Free chapter · Read without an account

Chapter 1 & 2

by Fatima Isa Manu · DANGIN MUTUWA

*DANGIN MUTUWA🔥*


A story of full hatred, vengeance of the spirit, betray, unconditional love and heart touching.



*STORY & WRITTEN 

           BY 

*FATIMA ISA MANU ( DR TEEMAH ✍️ )*


 *SAHIBAR JAJIRTATTU*




Comments section: ***


_Masu neman littafin *DANGIN MUTUWA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following din channel ɗi na dan samu_👇

___________________________________

               

****

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A) 

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


*DIAMOND 💎 STAR ⭐*

      *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*

          *(We stand together)*

                    🤝🤝🤝


___________________________________





*PAGE 1 & 2*





*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*




Typing ✍️ Date 18/10/2024






Da sauri ta fito daga cikin toilet din har tana k'ok'arin faɗi, matashiyar da ba za ta wuce shekara ashirin da hudu ba a duniya, doguwa ce fara siririya sai ƙaramin bakinta da ya ƙarawa dogon fuskanta kyau.


Numfashi take fitarwa a wahale tana kiran sunan su da karfi." AMJAD!  RUMAISA! MARWAN! help." 


A tare suka tashi daga zaunen da suke, wani saurayi ne wanda akalla bazai wuce shekara ashirin da biyar ba ya nufo gurin da take da sauri.


Bugesa ta yi tana k'ok'arin guduwa, kama ta ya yi yana cewa." AYMA me ya faru?." 


Kuka ta fashe da shi tana cewa." MARWAN na ji suna zuwa." 


A razane RUMAISA ta ɗaura hannu a kai, cikin kiɗima ta soma cewa." Na san ni ce gawar gaba, dama sun tsane ni, wayyo ni." 


Saurayin dake zaune a kan gadon ne ya ja tsaki yana lumshe ido, juyawa suka yi suna kallon shi, MARWAN ne ya ce." AMJAD baka ji me yake faruwa ba ne?."


Cikin siririn muryansa ya ce." Then sai na fara kuka? Kun hana mutum yin barci, mtsw." Ya ja tsaki.


Ƙulewa AYMA ta yi, hakan ya sa ta ce." Kai fa na lura kwata-kwata baka cikin bil adama, kuma.." Maganar ne ya maƙale ganin an turo ƙofa.


Wutan ɗakin ne ya ɗauke na wasu seconds kafin ya kunnu, da sauri suka ja baya suna kallon yaron.


Kamar dodo saboda gajarta, gashi baki sosai sai fararen idanunsa da shi kaɗai ne abu me haske a jikinsa.


Dariya RUMAISA ta sa tana cewa." Wannan ai jinjirin biri ne." 


Dariya suka kwashe da shi, MARWAN na cewa." Da alamu irin mutanen nan ne da aka ce za'a haifa a ƙarshen zamani."


Jin suna ta surutu ya sa AMJAD juyowa, saura kaɗan ya gudu amma sai ya tsare yana kallon yaron, zuciyarsa ce ta tsinke.


AYMA ce ta ce." Ai ni ko a birirrika ban taɓa kallon dan Gorilla ba sai yau, amma maganar gaskiya yaron nan kaga muni chabbb." Dariya suka saka masa kamar ba gobe.


Shuru suka yi sai yanzu abun ya fara basu tsoro, ta ya akayi ya shigo gidan? Ta ya akayi ya san ɗakin sirrin su? Waye shi?.


Washe musu baki yaron ya yi, a razane RUMAISA ta rike hannun MARWAN tana rawan sanyi, wutan ɗakin ne ya fara kawo ka ɗauke


Taku daya AYMA ta yi ta ɗale gurin AMJAD, wutan ɗakin ne ya tsaya me kyau, a gaugauce AMJAD ya nufi gurin da MARWAN da RUMAISA suke kwance kamar gawa, duk jini ya bata jikin su.


Duban AYMA ya yi ganin yanda take kallonsa ne ya sa ya ce." Suma an shanye jinin su." 


Waro ido waje ta yi tana nufo shi, murya na rawa ta soma cewa." YA MARWAN! RUMEEY! Ku tashi dan Allah, kun manta cewa tare za muyi wannan yaƙin ne?."


Hannunsa AMJAD ya saka a gefen wuyan MARWAN yana jin harbawan nunfashi, ɗago kai ya yi yana kallon AYMA, kafin ya ce." Ba mutuwa suka yi ba, da alamu tsorata suka yi."


" Amma ai basa yin magana." Ta yi maganar a tsorace.


" AYMA sau nawa kina ganin yanda ake kashe mutum a gidan nan?."


" Sau biyar."


" To ki natsu ba mutuwa suka yi ba, suma suka yi okay." Ya ida faɗar hakan yana dafa kafaɗarta.


Gyaɗa masa kai ta yi tana tashi ta wuce toilet, fitowa ta yi hannunta ɗauke da ruwa a cup, murmushi ya sakar mata yana ƙarban cup din.


Watsa musu ruwan ya yi, a tare suka sauƙe ajiyar zuciya, MARWAN na cewa." Wayyo Allah, ni kam na hakura ba zan iya ba." 


Hararan shi AMJAD ya yi yana cewa." Sai ka ce a kanku aka fara, an kashe mutum biyar a gaban ku, kun ga gawar mutum bakwai, amma har yanzu kuna tsoro." Shuru suka yi suna jin shi,,, cigaba da magana ya yi yana nuna in da MARWAN ke kwance. " MARWAN sai ka ce ba namiji ba, har da fitsari fa ka yi." 


" A maganar mutuwa babu zancen namiji AMJAD." Ya ida faɗar hakan ya tsarewa.


Kunshe dariyarta AYMA ta yi tana kama RUMAISA suka tashi, kallon su MARWAN ya yi rai a haɗe yake cewa."  A wa ku ke wa dariya?." 


Shuru suka yi, dan sun san MARWAN yanzu zai musu duka, AMJAD ne ya dube su yana cewa." Ku jira mu tafi tare."


Da haka ya kama MARWAN suna fita daga ɗakin, sai da suka yi tafiya sosai kafin suka fara bin lungu-lungu suna wucewa, wani ƙaramin hanya ne wanda shi ne kaɗai hanyar da zai kai ka cikin gidan.


Kuma ya yi duhu sosai, hakan ya sa AMJAD kama hannun AYMA yana cewa MARWAN ya riƙe na RUMAISA.


Rufe idanunta AYMA ta yi tana bin bayan AMJAD suka fara bin lungun, ita ma RUMAISA kama hannun MARWAN ta yi suka bi bayan su.


Kukan jariri suka fara ji, dake ba sabon abu ba ne a gurin su hakan ya sa basu wani ɗaga hankalin su ba, tafiya suka ɗan yi kafin suka tsaya a bakin ƙaramin ƙofar.


Ƙofan sirri kenan, bayan su babu wanda ya san akwai, kuma babu wanda ya iya buɗe kofar sai AYMA, hakan ya sa duk lokacin da zasu je gurin sai da ita.


Hannunta ta ɗaura a kan kofar tana danna yatsarta babba a tsakiya, a sannu a hankali kofar ta soma buduwa.


Da sauri suka fita daga cikin lungun, suna fita kofar ta rufu da sauri, AMJAD ne yake magana a hankali.


" AYMA ki kai RUMAISA ɗakin ta kafin ki wuce naku bangaren." 


Gyaɗa masa kai ta yi tana kama hannun RUMAISA, har za su tafi suka ji muryansa na cewa." Kun san dole gobe za'ayi mutuwa, kar ku tsorata, sannan kar ku nuna fargaba a duk wanda ya mutu."


" In Sha Allah." Suka faɗa a tare, kafin suka nufa wani bangaren gidan daga chan kudu, suna tsaye a gurin har AYMA ta raka RUMAISA bangaren su, kafin ita ma ta zo ta wuce bangaren su ta hannun dama.


Kallon MARWAN AMJAD ya yi yana cewa." Me ka ke jira kai kuma?."


" Raka ni zaka yi mana Big bro." Wani banzan harara ya wurga masa yana cewa." MARWAN ka wuce ka tafi ɗakinka."


" Haba Big bro, ni ne fa."


" Mtsw za ka ji da shi kuma." Da haka ya wuce ya tafi side din shi dake bangaren kudu, dole ta sa MARWAN wucewa ya tafi bangaren samarin gidan, yana tafe yana tsoro.


Haka kusan rabin GANDARA family suka kwana idon su biyu, kowa da abunda ya ke damun shi, haka kuma kowa yana tsoran abin da zai faru gobe, ta wani barin kuma ana tsoron gawar da za'a waye gari da rashin shi.







WASHE GARI






Dake dare ne jiya, shiyasa ban ƙarewa gidan kallo ba, babban gida ne wanda ya ɗauki apartment guda takwas, sai kuma wani babban parlor da yake a tsakiyar gidan, shi ne kuma parlon taro. Ta ko ina security ne da yan sanda, saboda binciken da ake yi a gidan, da kuma yawan mutuwar da ake yi.



A guje HANIFA ta fito daga apartment na su tana ihu, da sauri security's din suka nufo ta, kuka take yi har tana faɗi ƙasa.


Mutanen gidan ne suka fara fitowa da gudu, duk da sunsan cewa labarin gizo baya wuce na ƙoge.


Ihu HANIFA take tana nuna musu hanyar apartment na su, duka suka nufa gurin suna tunanin waye kuma ya mutu?.


Mazan gidan ne suka fara shiga parlon, da sauri suka kau da kai,,,, AMJAD ne yake kallon gawar cike da al-ajabi, kenan yau an canza salon kisan?. Ya tambaye kansa.


Kuka ABDUL ya saka yana nufan gurin mahaifiyarsa din, jin kuka ya sa Matan gidan shigowa parlon, cak kowa ya tsaya yana kallon gawar.


Kowa da abunda yake tambaya a ransa, kuma tambayar daya ce, ' Ya aka canza salon kisan?.' 


Su kan su ƴan sanda gagara motsi suka yi, saboda sun san kisan kala biyu ne, amma na yau ya canzu gaba daya.


HANIFA dake kuka ce ta ce." Na ga mutumin yau......











COMMENTS PLEASE 🙏🙏🙏





SHARING PLEASE






*SIGN BY DR TEEMAH ✍️*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.