Free chapter · Read without an account
NEMAN MAFITA
Page (4)
NEMAN MAFITA!
Mahaifiyar Irfan ce tayi k'ok'arin sa baki wajen shawo kan mahaifinsa.
"Abbansu ka taimaka ka sake mishi alfarma, gobe in Allah ya kai mana rayuwa sai ya bincika ko 'yar gidan wacece in...."
"Wannan ai duka k'arin b'ata lokaci ne Aysha". Ya katse ta daga zancen da ta soma.
"Hak'uri za ka yi Abban Irfan ka daure, kasan halin Irfan da shiririta."
Ta fad'a cikin sassanyar lafazi.
Shiru yayi na dogon lokaci kamar ba zai ce komai ba, sai can kuma yace,
"Shi ke nan na ji.
Amma ya tabbata nan da zuwa gobe ya kawo min labarin ko 'yar gidan wacece wannan yarinyar, kafin in tura Mutanena, ya tabbatar ya bincika, matukar gidan na su yayi, wanda za a iya neman Aure ne, zan tura Mutane, domin ban son ya wuce nan da sati guda ba a tsaida wata magana ba.''
Godiya Hajiya Aishat tayi masa, sa'anan ya mik'e matakalar benen dake falon ya taka sannu a hankali, wanda zai sada shi har zuwa k'ofar d'akinsa dake sama.
Bayan wucewarsa ne, Hajiya Aisha ta kalli d'an nata gami da fad'in cewa,
"To ka dai ji abinda Abbanku ya fad'a ko?
Sai kayi k'ok'ari ka binciko 'yar gidan wacece, ni kaina zuciyata za ta fi nutsuwa da hakan, duk da dai alamun yarinyar dana Mahaifiyarta sun nuna 'yan gidan mutunci ne.''
Sai da ta d'an dakata, kafin ta ci gaba da cewa, ''Kuma ka ji dai abin da Abbanku yace! In har ya aminta da yarinyar, da wuri za'a tura. Saboda haka sai ka sanar musu. Wuk'a da nama sun rage a hannun ka yanzu.''
Ita ma tashi tayi, had'e da wucewarta, ta bar shi, a gun.
Irfan na nan duk'e inda suka bar shi, tamkar ruwa ya cinye shi, gumi ne kawai ke keto masa ta ko'ina.
Babban damuwar dake zuciyarsa, rashin samun had'in kan khaleesat da bai yi ba har zuwa yanzu da ake maganar za a tura nema masa Aurenta, cikin abinda bai fi nan da sati guda ba, tirk'ashi!.
'Wannan wani irin rikici ne na d'ebo wa kaina lokaci d'aya?' Ya tambayi kansa.
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke!.
'Gashi sai k'aruwar sonta na ke ji a zuciyata.
Dole na sami Ummanta yau nayi magana da ita, a wurin ta kad'ai zan iya samun goyon bayan khaleesat. Zan rok'eta ta taimaka min, mai yuwa in tasa baki na sami amincewarta. Bani da wani zab'in da ya wuce wannan.'
A cikin zuciyarsa yake ta faman sak'e sak'e.
****
Ko da yaje gidansu khaleesat ana fad'a mata wanda ke neman ta, tace ba ta jin dad'i ba za ta iya fita ba.
Ummanta bata gida ya kai kusan awa uku a waje shi kad'ai.
***
Yana hango tahowar Umma lokacin da ta dawo, yayi saurin bud'e Motarsa ya fito.
Har k'asa ya tsugunna ya gaishe ta.
Ta amsa cikin sakin fuska, bayan ta d'an jima da shiga gida,
neman iso ya buk'ata kai tsaye domin magana da ita, tace a shigo dashi.
Ko da yaje gareta gabatar da kansa ya sake yi.
Dama kuma ita ma tunda ta ganshi ta shaida shi, shine wanda ya taimaki d'iyarta kwanakin baya da suka wuce, shine kuma ya nemi jin bayani dangane da larurar Khaleesat wajenta.
Irfan ya ci gaba da bayyanawa Umma dalilin zuwansa, tare da k'ara rokon alfarmarta, wajen shawo masa kan Khaleesat domin ita tafi kowa sanin halinta, mai yuwa taji maganar ta ya samu ta saurare shi, tunda ya kula tana da wani boyayyen dalili mai karfi na rashin son kula shi. Sannan ya bayyanawa Umma komai Aurenta yake son yi.
Kuma idan har sun amince, manyansa za su zo gidansu bada jimawa ba, kamar yanda Mahaifinsa ya shaida masa.
Umma ta yi na'am k'warai da nutsuwa gami da hankalin Irfan, tun bayan lokacin daya maido su gida daga asibiti, yanayin zaryar da yake yi a gidan tasan tabbas rana mai kamar ta yau zata zo. Don Khaleesat son kowa ce k'in wanda ya rasa.
Sai dai a b'angarenta ita ma ta nuna rashin goyon bayanta, dangane da ra'ayin Irfan na son Auren Khaleesat.
Duk da cewar tana son ganin d'iyarta ta yi Aure ita ma kamar sauran yan uwanta, amma ba za ta so abinda ke faruwa ga wad'an da ke neman Auren Khaleesat ya faru da Irfan ba, yaro mai cikakken hankali, nutsuwa gami da kamala.
Ba za ta so 'yarta ta zamo silar jefa iyayensa cikin maraicin rashinsa ba!.
K'ok'arinta, ta shiga yi wajen fahimtar dashi dalilin da yasa khaleesat ba ta son saurarensa, domin tana da hujjoji masu k'arfi a kan hakan.
A k'arshe ta had'a da rokonsa kan ya janye da maganar Auren, domin tsira da rayuwarsa....Tun da ya kasance, had'a inuwa d'aya da d'iyarta ga kowane namijin da yaso yin hakan, tamkar barazana ce ga numfashin da yake yi a doran k'asa!.
Saboda sun riga sunyi yak'ini a kan yadda al'amarin ke kasancewa duk bayan wani Aure da Khaleesat tayi.
Duk da cewar bayanan Umma sun sanya jikinsa yin sanyi sosai, don wannan lokacin ne ta fito masa da cikakken dalilin da ya kasa fahimta a baya, lamarin ya d'aure masa kai amma haka nan ya k'ara bugun kirji da nuna sam! Bai san zancen ya ja baya ba, hasali ma cewa yayi shi ya shirya fuskantar ko wace irin jarabawa ce, in dai akan Khaleesat ce, ko da ko hakan zai zama shine silar rasa rayuwarsa.
A ganinsa halin da Khaleesat take ciki taimako take nema, wani ya kasance kusa da ita, ba wai a guje ta ba.
Da tausasan kalamai na laffuza masu dad'i Irfan ya rink'a amfani dasu, wajen tausasa zuciyar Umman Khaleesat, tare da gwada mata amfanin yarda da k'addara, mai kyau ko akasin hakan. Inda ya rink'a k'arfafa mata gwiwa da nuna mata cewa kowane d'an Adam da irin tasa k'addarar, ba lallai ne abinda ya sami 'yan baya ya kasance ya faru da shi ba.
A haka har ya samu ya shawo kan Umman Khaleesat.
Da kanta tayi masa alkawarin taya shi rarrashin d'iyarta, ko za a samu ta saurare shi.
Amma duk da saukowar da Umma ta yi, a zuciyarta bata daina fargaba ba.
**
Tana kwance cikin d'akinta, kiran Ummanta ya tashe ta.
Jiki ba k'wari ta same ta babban falon gidan, a sanyaye ta nemi wuri ta zauna.
Bayani ta fara yi mata kan abinda ke tafe da Irfan wanda ke zuwa wajenta.
Khaleesat na jin kalaman dake fita daga bakin Ummanta, na son taje su gana da Irfan, wai ko za su dai-dai ta kansu har auren ta yake son yi.
Dam! Gabanta ya fad'i.
Mik'ewa tsaye tayi
tana fad'in "Ina sam! Ba zaiyu ba. Ba zan iya amsar wannan bukatar tasa ba, bama zan fita ba Umma, a fad'a mai ya yi hak'ura kawai ya koma".
Umman khaleesat tace
"Saboda me Khaleesat?
Ba kyau wulak'anta Mutum fa!
Wajen awansa uku a k'ofar gidan nan, an ce tun bayan la'asar yake son ganinki amma baki fita ba, sai daya gaji yasa akai mai iso wurina, mai yasa haka khaleesat uhm?''
Nan take idanunwanta suka ciko da hawaye tana fad'in
"Umma kinsan komai fa, menene abinda zan fad'a nayi bayani a gareki wanda baki sani ba, menene wanda yake sabo a gunki Umma?
Bawan Allah nan taimako na yayi, bai kamata ace na rasa abinda zan saka masa dashi, sai Aurena ba, bayan na riga na dad'e da sani cewa, k'addarar rayuwa ta ba ayi ta dan zama a k'ark'ashin inuwar Auren wani ba......''
Ta karasa maganar da rawar murya karshe kawai ta fashe da kuka.
Ummanta tayi shiru don duk abinda Khaleesat ta fad'a, ta san gaskiya ne.
'Amma kuma ta bakin Irfan d'in ne, kowa da tasa k'addarar, ba lallai ne abinda ya faru ga 'yan baya ba, ya zama ya faru dashi.'
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke, kafin tace,
"Ni kaina nayi wannan tunanin da farko Khaleesat. Amma maganganun da yaron nan yayi min yasa naji jiki na yayi sanyi sosai.
Ya na da tawakkali Khaleesat, yana ta ikrarin babu abinda zai faru sai alkairi, har Malamai yace zai sanya na musamman su duk'ufa da Addu'o'i, gami da rok'on tsari da kariya wurin Ubangiji kan alak'arku.
Kinga ko duk cikin maneman Aurenki na baya, babu wanda ya tab'a yin hakan ko?
Ki daure ki basa had'in kai Khaleesat mai yuwa shine silar zama k'arshen lalurar dake damunki.''
Pyar❤✍🏻