Free chapter · Read without an account

Page-8

by Aisha G Umar · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*

     (*F.W.A)*©✍️

     ⭐⭐⭐


Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍

___________________________________________________




بسم الله الرحمن الرحيم.

اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 





❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁





Free book📓




By



*Aisha G Umar*

_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_





Page8️⃣






Wata mota tafe a kan titi tun daga nesa su ke ta faman danna min hon, amma ina babu abin da ke shiga ƙwaƙwalwata, domin a yanzu na kai matakin da dishi-dishi ma na ke gani. Saura ƙiris motar ta bi ta kaina Allah ya taƙaita, sai dai garin kaucewa da masu motar su ke yi da ƙarfi motar ta gogeni, wanda hakan ya sanya ni yin gefe haɗi da faɗi, na buge kaina jikin ƙaramin ginin signboard ɗin da ke wurin, ta ke jini yafa zubar min daga kaina. Tsaida motar su ka yi da hanzari, drivern ne ya fara buɗe ƙofa ya fito, ka na wata mata da ke mazaunin baya ita ma ta buɗe ta fito.


Juyowa su ka yi suna kallon inda na ke kwance har mutane sun fara isa inda na ke tare da yin hayaniya, da sauri ita da drivernta su ka nufo ni hankalinsu à tashe. Suna isowa wurin cikin tashin hankali matar ta dubi drivernta ta ce. "Bala mu kaita hospital yanzu!" Shiru mutanen wurin su ka yi suna kallonta, dama suna shirin yi mata masifa amma kuma su ka ga itama ta shiga damuwa matuƙa.


Da to Bala ya amsa sannan su ka ɗauke ni zuwa motarsu, asibiti su ka nufa da ni direct. Ko da muka isa likitoci su ka ce sai anzo da police tukunna za su karɓeni, saboda kar daga baya ya dawo musu matsala, magiya matar tai ta mu su akan à fara yi min magani inyaso daga baya sai a yi maganar police, gudun wani abu ya same ni idan aka jinkirta su duba halin da na ke ciki, da ƙyar su ka amince aka shiga da ni emergency room.


Tsawon wasu lokuta daga bisani likitoci suka fito,

nan Doctor ya nemi ganawa da matar. Bayan ta isa office ɗin Doctor, ta dube shi ta ce, "doctor ina fatan babu abin da ya sami yarinyar nan? Ya take yanzu?" Doctor ya numfasa ka na ya ce, "buguwa ne akanta, sannan kuma anyi sa'a buguwan bai isa zuwa wasu ɓangarorin kwanyarta ba, kuma jininta bai zube sosai ba, da hakan ya faru ban san ya zan miki bayani ba, sai kuma ƙuƙƙurjewan da ta yi, amma it's okay, komai yazo da sauƙi.


Ajiyar zuciya matar ta yi da jin magan-ganun likita, "amma me alaƙarki da yarinyar?" Cewar Doctor yana kallonta, domin dai bai ga wani alama da zai nuna matar na da alaƙa da yarinyar ba, amma kuma yadda ta ta da hankalinta ya sanya masa shakku, kallonsa ta yi tana tunanin abin da za ta ce masa, kada ta ce wani abu kuma doctor ya yi mummunar fahimta, dama ta sha wahala kafin ya yarda ya amshi yarinyar, don haka ta ce, "ya za ka ce haka doctor? She's my daughter".


Ba don ya yarda ba yai shiru, sannan ya jawo paper tare da rubuta mata maganin da ake buƙata, tashi ta yi ta amsa haɗi da yi masa godiya, ƙara yi mata bayani doctor ya yi ka na tai ficewa don zuwa sayan magani. Bayan ta fita daga office ɗin Bala ya taho yana fadin, "Hajiya me likita ya ce jikin na ta da sauƙi?".


Ta amsa masa, "da sauƙi Bala doctor ya tabbatar min zuwa dare za ta farka" "Allah ya ba ta lafiya, am Hajiya ki gafarceni don Allah laifina ne" "ba komai Bala dama Allah ya ƙaddara faruwar hakan, muma godewa Allah da komai ya zo da ɗan sauƙi, yanzu mu jira farkawanta kawai, bari in je in siyo magani" ta faɗi tana shirin tafiya, Bala ya tsayar da ita da faɗin, "a a Hajiya ki bani ni in sayo" "a ah, gwara na je da kaina ba komai za ka iya ganewa a ciki ba" ta faɗi haɗi da wucewa.


Kan ta isa pharmacy wayar ta ya yi ƙara, hakan yasa ta tsaya tana ɗagawa, ta cikin wayar muryar yarinyar da ba ta wuci sa'ar Nur ba ta ce, "hello hello Momy?" Matar ta amsa, "na am my dear kina lafiya?" "Ina lafiya Momy, kin daɗe ba ki dawo ba, Daddy ya yi ta calling ɗin phone na ki amma baya samu", cewar yarinyar cikin damuwa, ta wani ɓangare kuma muryar wani ya ce, "Asma'u da Momynki ki ke waya?" ta amsa da, "yes Daddy ita ce".


Tahowa ya yi da sauri haɗi da amsar wayar ya sanya a kunnensa yana faɗin, "Rahama fatan komai lafiya? Mun shiga damuwa sosai da rashin samunki à waya, idan na kira switch off ake faɗa min, me ya faru? Ko kun kusa isowa ne?" Ya ƙarashe maganar cikin tsumayin amsarta. "Kwantar da hankali Dadyn Abba, matsala ne muka samu, a hanya mu ka gamu da accident, amma Allah ya taƙaita mana abun ya zo da sau...". 


A razane ya katseta da ce wa, "what! accident? Garin ya ya?" Asma'u da sauri cikin damuwa ta ce "Daddy accident? Me ya samu Momy?" "No my dear ba komai, je ki yi wasa abinki" cewar Dadyn, haka ta wuce cikin damuwa duk da Dadyn ya ce mata ba komai, bayan ya ga tafiyan Asma'u sai ya mai da hankalin sa ga wayan ya cigaba da faɗin, "ina jinki garin ya ya hakan ta faru, ba dai abin da ya same ku ko?".


Hajiya Rahama ta ce, "bayan mun kamo hanyan dawowa ne tsautsayi ya sa muka kaɗe wata yarinya, mun kaita hospital amma doctor ya ce da sauƙi jikin na ta" "subhanallahi! Kai wannan labari bai yi daɗi ba, Allah ya tsare na gaba, amma ya ki ke ganin jikin yarinyar yanzu?" Rahama ta ce, "ameen, alhamdulillahi kamar yadda na ce maka doctor ya ce da sauƙi, amma anyi mata alluran bacci".


Mijin na ta ya ce, "to masha Allah, Allah ya ba ta lafiya ya kuma tsare na gaba" da ameen ta amsa sanna ta ɗaura da cewa, "ni babban matsalata ma shine tunanin iyayen yarinyar, na san yanzu haka suna ta aikin nemanta" ya ce "haka ne amma idan ta farfaɗo sai ki tambayeta, sanar da ni wani asibitin ku ke? Zan kamo hanya inzo" ta ce "a ah Dadyn Abba, kar ka damu ka zauna da yaran nan kawai, ka sansu da saurin shiga damuwa, zuwa gobe da safe ma idan Allah ya kaimu jikin na ta ya yi sauƙi, kuma na haɗu ta da iyayenta zan dawo insha Allah" "to ba damuwa duk yadda ake ciki dai ki sanar da ni".


DARE.


Cikin dare kusan ƙarfe biyu da rabi. A hankali na fara buɗe nannauyun idanuwana tare da sauke su saman slim, motsa su na shiga yi ina kallon wurin da ban taɓa gani ba, samu damar juyawa na yi idanuwana su ka kuma sauka kan wata mata da ke kwance a ɗayan gadon gefen da ba kowa, sake matsar da idona na yi saman dogon ƙarfen da ke ɗayan gefena, ganin drip na ruwa na yi a saƙale yana tafiya a hankali, da sauri na maida kallona kan hannuna, nan na ga ashe ƙara min ruwa ake yi.


Motsi mai ƙarfin da na yi na neman tashi ne yasa na ji kaina ya amsa, rintse ido na yi da ƙarfi saboda zafin da na ji, na ɗaura ɗayar hannuna da babu allura zuwa kaina. Motsin na wa ne ya tayar da hajiya Rahama, ganin na farka yasa ta sauka daga kan gadon da ta ke da hanzari ta iso gu na. Cikin kulawa ta ce da ni, "yarinya ya jikin na ki da sauƙi? Kan na ki na yi miki ciwo ne?" Sai a lokacin na buɗe idona ina binta da kallo kamar ban fahimci kalmar ta ba.

Kuma tambayar da ta sa ke yi min ne yasa na ɗaga mata kai a hankali, alamar da sauƙin, "kina da buƙatar wani abu?" Kamar ba zan buɗe ba ki ba saboda nauyin da ya yi min na ce, "ina son zuwa, bayan gida" Taimaka min ta yi ta tsayar da tafiyan ledan ruwan da ke shiga jikina, sannan ta gyara min igiyar hannuna sannan ta kuma taimaka min zuwa toilet. Har sai da na fito nan ma ta kamoni ta mayar da ni kan gado, kallonta kawai ni na ke yi da tunanin wace wannan matar?.




Last page

___________________________________________________



Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?





_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.