Free chapter · Read without an account

HAMAL Chapter 4

by Aysha Ɗansabo · HAMAL

HAMAL

Arewabook@ayshadansabo

©️Ayshat Dansabo lemu

Chapter 4

10:30am

Engr.AR Attaheer ne tsaye a gaban dresser ɗin dake cikin ɗakin hotel ɗin yana sharce sumar kansa bayan ya fito daga wanka,a gurguje yake komi kasancewar ƙarfe 12 yake so yayi masa a garin KD.Shirya kansa yayi cikin ƙananun kaya baƙin wandon jeans sai ya ɗakko riga black anyi layi layi da cream colour a jiki,kuma kasancewarsa mai hasken fata wanda tsabar hutu ya taimaka wajen goge fatar ya bada wani irin colour mai wuyar kwatance sai kalan kayan ya amshesa matuƙa.Fresh guy ne na gaske,dogo mai matsakaicin jiki domin ba za ka ce dashi mai ƙiba ba,kuma ba siriri bane tsaka-tsaki yake.Fuskarsa na ɗauke da dogon hanci zar tare da manyan oily eyes masu azabar kyau da rikita ƴan mata,ganshin kansa kullum cikin gyara yake a kwance luff.A taƙaice dai Engr. Kyakykyawan guy ne ajin ƙarshe,bayan ya kammala shirinsa tsaf ne ya ɗauki car key ɗinsa tare da ƴar ƙaramar jakarsa da mac book ɗinsa yayo waje bayan ya kulle ɗakin ya basu mukullinsu.Parking space ɗin dake harabar hotel ɗin ya fito ya nufi wajen motarsa ya buɗe back seat ya ajiye jakarsa,saida ya shiga motar sannan ya ciro phone ɗinsa domin tunda ya tashi zuciyarsa ke matuƙar azalzalarsa da son jin muryar pretty ɗinsa duk kuwa da cewa baiji daɗin yadda tayi masa adaren jiya ba har yayi zuciya yace bazai kuma kiranta ba amma a yanzu kuma yana jin bazai iya jure rashin kiran ba.Ya daɗe yana kallon digits ɗin kafin yayi ƙarfin halin yin dialling numbers ɗin,sai dai ga mamakinsa wayar a rufe take.Ajiyar zuciya ya sauke tare da ajiye wayar ya tashi motar zuciyarsa na ayyana masa kodai ya je gidan daya aje tane kafin ya wuce? Wani sashi na zuciyarsa ya tuhumesa da cewa to idan yaje yace mata mene? Kuma bama lallai ya sameta a gida ba domin shi shaida ne akan cewa student ce watakila zuwa yanzu tana skull.Wannan tunanin da yayi ya sanya ya yanke wa kansa cewa kawai zai cigaba da bibiyarta through phone.Da

wannan tunanin ya ɗauki hanyar KD zuciyarsa cike da da son jin muryar Yarinyar,wacce daga haduwarsa da ita jiya zuwa yau ta fara rusa duk wani plan ɗinsa da tunaninsa.

Karfe 11:30 ya shiga KD bayan ya biya yayi sayayyan kayan fruit wa Momynsa kamar yadda ya saba duk idan yayi tafiya tsarabar data fisu taga ya shiga mata dasu kenan,12pm daidai ya danna horn a bakin tangameman gate ɗin gidan nasu.Baba mai gadi ne ya buɗe gate ɗin,kuma ganin motar A.R ya sanya shi murmusawa yana faɗin,"Yallaɓai barka da shigowa." Hannu Engr. ya ɗaga masa ba tare da yace uffan ba,ya shige cikin gidan mai ɗauke da ƙaton parking space,motoci ne birjik zasu kai 6 fake a wurin.Ya nufi inda zai aje motarsa ya faka tare da kashe motar,yana fitowa Mudi mai bawa flawers ruwa ya iso wajensa yana faɗin,"Yallaɓai barka da shigowa."Fuskarsa a sake yake faɗin,"Barka kadai Mudi ka kwaso kaya a bayan boot ɗina ka shigo dashi ko." Bai jira jin komi ba ya nufi hanyar dazai sadashi da cikin gidan.Kai tsaye ya nufi ɓangaren Mommynsa ya isa zuwa wawakeken falon Hajiya Amina wato Mahaifiyarsa,fuskarsa a sake yake doka sallama kafin ya danna kansa ciki bayan an amsa sallamar tasa.Teemah ce zaune tana kallo sai Momy dake riƙe da wani littafi na addini tana dubawa,Teemah tayi azamar rugawa da gudu wajensa tana faɗin,"Oyoyo Yaya A.R."Rungumeta yayi yana faɗin,"My Autar Mommy ya kike?" Ta amsa da faɗin,"lafiya lau Yaya AR." Daidai lokacin Hafsat ta ƙariso wajen da suke tsaye cikin takunta na yauƙi da yanga,gabaki ɗaya tana tafiya ne tana kaɗa mazaunan tare da turo ƙirjinta.Sanye take cikin shigar pitted gown wanda yayi asalin fito da shafe ɗinta,rabin ƙirjinta duka a waje suke kanta sam babu ɗankwali sai ƙananun Calaba da jelarsu suka sakko bisa saman kafaɗunta.Tana ƙarisowa wajen ta washe fararen haƙoranta tana faɗin,"Oyoyo Ya AR."Sakin Teemah yayi tare da haɗe annurin fuskarsa guri guda tamkar wanda bai taɓa dariya ba a duniya,ganin yadda ta ƙariso da sauri tana shirin rungumarsa yasa ya daka mata tsawar da saida ya tsorata har Teemah dake tsaye tana kallonsu.Tuni Hafsa ta tsaya cak tana zare idanu,lokaci guda wani takaici ya ziyarci zuciyarta.Cikin murya mai cike da masifa yake faɗin,"Ke wace irin jakace,sau nawa zan miki gargaɗi akan ki daina ƙoƙarin haɗa jikinki da nawa? Ke Teemah ce dasai dole kin rungumeni zaki yimin sannu da zuwa,wato ke ga yar iska mara mutunci ko? To this is the last warning da zanyi miki akan hakan banza shashasha! Kawai wacce bata da kamun kai." Ya ƙare kalamansa cike da matuƙar ɓacin rai.Tuni Hafsat ta fashe da kukan takaici tana ƙarisawa cikin falon ta zube a saman seater tana kuka bilhakki,faɗi take a cikin zuciyarta,"Me ta yiwa Ya AR ne ya tsaneta a rayuwa haka? Da yasan irin son da take masa da yaci ace yana ragamata domin batun yau take ƙoƙarin cusa kanta a gareshi yana gwasaleta ba,gashi abin takaici duk irin cin kashin da yake mata Momy bata taɓa tsawata masa ba saima dai ta ƙara a inda ya tsaya a faɗan nasa." Kamar yadda yake faruwa a yanzu duk abinda suke Momy na jinsu sai dai sam bata ɗago ta dubesu ba ballantana ta tanka,sai yanzu da take jin kukan Hafsat na tashi ta ɗago idanunta tana duban Engr. ɗin tare da faɗin,"My son miye kuma haka daga shigowa ko hutawa bakayi ba zaka fara faɗa da ƙanwar taka,koda yake ai laifinta ne tunda bata jin bari."Ta juya inda Hafsat take kuka tana faɗin,"Oya rufe min baki shashasha! Sau nawa yake faɗa miki baya son irin ɗabi'ar da kike yi,so nawa zan faɗa miki cewa Abdulraheem ba muharraminki bane da zaki riƙa ƙoƙarin lallai saikin dinga kusanta jikinki da nashi eyim? To gaki gashinan duk irin abinda yayi miki ke da shi ne bazan taɓa saka baki akai ba tunda ke bakya jin magana,kuma ki tashi ki bani guri kafin in saɓa miki."Sum-sum Hafsat ta tashi ta nufi ɗakinta zuciyarta tamkar ta faso ƙirjinta tana mai ayyanawa a cikin ranta cewa,"Dole ne tayi abinda ya dace akan Yayan nasu,ba za ta taɓa bari soyayyarsa ya illatata ba,dole tayi ƙoƙarin ganin ta bama zuciyarta abinda take so kota wani irin hali ne kuwa,da wannan tunanin ta kwanta akan bed ɗinta tare da share hawayen fuskarta.

Engr.AR wanda ya ƙarisa kusa da Mahaifiyarsa tare da durƙushewa a gabanta yana mai kissing fuskarta ya furta,"Momy barka da war haka,dafatan na sameku lafiya?" Shafa kansa tayi tana faɗin,"Lafiya lau my son."Ya zame jikinsa yayi zaman dirshan a gabanta yana faɗin,"Momy hope zan sami fura a fridge ɗinki,shi kaɗai nake da muradin sha." Yakai ƙarshen kalamansa yana shagwaɓe fuska tamkar wani ƙaramin yaro.Murmusawa Hajiya Amina tayi kafin ta shafi fuskarsa tana faɗin,"Indai fura ce ka samu ka gama." Daga haka ta

Ƙwallawa Rabi kira sai gata a guje tana faɗin,"Mah gani." Hajiya Amina ta furta,"Ki kawo ma son fura yanzu." Cike da girmama uwar ɗakin nata ta amsa da faɗin,"An gama Hajiya." Daga haka ta wuce bayan ta zube ta kwashi gaisuwa gurin Engr. ɗin.Tashi yayi ya zauna bisa kujerar dake facing Momyn bayan ya zaro wayarsa yana latsawa, sassanyar fura Rabi ta ciko ƙaramin jug ta ɗauro bisa ƙaramin tray ta kawo ta dire a gabansa.Bayan ta juya ta tafi ne ya tsiyayi furar yana kaiwa bakinsa haɗe lumshe idanuwansa,sanyi da garɗin furar na ratsa maƙoshinsa.Ahankali ya aje cup ɗin bayan ya kwankwaɗe wanda ya zuba ɗin,ya dubi Momy yana faɗin,"Momy Daddy yace yana bisa hanya zuwa jibi ko?" Gyaɗa kai tayi tana faɗin,"Eh haka yace kam." AR ya furta,"Lallai ina ga ba rabon mu haɗu kenan." Da sauri momy ta dubesa tana faɗin,"Meyasa? Ina ce ba jiyannan daga Abuja ka wuce Zaria ba,shine kuma jibi zaka ce baka nan ina kuma zaka sake harbawa? Haba son miyasa baka san ka riƙa zama kana hutawa ne,nifa bana son yawan bin hanyar da kake yi."Murmusawa yayi yana kallon Mahaifiyar tasa,inda sabo ya saba da irin wannan ƙorafin nata akan yawan tafiye-tafiyen da yake yi,sai dai kuma shi ya riga ya saba babu yadda ya iya.Cikin kwantar da murya yake faɗin,"Sorry Mom kedai kawai addu'ar da kike mini nake buƙata,Allah ya cigaba da tsarewa kawai,wannan karon Australia za mu nida Nura abokina,akwai kayan da za mu taho dashi ne domin ginin wani company da aka bamu kwangilar ginawa,kuma dole ne in kasance a gurin domin nina nafi kowa sanin irin kayan aikin dazai dace da tsarin ginin."Murmushi Momy tayi tana faɗin,"To Allah ya cigaba da tsarewa son,Allah yayi albarka ya kawo abokiyar zama ta gari." Cike da murmushi AR ya amsa da faɗin,"Ameen."Kuma daga haka ya lumshe idanunsa fuskar Hamal ya bayyana a cikin zuciyarsa,yana mai jin wani abu mai girma a tattare dashi.Hakan yasa shi miƙewa bayan yakai hannu ya ɗauki ragowar furarsa ya dubi Momy yana faɗin,"Mom bari na wuce part ɗina,ina bukatar na huta kafin lokacin sallah yayi." Momy ta amsa da faɗin,"To son a fito lafiya." Teemah na jin haka ta miƙe ta nufosa tana faɗin,"Big bros ina tsarabata?"Shafa kanta yayi sanin halin rikici irin nata yana faɗin,"Sorry my little Sis tsarabarki saina huta za mu fita Dalema ki siya duk abinda kikeso." Dariya sosai tayi har kumatunta na loɓawa kafin ta furta,"Thank you big Bros a fito lafiya." Daga haka ta juya tana murna.Teemah kenan yar Autan Momy mai shekaru 10 a duniya amma Allah ya zuba mata ɗan karan wayau da shagwaɓa,yar daru ce na sosai sai dai kuma ba ƙaramin so Engr.AR ke gwada mata ba kasancewarta mace tilo a cikin ɗakin nasu data rage musu bayan Yayunta mata 2 da suka rasu a haɗarin mota akan hanyarsu na komawa Base University dake Abuja.Wannan mutuwa ba ƙaramin gigita ahalin gidan Alhaji Attaheer yayi ba,bayan rasuwarsu da shekaru biyu ne Allah yaba momy haihuwar Fateemah bayan an fidda rai ma da za ta sake haihuwa in aka duba shekarun data ɗauka rabonta da haihuwar.Shiyasa su AR da ƙaninsa Abdallah ke matuƙar son Teemah tare da shagwaɓata,Abdallah a yanzu haka yana jami'ar Lynn University dake birnin florida a ƙasar America inda zai haɗo degree ɗinsa akan fannin Architecture,yana shekararsa ta karshe ma yanzu.....✍🏻

To masu karatu ku biyo ni domin jin tarihin waɗannan family,wai shin wane ne Engr.Abdurraheem Attaheer da kuma Hamal Abdulmutallab? Wani irin rayuwa Hamal keyi a gidansu har ta gwammaci ta koma zaman hostel?

*Wani irin matsi da takura take fuskanta daga gurin Hajiya Bilki? Shin Engr.AR zai sake lalubarta ko ya haƙura kenan?* Duka amsar yana tare dani Ayshat Dansabo lemu,sai kuci gaba da bina sannu ahankali domin jin cikakken labarin.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.