Free chapter 路 Read without an account
PAGE 50
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671
FREE-BOOK
PAGE 50
A daidai bakin 茩ofar shigowa Zauren daga cikin gidan Fakiha ta yasar da ledar turaren 茩amshin da Mama ta bata ta kawowa Beenafah bayan ta gama sauraren duk abinda yake faruwa ta koma da gudu ta fa蓷awa Mama.
Ba shiri ta iso zauren hankalinta a tashe domin ko takalmi babu a 茩afarta, jiki na rawa ta lalubo inda switch 蓷in zauren yake ta kunna sai ga Jafaru ta gani tsaye ya jingina bayan sa jikin bango tare da har蓷e hannayensa akan 茩irjinsa yana ta wani huci tamkar zuciyarsa za ta fashe saboda 茩unci da takaici.
A zafafe ta ce.
"Wai kai wane irin Yaro ne Jafaru? Uhm! Wace irin zuciya ce Allah ya yi maka haka?..."
"Ni wallahy Mama kawai an cuceni, kuma har abada ba zan daina son ta ba, dole ta rabu da shi ta dawo ta aure ni, saboda Beenafah tawa ce..."
Wasu tagwayen maruka ta sauke mishi a lokaci 蓷aya hankalinta a matu茩ar tashe ta ce.
"Wallhy! Wallahy Jafaru ka kiyayeni ka kuma kiyayi fushina! Wai kai wane irin yaro ne marar lissafi? Kaga fa ka rufa mini asiri ko Ince ka rufa mana asiri ka fita harkar matar mutane. Wallahy Mutumin nan idan ya 蓷aure ka babu wanda zai iya amsoka gare shi. Ka 蓷auki 茩addara, daman can ita 蓷in ba matarka ba ce. Muna zaune lami lafiya da iyayenta wa蓷anda suka kasance masu mutunci da karamci, tunda idan ba dan Allah ya sanyo su a cikin rayuwarmu ba har ta bamu wa蓷annan ku蓷a蓷en da ina za ka samu shagon zuwa har ake biyan ka? da kuma tura maka ku蓷i idan kana makaranta? Ka yi ha茩uri ka mayarda hankalinka a shago da karatunka, In Sha Allahu za ka samu wata wacce ta fita"
"Ni Wallahy....Wallhy! na rantse da Allah ba zan 茩yale mishi ita ba, sai ya sake ta. Ba zan ha茩ura ba wallahy.."
Daga haka ya yi fuu! Ya nufa ci hanyar waje cike da takaici da ba茩in ciki.
Murya Maman ta 蓷aga hankalinta a tashe tana fa蓷in.
" Jafaru! Jafaru! Jafaru kiran ka nake...ka raba kanka da wahala ka manta da Beenafah."
Har wajen ta bishi tana kiran sunan shi, amma ko ka蓷an bai saurare ta ba, haka ya mi茩e ba tare da ma sanin ina ya nufa ba. Zuciyarsa na yi masa wata irin azalzala da gobarar Son ta, shi sai yanzu ne ma yake 茩ara jin wata sabuwar 茩aunar ta da sonta wanda bai ji zai iya rayuwa da wata 蓷iya mace ba idan ba ita ba.
Cikin gida suka koma daga Maman har Fakiha mamakin duniya ya ishe su. A raunane ta kallin Maman ta ce.
"Wai an ya Mama Ya Jafaru yana cikin hankalin shi kuwa? Ri茩eta fa ya yi....ina jin irin maganganun da yake ta gasa mata masu zafi kamar wanda aka ce ta yaudare shi...wallahy hankalinta ya tashi sosai domin har da marin shi ta yi...Allah yasa dai kada ta fa蓷awa Mijinta ko Ammie..."
Hankalin Mama ne ya 茩ara tashi jin irin abubuwan da Fakiha ke fa蓷a mata, nan take ta sake mi茩ewa tsaye tana fa蓷in.
" Na shiga uku! Mi茩omin wayar nan in kira Babanku...Jafaru ya fara wuce gona da iri. Gwanda a taka mishi burki tun yanzu.."
Wayar ta mi茩o mata ta kira shi tace ya dawo gida....nan ta yi mishi bayanin komai nan take yace yana nan zuwa.
*******
Ni kuwa, koda na shigo motar ko gani bana yi sosai akan yanda zuciyata ta rufe da ba茩in cikin Ya Jafaru. Dama ashe akwai irin wa蓷an nan mazan a rayuwa? Wa蓷an da ba su san 茩addara ba. Na yarda cewa ya so ni can baya, to amma na kasance ba rabon sa ba sai yayi ha茩uri ya manta komai. Amma saboda rashin sanin ya kamata shi ne wai har zai iya bu蓷e bakin shi ya ce wai auren ku蓷i na yi har ma ya ri茩a fa蓷in munanan kalamai akan Mijina wanda ya kasance duniyata kuma rayuwata a yanzu.
Dole cikin da茩i茩u na yi 茩o茩arin sai ta kaina domin idan har ya tuhume akan halin da nake ciki a yanzu ban san ta ina zan fara masa ba. Ce masa zan yi Ya Jafaru ne ya tareni har da ri茩e ni yana fa蓷amin maganganun banza ko me? To idan ma ya turkeni akan mine ne abinda Ya Jafarun ke fa蓷amin nan ma in ce me? Ko kuma in ce Mama ce da Fakiha suka 蓳atamin rai? No..! Babu abu 蓷aya da zai faru, domin dole na bar wannan maganar a zuciyata ko don zumunci da amanar da ke tsakanin Iyayenmu a yanzu.
Wayar da na tarar yana yi da Jadda ita ce abin da ya 茩ara kwantar min da hankalina sai na kar蓳i Wayar ina mai kawar da fuskata domin har yanzu idanuna da sauran hawaye a ciki amma ba don na manta da abin da ya yi mini 蓷in ba.
Nan na shashashace muna ta Waya har da su Suhaib sai dariya nake jin yanda yake cewa wai ko a Keke ne sai an 蓷aurani an kai ni bikin sa, tun da ya ji Ya Mohaa yana fa蓷in bani da lafiya kuma ina bu茩atar hutu.
Bayan mun koma gida, sai da muka gama duk wani night routines 蓷inmu sannan muka kwanta. Bayan na kwanta a inda ya fiye mini ko'ina sanyi da da蓷i, wato saman 茩irjinsa na ji wasu irin sabbin hawaye sun kwararo mini tuna irin wula茩ancin da Ya Jafaru ya yi mini a 蓷azu, da mutuncina da komai wai haka ya ri茩e ni don kawai yana marar mutunci wanda bai san darajar aure ba.
"Dayaa!"
Na kira sunansa a raunane ina mai 蓷ago fuskata na kallesa da sauran hasken bedside lamp.
"Bibi! What's wrong? I notice that you are not ok, tun da muka dawo kamar ba ke ba."
" Yaushe zamu tafi?"
Na tambaye shi kai tsaye domin tsoron Ya Jafaru ya yi matu茩ar sanyani a fargaba. Tsoro nake kada ya sake ri茩eni watarana duk da cewa yana da wahala ya sake kwatanta irin hakan domin naga kamar ya razana da irin garga蓷in da na yi masa. Gaba蓷aya sai naji zaman garin ma ya fice mini a rai.
Hannuna ya kama tare da twisting 蓷insa a cikin nasa yana kallona, muryarsa ya kwantar a hankali yana fa蓷in.
" Gobe da yamma In Sha Allah nake tunanin mu tafi. Ina so mu koma gida domin ki fara ganin likita cikin lokaci, kuma kina da bu茩atar ki huta, idan kina nan ba za ki daina yawo ba. And nima kin ga ayyuka sun taru a kaina sosai, I need to go back..."
Murmushi na yi masa, a raina ina mai jin tausayinsa sosai akan yanda yake ayyuka ba dare ba rana kullum kamar wani Engine.
" Ba fa wani damuwa. Duk ka wani 蓷aga hankalin ka sai wani lalla蓳ani kake...To ai nima so nake mu tafi."
Dariya ce ta su蓳uce masa ba tare da ya shirya ba,domin jin irin yanda na amsa shi abun ba 茩aramin dariya ya bashi ba. Bayan ya tsahirta da dariyar ne ya ce.
" Wato in dai na ma wahalar da kaina ina lalla蓳aki domin kin riga kin shirya bin mijin ki..."
Hannu na saka da sauri na rufe masa baki ina dariya tare da runtse idanuna na jin wannan maganar da yake furtawa. Yanzu daga yin magana ta har ya juya mata fassara zuwa wani abu daban.
Lafewa na yi wanda ina jin sa yana ci gaba da tsokanata har bacci ya sace ni ban 茩ara yi masa magana ba.
Washegari muna zaune muna breakfast sai ga kiran Aunty Labiba tana shaida masa cewa Aunty Ziza ta haihu ta samu 蓷iya Mace. Warce wayar na yi cike da zumudi ina ta fa蓷in Allah ya raya gamu nan zuwa.
Kallona ya yi bayan na ajiye wayar ya ce.
"Gaku nan zuwa a ina? Kin manta yau ne zamu tafi.."
Jikinsa na kwanta a hankali tare da shagwa蓳e murya na ce.
"Ni dai dan Allah ka tafi to ka barni,daga baya idan an yi sunan sai ka zo mu tafi.."
"Me ne? In bar ki ki zauna don ki wahalar da kanki da kuma Babynmu Bibi? No..! gaskiya ban amince ba..."
"Eyyah! Please please! Dan Allah mana!...bai kyautu ace an yi haihuwar nan muna gari ba kuma mu tattara mu tafi...atleast ko don kasancewar Matarka karon ta na farko a cikin hidimar gidanku ya kyauta ace na tsaya...and Emraan will be happy ace matakar tana nan a hidimansa, su Aunty Labiba too..please!"
Jin ya yi shiru bai ce komai ba yasa na 蓷ago na kallesa tare da kama hannayensa na kwantar da Murya na ce.
" Na san ka fini sanin abin da ya kamata Mijina..tunani, hankali, da sanin ya kamata duk ka fini sam ba za'a ha蓷amu ba. Ban isa na zartar da hukunci ba domin kai ne shugabana kuma kai ne kake gaba da komai. Amma tunanine na yi da ganin kamar hakan zai yi amfani, domin ta hakanne 茩annenka za su 茩ara ji a ransu cewa ka zubar da komai ya wuce, Hajiya ma haka. Idan kuma kaga tafiyar tamu yafi ba damuwa za mu iya tafiya..."
Kallona yake a hankali jin irin maganganun da nake furta masa. Sosai ya ji manganuna sun shige sa domin ban ta蓳a neman sa alfarma irin wannan ba sai a wannan karon. Idan ya 茩i ya amince kuma hakan har abada ba zai barshi ya samu sukunin zuciya ba. Tunanina da iya maganata suna 茩ara sanya shi jin akoda yaushe cewa ni 蓷in dai ni ce nafi dacewa da rayuwar sa sama da kowace a duniya....
"Ka ce wani abu mana dan Allah..."
"Bibi...lafiyar ki da ta jaririnmu sun fi mini komai muhimmanci a yanzu..."
"In Sha Allahu babu abin da zai same ni. In Sha Allahu Allah zai tsare maka ni a duk inda nake a fa蓷in duniyar nan, and I promise zan kula maka da kai na sosai da kuma Babynmu babu abin da zai same mu.."
Cikin yarda da kalamai na ya jinjina kansa sannan ya ce.
" Yau wace rana ce?"
Da sauri na ce.
" Saturday ce."
"To zan dawo Sunday, Monday mu wuce..."
Rungumeshi na yi tare da kwararo masa addu'o'i da kuma yi masa kalamai sannan na janye daga 茩arshe ina kallon sa ina murmushi na ce.
"And saura naka al茩awarin da za ka 蓷aukar min.."
"Na me kenan?"
"Cewa za ka yi..Ni Mijin Beenafah, Abban Babynmu mai zuwa, I promise to take care of my self kamar yanda Bibina ta yi al茩awarin cewa za ta kula da kanta da Babynmu, zan ri茩a cin abinci cikin lokaci, sannan zan yi bacci ma cikin lokaci, kuma na yi al茩awarin rufe idanuwana daga kallon kowace irin Mace koda ta Kara ce...."
Dariya ya shiga yi sosai wanda sai da yaga na 蓷an 蓳ata fuska sannan ya daina yana mai rungumoni zuwa Jikinsa ya maimaita min duk abinda na ce masa ba tare da gargada ba sannan daga 茩arshe ya ce.
"Bibi! Ki yarda da magana ta, duk wata Macen da za ta tsaya a gabana idan har ba ke bace to ni a wurina ba Mace ba. Ke ce komai tawa Bibina...ban san yanda zan iya rayuwa da wata Macen a duniyar nan idan ba ke ba. Ina 茩aunar ki sosai.."
"Uhmm! Ni ma haka fa. Sosai nake son ka,.."
Mun jima a zaune muna ta shan nisha蓷in soyayyarmu sannan daga 茩arshe muka tashi muka koma 蓷aki muka 蓷ora sabon zama wanda sallah ka蓷ai ke tashinmu. Sai kusan 5pm muka fito har Biba muka wuce gidan Hajiya Inda Aunty Ziza take.
Sai da ya gama ganin Babyn sannan na rako shi tare da Aunty Labiba muka fito har bakin mota sannan ta Juya ta koma. Duk budurin nan da muke ban ji hankalina ya tashi ba sai da ya shiga mota zai wuce.
Motar na shige na zauna tare da 蓷ora kaina a gefen shoulder 蓷insa na fara rera masa kuka..a ru蓷e ya juyo da fuskar sa yana kallona ya ce.
"Subhanallah! Miye kuma na kuka?ko kin fasa zaunawa Mu tafi?"
Saurin ha蓷iye Kukana na yi ina mai jinjina kai na na ce.
" Ni fa bana son ka tafi ka barni.."
Kallon Drivernsa ya yi ya ce.
"Mu tafi kawai Sidat..."
Waro ido na yi da sauri na ce.
"Ni fa ban ce mu tafi ba.."
Dariya ya yi sannan ya girgiza kansa ya ce.
"Bibi rigima...ba za ki je ba, kuma bakya son na tafi na barki...to ki yi ha茩uri kinji.. Ni ma ba don na so hakan ba. Amma In Sha Allah kamar gobe ne.."
A hankali na kai bakina na ha蓷e da nasa na yi kissing 蓷insa har zuwa wuyansa still da ruwan hawaye a idona na janye ina kallon sa na ce.
" Allah ya tsare min gabanka da bayanka. Allah ya taimakeka ya biya maka bu茩atunka na alheri."
"Amin Bibina..na gode sosai."
Fitowa na yi daga motar still ina yi ina share hawayena har na koma cikin gidan. 茒akin Aunty Ziza na sake komawa inda na tarar ida ita zaune ita ka蓷ai tana kiran su Munira wai su zo su canjawa Baby Pampers ta yi kashi. Kar蓳ar ta na yi kai tsaye na shige na wanke mata na dawo da ita na zauna na canja mata diaper 蓷in da kaya sannan na rungumeta a jikina tare da janyo wayata na lalubo numbern Ammie na kira ta.
Duk wayar da nake tana nan zaune da wayar ta a hannu tana chart amma kuma hankalinta yana kaina.
Ina nan ina magana a wayar sai ga Aunty Labiba ta shigo. Wuri ta samu ta zauna suka ci gaba da magana da Aunty Ziza, bayan na kambala na biye su muka ci gaba da firar har aka kira sallar magriba sannan muka tashi muka yi.
Bayan Aunty Labiba ta wuce gida. Wani 茒aki Hajiya ta bu蓷emin tace na shiga, idan kuma ina son na ta ne to in zo mu kwanta. Wato yanda take ta wani nan-nan dani wallahy har tausayi ta bani. Hakan yasa na saki jikina da ita komai na yi kamar bai faru ba. Sannan ni ko Hajiyar ma bana kiranta Momma na dawo ce mata kamar yanda na ji Dayaa yana kiranta, wanda na lura hakan ba 茩aramin farin ciki ya sanyata ba.
Washegari, Ammie da Maman Fakiha a tare suka zo barka har da Aunty Aysha wanda na ji da蓷in hakan sosai.
Ba su wani jima ba suka fito na rako su har bakin gate na biyu sannan Mama ta jani gefe 蓷aya with a pleading tone ta fara mini magana da cewa.
"Beenafah dan Allah ki yi ha茩uri da abin da Jafaru ya yi miki kinji. Dan Allah ina baki ha茩uri, In Sha Allahu ba zai sake ba...Tun jiya na tambayi Hajiya Mulaifa numbernki ta turo mini amma na kira baki 蓷auka ba. Dan Allah ki yi hak'uri, shirme ne kawai irin na shi amma na yi masa fa蓷a sosai kuma na ja masa kunne..."
Murmushi na yi mata sannan na ce.
" Ai ba komai, In Sha Allahu ya wuce. Wayata kuma wata 茩ila bana kusa ne shiyasa ban lura ba, saboda a silent nake barinta. "
" To ba damuwa, na gode. Allah ya 茩ara miki zaman lafiya da kwanciyar hankali."
"Amin Mama, Allah ya tsare."
Daga haka muka yi sallama da su na koma ciki. Wurin su Munira na wuce direct muka sha firarmu sosai sannan na tashi na koma ciki.
Lafiya lau muka zauna tsawon kwanaki uku, wanda na ji da蓷in zaman gidan ba ka蓷an ba, musamman da Ziza ta sake dani sosai tana ta wani ja na a jiki tamkar ba Zizar da na sani ba. Kwata kwata sai naga ta sauya min, sai yanxu ne nake ganin kirkinta da ake ta fa蓷in cewa tana da shi, tana da kirki sosai tana son mutane, abun da na fahimta shi ne, tana da matu茩ar kishi ne wanda yake rufe mata ido yake sanyata yin wasu abubuwan da ba su kamata ba. Kuma a yanzu ni sam ban ga laifinta ba, domin kishi gaskiya ne, kuma a yanda nake jin kai na a yanzu wallahy komai zan iya yi akan Mijina.
A hankali en uwan Ya Emraan 蓷in dana Ziza suka fara taruwa. Shi ma sai wani farin ciki yake ya kasa nutsuwa wanda na fahimci sosai yake cikin farin cikin wannan Haihuwar da aka yi masa. Lafiya 茩alau muka gaisa da shi kamar yanda muka yi a waya lokacin da ya kira Ya Mohaa yayi min ya jiki.
Yanda kowa ya kar蓳eni ba 茩aramin farantamin yayi ba. Duk wanda ya zo sai sun janyoni suna nuna ni suna cewa ni ce matar Muhammad. Addu'ar da suke min itama ba 茩aramin farantamin take ba wanda tsakanina da su sai son barka.
Aunty Nadeeyah ta yi takaicin rashin zuwan ta domin Babansu Dija yace tunda akwai aure nan kusa ta yi ha茩uri ta bari sai lokacin ta zo.
Dangi Hajiya suna da matu茩ar kirki sosai da kuma nuna kara, Baba Ustaz ma bai zo ba amma Mummy Na'Imatu ta zo ita da yaranta su uku.
Ina nan zaune a 蓷akina bayan sallar Magriba ina Azkhar sai ga kiran ba茩uwar number na gani, bayan na duba ta a true caller ne naga sunan Maman su Fakiha.
Ina 蓷agawa ashe Fakiha ce take shaidamin auren Hafsa wai wannan juma'ar za'a yi. Dariya na yi sannan na ce.
"To Fakiha ni miye nawa?"
苼ata fuska ta yi daga can 蓳angaren tamkar tana a gabana ta ce.
"Haba Beenafah! Hafsa kin san yanda take 茩aunar ki. Wallahy bata san cewa kina gari ba sai shekaranjiya dana sanar mata, kuma ta so zuwa har gidanki ta kai miki kati na ce mata kina gidan Surukanki matar 茦anin Mijin ki ta haihu. Numbernki kuma na ce mata bakya 蓷aukan ba茩uwar number. Please ki daure ki zo ko 30mnt ne ki yi. "
Girgixa kai na na yi ina fa蓷in.
" Fakiha na yiwa Mijina al茩warin ba zan fita yawo ko'ina ba, ba wai zai hanani ba ne a'a, kawai ya kamata komai mutum zai yi ya ri茩a lissafi..amma zan gwada tambayar shi inji idan ya amince zan le茩o ko 30mnt 蓷in ne kamar yanda kika ce. Ki bata numbernta ki ce ta kirani, ko banzo ba muna iya ri茩a gaisawa koda a what'sapp ne."
"Ok tau, in sha Allah..."
Dariya na yi sannan na ce.
"Oh Allah! Wai Fakiha ashe akwai ranar da za ta zo ki yi hankali ki daina rawar kai??"
Tsaki ta buga tare da kashe wayar baki 蓷aya.
********
Jafaru kuwa, duk tsawon kwanakin nan ya kasa zaune ya kasa tsaye, ko baccin kirki baya iya yi gaba蓷aya ya zabge lokaci 蓷aya kamar wani Naman Miya abin duniya duk ya bi ya ishe sa. Tun jiya ya kamata ace ya koma makaranta amma sam ba wannan ne a gabansa ba, tunda har Beenafah tana garin to wallahy sai ya ga abin da ya turewa buzu na蓷i. Tunanin ta da soyayyar ta sun hana masa sukuni, komai yake ita yake gani a idanunsa.
Duk kwanakin nan yana yawan zuwa gidan su wani babban abokin sa Baba Kali amma baya samun shi a gida sai yau ne ya ci sa'a ya tarar da shi.
Baba Kali na ganinsa ya ce.
"Wai daman baka koma Zaria ba Jafar?"
Wuri ya samu a bencin da Baba Kali 蓷in yake zaune ya zauna yana fa蓷in.
"Mts! Ka bari kawai abokina, komai ya kwance mini.."
"Kamar ya kenan? Ba ku蓷in registeration ne?"
"Ba shi ba, zance ne akan Beenafah.."
Waigowa ya yi suna fuskantar juna da kyau ya ce.
"Miye ya faru da ita Beenafahr? Ba ka ce an aurar da ita ba?"
Tamkar zai fashe masa da kuka haka ya shiga bashi labarin komai da yake faruwa da abin da ya wakana sannan daga 茩arshe ya ce.
"Wallahy Kalifa ba zan ha茩ura ba. Ina son ta, kuma ina ji a jikina ita ce Matata..."
Jinjina kai Baba Kali ya yi sannan ya ce.
"To ai kaima dai Jafaru ka yi wauta tun farko da ka bari wannan santaleliyar yarinyar ta ku蓳uce a hannunka. Yanda ka raineta kuka sha茩u 蓷in nan ai in ni ne wallahy tallahy ko gidanmu za'a siyar sai dai a siyar amma sai an aura mini ita....sannan da kake mahaukaci waye ya fa蓷a maka cewa yanzu za ka iya janyo ra'ayinta ta 茩arfi? Ku蓷i fa aka ce maka Jafaru. Ku蓷i manya-manyan ku蓷i ba 茩ananu ba. To idan baka kwantar da kai ba ta ya ya za ka samu ta dawo hannunka?"
Wani irin abu yaji ya tartsa masa a zuciya wanda sai yanzu da Kalifan ke wannan maganar ya ji dama ce tun farko ya haukace musu da gasken, da yanxu Beenafah tana hannun sa.
茦ara marairaice fuska ya yi yana fa蓷in.
" Wallahy Baba Kali sai ma ka ganta a Yanxu..Yanda ta 茩aro wani irin kyau da wani shape za ka rantse da Allah ba mutum ba ce. Kyaunta ya 茩ara bayyana fiye da da, kuma tana nan da halin kirkin nan nata,...kai ko shi kirkin kamar 茩aro mata shi akayi, domin duk daular nan da take ciki ko ka蓷an ba sai ta sauya ba...Wallahy Kalifa har yau har abada banga mai kyau Beenafah ba da duk wasu good qualities da ta tara. Rasa ta ba 茩aramin asara ba ne a wurina, ina masifar sonta, son da ba zan iya ha茩ura ba..."
Dariya Baba Kali ya bushe da ita sannan ya ce.
" Abokina ba dole ka ru蓷e ba, Kaga jinin Larabawa, fata tayi kyau sai walwali take, ai dole ka fice hayyacinka.. "
" Don Allah ni dai ka taimaka mini domin in samu yanda zan yi ta dawo gare ni..Kaga numebrn wayan ta nan na 蓷auko a waye Mama tun jiya da dare bayan Fakiha ta gama magana da ita. "
Still da dariya a fuskarsa ya ce.
" To ni dai shawara ta guda 蓷aya ce, daman can tun farko ai kasan tana sonka..to muddin dai son nan da take maka na gaskiya ne to yana nan babu inda ya tafi. Saboda haka ba da fa蓷a za ka je mata ba, ka lalla蓳a ta ka nuna mata cewa kafi ta ma son abin da take so...ka kwantar da kanka ka lalla蓳a ta ka nuna mata irin son da kake mata, In Sha Allahu za ka da ce.."
Wani uban tsaki ya buga tare da Girgixa kai cike da takaici ya ce.
" Wai har da wani ciki take da shi, su kuma sai wani murna suke..wallahy sai na yi maganin su, gaba蓷ayansu sai na yi maganin su..."
"Uhm to! Ka dai yi a hankali kam, kada kwa蓳arka ta yi ruwa,domin idan Engineer ya kama ko wallahy sai ka yi warin mutuwa..."
Tsaki ya buga sannan ya ce.
"Engineern banza da wofi! Mugu kawai mai raba masoya..."
Dariya Baba Kalin ke yi har yana kwantawa tsabar yanda abokin na shi ke bashi dariya wanda har sai da ya ga ya fara tsarguwa sannan ya daina. Sosai ya shiga bashi shawarwarin yan da zai yi har ya samu ta dawo gare shi. Wannan shawara ba 茩aramin farin ciki ta bashi ba domin ta sanyaya mishi zuciya ba ka蓷an ba.
********
Da 茩yar na samu ya amince min, ko shi don Hairi ta dawo ne yasa ya amince,amma cewa ya yi kada na wuce hour 蓷aya highest Idan na jima a gidan.
Sosai na yi masa godiya sannan washe gari muka shirya muka fito misalin 茩arfe hu蓷u na yamma. Oga Sule muka tarar ya kawo wata sabuwar Mota babba ba茩a wulik har bakin harabar gate na biyu ya kara ta.
Muna shiga na yi masa bayanin gidan su Hafsa sai gashi nan da nan ya kaimu har 茩ofar gidan, daman gidan su ba shi da wani nisa da Islamiyyarmu domin kan hanya suke.
Sosai ta ji da蓷in ganina kamar yanda nima na ji da蓷in ganin su har da en ajinmu. Nan muka zauna muka yi ta fira ana ta nisha蓷i har aka shirya za'a wuce da ita wurin wanka, nan na bata 50k sannan Hairi ta bata jakar turaruka da Hajiya ta bayar da kuma package na spices da Aunty Ziza itama ta aika aka kar蓳o da Eatry 蓷inta. Sosai taji da蓷in wannan kyautar har da Maman su sai da tayi godiya domin kayane masu yawa masu kuma tsada.
A tare da Fakiha muka fito ta rakomu har mota, Babu wanda bai yi mamakin ganin Ya Jafaru tsaye a gefe ba yana aikin kallon mu. W
Take annurin fuskata ya 蓳ace domin idan akwai wani wanda na tsana a rayuwata yanzu to Ya Jafaru ne. Kallona Fakiha ta yi ta ce.
"Dan Allah Beenafah ki yi ha茩uri, cewa yayi ki 蓷an basa lokaci ka蓷an yana so ya baki ha茩uri ne akan abun da ya faru ranar.."
"To kuma babu inda zai bani ha茩urin dole sai nan gidan mutane?"
Da sauri ta girgiza kanta tana fa蓷in.
"Ba haka ba ne, ya ce min dan Allah kada ma in bari su Mama su ji, shiyasa ya za蓳i nan 蓷in."
Ta蓳e baki na yi tare da 茩ara 蓷aure fuskata na ce.
"OK! To ki ce yazo nan mana ya fa蓷i dukkan abin da zai fa蓷a..."
Girgiza kai Hairi ta yi tana fa蓷in.
"A'a Mummy! Tun da yace ki je dan Allah ki je, ba gamu ba...ga mutane ko'ina. Ki je ki saurare shi."
Jin maganar da Hairiyya ta yi ne yasa na taka tamkar zan ha蓷iye zuciyata na mutu saboda ba茩in ciki. Ina zuwa na tsaya tare da kallon shi a she茩e茩e na ce.
" Ga ni..."
茦asa ya yi da murya kamar da gaske ya ce.
" Zuwa na yi in fa蓷a miki wallahy tallahy har abada ba zan ta蓳a ha茩ura da ke ba. Na san cewa kina so na Beenafah, kawai dai 茩addara ce ta yi mana rigaye a tsakaninmu. Saboda haka na ba ki lokaci ki je ki yi nazari. Dan Allah Beenafah ki dawo gareni...Ya Jafarun ki ne fa! Ban san komai ba idan ba son ki da 茩aunar ki ba. Ba zan iya rayuwa ba idan babu ke Beenafah..Na san cewa fushin zuciya ne ya sanyaki aikata abin da kika aikata kamar yanda nima fushin zuciyar ne. To amma ki sani ni babu wata mace a raina har abada sai ke. Ko shekara 蓷ari za ki yi zan iya zaunawa na jira k... "
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Jikina na rawa na furta masa hakan ina mai Girgixa kaina,sannan daga 茩arshe na ce.
" Ubangiji Allah ya shirye ka."
Daga haka na juya na je na shige mota ina mai yiwa su Fakiha ya茩en 茩arfin hali domin ka蓷an ya rage zuciyata ta tarwatse tsabar ba茩in ciki. A yau tabbas yaci darajar su Hairi ne,domin hana so in yi wani move 蓷inda za su gane cewa akwai matsala, amma da ba dan haka ba wallahy tallahy da sai na yi masa abin da yafi na ranar ma.
Wai anya Ya Jafaru bai haukace ba kuwa? An ya bai fara shaye-shaye ba?
Idan ba shi ba wane irin 茩arfin hali ne haka 蓳arawo da sallama? Shi yanzu ashe har yana da guts 蓷in biyoni cikin taron jama'a yana fa蓷amin maganganun banza? Wallahy darajar Su Mama na ke dubawa amma Kada ya bari ya kai ni ma茩ura. Ji yanda Mama ta dinga magiyar bani ha茩ura dan Allah? Amma saboda Jakki ne shi shi ne yau ya sake dawowa. Ya Hamza ma ko 蓷azu sai da ya kirani da safe muka gaisa lafiya lau ya yi mini ya jiki. Amma da yake 茩wa茩walwar kifi ne da shi ya kasa gane kawaicin da nake masa. Shi ne fa dalilin da yasa na cire son zuwa gidan su Yaya Ashiru a raina da nake ta 蓷oki,domin ban san shi ma ta ya ya zai kar蓳eni ba daga har iyayensa. Ina jin kewar sa a raina, kuma na so zuwa gidan su kamar me, to amma hakan ba zai samu ba, domin kada ya gaza fahimta ta kamar yanda wannan shashashan yake.
Koda muka isa gidan na tarar wai Aunty Ziza ta kawo min 茒inkin da zan sanya gobe wanda sun yi kyau ba ka蓷an ba. Amma kuma ni dai ban yanke saka su ba, domin Aunty Labiba ta kawo mini 蓷inkunan da Ya Mohaa ya biya domin a 蓷inkamin tun daga Kaduna wurin Aunty Nadeeyah. Kuma kayan Mijina sun zan saka gaskiya, sai daga baya watarana can na saka idan ina ra'ayi, amma ban nuna mata ba, domin sosai na yi ta zuba mata godiya tare da yaba yanda 茒inkunan suka tsaru.
Washe gari da wuri aka gama tsara komai. SOS event aka gayyato na musamman suka 茩awata harabar gate na 蓷aya da decoration wanda ya ha蓷u sosai. Wani abun burgewa da farin ciki shi ne, RANIA (Mima) shi ne sunan da Emraan ya ra蓷awa Babyn. Hakan ba 茩aramin farin ciki ya sanya Ya Mohaa ba, domin daga yanda yake ta nanata min maganar cike da jinda蓷i shi ne ya tabbatar min da cewa ya yi farin ciki sosai da wannan karamcin da Emraan ya yi masa.
Nan aka sha Hidima wanda ni ina wuri 蓷aya domin ban yi wani zirga-zirga ba kada na wahala da yawa. An ci an sha Alhamdulillah! an sha hotuna kamar ba gobe ga kayayyakin rabawa nan kamar banza komai an yi shi Masha Allah. Su Ammie na wuce nima na tattara ni da Hairi muka shige ciki.
Bayan na kambala sallar Isha na mi茩e daga parlourn da muke zaune na ce musu zan shiga na yi wanka na kwanta domin na gaji sosai.
Na gama cire kaya kenan na 蓷ora towel na ga wata sabuwar number tana kira na. Ba tare da kawo komai a raina ba na yi picking domin na san cewa na baiwa en ajinmu numbernta da yawa, to wata 茩ila daga cikin su ne wata ta kira. Sai dai kuma, muryar da na ji ita ce ta kusa Sumar da ni tsabar mamaki da al'ajabi.
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍