Free chapter · Read without an account
A Bespoke Romance❤️🔥🤑
by NorthernAngel · His Rose
suna fita ta shiga motan shi yaja suka nufi side ɗin su, suna shiga suka nufi ciki suka hau staircase yana gaba tana binsa a baya har suka gama hawa suka hau wani benin inda suna hawa taga gym ne gurin sai wani kofa guda ɗaya wanda tasan nan ne office ɗinda muazzam yace mata, elavator taga sun nufa Ahmad ya jugo ga kalleta yace
“to make it easier for you shiyasa na biyo dake tanan tunda asama kike but you’ll see the main way in muka shiga” gyaɗa kai kawai tayi suka shiga elavator ɗin yayi pressing LL, suna isa kofar ya buɗe yace mata
“facial recognition ne doors ɗin duka but I’ll give you the key card”
“Okay” ta amsa suka shiga shima dai staircase ne suka fara sauka tun daga saman take hango haɗuwar ƙasan da erin motocin dake ciki, wani erin ƙaton garage ne wanda ya haɗu ga motocin da ke ciki ba na banza
“Oh my god” kawai Zara ke ta furtawa tana ware manyan idon ta har suka gama sauka da gudu ta isa tsakiyar garage ɗin tana rasa wanne side ma zata fara zuwa, latest most expensive cars kawai take gani wata Aston Martin Vanquish tagani guda biyu eri ɗaya ɗaya fara ɗaya baƙi ta kalli ahmad tace “na waye wannan”
“Zafar and muazzam, mostly cars ɗinsu eri ɗaya color ne difference ɗin, muazzam often buy white and red cars while Zafar cars are always black or sometimes xenon grey” nan fa yafara nuna mata motar kowa, wasu 2025 Rolls-Royce tagani, phantom, spectre and cullinan but the Cullinan series II caught Zara’s eye, it’s seems unique, saboda gurin RR logo ɗin crown ne, and the car's black colour is also so shiny and unique it's storm black, daga gani custom made ce
“who owns this ya Ahmad?” ta tambaye sa with surprise
“The RR spectre is for Muazzam, sauran kuma na Zafar ne”
“I’m definitely going to drive one, cullinan ɗin nakeso” Zara tafaɗa with excitement
“Kai the bespoke RR? ba ruwana, i told you it’s for Zafar, bai ma taɓa using ɗinta ba, he mentioned about it being a gift, maybe Salma ya siyama” nan da nan mood ɗin Zara ya canza, kanta har wani sara mata yayi amma bata nuna ba tace masa
“where are the keys?” nuna mata wani smart safe key box yayi daga jikin bango, suka ƙarasa gurin, taga erin mai password, app lock, finger print da keycard ne, keycard ɗin taga yaciro ya bata ta karɓa kafin ya gaya mata password ɗin safe box ɗin yana cewa “wannan card ɗin dashi zaki samu access da every door that concerns the garage, so keep it safe kafin ayi adding finger print ɗinki and when you come back you can drop the car daga bakin garrage ɗin it’s an automated valet parking system, ko kuma ki shigo ta front gate the valet guy zai kai miki garage ɗin” gyaɗa kai kawai Zara take tana jinsa ita dai ta matsu bai bata key ɗin RR ɗinnan ba, nan Ahmad ya miƙo mata key ɗin motar ta ta kalla tace “l’m not driving my car, I’m driving the cullinan” tafaɗa cikin shagwaɓarta
“Rose are you sure? kinsan nace miki na Zafar ne and he clearly mentioned he bought it for someone which that someone maybe his wife to be, i don’t want you to get in any trouble with him, you can drive any of my cars if you want” Ahmad yafaɗa dan yasan babu mai taɓawa Zafar cars ɗinshi, Zara rolling ɗin eyes ɗinta tayi tana cewa “don’t worry, I won’t get in any trouble”
“a’a let’s ask him first” yafaɗa yana ciro wayar sa ya saka kiran Zafar, yana fara ringing ya ɗaga da deep voice ɗinshi yake cewa
“what’s up?”
Ahmad yace “ya Zafar we are in the garage with Rose, she wants to drive one of your cars shine nace she should ask you first”
“give her the phone” kawai Zafar yafaɗa, miƙa mata wayar Ahmad yayi duk da har lokacin haushinsa take ji amma sai ta karɓa ciki ciki tace
“hello”
“princess” taji yafaɗa da low resonant tone, wani sanyi taji na shiga zuciyar ta, ta lumshe ido ahankali ta furta
“yea?”
“which car do you want to drive?” ya tambayeta ahankali yana jinta har cikin ransa
“the RR cullinan” tafaɗa a mugun shagwaɓe
“oh that, it’s yours, I wanted to send it to you on your birthday but I heard muazzam saying you’ll be coming home the next day” Zara kasa ma magana tayi tana tunanin daidai taji kuwa, Jin tayi shuru ne Zafar yasake cewa
“drive safe, karki wuce 6pm awaje” daga haka ya kashe wayan, daga haka tabi wayan da kallo cikin mamaki kaman yanda tun sanda tafara wayan Ahmad ke mata kallon mamaki dan yanajin abunda Zafar ke faɗa saboda silence ɗin garage ɗin
kallon shi Zara tayi tana wara masa manyan idanun ta tace “he said it’s mine” tafaɗa cikin mamaki kaman mai son tabbatar wa, smirking ahmad yayi yana cewa
“well, it’s seems like you two have something going on, shiyasa kika ce you’ll drive his car confidently daman” Zara da hankalin ta bama gurin shi yake ba, miƙa masa wayar kawai tayi tana cewa
“give me my keyyyy” tafaɗa excitedly
ɗauko key ɗin yayi ya miƙa mata ta karba da gudunta ta ƙarasa gurin motar tana dariyan jin daɗi wani son Zafar na taso mata ta nemi duk haushinsa da takeji ta rasa, dariyar ta ya cika garage ɗin she looks so happy, haka ta buɗe motar ta shiga batama sake bin takan Ahmad ba dake tsaye cikin mamakin yanda yaji Zafar na mata magana kaman bashi ba
Zara na shiga motar taga wani bunch red roses flowers awurin driver seat ɗin, ta ɗauka tana murmushi ta ɗauki card ɗin jiki taga anyi rubutu da cursive handwriting
𝓕𝓲𝓿𝓮 𝔂𝓮𝓪𝓻𝓼 𝓸𝓯 𝔀𝓪𝓲𝓽𝓲𝓷𝓰, 𝓪 𝓵𝓲𝓯𝓮𝓽𝓲𝓶𝓮 𝓸𝓯 𝓵𝓸𝓿𝓲𝓷𝓰.
𝓗𝓪𝓹𝓹𝓲𝓮𝓼𝓽 𝓑𝓲𝓻𝓽𝓱𝓭𝓪𝔂 𝓟𝓻𝓲𝓷𝓬𝓮𝓼𝓼!
𝓒𝓸𝓾𝓷𝓽𝓲𝓷𝓰 𝓽𝓸 𝓯𝓸𝓻𝓮𝓿𝓮𝓻...
— 𝓩𝓪𝓯𝓪𝓻
sai alokacin Zara taƙara yadda da cewa da gaske dai motar tata ce ahankali ta lumshe ido hawaye na zubowa, kenan shima she’s been on his mind all those years, ashe ma he was planning on going to her yanzu da five years ɗin ya cika kenan, wlh tana son Zafar, son da bata tunanin zata rayu inta rasa shi, haka zalika kuma bata jin zata iya sharing ɗinsa da wata mace, ita abunda tasani Zafar nata ne ita kaɗai dan haka duk yanda zatayi saita rabasa da salma amma ba yanzu ba saboda maman shi is 100% on salma’s side so she have to be very careful dan karta rasa shi gaba daya, daga haka tayi murmushi tana kawar da abun daga ranta ta tada motar ta fita daga garage ɗin da tunani kala kala a ranta na yanda zata fitar da salma daga rayuwar Zafar ɗinta, haka ta fita daga estate ɗin da speed sosai ta hau hanyar gidan saurayin Ana
45 mins ta isa destination ɗinta ta hau kiran Ana sai gashi securities sun buɗe mata gate ta shiga cikin mansion ɗin saurayin Ana yana da kudi kam kuma celebrity ne he is nollywood actor, tana shiga Ana tafito tarban ta da gudun ta tazo ta rungume Zara amma duk hankalin ta naga motar da zara tazo da ita
“Rose where did you get this expensive baby?” Zara tayi wani murmushi tana kallon motar cike da iyayi tace “it’s a birthday gift from my man” da sauri tace
“your man? you mean Zafar?“ Ana ta tambaya dan tasan dai Zara batada wani saurayi sai Zafar ɗinda ta addabesu da labarinsa wanda batama taɓa bari sunga hotonsa ba duk bibiyarsa da take a instagram iyakaci ta kallesa ita kaɗai abunta
“Who else?” Zara tafaɗa tana rolling eyes ɗinta, nan dai Ana tayi ta sambatun motar har takira saurayin yafito shima ga motar wanda shima sosai ya koɗa motar Zara dai sai murmushi take ta tunanin yanda zata godewa Zafar ɗinta
haka suka shiga cikin gidan suna hiransu suna shiga saurayin Ana Nick yacewa Zara “what will you take rose?”
“Just coffee, I didn’t sleep much yesterday so I need it” ya karasa faɗi tana yar dariya
haka ya nufi kitchen ya haɗo mata coffee ya kawo mata ta amsa ta mishi godiya, nan fa suka fara maganar house party ɗin da za’ayi anjima wanda It’ll start by 5pm Kuma till dawn ne, ita dai Zara tasan ba scene ɗinta bane but she just wants to take her mind off Zafar saboda ji take kanta na kuncewa da ta tuna zai auri wata ba ita ba
haka dai tayi kusan 2 hours a gidan nan ma taji bata jin daɗin rayuwar ta kishi ne kawai ke addabar rayuwarta ji take komai zata iyayi dan Zafar yazama nata ita kaɗai
Miƙewa kawai sukaga tayi tace musu tana zuwa zata dawo in time ɗin partyn yayi, daga haka tafita
gidan brother Obi kawai ta nufa tana zuwa luckily ta tarar susan da Dike na gidan daman kuma su take nema, nan fa suka zauna sukai ta hira sai alokacin taji ɗan sanyi a ranta kuma koda wasa bata gaya musu wani abu na damunta ba kawai dai daman she needs them dan tasan dasu kaɗai ne zatayi hira su sata dariya mussaman dan uwanta Dike
haka suka wuni suna hiran sallah kawai ke tada Zara, anan tayi lunch, tana ganin kiran Ana batayi picking ba dan batason zuwa wani party har 7pm tana gidan har brother Obi ma yadawo ya tarar da ita kuma tana ganin kiran muazzam tun da rana amma taƙi picking dan baya son komawa gidan, sai da tayo sallahn isha tayi dinner ɗinta anan gidan sannan takama hanyar komawa