Free chapter · Read without an account
Capter 3&4
*DANGIN MUTUWA 🔥*
A story of full hatred, vengeance of the spirit, betray, unconditional love and heart touching.
*STORY & WRITTEN BY ✍️ FATIMA ISA MANU 🥀🌻*
*( DR TEEMAH ✍️ )*
*( SAHIBAR JAJIRTATTU 💃🌼 )*
_Masu neman littafin *DANGIN MUTUWA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following din channel ɗi na dan samu _***
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
___________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
__________________________________
*PAGE 3 & 4*
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
Typing date ✍️ 19/10/2024
Su kan su ƴan sanda gagara motsi suka yi, saboda sun san kitsan kala biyu ne, amma na yau ya canzu gaba daya.
HANIFA dake kuka ce ta ce." Na ga mutumin yau."
Gaba daya sai da suka juyo suna kallon ta, tun kafin wani ya yi magana KAWU YA'U ya ce. " Ke fa dama HANIFA baki da hankali, a ina ki ka ga mutumin."
Inspector LAWAN ne ya ɗagawa KAWU YA'U hannu yana cewa." Ina ruwanka? Ta kira sunanka ne? Ko kana zargin kanka ne?."
" A'a ko kaɗan, Allah baku hakuri." A cewar KAWU YA'U.
Kallon HANIFA Inspector LAWAN ya yi yana cewa." Cigaba da maganar ki."
Har ta buɗe baki za ta yi magana, suka haɗa ido da KAWU AMADU, kallon warning ya mata, nan da nan ta sunkuyar da kai.
Inspector ne ya ce." Kin yi shuru HANIFA muna jiranki fa." Girgiza kai ta yi tana goge hawayen fuskanta.
Gaba daya gurin shuru ya yi, Inspector ne ya ƙaraso gurin gawar yana kallon yanda jini ya bata gurin, da alamu ba'a daɗe da yin kisar ba, saboda har yanzu jinin bai bushe ba.
" Sergeant ADAMU a kori kowa daga nan gurin." A cewar Inspector LAWAN.
Sara masa ya yi yana mai nuna musu hanya, daya bayan daya suka fara fita daga parlon.
Duban AMJAD ya yi ganin bai fita ba, kafin ya ce." Malam an ce kowa ya fita." A cewar sergeant ADAMU.
Juyawa ya yi ya fita daga parlon.
Kallon parlon Inspector LAWAN yake yi, idanunsa ne ya sauƙa akan hannun kujera, da sauri ya miƙa hannun aka ba shi hand glove, sakawa ya yi yana lakutan jinin.
Shinshinawa ya yi yana saurin ɗagewa daga kusa da hancin shi, magana ya fara yi yana kallon ko ina a parlon.
" Anyi amfani da Acid ne gurin ƙona gangar jikin gawar, amma Acid din da akayi amfani da shi ba'a ko ina ake samun shi ba."
Idanunsa ne ya sake sauƙa akan cup din dake kan table, duban Sergeant ADAMU ya yi yana mai cewa." Ina buƙatar doctor ASAD a nan yanzu."
Sara masa sergeant ADAMU ya yi yana mai fita daga parlon.
A main parlon gidan kowa ya shiga ya yi zaman ƴan bori, kowa da abunda yake zargi akan ɗan uwansa.
Kallon kallo aka shiga yi a junansu, rai a mutukar ɓace KAWU BELLO ya tashi tsaye yana magana.
" Wai har yaushe za'a dai na ɗauke daya a cikin mu ne? Kuna kallo muna rasa ƴan uwanmu, sannan dole akwai haɗin bakin daya daga cikin mu ake wannan kisar."
Kallon juna suka shiga yi, kowa na zargin ɗan uwansa, KAWU AMADU ne ya fusata yana magana har jijiyoyin kansa na tashi.
" Me kake nufi YA BELLO? So ka ke kace mu muke kashe junan mu?."
" Kwarai kuwa, tabbas." KAWU BELLO ya faɗa.
KAWU YA'U ne ya ce." Ai kowa ya yi haushi a kasuwa ya san da wanda ya ke, kuma karyan mutum ya ci namana Wallahi, saboda ɗaci ne da shi."
" YA’U ma ni ka ke faɗawa haka?." Cewar KAWU BELLO.
" Ni ba da kowa nake ba Yaya, Allah ya huci zuciyarka." Cewar KAWU YA’U.
Kai KAWU BELLO ya gyaɗa yana mai cewa." An kashe min yarona na yi shuru, an kashe min yarinyata na yi shuru, amma wanna karan da aka kashe min matata kuma kisan wulakanci, to billahillazi sai kowa ya ji a jikinsa."
Shuru kowa ya yi yana sauraran maganar KAWU BELLO.
AYMA ce ta dubi RUMAISA tana magana ƙasa ƙasa.
" Ni fa na fara zargin KAWU AMADU."
" AYMA bake kaɗai ba har ni na fara zargin shi, kuma ko an faɗawa YA MARWAN ba yarda zai yi ba saboda Mahaifinsa ne."
AMJAD dake kusa da su ne ya mintsine AYMA, da sauri ta rufe baki tana sunkuyar da kai.
Cigaba da magana KAWU BELLO ya yi. " Kuma na tabbata akwai wanda ya ke aikata wannan abun a cikin mu."
Ɗaka masa tsawa IYA ta yi ta hanyar cewa." BELLO baka da hankali ne ko me? Matarka kadai ne ta mutu aka ce maka? Ko sauran ba mutane ba ne? Kana magana kamar ba babba ba."
Yaran ne suka fara zame jiki suna fita a parlon, ganin ana son zage-zage a gurin, duk da kuwa ba abun mamaki ba ne dan anyi zagi.
Parlon ya rage KAWU BELLO, KAWU AMADU, KAWU YA'U, da matan KAWU YA'U da KAWU AMADU, sai IYA dake ta sababi.
Murmushin da ya fi kuka ciwo KAWU BELLO ya yi yana cewa." IYA ke fa Uwa ce, amma kina nuna banbanci a cikin mu, an kashe min mata amma kina goya musu baya, shin wani laifi na miki ne?."
" Sai aka ce maka su suka kashe maka mata?." A cewar IYA.
Girgiza kai ya yi, kana ya ce." Ba laifi ba ne idan su suka kashe min mata, amma bazan taɓa yafewa ba." Daga haka ya yi ficewar shi a parlon.
KAWU YA'U ne ya ce." Aikin banza da wofi kanka ne farau."
Matar KAWU YA'U ne me sunan HAFSAT ta tashi zata fita ta ce." Ku ringa adalci a tsakanin ku, shi din yayan ku ne, amma kun mai da shi tamkar bare a tsakanin ku."
Da mamaki suke kallonta, KAWU YA'U ne ya ce." HAFSAT hauka ki ke ne?."
Murmushi ta masa tana cewa." Ba hauka nake ba, gaskiya kawai nake faɗa muku." Nunfasawa ta dan yi kana ta cigaba da cewa.
" IYA ke fa Uwa ce, amma kwata-kwata bakya yin gaskiya a tsakanin yaranki, kuma..."
Tsawar da KAWU YA'U ya ɗaka mata ne ya sa ta yi shuru, jiki har rawa yake gurin cewa." HAFSAT ma Mahaifiyata ki ke faɗawa haka?."
" YA'U kenan, ma ita nake faɗawa ai gaskiya ce."
Sauƙan mari ta ji a kuncinta, da sauri ta dafe tana kallon shi, murya a raunane ta ce.
" Ni ka mara?."
" Ba mari ba, abunda ya fi mari zan miki, kuma ina mai sanar da ke cewa na sake ki saki daya, biyu, uku."
A razane ta kalle shi!!! AYMA da ke bakin kofa ne ta daskare a tsaye, dama Inspector LAWAN ne ya ce ta kira su.
Murmushi MAMA HAFSAT ta yi tana cewa." Na gode sosai YA'U da ka cire ni a cikin ƊANGIN MUTUWA, kuma In Sha Allah sai asirin ku ya tonu." Da haka ta juya zata fita, haɗa ido suka yi da AYMA.
Murmushi ta sakar mata tana bi ta gefe ta wuce, binta ta yi da kallo har ta ɓacewa ganinta, kana ta juyar da kallonta zuwa ga su.
Murya na rawa ta ce." ABBA ita ma sakinta ka yi?."
Banka mata harara ya yi yana mai cewa." Uwar me ya kawo ki?."
Murmushi ta masa tana cewa." Babu abunda na zo yi, Inspector ne ya ke kiran ku." Tana gama faɗar haka ta yi wucewar ta.
Tsaki IYA ta yi tana tashi ta fita, suma suka mara mata baya kamar wasu rakumi da akala.
@@@@@@@@@
Bayan sun shigo parlon ne kowa ya tsaya yana kallon Inspector LAWAN.
Kallon su ya ke cike da zargi, kafin ya sauƙe idanunsa akan IYA.
Nunata ya yi da hannu yana mai cewa." Ke ce ki ka kashe matar nan."
Gaba daya sai da su ka juyo suna kallon ta cike da mamaki, IYA ko a jikinta sai ma samun gurin da ta yi ta zauna tana bin Inspector LAWAN da kallo.
Murmushi ya mata yana cewa. “ Me ta miki da za ki kashe ta?.”
Tsaki IYA ta ja tana cewa.” LAWAN ka ke da suna ko waye?.”
“ Ah ah ba LAWAN ba ne, SALLAU ne.”
“ Ko ma me kai ka sani, so nake na ce maka ni din nan nafi karfin na kashe mutum bari ka ji.”
“ Kinfi karfi shi ne za ki kashe sirikarki?.”
“ Binciken da ka yi ya nunamin kai baka san aikinka ba har yanzu.”
Gyara tsayuwarsa ya yi yana sakar mata murmushi, kafin ya ciro leda a aljuhunsa yana nuna mata.
A razane IYA ta tashi tsaye tana nufo gurin shi.
Saurin mayar da ledan ya yi aljuhu yana murmushi.
Kallonsa take da wannan idanun nata masu kama dana mujiya.
Duban sergeant ADAMU ya yi yana cewa. Arrest her, ita ce abun zargin mu na farko.”
KAWU YA’U ne ya ce.” Inspector ta ya zaka kama mahaifiyarmu ne?.”
Duban sergeant ADAMU ya yi wanda tuni ya sakawa IYA handcuff, murmushi ya yi yana cewa. “ Saura wannan.” Ya faɗi hakan yana pointing din KAWU YA’U.
“ Kai haba hauka ake ne daga magana sai a kama ni.” A cewar KAWU YA’U.
Duban su AYMA ya yi yana cewa. “ Ba ke ce kika mari JUNAID ba a clup?."
Sunkuyar da kai ta yi, murmushi ya yi kana ya ce.” Gaskiya family nan akwai kura chabb, ba manyan ba har yaran duk ƴan iska ne.”
AMJAD ne ya ce.” Inspector wannan maganar ya dade da mutuwa fa.”
Dariya Inspector ya yi mai sauti yana cewa.” A gurin ku ne ya dade da mutuwa? Kuma ai kai ma kamar ka taba raped din yarinya a hotel din Kaduna…
COMMENTS AND SHARING PLS🤝🙏
*SIGN BY DR TEEMAH✍🏼*