Free chapter · Read without an account

Chapter: 6

by Rabi'atu Abubakar Umar · KO BA SO..

Layla....

A diririce ta je aiki yau, ko ido ta hada da ma'aikatan wajan sai gabanta ya fadi, jiran tsammani kawai ta ke yi na sakamakon abin da zai faru da ita. Babban abin da ya fi dauke mata kai bai wuce na yadda aka ce ta sake girka abin da ta yi jiya ba.

'Abin da na yi jiya?' Ta dinga nanatawa a ranta. 'Ke nan dai laifin daga gare ni ne? Girki na ya bata masa ciki?' Ta dinga zarya hankalinta sam ya gaza kwanciya. Zee ta dube ta

"Wai lafiya? Ko baki lafiya ne?"

Ta kakalo murmurshi ta ce

"Lafiya lau fa"

Sannan ta wuce ta fara aiki. Komai cikin tsantsani ta ke yin sa, wata kilan so ake a tantance abinda ya faru ne ko dai wani abu dangane da abincinta na jiya. Ta samu ta gama ta ci gaba da baza ido kuma bata ji an ce ta kaiwa FJ ba.

'Ko bai warke ba? To koma dai ya na asibiti? Na shiga ukku!'

Tana zaune ta na jiran tsammani sai ga sarah, gabanta ya fadi ganin yadda ta nufo ta ga fuskarnan babu alamun dariya.

"Ki kai abin da kika girka 050"

Kawai ta fada ta wuce. Haɗa abincin ta yi dai-dai na mutum daya ta dauka ta wuce. Bakin ta dauke da addu'a har ta isa, ta dan yi jim kafin ta kwankwasa. Kamar jira ake aka bata damar shigowa. Ta yi sallama ta shiga.  Wannan karon a zaune ya ke bisa kujera wadda za ta iya cin mutum biyu, ta na kallon gadon. Saurin kauda idonta ta yi daga damtsen hannunsa da ya fito sakamakon rigar jikinsa da ke da karamin hannu, mai ruwan ƙasa. Ajiyewa ta yi ta koma gefe ta tsaya

"Ki tafi"

Kawai ya faɗi. Ta dan yi jim ta na kyautat zaton babu abin da ya same shi. Ganin bata tafin ba ya dago ya kalle ta. Da sauri ta fice ta ja masa kofar. Waje ta samu ta tsuguna daga waje ta fi awa daya kafin ta mike bisa shawarar Zee ta jiya, ta kwankwasa dakin. Ko ba haka ba ma ya ci ace ta tambayi ya jikinsa, ta san ko yana da allergy ne da wanu abu a cikin girkin nata don ta daina sakawa. Bayan ya bata izini ta shiga, idanu suka hada, ya na zaune da alamar har ya gama cin abincin ma.

"Are you a parasite or what?"

Ya fada muryarsa can kasa. Ta yi tsaye ta na kallon sa da mamaki.

"Just get out please"

Ya nuna mata hanyar fita, har a lokacin muryarsa a kasa ta ke. Ranta ta ji yayi wani daci, kawai ta juya ta fita. Ba ta ko tsaya daga wajan ba ta koma ta ci gaba da aikin gabanta har a ka tashi, ta wuce gida a binta.

***

FJ...

Tun aman da ya yi, jiya bai sake cin komai ba, kawai ya samu waje ya kwata da tsananin ciwon kai, wanda tunani ne ya haddasa masa shi. Da Khalid ya kira shi ma akan batun shirye-shiyen ce ma shi ya yi duk yadda ya yi dai-dai ne. Jin hakan Khalid ya san ba lafiya ba don haka tun a daren jiyan da su kayi waya ya zo hotel din, don daman ya za ci Fahad din yana gida har lokacin. Juyin duniyar nan Khalid yayi, amman sam Fj bai fada masa damuwarsa ba kawai kansa ke ciwo ya ke fada masa. Sai dai bai wani yadda ba musamman da ya bashi excuse din ya karce gefen ido na bayan ya tambaye shi game da plaster da ya gani like. A dakin kusa da shi ya kwana kamar yadda suka saba duk idan suka zo daki biyu ne.

Da safe ma bai ci abincin da aka kawo masa ba, kai tsaye ya tuna da sakwarar jiya, ba karamin dadi ta yi masa ba sai kuma bai samu ci yadda ya so ba saboda aman da ya dinga yi, shi ya sa ma yau ya nemi da a sake kawo mashi ita.

Knocking kofar aka sake yi kafin a turo kofar da a ka yi ya saka shi dago kai, ransa na ɓaci. Ganin Khalid ya saka shi ajiyar zuciya, don a zatonsa yarinyar nan ce ta dawo. Gefen gado ya samu ya zauna yana fuskantar FJ.

"Ya jikinka?"

Ya gyada kai

"Da sauki."

"Ka tabbatar zaka iya? Ko dai mu daga abin nan har ka samu sauki?"

Ya girgiza kai "Zan iya fa"

"Ma sha Allah. Kayanka sun zama ready zuwa dare ma za su aiko su"

Ya gyada kansa. Ya so daga fans eve din nan ko don kansa da har yanzun bai gama sarawa akai akai ba, to amman hutun jaki ne kawai zai yi, bayan haka ma bai cika son saɓa abubuwan da suka shafi wakarsa ba.

Magana suka ci gaba da yi akan shirin goben har yamma, kafin Khalid din ya fita da nufin bincikar duk wasu ayyukan da ya saka ayi.

*******.         ********

**FJ Fans Eve**

Hasken kalolin camera daban-daban ta ko ina ke hasko fuskarsa ta ko wanne sako da lungu daga yan jarida zuwa fans din da ke cike a hall din. Haka ya ratsa a siririyar hanyar da aka bude kuma aka kawata domin shi, ya haye can saman step din. Ya fuskanci kowa ya na daga masu hannuwa dukka biyun.

Wakokin da ya yi na karshe guda biyu su ya yi, a wajan tare da fans suna bin wakar su na dago masa hannu. Sai bayan ya gama ne ya zauna, kamar yadda ya yi alkawarin hoto da fans hakan ce ta kasance sai dai abin da yawa don haka ne mafi yawan da su ka samu damar yin hoto da shi din duk masu vvip da stall ne. Duk wanda ya je zai aje gift din da ya zo da shi sai ya yi hoto ya tafi.

Daga in da ta ke hankalinta ya yi matukar ta shi, tunaninta bai wuce ta yadda za ta isa wajan ba, har ta samu su yi hoto. Hoton nan dan ta yi shi ta yaye kaso arba'in na burikanta a kan Fj. A yau ta yi Allah wadai da rashin kudi wallahi, don dai ita kudin ticket din ta ma regular ne a haka ma ta sha wahalar tara kudin, ban da sauran shirye-shiryen.

"Kin san Allah ko za a mutu sai na yi hoto da Fj, ko da bayan ya fita ne"

Ta fada ta na gyara zaman gift dinta, ba tare da ta kalla Meenah da ke kusa da ita ba. Don hankalinta duka ya na ga Fj.

"Idan ya tafi kafin ki fito fa?"

Wani kallo Farha ta yi mata na takaici.

"Wannan ba fatan alkairi ba ne, yau road to Fj sai ya shaida hotona da na Fj wallahi "

"Ni ma zan so haka ai, ko don ma mu yaki zuciya zan so a samu hoton nan"

Suka yi da riya a tare ta ce

"Yau ko bacci ba zan iya ba ai"

Dariyar su ka sake yi.

*

Ta na jin bidirinsu a kunnuwanta, ta yi murmushi. Ita ce mai road to FJ kenan? Duk a zatonta ta zaci wata shegiya ce ma ashe bata da ko sisi. Page din sananne ne gaskiya sosai ga duk wasu fan din Fj don za ta je ma zai iya zuwa na daya a cikin fan fages dinsa. Ba ta zaci yarinya ba ce haka.

Cikin dan calculation din da tayi cikin kanta, ta gama yanke shawara kawai ta tabo Farha. Ta juyo da niyyar sauke bala'in da ke cikin kanta ga mai tabo ta sai ta yi arba da kyakkyawar mata, yar gayu da ita. Ta na sanye cikin wata doguwar rigar bubu mai dankaren laushi ko a ido, da veil dinta da ta zagaye kanta da shi. Duk da facemask din da ya rufe rabin fuskarta za ta shaida cewar kyakkyawa  ce duk da ba ta da farin da take mutuwar so kalar na Layla.

Murmushin da ta yi mata, ta maida mata ita ma.

"Ina da stall, ba zan yi hoton bane.."

Ta mika mata ticket dinta.

"Seat dina empty ne"

Da mamaki Farha ke kallonta. Ta sake yin murmushi.

"Biyu na siya"

Ta fadi, don ta san mamakin da ta ke yi. Mamaki dai bai bar Farha ba, wato ita har biyu ta siya, kuma shi ne ta tsaya a regular? Ita dai ta karbe kawai don kar ma matar ta sauya shawara.

Da dukkan farinciki ta juya ba ta ko tsaya godiya ba. Sai dai hankalinta yai matukar tashi ganin ya na saukowa daga step din alamun tafiya ma zai yi, wajan ya rikice da hayaniyar bankwanar da ake masa. Ba tare da tunani na biyu ba kawai ta gaggauta fita hall din, don ta san zai dauki lokaci kafin ya fito saboda yan nacin hoto.

Kuma duk cukuiniyar da ta sha ta isa gare shi bayan ya iso, zarafin bada gift kawai ta samu, ba ta samu hoto ba. Saidai yadda ta samu mika masa gift din kuma ya shiga da shi mota rike a hannunsa ba tare da an hade su da sauran gifts din da aka tattara ba yai matukar yi mata dadi nesa ba kusa ba. Kallon da ta masa ido da ido bai fi na 30 seconds ba amman har wani rawa jikinta ya ke yi don tsabar farinciki ina ga ace ta samu zuwa in da ya ke sosai har su yi hoto? Ba zata iya fasalta me zata ji ba ai.

Yamitsin mutane ya sa aka ture ta can gefe, a haka dai ta fito cikun mutanen ta na ci gaba da daga wuya da hannu kamar yadda ake masa bankwana.  Har ta juya za su tafi ta hango wannan yar gayun ta dazun. Da sauri ta isa wajanta.

Su kayi murmushi.

"Ba ki samu kin yi hoton ba ko? Sorry"

"Ba komai, na samu na mika gift ai a nan waje"

"Congratulations "

Ta sake fada ta na dai murmushin. Farha ta gyada mata kai.

"To Road to Fj zan ce ko me? Sai anjima ko?"

Farha ta yi dariyar jin dadi.

"Sunana Farha, za ki iya kirana da na farkon ma"

Su kayi dariya.

"Kar ki damu, za ku yi hoto, zan tabbatar maki da hakan"

Wani dadi da mamaki ya lullube Farha, amman bata tambayi ko ta yaya ba ta ga dai gara ta dan ja class dinta ita ma ta nuna yar gayun ce.

"To sai anjima ko?"

Ta juya da nufin ta fiya.

"Uhmm, number fa?"

Ta daure ta tambaya ganin za ta tafi, a to ina za ta sake ganinta? Wani murmushi ta yi cikin ranta, ta juyo tare da karbar wayar Farha Techno Pop 3 ta saka mata number ta.

"Ba ki fada min sunanki ba?"

"Beelah"

Ta fada dai-dai sadda wayarta ta dauki kara. Ta daga kiran tare da dagawa Farha hannun ta wuce. A kan idon Farha ta bude hadaddiyar motarta ta shige.

**

A razane Layla ta juyo har wayarta na sabulewa ta kalli Farha, sakamakon ihun da ta buga ba shiri.

"Heeheeee!"

Ta sake maimaitawa ta na fadawa a rigingine saman gado, hankalinta gaba daya akan wayarta.

"Kanki daya kuwa Farha?"

Ta tambaya ganin ba wai wani abu bane ya samu Farha din kamar yadda ta zata. Farha ba ta ko kalle ta ba ta ce

"Ba za ki gane bane kawai"

Don ba ta ma san ta ya zata fara mata bayanin dadin da ta ke ji a yau ba. Ita ce ido da ido da Fj ta mika masa gift. Wayyo dadi, har wani zazzabi ta ke ji yana shirin mamaye ta. Yanzun ne ta gano dadin da ake ji in an ga masoyi. Wai!

Ta dago kanta ta kalli Layla da ta fita batunta, ta ce

"Wallahi da kin je abin nan ko..."

Wani kallo da ta biyo ta da shi ya saka ta yin shiru kawai ta turo baki gaba, ta na maida hankalinta akan wayar. Firarta ta dinga yi a wani group da ba ta dade da bude shi ba na whatsapp duk dai fans din ne a ciki. Ta na ta faman tura masu hotonan da aka yi yau din, da ita ma a mabambanta kafafe ta samo su.

Yanzu da ace ta samu sun yi hoton nan ai wallahi mutuncinta da ajinta ba karamin daguwa zai sake yi ba. Amma ai ba komai tun da akwai gaba. Don kuwa ta ci alwashin in dai zai yi concept ko ba a Katsina ba ne sai ta tabbatar da ta je ko da za ta saida duka kayanta ne ta siya ticket.

'Beelah Fan' Haka ta yi saving number Beelah a wayarta. Ta yo seaching din ta a whatsapp. Dp dinta hoton wata flower ce baka.

"Hello" Ta rubuta mata ta tura. Ba ta ga alamun ta na online ba don haka sai ta fito kawai, ta koma group dinsu suka dasa firar event din yau.

****

Kwalin lemon ta aje, kafin ta dauki glass cup din da ta cika da lemon. Rufe idanuwanta ta yi a hankali ta na jin yadda sanyin lemon ya zirara ta cikin makonshinta ya wuce. Yar karar da wayarta ta yi mai nuna alamun charging da ake mata ya cika, ta saka kai dubanta ga wayar. Ajiye lemon ta yi a side table  din da ke gefen kujerar, ta mike ta zare wayar ta dawo. Kai tsaye data ta kunna ta nufi shafin FJ na Instagram in da ya bayyana tarin farincikinsa da kuma godiya ga fans dinsa. Ta cije lebenta na ƙasa ta fita shafin, har zata fito sai wani tunanin ya kai ta ga road to FJ a take ta yi seaching ta shiga. Nan din ma dai duk hotuna da videos din event din ne. Ta yi guntun murmushi kafin duk ta bi posting din ta yi like.

Sunan da ya leko ta saman wayarta daga whatsapp ya saka ta fita daga IG din baki daya ta hau whatsapp.

**FJ Die Fan:** *Hello*

**Beelah:** *Hey, kin koma gida lafiya?"*

Kafin ta fito daga chat din ta ga har ta karanta har ta na ma typing. Wata kalar dariya Beelah ta saki, sa'ilin da ta ke mika hannunta ta dauki lemon ta.

"Kin ga Mamma a nan"

Muryar Naseer ta janye hankalinta ga abinda Farha ta turo"

Dole ta kashe datan ta aje wayar, sannan ta juyo ta na fuskantar su shi da Noor da ya ke dauke da ita. Su dukansu bakinsu bude da dariyar da su ke watso mata da ta ke jin wata kalar takura na taso mata. Ta murmusa ita ma, don ba yadda za ta yi.

"Har kun yi me?"

Ya dan yi turus ya na kallonta

"Wato ma baki ga dadewar mu ba?"

Ta sake yin dariya

"A'a fa, kawai na san halin 'yar taka ne in kuka fita"

Shi ma dariya ya yi, ya na karasawa gareta ya ware hannunsa daya ya na mata waje a gefen Noor. Ta isa ta lafe duk ya rungume su biyun.

"Abbu yunwa"

Noor ta fada a cikin kunnensa. Ya kalla Beelah da ya san ta ji yana dage gira alamun tambaya. Sai da ta zare jikinta ta kalla Noor

"Golden morn din da kika gama sha fa ko awa daya ba ayi ba? Ko Sophie bata baki ba?"

Noor ta sunne kanta cikin jikin Naseer.

"Ai goldenmorn ba abincin da zai rike mata ciki bane, yarinyata ta girma ko?"

Ya ida maganar yana maida dubansa ga Noor. Dan tabe baki ta yi

"Sai ka koya mata cin abinci ai, cikinta yai rusheshe"

Ta gwada yadda cikin zai yi da hannunta. Duk suka sa dariya. Noor na girgiza kai tana noke kafada.

"Mu je mu ci abinci ko"

A dining duk suka zauna. Ta bude kular da bata san ko meye a ciki ba tun da ba ita ta girka ba. Taliya ce jallof ta yi share share kwance cikin ruwa abinta. Ta yamutsa fuska jin karni karnin kifin da ke tasowa. A haka dai ta zuba mashi ta tura gabansa ta zubawa Noor kafin ita ma ta zuba.

Tana latsa wayarta ta na cin abincin.

**FJ Die Fan:** *Ya gajiyarki ta jiya? Sannu"*

Ta karanta sakon Farha. Bayan ta maida mata amsa ne ta dago ta kalli Naseer yadda ya ke ta juya cokalin da alamun ba ci ya ke ba, haka ma Noor.

"Babe ya baka cin abincin?"

"Ke kina jin dadin cin shi?"

Ta kalli plate dinta da ta ci fiye da rabi ta kalle sa

"Me ya samu abincin?"

Ya yi yar dariya

"Ba komai. Ci gaba da ci"

Murmushi ta yi masa ta na maida hankinta a kan wayar ta na kuma cin abincin, duk da a zahirin gaskiya ba wai ya na mata dadi bane da danbanzan tarugu da yayi yawa kuma ba maggin kirki. To amman da ta nuna ba dadin ba wai za su ci bane su ma, karshe kuma ya roke ta ta girka masu wani abu, abin da ta ke jin wahala da kuiya

kenan don haka gara su ci abincin shophie da hakuri in ya so gobe ta ci uba*nta.

Abincin da Naseer bai ci ba kenan, sai dai ya sha coffee don ba zai je gida ba yau Hajja ta tusa shi gaba. Noor kuma ya hada mata cornflakes ta sha.

🦋🦋🦋

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.