Free chapter · Read without an account
Chapter 1
by Queen Jiddah · GAMO MUKA YI
🥹GAMO MUKA YI🥹
Chapter 1
True Life Story😱🙆♀️
By Queen Jiddah....✍️
Zaune muke kamar koda yaushe a cikin 'dakin mu, da misalin karfe goma na dare tare da Kanwa ta, dukan mu waya ce a hannun mu sai dai ita indian film take kallo sa'banin ni da nake yin Chat da wani class mate 'dina mai suna Kokanii ! Shine nick name din da muke kiran sa a school.
Film din take kallo tana dariya, yayi dana juyo ina tambayar ta me take ma dariya, sai tace min na daina damun ta idan bazan kalla ba na kyale ta, sai nayi murmushi na cigaba da chat 'dina ba tare da na tankata ba.
"Assalamu Alaikum".
Naji wata murya mai amo da 'karaji tayi sallama, ban saka komai a raina ba na kar'bi sallamar tare da waigawa domin ganin meyin sallamar, kasan cewar a uwar 'daka muke amma daga inda muke zaka iya hangar kofar falon mu, gashi kuma kwan lantarkin mu na falo ya lalace shiyasa baka iya ganin falon sosai sai dai kana iya hangar waje dai dai kofar falon.
Koda na juyo nayi GAMO da abinda ya gigita tinani na, nan take na fara karkarwa jiki na na bari na sake kallon kofar.
Wata mata ce tsaye a bakin kofar sanye da farin hijabi zanen jikin ta iya guiwa yayin da take 'dauke da ,kafa daya tal👌 kuma tayi tsaye, ga zanin ta a yaye ballan nata nace ko ido nane, gashi bana iya ganin fuskar ta, farin watan daya haska waje ne ma ya bani damar ganin siffar ta.
Da sauri na waigo kusa da kanwata dake zaune tana kallon, da yake ba wata tazara ce mai yawa tsakani na da ita ba, domin shekara daya da watanni na bata, sai na kalle ta cikin firgici ba tare da nace komai, domin tsoro nake ji kar aje nikadai ce ke ganin matar ganin kanwata bata tsorata ba, murmushi Maryam tayi ka na cikin kwanciyar hankali tace min, "baby ki kwantar da hankalin ki duk abinda kika gani nima na ganshi" sai muka sake tsinkayi muryar matar tana fa'din.
"Maman ku ta dawo daga Tudun Wada?".
Sai nayi karfin halin ce mata " A a bata dawo ba, duk da kuwa nasan maman mu bata je can ba, domin can din gidan kakar mu ce kuma yau a can muka wuni, dawowar mu kenan ma saita shigo ta same mu.
"To daman sa'ko ne nazo na bata, saboda haka idan ta dawo ku gaya maya na dawo ban tarar da ita ba" ta sake fa'da cikin murya mai amo tana kallon mu.
Yayin da na 'dan sake juyowa 'kirjina yana harbawa na sake kallon kafar ta still dai Kafar 'daya ce har yanzu, cikin karfin hali na ce mata.
"To shi kenan idan ta dawo insha Allah za'a gaya mata".
Daga budar bakin ta saita ce min.
" To idan maman taku ta dawo wa zaku ce tazo tana neman ta?".
Sai nace mata "to wa za'a ce mata?" Kuma jiki na har yanzu bai dena karkarwa ba, yayin da ita kuma Maryam duk wannan musayar zancen da nake da wannan matar wacce na kasa gane shin mayya ce ko Aljana, bata tanka mu ba, kuma bata tashi daga kwancen da take ba saima shiru da tayi tana sauraron mu.
Sai naji muryar ta ta 'kara girma da amo ta sake ce mana.
"Kuzo na baku sa'ko idan ta dawo sai ku bata!".
Na 'dago da sauri na kalle ta, zuciya ta na tsananta bugawa, domin idan harba gizo ido na kemin ba tabbas babu komai a hannun ta kuma sannnan hannayen ta zube suke a cikin hijabi ko ganin su ba ma yi, to wane sa'ko zata bamu?
Sai na aro duk wata jarumta na sanyawa kaina, ka na nace mata.
" A a gaskiya ba sai munzo ba, kawai ki fa'di sa'kon ki inyaso idan ta dawo sai mu gaya mata".
Sai tace min.
"Me kike nufi kenan ba zaku zo ba ko?".
Nace mata "Eh mukam ba zamu zo ba"🥹 jiki na a matukar sanyaye.
"To shi kenan tinda ba zaku zo ba, ni bari nazo na kawo muku!" Ta fa'da tana tunkaro mu....✍️
Idan kuna so na saka maku cigaba da wuri, to kuyi sharing kuma kumin react👌🤓.
Kuyi following wannan channel din domin samun cigaba daga zarar na 'daura👇👇.
***
Daga Al'kalamin👑 Queen Jiddah....✍️