Free chapter · Read without an account
Chapter: 8
Fj..
Ya na tsaye kofar washroom yana tsane gashin kansa da ya jike wajan wanka, wayarsa ta yi kara. Sharewa yayi har ta tsinke, aka sake kira. Rataye towel din yayi jikin kofar kai tsaye ya nufi in da wayar ke aje ya dakko ta. Gabansa ya fadi ganin sunan Suraj, ya san kiran daga Daddy ne, don baya kiran shi, a duk lokacin da yake son sanar da shi koma meye to ta wurin Suraj sakon ke biyowa. Suraj PA din Daddy ne sun dade tare tun ma kafin Daddy ya tsunduma a harkar siyasa, don a lokacin duk wasu shige da ficen kayayyakin Daddy Suraj din ke kula da su, sakon cikin gida da sauransu.
"Babban tauraro"
Ya jiyo Muryar Suraj kamar yadda ya ke kiran shi a duk sadda suka hadu a zahiri ko ta cikin waya. 'yar dariya ya yi kawai, don baya cikin yanayin daukar tsokanar duk da Suraj din ya shiryo. Kusan Suraj din ya fahimcici hakan, don ya san Fahad sarai ba tun yanzun ba don haka kawai ya zarce da fadin sakon da aka bashi ya isar.
"Oga ya ce akwai Event da za a gudanar on 10th November a can..."
"Ina da abubuwan yi a ranar"
Ya katse shi.
"Don Allah ka samu ka je din, ko mintuna talatin kawai ka yi, ya ga cewar ka je..."
"Ko kuma duniya ta shaida zuwana?"
Ya sake katse shi a karo na biyu.
"Ba yadda kake zato bane, ba haka bane. Ka yi kokari ka kashe wani abun, zan kira Khalid mu yi magana."
A yadda Fahad yai shiru ya san ba wai zai sake samun amsa bane don haka kawai ya kashe wayar.
Wayar ya jefar kan gado, Ya zauna ya na dafe kansa. Har sai yaushe ne Daddy zai bar shi ya shakata da rayuwarsa ne wai? Har sai yaushe zai bar danganta shi cikin harkokin siyasar shi ne? Baya so, ba tun yau ba don wannan tsohon zance ne kan sanin baya da sha'awar harkokin Daddy, kamar yadda shi ma Daddyn baya shaawar ta shi sana'ar.
Kwankwasa kofar a kayi, kai tsaye ya san Khalid ne don ya riga ya hardace kalar yadda ya ke kwankwasa masa kofa sau biyu kawai kafin ya murda idan bude take ya shigo, idan a kulle ne zai jira har ya zo ya bude masa. Yanzun ma haka yayi. Karasa zura brown shirt din da ya ke sawa yayi kafin ya isa ga kofar ya murda makullin sannan ya dawo baya ya na bawa Khalid din damar shigowa.
"Malam Suraj ya kira ni..."
Ya fadi sa'ilin da ya ke zama kujerar da ke fuskantar Fahad din. Ya ci gaba da fadin.
"Ba ka da komai ranar don haka kawai na shaida mashi za ka je din. Gifts dinka gasu nan za a shigo da su, shaf na manta ba a kwasosu daga motar ba"
Tun da ya fara magana Fahad ya zuba mashi ido yana kallon shi, cike da mamaki. Mamakin yadda Khalid kai tsaye ke yanke mashi hukunci a kan duk wasu harkokin sa.
Ya na gama fadin abin da zai fada kuma ya aje wata paper bag mai dauke da hoton Fj din, da tun shigowar shi take hannunsa, a saman kujerar da ya tashi. Bai sake kallon shi ba ya bar dakin da sauri, ya sani in har ya tsaya gardama ce za su dasa da karewarta ba yanzun ba.
***
Farha..
Bata sha wani wahalar gane kwatancen ba tun da gidan ba wasu lunguna bane kamar na su da sai a shiga kwana ta fi biyar kafin a gano layin gidansu. A daidai gidan mai lamba biyar da milk din gate ta tsaya, kamar yadda Beelah ta kwatanta mata. Ba kowa bakin gate din sai dogon benci da jambox aje a sama, da alamu na mai gadin gidan ne. Tura gate din tayi ta ji shi gam, bai ko yi alamar matsawa ba, don haka ta shiga kwankwasawa.
Yar karamar kofar aka bude, mutum da ba zai haura shekara talatin da biyar ba ya fito, sanye cikin uniform din da take zaton jami'in tsaro ne. Da sauri ta matsa baya tana gaishe shi. Bai amsa ba sai gaisa ta da yayi shi ma. Ya daura da fadin
"Ai ba za a ji karar bugun gida ba, na dan shiga ne na dawo ayi hakuri."
Da mamaki ta ke kallon shi tana son danganta hakurin na meye to?
"Hajiya ta sanar min tana da bakuwar da zata shigo..."
"Oh..ah.. ba komai"
Ta katse shi. Tana shanye mamakin ta na fahimtar shi ne mai gadin.
"Bismillah" Ya sake fadi ya na bata hanyar wucewa.
"Wow!" Ta furta kasan ranta, kai tsaye ta hango yadda hotuna za suyi matukar yi mata kyau a harabar gidan nan. Ga wasu motoci masu daukar ido da aka jere kamar ta jingina jikin daya ta dalla selfie ta ke ji. Bayan haka ma fulawowin da aka kawata gidan da su kadai ma sun isa jawo mata duk wata kima a wajan kawayenta, musamman na social media. Motsin da ta ji ya saka tayi saurin kama kanta ta kauda idonta daga wajan.
"Kofar da ta ke kallon ki ita zaki shiga, Hajia na ciki"
Maigadin ya fada sa'ilin da ya ke mata nuni da kofar da hannu. Ta kaɗa kai ta wuce, shi ma ya koma bakin aikinsa. Murda kofar tayi, ta kuwa buɗe wani sassanyan kamshi hade da sanyin AC suka ratsa ta bata san sadda ta lumshe idanuwanta ba da wani kalar fata da ya bijiro a zuciyarta lokaci daya. A cikin ranta take jin ita din mai Sa'a ce, ah to in ba sa a ba ina ita ina Beelah? Ina ita ina sanin wani mahaluki ma a irayen wadan nan gidajen? Lallai yau Fj ya mata rana! Ko ba komai ta silar shi ta san ta, kuma ta ke fatan ta san shi ido da ido ta sanadin dai Beelah din.
Sautin takalman Beelah ya dawo da ita sabuwar duniyarta. A lokacin tana zaune ne a daya daga cikin tantsama-tsantsaman kujerun tana karewa falon kallo.
Lokaci daya fuskarta ta fara fiddo murmushin maida wa Beelah martanin na ta murmushin. Ta na sanye da doguwar rigar kanti, mai gajeren hannu daga kasa kuma tsagu ne gefe da gefe da suka bayyana anklet din da ke kafarta wadda ta kai inci biyu. Kanta bandana ne cewai da jelar gashinta ke lilo tsakiyarta. Ai gaba daya ta gama tafiya da Farha, ji take in m ta bude ido taganta kanar Beelah, daman zata bude ido ta ganta 'yar gayu haka kamar ta.
"Oyoyoo!"
Beelah ta fada ta na ware hannuwanta tare da dan dukowa wajan Farha. hakan yasa Farhan ma ta bude na ta hannun ta karbi gaisuwar rungumar hannu bibbiyu, cikin fasuwar kai. Ita fa duk yadda ta ke son mutum ta hange su tsaf a wajan Beelah.
"Sannu da zuwa"
Ta kuma fada ta na zama kusa da Ita.
Ta amsa da "Yawwa." Kafin su ci gaba da gaisawa.
Duk dai firar akan Fj ne, wanda Beelah sosai ta sha mamakin yadda Farha din ta san kusan komai a kan Fj. Order snacks ta yi masu suka ci da lemo ko ba a fada ba ba girki za ta yi ba. Ita kam Farha ba tayi mamaki ba hakan ma dadi ya mata don kayan ciye ciye ne birjit haka aka baje mata su da kusan rabi da kwata bata taba cinsu ba sai dai ta hango, ko kuma in Layla na online classes ta leka tana gani.
"Kin taba zuwa GHC?"
Beelah ta tambaye ta. Zaro ido ta yi waje
"Ni?" Sai ta saka dariya, ta na jin kamar Beelah ta so zagin ta ne kawai.
Sai ta dan yi shiru. Ganin Beelah na kallon ta ta san karshen maganar ta ke jira
"Akwai tsada sosai, bayan tsadar ma wa zai gayyace ni?"
Ta ida fadi a kunya ce. 'Yar dariya Beelah ta yi.
"In dai kina so ba wani abu ai, sai in biya maki, don gayyata baki da matsala da wannan"
Ta sake waro idon ta akan Beelah.
"Da gaske?"
Tab! Ita a Golden Hour Club?Ga koshi ga kwana yunwa. Don kuwa ba karamin daukaka ba ce a ke mutum ya je 'GHC' kamar yadda suke takaita sunan. party ne ko ma ta ce Club, bakar tsada ne da shi, don celebrities da masu kudi ne sosai wajan kuma hoto wannan guarantee ne ma sai kun yi shi da duk wanda kake so. Duk bayan wata uku ake yi, in ka siya ticket ne ko an aiko ma katin gayyata kawai zaka iya shiga. Ba ma kowa ake saidawa ticket din ba sai ka isa. Party ne ake yi kusan tun dare har asuba ma, wasanni ne, waka, games da abubuwa da dama ake yi. Kuma in har ta je mutuncin ta zai karu sosai a fans din Fj, babu kuma abin da zai sauko da wannan mutumcin!"
"Ina so"
Ta fadawa Beelah kanta tsaye, a ranta tana tsara ko za a mutu sai ta san yadda ta yi ta je wajan nan.
"Kar ki damu, za mu yi magana, ba zai wuce sati uku ba za ayi wani ai."
Dadi kamar ta taka kan jariri haka take ji. Sai da tayi la'asar sannan ta shirya tafiya. Wata leda katuwa Beelah ta dakko ta bata sannan ta sa, direban ta ya kai ta har gida.
*
Layla...
Ba karamin dadi ta ji, yau da ba a ce ta kai ma mutunen can abinci ba don har yanzun bata huce daga sunan da ya kira ta ba.
"Sai tafiya?"
Ta ji muryar Zee. Ta juyo bayan ta ida rufe locker din kayanta. Suna tsaye ita da Maimuna da alamun zuwan su biyun kenan.
"Wallahi fa" Su ka gaisa sama sama ta wuce, don ta san halin Zee in ta biye mata surutu ne za ta yi ta zuba mata bata gajiya ita sam da magana.
Kanta duke tana laluben wayarta da ke tsuwwa cikin jikka, sai ji tayi tayi karo da mutun. Yayi saurin ja da baya gudun kar kayan da ya kwaso su zube, duk da haka sai da wani abu mai kama da kwali ya fado.
"Ya Allah! Yi hakuri don Allah"
Ta fada ta na dakko abin da ya fadin. Ganin babu wajan da zata jogana shi ya sa ta ce
"Ina zaka kai ne?"
"Yawwa Allah iso min da shi Please"
Ya fada da fuskar roko. Khamis, Yana daya daga cikin ma aikatan wajan. Ta gyada kai kawai ta bishi baya. Turus! Ta ja ta tsaya ganin lambar dakin da ya shiga, tana nadamar biyo shi din. 'Ba kuwa zan shiga ba' Ta fada a cikin ranta, tana samun waje ta tsaya da nufin in Khamis din ya fito ta mika masa, amman wani abin takaicin yadda Khamis din ya fito ya wuce kamar walkiya, sannan ya bar kofar a bude da nufin ita ya bar mawa ta shiga, shi ya matukar kona mata rai. Don haka a cikin hade ran ne ta shiga da sallama.
Kallon me ya kawo kin da ya ke mata ya saka ta daga gift din sama tana nuna mashi, alamun shi ta zo kawowa.
"Je ki da shi"
Ya fadi sa'ilin da ya ke daukar wayoyinsa da ke zube bisa gado tare da zura takalma. Hakan ya nuna mata fita zai yi, kuma yadda ya tunkaro kofar fitar ne ya saka dole ta koma baya ta bashi waje ya fita tare da jawo kofar dakin ya rufe. Ta bi shi da kallo sannan ta maida kallon ta ga abin da ke hannunta da tunanin ina zani da shi? Bata sake wani dogon tunani ba ta bi bayansa. Yana daf da shiga mota ta isa wajan, har ta na dan nishin saurin da ta dinga bugawa don ta isko shi.
Cikin gundura da sake ganinta ya ce
"Me ye kuma? "
Ta sake daga masa gift din.
"Na ce ki tafi da shi ko baki jin hausa ne? Wait...are you stalking me?"
Ya fada ya na zuba idanunsa cikin na ta tare da gyara tsayuwa. Wani malolon bakin cikin duniya, da wata matsiyaciyar kunya suka lullubeta lokaci daya ganin yadda hankalin mutanen wajan ya dawo wajansu. Da kasa zata tsage a lokacin babu abin da zai hana ta shige ta huta da ruwan idanun da ke binta a jiki. Ta janye idonta cikin sauri har ta na tuntube ta bar wajan. Allah ya rufa mata asiri ta na fita ta hangi napep ta yi saurin tsaida ita, ko ciniki bata yi ba ta fada kawai.
*
Har ta isa gida ranta cike fal da takaicin yarfa ta da yayi a bainar jama'a. Don haka wardrobe dinta kawao ta bude ta jefa sheg**n gift din da duk shi ya ja mata, da nufin in ta koma ta ba Khamis can ya bashi abinsa don bata da bukatar koma meye a ciki.
Wasu 'yan kunne suka dauki idonta aje bisa gadonsu, sai shining stone din da akayi ado da shi ya ke, wanda ko ba a tambaya ba zai bayyyana cewar da tsadar shi. Cikin mamaki ta dauka tana tunanin na waye ?
"Yaa Layla?"
Farha ta kira ta, da dan karfi da kuma mamakin yadda bata ji shigowar ta ba.
"Wannan fa?" Ta dago 'yan kunnen.
"Nawu ne"
Farha ta bata amsa tana dan cizon akaifar hannunta. A ranta tana fatan kar ta fara jero mata tambayoyin nan nata na tuhuma.
Daga waje suka juyo muryar Umma
"Laylan ta dawo ne?"
"Umma..." Ta fada tana mika mata yankunnen ta fita.
"Ai ban ma ji shigowar ki ba, ina nan da Farha da yawon nan na ta kamar ta ci kafar kare.. abincinki na cikin jar kular nan ta tsakiyar na zuba maki shi"
"Kamar ko kin san donut kwara daya ne kawai cikina duk yau"
Ta fadi tana nufar hanyar kitchen din. Tana jiyo sababin Umma akan bata tsaya taci abinci ba, kuma acan din ma bata ci komai ba. Bayan ta zuba abincin tsakar gida ta dawo in da Umma ke zaune a tabarma ta zauna ta na ci suna fira, tuni ta manta da bacin ran da ta shigo da shi. Anan Baba ya tadda su suka ci gaba da fira har gabatowar magriba kafin Abban yayi alwala ya tafi masallaci, su din ma duk suka tashi. Kasancewar bata sallah sai ta shige dakinsu kawai ta kwanta don a gajiye take, aikin da su kayi yau da yawa na wani workshop ne da ake yi aka basu kwangila, kuma hada ita cikin wadanda aka zaba za su dinga abincin workshop din har na sati daya. Nepa aka maido, da sauri ta tashi ta dakko wayarta ta jona caji don wayar tata har ta yi ja ma.
"Ya Laila ni zan saka a jikin bango.."
Farha da ta fito daga toilet ta fada tana jan hular kanta. Bata ce mata komai ba don ta san dalilin baya wuce ta na danna waya tana caji ne, tun da ba gajiya ta ke da latsar waya ba a rayuwarta.
**
Farha...
Ajiyar zuciya ta yi jin har ta gama sallah Layla bata tambayeta akan yankunne ba kuma. Ta matsa jikin bango ta jona wayar caji sannan ta shiga tayi editing yankunnen da tana dawowa daga wajan Beelah ta ciro su a cikin ledar da ta bata. Ta shinfida wani plain purple veil dinta ta daura yankunnen tayi masu hoto. Bayan ta gama hoton ne Umma ta kira ta sai ta manta bata maida a cikin ledar ba, shi ne ya saka ma har Layla ta gan su. Don da ma nufinta idan ta gama hoton ta ida zazzage sauran kayan ta gani. Bayan ta gama editing ta shiga shafinta na Instagram ta yi posting hoton tare da caption 'Thank you for the stunning earring. I can't wait to wear them...❤️✨'
Murmushi ya kasa barin fuskarta yadda ake ta liking hoton, ita ta sani daman shigowar Beelah rayuwarta alkairi ne, dagawarta ce ta zo, don ba karamin mutunci zata kankaro
mata ba da alama..
Tagging dinta da aka yi a wani post ya saka ta janye idanunta daga kallon yadda 'yankunnen ke sake burgeta ta koma akan posting din.
Fj's stalker...
🦋🦋🦋