Free chapter · Read without an account

AMRAH PART 02

by Hussain Yusuf · AMRAH

AMRAH

<<PART 02>>

Hajiya Laila ta kalli Alhaji Kabir, zuciyarta cike da zafi da baƙin ciki. Ta fashe da kuka ta ce masa, "Alhaji, ‘Yan Biyu na haifa! Na gansu da idona! Amma yanzu sun ce min ɗaya kawai na haifa."

Alhaji Kabir ya riƙe hannunta, ya jawo ta a hankali suka zauna gefen gado. Sai da ya ga ta ɗan nutsu, sannan ya dubeta, "Ki kwantar da hankalinki, Matata, ki daina ruɗewa haka. Kin sani, lokacin da ki ka haihu ba kya cikin cikakken hayyacinki. Wataƙila hakan ne ya sa ba za ki iya tabbatar da adadin 'ya'yan da kika haifa ba."

Ta ƙara fashewa da kuka, "Haba Alhaji! Me kake faɗa haka? Don Allah kar ka yarda da abin da suke gaya maka. Wallahi tallahi 'Yan Biyu na haifa duka mata, kuma sun yi kama da juna, babu abin da ya raba su!"

Jikin Alhaji Kabir ya yi sanyi. Yadda Hajiya Laila ke ta kuka ba tare da ya iya rarrashinta ba, ya sa shi fara jin cewa da gaske take. Amma kuma babu wata hujja da zai kama wacce zai iya kai ƙarar asibitin da ita. Da ƙyar ya lallaɓa ta har ta yarda suka tafi gida, bayan ya yi mata alƙawarin zai kai asibitin kotu har sai sun gano inda ɗiyar tasu take.

***

Ƙauyen Kiyawa

Tsakiyar dare ne, ƙauyen Kiyawa ya yi tsit. Ba a jin sautin komai sai kukan gyare da tsuntsaye da suka mamaye ko’ina. Duhun ya yi tsananin gaske, ko tafin hannunka ba za ka iya gani ba.

A can bayan gari, wata bukkace ita kaɗai, kewaye take da manya-manyan bishiyoyin kuka da tsamiya. Cikin bukkar, wasu ma'aurata ne kwance a kan gadon ƙarfe. A gefe kuma, wani ƙaramin gado ne na katako, a kansa wata matashiyar budurwa ce mai suna Amrah, take sharar barcinta cikin kwanciyar hankali.

Wani baƙin hayaƙi ne mai yawa ya taso daga kan wata doguwar bishiyar kuka da ke kusa da bukkar. Ya fara shiga cikin bukkar, ya sauka kai tsaye a kan gadon Amrah, ya haɗe wuri guda. Yana gama haɗewa, sai ya fara jujjuyawa har ya koma siffar wata ƙatuwar kunama baƙa ƙirin mai ban tsoro. Jikinta duk gashi ne mai kaifi kamar allura, kuma a tsakiyar kanta wani dogon ƙaho ne mai tsini a kafe. A ƙarinta kuma baƙin ruwa ne ke ɗiga, cike yake da ƙananan baƙaƙen ƙwari waɗanda ke fitar da wata irin ƙara kamar an cusa wa mutum ƙwari a cikin kunne.

Kunamar ta hau kan ruwan cikin budurwar, ta kwanta a kan ƙirjinta. Hakan yana faruwa, baccin Amrah ya ƙara nauyi. Kunamar ta matso da ƙarinta kusa da bakin yarinyar, nan take bakin ya buɗe da kansa, sai kunamar ta ɗiga mata baƙin ruwan dafin a baki, nan take ta haɗiye shi. Bayan haka, kunamar ta koma baƙin hayaƙi. Hayaƙin ya rinƙa shiga jikin Amrah a hankali ta hanci, baki, kunne, da dukkan ƙofofin gashin jikinta.

Yana gamawa, Amrah ta farka a firgice, ta kwalla wani irin ihu mai ƙarfi wanda ya cika cikin ƙauyen da wajensa. Amma babu wanda ya ji, balle ya farka, har da iyayenta da suke a ɗaki ɗaya. Nan take wani irin tari ya sarƙe ta har numfashinta ya fara sarƙewa. Gumi mai zafi ya fara fita daga ko'ina a jikinta. Ta yi tsam a kan ƙaramin gadon tana jin yadda jikinta ke ɗaukar zafi kamar ana gasa mata garwashi. Bayan kusan minti ashirin, komai ya daidaita, sai ta koma ta kwanta, ta cigaba da baccinta tamkar babu abin da ya faru da ita.

Kiran sallar farko, Malam Buba ya tashi daga barci kamar yadda ya saba. Ya fita daga bukkar, ya ɗauro alwala, ya dawo ya hau tashin matarsa Ladidi don ta yi sallar. Yana shirin fita sai idanunsa suka sauka kan Amrah da ke ta minshari a kan gado. Da farko, sai ya ga wasu baƙaƙen kunamai sun yanyame gadon da take kai, hatta bargonta sun rufe shi, ba a ganin gadon sai baƙaƙen kunamai. Cikin tsoro, ya murza idanunsa, ya sake kallon gadon, sai ya gan ta a kwance tana barcinta, babu kunama ko ɗaya a jikinta.

Ya sauke ajiyar zuciya, ya ƙarasa jikin gadon ya fara tashinta, "Amrah! Amrah!! Ki tashi, lokacin sallah ya yi." Ta yi miƙa, sannan ta tashi zaune. Ta kalli Malam Buba, sai ta ga wata ƙatuwar macijiya ta buɗe baki za ta haɗiye ta!

Nan take Amrah ta saki wani irin ihu, ta diro daga kan gadon, ta kwasa a guje tana ihu tana cewa, "Don Allah kar ka cinye ni! Wayyo na shiga uku! Baffa, ku taimake ni, wannan macijiyar zata haɗiye ni!" Duk lokacin da ta buɗe baki da niyyar karanta addu'oin da Baffanta ya koya mata, sai ta ji bakin ya yi mata nauyi, kuma ta kasa karantawa a cikin zuciyarta.

Malam Buba ya bi ta da gudu yana kiranta. Amrah kuwa, duk lokacin da ta waigo sai ta ga wannan ƙatuwar macijiyar ce ke biye da ita za ta haɗiye ta, ba mahaifinta take gani ba. Da Malam Buba ya ga tana shirin shiga cikin daji, sai ya fara ihun neman taimakon mutane. Allah Ya taimake shi, mutane sun fito daga masallaci kenan, suka hango Amrah tana gudu tana ihu ta nufi daji. Nan take suka bi bayanta, suka kamo ta, tana wani irin ihu wanda bai yi kama da irin na mutane ba. Kai tsaye suka nufi gidan Boka Rubbas da ita, domin ya shahara a cikin ƙauyen da wajensa wajen yaƙar aljanu, komai hatsabibancin aljani ƙone shi yake ƙurmus.

Hussain Yusuf✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.