalibai ba malamai.
A daidai wannan lokacin ne ita ma Ramatu da kullum take jin baƙin cikin yadda Humaira ita kaɗai aka tsame a cikin yaran gidan aka saka a makarantar kuɗi, ita ma ta ƙuƙuta ta haɗa hammun da gammun ta ciro Hadiza da Aliya daga makarantar gwamnati, ta mayar da su makarantar Tatbikutta'alim Islamiyya Academy Kasuwan Magani.
Aliya ta shiga J.S.S 1, ita kuma Hadiza tana primary 5. Saboda ba ta da ƙoƙari ko kaɗan, da ƙyar ma aka karɓeta a primary 5 ɗin, don sai da aka saka Ramatu da ita kanta Hadiza suka yi alƙawarin lallai za ta watsar da wasanni da shiririta ta mayar da hankali a karatu.
Shigar Aliya da Hadiza makarantar su Humaira za'a iya cewa ta wani fannin Binta ta sami sauƙi, musamman a yanzu da take fama da laulayin ƙaramin cikin da take ta ɓoyo bata faɗa ma Malam ba. Ta wani fannin kuma bata samu sauƙi ba.
Sai dai kuma a dunƙule idan za a faɗi gaskiyar abinda aka samu shi ne an sami cigaba, amma irinna mai haƙar rijiya. Sannu a hankali cikin hikima da ƙwarewa a ɓoyo irin nasu suka fara gigita rayuwar Humaira suna azabtar da ita, bayan sunyi mata mummunar barazanar hallakata har lahira idan tayi gigin faɗa ma malamansu, Binta, ko Babansu abinda suke mata a makaranta, hanyar zuwansu makaranta, da hanyar komawarsu gida...