Free chapter · Read without an account
Page 29 _ 30
💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
🅿️ 29 _ 30
⭐️
Sadeeq ya ce, "Umar what did you mean? And me kake cewa? Sadiya ni take so? When did she told you? Kuma a ina ta sanar da kai haka? Umar please keep this as secret kamar yadda nayi keeping nashi for all those year's, Sadiya Haidar take so kuma shi za ta aura."
"Mtswww!, na bi soyayyar da ita Sadiyar da Haidar ɗin da mugun gudu, kai Sadiya za ta aura, batun tana sonka ko ba ta sonka kuma kai ka fi ni sani, tunda kai kana sonta."
"Sadiya ba ta so na, Haidar take so", Sadeeq yayi saurin faɗa yana katse Umar.
Umar taɓe baki yayi har sannan fiskarshi a haɗe, ya ce, "Sai ta mutu da son Haidar ɗin, amma kai za ta aura."
"Don't try this Umar, kar ma ka sake faɗan irin haka, na fi son ta rayu fiye da na rayu, ka barta ta auri wanda take so ta rayu da shi."
"Lemme tell you Sadeeq, yanzu ina barin nan sai wajan Mama first, in tabbatar mata har da shaidu, ina da tabbacin a take za ta mallaka maka Sadiya, kuma da mace na ɗaura aure to ina da tabbacin a wajan za ta aura maka Sadiya ba tare da na motsa ba, sai dai daga wajan Mama zan wuce wajan mai ɗaura wa Sadiya aure, wato Abba, na sanar mishi da komai da saƙon Mama shi kuma ya shige gaba a ɗaura auren da kai, su kuma waɗancan a ba su haƙuri."
"Umarr!", da ƙarfi kuma a tsawace Sadeeq ya ƙira sunan Umar ɗin.
Umar ma a tsawace ya ce, "You can't stop me Sadeeq, na faɗa maka ba ka isa ka sa nayi shiru ba, ba ka isa ka sa nayi abinda banyi niya ba, baka isa ka sa na ɓoye munafurtata da kayi ba, duk abinda za ka yi ga fili ga mai doki ka yi, amma sai an ɗaura muku aure da Sadiya in sha Allah muddin ina numfashi."
"Wai Umar ina ruwanka da ni? Umar me damuwarka da ni? Ubanwa ya ce ka je ka mini bincike? Akan me ma za ka mini bincike? Waye ya buɗe maka box ɗin?"
"Ina da ruwa da kai, damuwata da kai ka samu abinda kake so sai kuma munafurtata da kayi, sannan uban da ya ce ka ɓoye mini halin da kake ciki shi ya ce na maka bincike ɗan rainin hankali kawai, kuma na binciko ka jima baka yi abinda za ka yi ba, ai kai ka ƙalubalance ni a kan hujja, kuma ga shi na kawo maka, batun buɗe box bazan faɗa ba idan kana da ƙarfi ka sa na jiyo ƙamshin barzahu sai na faɗa maka."
"Umar a karo na ƙarshe, am warning you, kada ka bari kowa ya ji wannan magana."
"Assume it as topic of the day, daily news, or even international newspaper, duk wadda ranka ya so ka ba shi wannan matsayin, domin loudspeaker ne kawai bazan ɗauka ba, but babu wanda ba zai ji maganar nan ba, take Khausar as example domin ta sani kamun na taho ma."
Sadeeq ya ce, "Umar don't try me."
"Sai na kai ka bango Sadeeq yadda ka kai ni, Sadeeq ka gama raina mini wayo wallahi."
"Okay, then go ahead, ka je ka sanar musu, kai ne ni? Ko kai ne baki na? Ba dai ga box ɗin da ka ƙwaƙulo dan shegen gulma ba, to ga box ɗin a wajena idan ka sanar musu sai ka nemo wata hujjar ka basu, domin baka isa ka matse mini baki ba balle har ka saka ni dole na amsa akan gaskiya kake faɗa, kuma duk abinda kayi creating tsakanina da Sadiya na ƙiyayya ta sanadin haka, ka kwana da sanin you'll pay for it."
Wata iriyar dariyar rainin hankali ce Umar ya saki, yana nuna Sadeeq ya ce, "Duk sammakonka to ni a hanya na kwana, eh tabbas picture's, letter da sauran tarkacenka suna ciki har ma waya, duk da dai komai na duba wayar ce ɓacin rai ya hana ni tsayawa na duba shi dan nayi plugging nashi a chaji, amma fa ka sani wannan keyn yana hannuna, wanda nake da tabbacin na secret lockern da na gani a home office naka ne ko studying room oho maka, na tabbata zan samu wata shaidar a can, dan haka ka sha zamanka ka rungume box naka da kyau, ban damu da sanin me ke a wayar ba, na drawern ne yanzu next target na, kuma muddin na tafi to ko ma menene a ciki sai na yi presenting nashi wa su Abba, ko da kuwa menene ka ɗauka kawai su Abba sun gama gani, and you should start practicing how to explain your self to Mama.
Dammm! Haka ƙirjin Sadeeq ya ba da bugu, jin Umar na tare da keyn wancan lockern, dairyn da ke a ciki yana ɗauke da abubuwan da suka fi wanda Umar ya gani a cikin box, domin ya ji hamdala da Umar bai kunna wayar ba, domin password na buɗe wayar shi ne na buɗe box ɗin, tunda har ya iya buɗe box to zai iya buɗe wayar, shiyasa yake hamdala da bai buɗe ba, amma ba zai taba yarda ko Umar ɗin ya karanta diaryn ba, balle kuma su Abba, Umar ɗin ma wanda ya gani yanzu a box ɗin ya ishe shi tunda ya samu tabbacin abinda yake neman.
"Ka shirya yiwa su Abba bayani", Umar ya faɗa tare da juyawa da niyan barin ɗakin.
Da sauri Sadeeq ya girgiza kai, cikin dauriya da dakiya ya ce, "Ka tsaya mu yi magana."
Umar tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba ya ce, "Au!, wai yau za muyi magana kenan? Duk da nake ta bin ka muyi magana muyi magana ta fahimta me kake maida ni? Mahaukaci ko? To ni ma ba zan saurareka ba Sadeeq, ka yi maganarka da su Mama."
"Please bro ka dakata mu yi magana dan Allah, tambayeni duk abinda kake so zan baka amsa, sannan zan amince da auren Sa'adiyah amma sai idan ta yarda tana so na, kuma ban hana ka sanar wa kowa ba, amma duk zan maka hakan ne idan ka bani keyn da ke wajanka", Sadeeq ya ƙarishe maganar very gentle yana lumshe idanuwanshi, zai amsa wa Umar komai, ko wataƙila idan ya fidda abinda ke zuciyarshi sanadin haka zai ji relief, sannan zai auri Sadiya muddin ba dole aka mata ba, domin dama fatanshi kenan da burinshi wato mallakarta, batun sanar da su Abba kuma ya san yadda zai yi da su, Mama ba za ta yi dogon fushi da shi ba za ta sauƙo, Abba da Umma idan ya musu bayani faɗa za su mishi kawai wataƙila shikkenan, Sa'adiyah! "Ya Rabbi ka sa tana so na ko da kuwa kwatan-kwacin yadda nake son ta ne, ta so ni ko ɗan kaɗan shikkenan ya wadatar da ni, domin tulin ƙaunar da nake mata ya ishe mu rayuwa cikin lafiya da aminci da soyayya", Sadeeq ya ƙarishe maganar zucin da bai san a fili yayi ba.
"Hmm!", Umar ya ce saboda ya ji duk zancen Sadeeq na zuci, duk da kuwa ƙasa-ƙasa yayi maganar.
Sadeeq wara idanuwanshi yayi tare da kallon Umar, ya ce, "Bani keyn, sannan ka tambayi komai."
"Da haƙora na ciff a baki na, kai baka isa ka mini wayo ba, sai ka gama bayanin sannan zan baka keyn, sannan da ka lissafa kowa banda ni a ciki, wato dai da gaske matsayin da ka bani kenan? Munafurtata da ka yi ba komai bane ko?"
Sadeeq mai da idanuwanshi yayi ya kulle, ba tare da ya bai wa Umar amsar tambayar da yayi a kan munafurtarshi da yake claiming yayi ba, kawai ya ce, "Let's get direct to the issue."
"Tambayata na daga cikin issuen, so you most answer it first, munafurtata da ka yi baka ɗauke shi a bakin komai ba ko?"
"Ban munafurce ka ba, na bari ne kawai akan sai lokacin da na nemi yardarta kamun na sanar da kowa ciki har da kai, but am sorry for that."
"Hmmn! Riƙe sorrynka, domin idan aka kammala bikin ku za mu sake zama a kan haka, dole sai na shaƙe ka don ka tabbatar mini Amininka nake ko mara amfani a gare ka."
"Ohk, then Allah ya nuna mana lokacin", Sadeeq ya faɗa a taƙaice kaman ba ya son yin magana.
"Amin, amma meyasa lokacin da ya kamata ka nemi yardarta baka nemi yardarta ba?"
"Na barta ta kammala secondary school ne."
"Da ta kammalan meyasa baka sanar mata ba?"
"Before ta kammala ta soma kawo mini batun Haidar."
"Me yasa baka dakatar da ita ka faɗa mata soyayyarka gare ta ba."
"Saboda na fahimci ta soma son Haidar, shi ne farincikinta kuma farincikinta nake so, dan farincikinta shi ne nawa."
"Hmmn, Sadeeq kenan, amma dududu yaushe Sadiyar ta haɗu da Haidar?"
"Na riga kowa sanin haɗuwarta da shi, ku ne sai daga baya kuka sani."
"Amma dan Allah me yasa ka shige wa Haidar gaba? Wannan ai ragwanci ne."
"Saboda farin cikinta."
"Amma Sadeeq idan ka sanar mini ko Umma za mu ɗau mataki cikin salama, meyasa duk baka yi hakan ba?"
Sadeeq ɗan hararan Umar yayi, domin ya tsani tambayoyi iri ɗaya mabambanta, amma ƙoƙarin miƙewan da ya ga Umar na shirin yi, ya sanya shi cewa, "Duk saboda farincikinta ne ban yi haka ba."
"Meyasa kuma bayan kana sonta yanzu kake ce mini ba za ka aureta ba?"
"Saboda ba nine farincikinta ba, Haidar ne farin cikinta."
Umar a ƙufule ya ce, "Farincikinta, saboda farincikinta, dan farincikinta, bla bla bla, wai Sadiya ce kawai mutum? Are you not a human? Sadeeq da gaske ma kuwa kana son Sadiyar nan? Ai indai kana sonta da gaske to za ka so mata rayuwa da kai, domin kai ka san ka isa mijin taƙama da tinkaho ga ko wace mace mai sa'ar da ta samu damar mallakarka, so so ne Sadeeq amma son kai shi ne asalin so, ka so wa kanka ita ba wai ka so mata rayuwa da waninka ba."
Murmushin gefen baki Sadeeq yayi, bai shirya wa murmushin ba amma dole sai da yayi, cikin haɗaɗɗiyar muryarsa ya buɗe baki kamar wanda bai son magana ya ce, "A wajena son Sa'adiyah ya fi son kai na, farin cikinta kuma da nake ambata to ya fi mini komai, kuma zan iya ba da komai dan ta samu farinciki, a cikin abinda zan iya bayarwa kuwa to har da sadaukar da rayuwata, tun ranar da Mama ta haifi Sa'adiyah ƙaunarta ya shigar mini ko ina, am 17years lokacin da Mama ta haifi Sadiya, na san so wanda da za a mini auren wuri to na kai aure tun a lokacin, amma tun daga lokacin na ƙuduri aniyar jirarta..."
Maganar Sadeeq ne ya katse saboda Umar da ya ce, "And after all this ka jagoranci wani ya samu soyayyarta, so you'll keep on waiting for her kake nufi ko me da ka cigaba da yin shiru? Ko mutuwar da gaske kake shirin yi tunda za ka sadaukar mata da rayuwarka dan farincikinta? Sadeeq you're nonsense, very very nonsense, domin ban ga ta yadda za ka ɓille a wannan shirmen naka ba, ko za ka cigaba da jiranta har Haidar ɗin ya mutu sannan ka aureta? Ko kuwa ya sake ta ka aureta?"
"Umar enough dan Allah, magana ya isa, ka yi fatan alkairi dan Allah, in sha Allah idan ta shiga gidanta sai mutuwa ne zai fiddata, ba na son yadda kake tsaurara wasu kalamanka, na faɗa maka ina son ta fiye da kai na."
Umar ya ce, "Amin Ya Rabbi, kuma in sha Allah a gidanka za ta mutu", ya ƙarishe faɗa yana miƙewa tsaye.
Da sauri Sadeeq ya kalleshi, tare da ɗago hannunshi ya miƙa mishi, alamar ya ba shi keyn.
Murmushi Umar yayi tare da sanya hannayensa duka biyu a cikin aljihun jallabiyar da ke jikinshi, ya ɗage kafaɗa tare da cewa, "Ba wani key a wajena, duka tarkacenka suna cikin box naka, in ka so ka haɗiye su ma, na gano abinda zan gano, kuma ko ba hujja na san ya zan yi da su Abba, in Allah ya yarda sai ka auri Sadiya ko tana so ko bata so, ko kana so ko baka so, balle ma ɗan rainin hankali kana mutuwar so, kuma daga yau daga yanzu babban Yaya nake, Yaya sama Yaya ƙasa, Yaya Umar za ka ke ƙirana baki a cike, tunda ka aje kunya a gefe ka ce ƴar da ka kusa haifa kake so ƙanwar bayarka, kuma shirmammiya irin Sadiya, to sai ka ƙarata kai ka sani, Allah ya tabbar da alkairi amma daga yau Yaya za ka ce, kayi biyayya tunda ka zama babban gwaza, na ƙwace girman", daga haka Umar ya juya ya fice bai kuma sauraran me Sadeeq ke cewa ba, domin ya san tabbas sai ya zage shi, tunda ya shammace shi ya nuna mishi keyn na wajanshi, har ya sa ya saki baki yake ta zubo maganganu.
"Ɗan iska, zan dawo gidan ne za ka yi bayani", Sadeeq ya faɗa yana jin nauyin da ke a zuciyarshi ya ragu, gefe guda kuma zullumi da tunanin Sadiya ne ya sake gilmawa a zuciyarshi, maganganun da take yawaita mishi na jaddada mishi, cewar Haidar ne farincikinta sai amsakuwwa suke mishi a kunnuwa, hakan ya sanya ya kunna karatun Ƙur'ani tare da ɗaukan box ɗin ya ajiye a gefen pillownshi, he wish maganar Umar ya tabbata kuma cikin son ran Sadiya da amincewarta, domin zai so gabatar mata da abubuwa da dama, sannan ya gwada mata soyayya fiye da wanda take mafarkin samu a wajan wani.
Wannan tunanin ma katsewa yayi saboda tuno Haidar da yayi, "Ya Rabb", iya haka ya faɗa tare da watsar da ko wanne tunani ya shiga bin karatun.
Umar yana ficewa ya yi da su Sa'ad magana ya kammala za su iya komawa ciki, Allah tsare hanya suka mishi, ya shige mota ya fige ta yayi gida, su kuma suka shige ciki suna Allah kyauta ya sauƙaƙa ko ma menene, ko da suka shiga ɗakin, a kwance suka samu Sadeeq yana bin karatu, sai suka samu waje suka zauna kowa ya cigaba da danna wayarshi.
Ko da Umar ya dawo anguwarsu, gidan Mama ya wuce tare da ƙiran Khausar a waya, ba jimawa ta shigo gidan, a madaidaicin harabar ta same shi dan bai shiga ciki ba, da sallama da buɗe ɗaya side na gefen direba ta zauna tare da barin ƙofar a buɗe kamar yadda Umar ma ya bar nashi a buɗe, cikin nitsuwa ta ce, "Uncle U, ya ake ciki? Ya kuka yi da shi?"
Tiryan-tiryan Umar ya labarta mata komai, tare da sanar mata abinda yake shiryawa, na sanar wa Mama zuwa anjima, sannan ya sanar da Abba da Umma da dare.
Numfashi Khausar tare da cewa, "Yaya Sadeeq bai kyauta ba uncle U."
"Shiyasa na mishi tas ban raga mishi ba, domin wannan munafurtata yayi."
"Amma uncle U, wani hanzari ba gudu ba, ita small Mum fa? Ya kamata a ji ta bakinta, ka ga kuma Yaya Sadeeq ya ce in ba amincewarta ba zai aure ta ba, kuma gaskiya ina tunanin za a iya samun issue da ita."
Umar girgiza kai yayi tare da cewa, "Ki ƙyale ta shirmammiyar nan, ita ma tana son shi sarai, daga kalamanta kana ji ka san tana son shi."
"Amma bata fahimci tana son shi ba uncle U, small Mum yarinya ce kuma Haidar ne first love nata, dole sai an fahimtar da ita cikin lallami da salama, in ba haka ba kai ka san matsayin da ta bai wa Haidar da irin son da take mishi."
"Wa zai tsaya lallasan Sadiyar? To ko Sadeeq da ya ɗauko wa kanshi hanyar mutuwa ban lallashe shi ba, ko za ta mutu Sadeeq za ta aura, yaushe ma na fara wasar musu da Sadiya? Ki bar hasaso wani matsala daga gare ta, domin Sadeeq ɗin dai shi ne mijinta, su je can daga baya sai ya fahimtar da ita da kanshi, ya kuma lallasheta dan daman shi ke jure shirirtarta da shirme, tunda shi ya sangartata."
"Uncle U, batun soyayya ya wuce duk yadda kake tunani, balle ga irin small Mum yarinya ƙarama, dole sai an fahimtar da ita."
"To ke sai ki fahimtar da ita, domin ni yiwa su Abba magana ne a gabana yanzu, in ta so ta fahimceki in ta so ta ƙi fahimta, sai dai ta ganta a gidan Sadeeq."
Khausar numfashi ta sauƙe mai nauyi, tare da cewa, "Allah ya rufa asiri ma uncle U, Allah ya sa ta fahimtar dai ,sai abun ya fi armashi."
"Ita ta sani in bai yi armashi ba, mu dai muka ɗaura musu aure shikkenan, shi kuma idan ya so ya je ya cigaba da zama mata soko, ko kuma ya biye mata ya sako ta, ta zo ta auri wanda take son in dai ta nuna bata son shi."
"Yanzu duk ba wannan ba, batun su Abba", Khausar ta faɗa cikin son kawar da wancan shafin, domin ta jima da sani a kan Sadeeq Umar ba abinda ba zai yi ba, kuma idan ya ce zai nuna zuciyarshi da ikonshi, to za a samu jibgegen matsala.
"Yanzu zan fara yi da Mama magana, zuwa muka dawo sallahn isha'i ko magrib sai nayi wa Abba bayani na maida mishi har da yadda muka yi da Mama."
"A shawarce dai ka bar Mama da kanta ta je ta samu Abban su yi magana ta fahimta."
"Kar ki damu sister, na san yadda zan fitowa Abba ya dube mu, in ya so sai a bai wa mutanen Haidar ɗin haƙuri."
"Shikkenan uncle U, ba damuwa Allah ya shige mana gaba, ya tabbatar da alkairi, kuma duk abinda ya tsara ya biyo baya, Allah ya bamu zuciyar ɗauka daga mu har su masoyan."
"Amin Ya Hayyu Ya Qayyum."
Daga haka ɗan tattaunawa suka yi, sannan suka fice a motar, Umar ya kulle abarshi suka nufi ciki da sallama, kasancewar la'asar ta yi, to ba kowa a palourn, Mama na ɗakinta tana salla, Sadiya na nata ɗakin tare da ƙawarta Zahra da su Najla.
Umar ɗakinshi ya wuce ya ɗauro alwala ya zo ya fice masallaci, Khausar kuma ta wuce ɗakin Sadiya, tana shiga Nayla ta taso ta mata oyoyo, Najla dai sannu da shigowa ta mata ta amsa, Sadiya ta ce, "Aunty sannan da shigowa."
"Yauwa small Mum amarya, ashe har cheif best ɗin ta iso?"
Zahra na murmushi ta ce, "Na samu isowa Aunty, fatan kun zo lafiya?"
"Lafiya Alhamdulillahi Zahra amare, kinsan an ce ƙawar amarya ma amarya ce, wataƙila cikin abokanaye wani yayi wuff da ke, nan da satanni mu kuma zuwa Jos shan biki."
Ƙasa da kai Zahra tayi tana murmushi, sai Sadiya ce ta ce, "Ai aunty ita ma tana da tsayayye, kawai sai mun samu admission ta fara zuwa school sannan za a yi auren, dan Abbanta ya fi so ta fara karatun kamun ta shiga daga ciki."
"Da gaskiyarshi ai, yanzu rashin tabbas irin na mazan zamanin yau, ai gwanda ƴar ka ta kama dahir, dan ba a yarda da alƙawarin maza, suna mallakar yarinya su fara gwada ikonsu da rashin mutunci, wasu har ya kai ga rashin kunya ga iyaye ko saki, Allah dai ya rufa asiri ya kyauta, amma duk indai har aka ce ka riga ka fara kamun aka yi auren to ma sha Allah, komai zai zo da sauƙi duk kuwa yadda mutum ya kai ga rashin kirkinsa."
"Haka ne wallahi aunty, Allah dai ya shige mana gaba", faɗin Zahra, domin ta ga tabbacin zancen Khausar, akan wata cousin sisternsu da har yanzu ake fafatawa.
"Amin Zahra, ya kika baro su Umma da kowa."
"Duk suna lafiya suna gaida ku."
"Ma sha Allah", Khausar ta faɗa tana nufar toilet.
"Aunty kin gama bayani, to ni kuma fa kar dai Al-Sad ya mini halin maza", Sadiya ta faɗa tana langwaɓar da kai.
"Idan ya miki shikkenan kin huta, dama Yaya Sadeeq ke so ki yi karatu ai ke ba so kike ba, balle ma Haidar ba zai yi haka ba in sha Allah, in kuma yayi to Yaya Sadeeq da uncle U sun ishe shi tuwo da miya", Khausar ta ƙarishe faɗa tare da shigewa toilet bakinta ɗauke da addu'a.
Zahra ƙasa-ƙasa ta ce, "Wallahi gaskiyan Aunty ba kya son karatu, amma dai duk da haka ki daina lissafo wani abu mara kyau daga mijinki tun ba ki shiga ba, is not good."
"Ke dalla malama kauce, barmu mu da muka kusa shiga daga ciki muyi bayani, idan kina son ki zauna lafiya a gidanki, to ki saka a ranki namiji is capable of doing anything, zai iya yin komai, kinga ko gani kika yi yayi, ko kuma aka baki labari yayi, ko kuma ya aikata miki wani abun, to hankalinki kwance daman kin tsammaci zai yi hakan ba zai dame ki sosai ba."
"Hmmm!, kuma fa da gaskiyarki Sady, Allah dai ya ƙarawa waɗanda suke ciki haƙuri da zaman lafiya, ku masu shirin shiga Allah ya sa ku shiga a sa a ku zauna lafiya har mutuwa, mu ma kuma Allah tabbatar da alkairi da na gari mu shiga a sa'ar."
"Amin Aminiyas", daga haka suka cigaba da shirye-shiryensu, wanda za su fara ranar Wednesday Henna day, Thursday Nupe day, Friday walima sai ɗaurin aure ranar Saturday.
Khausar tana fitowa ta kabbara salla, Sadiya ma toilet ɗin ta shige ta ɗauro alwala, ta fito ta kabbara salla, Zahra dai tana zaune dan fashin salla take.
Najla ma alwalan ta yi ta zo ta bi sahun Sadiya, Nayla kuka ta fara wai ita ma salla, Zahra ce ta ɗauketa ta kai ta toilet ta mata alwala, sannan ita ma tayi salla kunnen kowa ya huta.
Umar ko da ya dawo masallaci, ɗakin Mama ya wuce kai tsaye, da sallama ya shiga bayan ta amsa ta bashi iznin shigowa.
Waje ya samu ya zauna tare da mata barka da gida.
Mama da ke zaune kan sallaya ta ce, "Yauwa Umar, ya labarin jikin mai babban suna? Yau duk baka leƙa shi ba tunda ka dawo da safe."
"Abba ne ya ce in zauna a gida Mama, amma zuwa dare zan koma mu kwana kamar ko yaushe."
"To ma sha Allahu, Rabbi ya yi muku albarka duka, Allahu ya tashi kafaɗun mai babban suna a sallamo mana shi da wuri."
"In sha Allah a cikin kwanaki biyun nan za a sallameshi, na leƙa shi ɗazu, ina dawowa wajanshi na wuce masallaci, shigowana yanzu kenan, kuma na baro shi jikin da sauƙi sosai."
"Alhamdulillah, amma wannan abu yayi mini daɗi, Allah ya ƙara mishi lafiya."
"Amin Mama, uhmn dama akwai maganar da nake so muyi akan Sadeeq ɗin", Umar ya faɗa yana yin ƙasa da kan shi.
Gyara zama Mama tayi tare da fiskantar Umar ta ce, "Ina saurararka Umar."
"Mama akwai matsala, amma in kuka yi haƙuri kuka fahimcemu, kuma kuka mana uzuri to matsalar ba babba ba ce, tabbas bamu kyauta ba, amma dan Allah a fahimce mu."
Mama cikin rashin gane kwana-kwanar Umar ta ce, "Wannan dogon labarin ba ni fahimtar shi, je kai tsaye ka faɗa mini menene, tunda ka ce a kan mai babban suna ne, ai dole zan fahimta na muku uzuri, ina jin ka."
"Mama dama akan ciwon da yayi ne, asalin abinda ke damunshi."
"Menene asalin abinda ke damunshi? Me ya kayar mini da yaro lokaci guda? Faɗa mini ina saurara, domin abinda muke ta mararin ji kenan, dan mu san ta yadda za mu ɓullowa lamarin, mu samu muyi wa tufkar hanci", Mama ta faɗa cikin ɗaukin son jin damuwar Sadeeq dan su nema mishi mafita.
"Soyayyar Sadiya ce tayi sanadin faɗuwar Sadeeq", Umar ya faɗa yana mai ɗagowa dan kallon reaction na Mama, da kuma ya ji me za ta ce.
Cikin rashin fahimta Mama ta ce, "Ban gane ba Umar, ban fahimci me ka ce ba."
"Mama Sadeeq yana son Sadiya, kuma ya jima yana son ta, domin soyayyar Sadiyar ce ma tayi sanadin ciwon da yake yi."
"Sadiya dai Sadiyar da na sani ita mai babban suna yake so? Kuma har sanadin soyayyarta ne yake a cikin wannan hali?"
"Eh Mama", Umar ya faɗa yana jinjina kai almar tabbaci.
Mama shiru tayi na wasu mintuna, idanuwanta tsurr a kan Umar, sai ta ce, "Amma saboda ba ka da hankali, kana sane da duk wannan, shi ne har sai yanzu kake sanar mana? Da mai babban suna ya mutu kuma shikkenan ba za ka faɗa mana ba ko? To da wallahi ba zan yafe maka ba Umar..."
Da sauri Umar ya katse Mama ta hanyar cewa, "ki yi haƙuri Mama dan Allah, wallahi nima sai yau nake sanin gaskiyar, da a ce na san a kan Sadiya ce da ko ni da kaina na biya sadaki an ɗaura musu aure, Allah nima yau nake sani, kuma ke na fara sanarwa yanzu, sai zuwa anjima zan sanar da su Abba a san me ake ciki."
Mama kallon rashin yarda da cewa wai sai yau ya sani take jifarshi da shi, fiskarta a haɗe tamau, tana ƙoƙarin buɗe baki ta sake yin magana, Umar ya yi sauri katse ta, ta hanyar girgiza kai tare da cewa, "Wallahi Mama da gaske nake.............", Tiryan-tiryan ya labarta mata komai duk yadda aka yi, amma ya ɓoye mata wasu abubuwan da zai sa ta ji haushin Sadeeq, wanda za ta tausaya mishi har ta shige gaba a yi auren kawai ya sanar mata, kuma yayi nasara domin Mama ƙwarai ta tausaya wa Sadeeq, har da ƴar ƙwallarta ta ce, "Allah sarki, mai babban suna ba laifinka kawai bane, har da namu da muka kasa harbo cewa kana son Sadiya, yadda kake bata kulawa da ɗawainiya da ita da komai, dama ya kamata mu fahimci son ta kake a matsayinmu na manya, amma ba mu kawo hakan ba har kana ƙoƙarin rasa rayuwarka, a kan wacce kake da cikakken ikon mallakarta, ka yafe mu, kuma in sha Allah muddin ni ce na haifi Sadiya ba wani ya haifar mini ita ba, to Sadiya matarka ce da yardar Allah."
Umar wani irin wawan ajiyar zuciya ya sauƙe, yana jin quite relief, duk da daman ya san hakan ne za ta iya faruwa, domin Mama tana matuƙar ƙaunar Sadeeq, a nitse ya ce, "Zan je mu yi magana da su Abba zuwa anjima, in ya so sai a san yadda za a yi da su Haidar, Allah ya sa kada a samu damuwa."
"Amin Umar, kuma in sha Allah ba damuwar da za a samu, ni ce fa na haifi abata, kuma na ce na bai wa mai babban suna ita duniya da lahira, ai ko shi Haidar ɗin ma zai tausaya wa babana tunda dai har ƙoƙarin rasa rayuwarsa yake yi saboda ita, irin wannar ƙauna da babana ke yiwa Sadiya, in bata aure shi ba ai ta yi rashi, namiji ya zaɓi farin cikinka a kan nashi, namiji ya so ka da dukkan komai nashi, ai muddin ba halin banza mace za ta nuna wa namiji ba, irin wannan ai sai mata sun dinga nuni da ita, suna addu'a da fatan da su ne a matsayinta, dan ba a ƙin mutum sai dai a ƙi halinshi, duk yadda miji zai so mace, idan tayi halin kirki na arziƙi barkanta, idan tayi ta tsiya kuma za ta gani a ƙwaryar tuwonta, kuma iya sanina daidai gwargwado halin kirki muka koyar da Sadiya."
"In sha Allah ma lafiya lau za su zauna ba komai Mama, Sadiya ai kawai a barta da shirme da shiririta, amma in ba haka ba tana da hankali daidai."
Jinjina kai Mama tayi tare da cewa, "To Allah ya tabbar da alkairi ya ƙara wa mai babban suna lafiya, shi kuma Haidar ɗin Allah ya ba shi haƙuri, dan ta Sadiya bana jin komai dan already tana ƙaunar babana, kuma duk inda aka shaƙu ake ƙaunar juna, dan lamarin aure ya shigo ciki ba komai bane."
"Ni ma abinda na ce kenan, amma Khausar ta dage wai sai an fahimtar da Sadiyar."
"Eh duk da akwai shaƙuwa da ƙauna tsakaninsu, amma tana da haƙƙin a fahimtar da ita, zan kuma mata magana dan ina da tabbacin Sadiya ba za ta musa ba."
Jinjina kai Umar yayi cike da gamsuwa da hasashen Mama, domin ko shi haka yake hasashe, ƙauna da shaƙuwar da ke tsakanin Sadiya da Sadeeq ai a bayyane yake, sai dai fatan alkairi, dan ma dai duk hankalin mutane yayi nisa ne, kuma ba wanda ya taɓa lissafo haka, Allah ya kauda wa kowa basirar tuna wannan, in ba haka ba da an fahimci soyayyar su ko ba su furta ba.
Tattaunawa Mama da Umar suka yi, musamman a kan danginsu da suke saka ran za su fara zuwa daga gobe litinin, duk da ba wani nisa sosai na a zo a gani bane tsakanin Jos da Minna amma dai akwai masu zuwa da wuri, musamman dangin Mama, dan daga dangin Mama har na Babansu mutanen Niger Minna ne, duk yarensu guda Nupawa ne.
Daga haka Umar ya tashi ya fice, ɗakinshi ya wuce ya jawo ayyukansu na company ya fara dubawa.
Sadiya da Zahra sun gama shirya komai in da Khausar ta gyara musu, sannan suka ƙira sauran ƙawayen da wayar Sadiya, conference call suka yi, dan ƙawaye shida ta tsaida, uku duk school mate's nata ne, Zahra tana cikinsu, sai guda ɗaya mai suna Salma, ita kuma ƴar anguwarsu ce, amma presently bata nan, sun yi tafiya zuwa Nasarawa sai Wednesday za su dawo ranar da za a fara events, sai kuma sauran biyu daga dangi, ɗaya ƴar ƙanwar Mama, ɗaya kuma ƴar ƙanwar Baba.
Goshin magrib Zahra ta yi ma Mama da Khausar sallama, Sadiya ta raka ta zuwa bakin hanya ta samu mashine ta yi gida, Mama sai faɗa take akan Zahra bata tsaya an idar da magrib ba tukunna, don daga Sadiya har ƙawayenta sun san dokar Yaya Sadeeq, babu fita goshin magrib, irin Sadiya kam ma muddin aka yi magrib to ba inda take zuwa sai ko idan gidan Umma, nan ma Sadeeq faɗa yake wai ranar da za ta kwana wajan Umma to ta tafi tun kamun magrib, ranar da ta kuskura kuma ta je anguwa ta kai magrib to kashinta ya bushe.
Sai da suka ida sallar magrib suna zaune duk kan darduma jiran a ƙira isha'i, Khausar da kuma Sadiya har da asu Najla, Khausar ce ta numfasa tare da cewa, "Small Mum."
"Na'am aunty", Sadiya ta faɗa tana tsayar da danna counter da take yi, saboda yanayin sautin muryan Khausar, ya nuna magana za ta yi ta serious.
Khausar jim kaɗan ta yi shiru, sai can ta ce, "Small Mum ban san ya za ki ɗauki lamarin ba, amma dai kamun na miki dalla-dalla, bari na baki a dunƙule na ga ko za ki fahimci wani abu, amma kada ki mana gurguwar fahimta, muna sonki kuma muna sonki da alkairi, muna kuma miki addu'an samun duk abinda yake mafi alkairi a rayuwarki."
"Amin aunty, na san ba za ku so ni da abinda zai cutar da ni ba."
"Yauwa small Mum tawa, kinsan Yaya Sadeeq da ya faɗi aka kai shi asibiti me likitoci suka ce?"
"A a aunty", faɗin Sadiya tana girgiza kai.
***
Umma da Abba duk idanuwa suka zuba wa Umar, cikin rashin fahimtar me yake faɗa.
Umma na ƙoƙarin magana Abba ya rigata ta hanyar cewa, "Umaru bana son shirme da shiririta, kana cewa auta shirmammiya, kai yanzu me kake yi? Abubakar ɗin ne ya ce maka Halimatu yake so? Yaushe kuka yi haka da shi? Kai duk ma ba wannan ba, a ina ka taɓa jin an nemi aure cikin aure ko a wasa?"
Umar Marairaicewa yayi, tare da sake yin ƙasa da kai, cikin muryar magiya da sigar tabbatarwa ya ce, "Wallahi Abba Sadeeq yana son Sadiya, kuma ai ba wani neman aure kan nema tunda....."
Abba cikin haɗe rai ya katse Umar, tare da cewa, "Ba na son shirme Umaru, ka tashi ka bani waje, ba mai maidamu ƙananun yara, auta da yardar Allah Aliyu za ta aura, daga kai har Abubakar ɗin ku bar wasar kwaikwayonku, domin ba zan ba shi auren Halimatu ba, ya mutu ɗin, Allah ya ji ƙan shi muma duk hanyar muka kama."
Da wani irin sauri Umar ya ɗago kan shi jin furucin Abba, Umma ƙasa tayi da kanta ta ma rasa me za ta fara tunawa, Umar na ƙoƙarin magana, Abba ya dakatar da shi tare da ɗaga mishi hannu ya ce, "Tashi ka je na gama magana, ba zan bai wa Abubakar auren auta ba, Aliyu za ta aura."
***
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
●BAKANDAMIYA HIKAYA.
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
***
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# ***
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚