Free chapter 路 Read without an account

KADDARAMU CE....3

by Nusaiba Ibrahim Rimi 路 茦ADDARARMU CE TA ZO A HAKA

馃 茦ADDARAR MU CE....馃憣
(Ta zo a haka)




鉁嶏笍 Nusy bee 
鉂わ笍 *Young talented writers association YOTA*鉂わ笍 


Page 3


My TikTok account 馃憞


***



My Instagram account 馃憞

***


My arewa pen link 馃憞


https://arewapen.com/u/nusybee143


*TALLA!TALLA!!TALLA!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU茒I 茦ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA 茦WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA茒EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU苼A TA KAI TSAYE KU TUNTU苼E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,****, 
***

ASOKORO,ABUJA, NIGERIA 


Matashiya ce kyakkyawa,a kallo 蓷aya mutum zai tabbatar wa kanshi ita 蓷in ruwa biyu ce(halfcast)sanye take da Black luxury abaya,ta yane kanta da mayafin rigar, fuskarta sanye da wani ba茩in spec da ya haska farar fuskarta,a hankali ta gama daidaita parking motarta 茩irar land cruiser,sai da ta 蓳ata kusan mintuna biyar tana kalle kallen compound 蓷in gidan nasu a yatsine sannan ta bu蓷e murfin motar ta fito,ri茩e da wayarta 茩irar iphone 15 pro max tana daddannawa 

"Barka da dawowa ranki ya da蓷e!"蓷aya daga cikin ma'aikatan gidan ya furta yana rissinawa gami da washe baki don neman shiga 

Fuska a yatsine ta kalle shi,a maimakon ta amsa masa sai ta ce"wanene wanda yake da alhakin share compound 蓷in nan?"

Har yana 茩ara rissinawa ya ce"Shu'aibu ne ranki ya da蓷e"

"Shu'aibu!then me ya hana shi share compound 蓷in yau?ko ya gaji da aikin shi ne?ko don kwana biyu an ga bana nan shiyasa kowa yake abinda ya ga dama?ga flowers can ba'a rage su ba,ga compound ba'a share ba, I can see motar Ammina ma 茩ura ta yi yawa babu wanki,what you guys do you mean by all this?"

茦ara 茩asa da kanshi ya yi yana mai nadamar yi mata magana da niyyar neman shiga, saboda kowa ya san yadda take son a girmamata,amma sai ya ce cikin kwantar da murya 

"A yi ha茩uri ranki ya da蓷e, in sha Allahu zan yi musu magana kuma zasu gyara"

"Better for you!hour 蓷aya na bayar kar na zo na samu wani abu kamar datti a compound 蓷in nan, otherwise mutum yayi ta aikinshi,ka tabbatar ka sanar da wa蓷anda abin ya shafa"ya sake rissinawa ya ce"an gama ranki ya da蓷e"bata sake magana ba ta wuce shi ta nufi cikin gidan tana 茩o茩arin aika kira da wayarta

Kai tsaye ta kutsa kai rantsatstsen parlourn gidan ba tare da tayi wani abu wai sallama ba, Mimi da ke zaune akan 蓷aya daga cikin luxury sofa dake parlourn ta taso da gudu ta rungume ta tana fa蓷in 

"Welcome welcome aunty MALIKA! I miss you so much"sai yanzu ta yi 蓷an murmushi tana zare spec 蓷in da ta rufe 茩wayar idanunta,茩wayar idanun ta bayyana

Blue eyes ne da ita exactly kamar na turawan kasar Estonia ko Finland,tana murmushi ta shafa kan yarinyar tana fa蓷in"Mimi I miss you too,Ina Ammi?"yarinyar ta yi 蓷an murmushi ta ce"Ammi ta je gidan momy Zarah,suna tattaunawa akan wasu kaya da za su fitar, aunty Malika dama the house is so boring,su aunty basa nan, Ammi ma haka,kenan kuma ba kya nan "wani murmushi Malika tayi ganin yadda Mimi take ta shagwa蓳ewa,itama dai da gaske ta yi kewar yarinyar,cikin kulawa ta sake rungumeta ta na fa蓷in"let me get my shower first,just give me thirty minutes,uhm?"murmushi Mimi ta yi ta 蓷an matsa baya tana fa蓷in "I'm waiting for you lovely aunty"Malika ta shafi kanta tana murmushi sannan ta wuce sashenta 

Wani luxury apartment ta nufa,tun daga staircase 蓷in har har zuwa tiles,fitilun sashen duka abin kallo ne, ballantana kuma tsadaddun sofa da suka mamaye parlourn,babu wata hayaniya sosai a parlourn,amma an narka masa ku蓷i sosai

A yatsine take bin ko'ina da kallo don tabbatar da an gyara ko'ina?ganin babu wata matsala,ko'ina a share yake, asalima 茩amshin insence sticks masu asalin tsada da 茩amshi ne yake tashi,ta yatsina fuska tana cire mayafin kanta,dogon jan gashinta ya bayyana,ya sauka har gadon bayanta,ta mi茩e kai tsaye izuwa tangamemen bedroom 蓷inta 

Ashe parlournta ba komai bane akan bedroom,hatta da gadonta 茩irar jado steel style gold bed an lullu蓳e shi da wani tsadadden zanin gado,hatta da best side lamp 蓷inta abar kallo ce,ba'a maganar closet 蓷inta da shoe rack 蓷inta da ke gefe,shi kanshi rack 蓷in abin kallo ne

Kan gado ta zubar da wayarta da mayafinta,kai tsaye ta fa蓷a toilet,ta samu a茩alla mintuna talatin kafin ta fito,sanye da bathrobe kanta na蓷e da madaidacin towel 

A cikin 拼an mintuna ta yi drying kanta ta shirya cikin wasu riga da wando masu tsada,ta 蓷aure dogon gashinta da wani 蓷an 茩aramin ribbon ta sake shi baya ta sauko izuwa parlourn Ammi inda Mimi ke zaune har yanzu tana karatu

A stairs 蓷in 茩arshe ta yi tsaye tana kallon wa蓷anda suka shigo fuskarta babu yabo babu fallasa,拼an mata ne su biyu,sun yi kyau sosai cikin English wears da suka yi musu matu茩ar kyau,kusan a tare suka furta

"Maleeka!You are welcome!!!"

茒an yatsina fuska ta yi tana shafa brown girarta kafin tayi magana kamar an tilasta ta

"You are welcome too"daga haka ta 茩arasa sauka daga kan stairs 蓷in ta nufi dinning area inda aka shirya mata abincinta ba tare da ta sake kallonsu ba

Kallon juna suka yi,蓷aya daga cikinsu ta nufi inda Maleeka take ta zauna tana cigaba da danna wayarta,ta fara serving 蓷inta tana fa蓷in "kin san ba iya serving kanki kika yi ba,amma kamar wata yarinya sai jin zauna kina wani nu茩u-nu茩u"ko kallonta Maleeka bata yi ba ta cigaba da abinda take yi, budurwar bata damu ba ta cigaba da serving 蓷inta 

Tana gamawa ta turawa Maleeka plate 蓷in,ciki-ciki ta ce"thanks!"ta fara cin abincinta,budurwar ma ta ja plate ta yi serving kanta tana 蓷an murmushi ta ce"babu yadda ban yi mu shiga restores ba amma uwar taurin kan nan ta 茩i yarda,gashi na dawo a yunwace sosai"ita dai Maleeka ko kallonta bata sake yi ba

Shiru ya 蓷an ratsa tsakaninsu, ba'a jin 茩arar komai sai na plates da cokula,kafin Maleeka ta yi breaking silence 蓷in ta ce 

"Maleeka when are we leaving this annoying country ne?"Maleeka ta 蓷aga kai fuska a 蓷an 蓷aure ta kalle ta,a hankali tace"for where?"

"Like US haka,ko Cuba,ko dai Canada,ko Luxemburg ko......"da sauri ta gintse bakinta tana kallon Maleeka da take aika mata da wani mugun kallo,a nutse kuma cikin isa ta ce"tell me the truth LATEEFA!are you here to talk about someone?"

Da sauri Lateefa ta girgiza kai tana fa蓷in"not at all,ni ba haka nake nufi ba, I'm sorry if I offended you in anyway "Maleeka bata kula ta ba ta cigaba da cin abincinta a nutse,itama Lateefa cigaba da cin abincinta ta yi tana satar kallonta 

瞥an seconds Lateefa ta kasa jurewa ta kalli Maleeka ta ce"but I don't understand the reason da za ki ce bakya son zancen......"

"Lateefa!get out of my side!!leave this place please!!!"a razane Lateefa take kallon Maleeka da mamakin haukan da takeyi mata, Maleeka ta mi茩e tsaye jikinta yana tsuma,ta nunawa Lateefa hanya ta ce"leave this place, don't let me repeat myself!!!"babu musu Lateefa ta mi茩e jikinta na rawa ta wuce 蓷akin 蓷aya matashiyar da already ta da蓷e da shigewa ma, Maleeka ta raka ta da dogon tsaki kafin ta cigaba da cin abincinta a nutse tana danna wayarta 


SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 




Kwanan Major Ahmad biyu a gida ya koma bakin aikinshi, ya ji matu茩ar da蓷in ganin yaran nashi basu chanja mata ba,itama Ammi da ta fusata yanzu ta sauko tun zuwan Alhaji Nasir 

Yau kwana biyu da tafiyar Abba, Aneesa tana kwance akan gadonta tana chatting da 茩awayenta na makaranta game da WAEC 蓷in da ta tunkaro su nan da 蓷an lokaci,shirye shirye suke yi ka'in da na'in don ganin sun rubuta jarrabawarsu ba tare da wata matsala ba

Wayar Ammi da ke gefenta ce ta fara 茩ara,ta 蓷auki wayar ta fice daga 蓷akin don kai wa Ammi da ke kitchen tana girki 

Mi茩awa Ammi wayar ta yi ta zauna tana 茩o茩arin cigaba da ha蓷a miyar da Ammin takeyi,Ammi kuma ta 蓷aga wayar tana sallama cikin sanyin muryarta

Daga 蓷aya 蓳angaren aka amsa cikin karsashi"waalaykis Salam maman Aneesa mun wuni lafiya?ya yaran kuma?

Ammi ta 蓷an ja numfashi ta ce"lafiya 茩alau,yaran alhamdulillahi kowa lafiya,sai dai ban gane mai magana ba"

Matar ya 蓷an ja numfashi,sannan ta ce "baki sanni ba ma maman Aneesa,ni matar abokin mijinki ne,na kira ki ne kawai don batun abokiyar zamanki"gaban Ammi ya buga,amma ta dake ta ce"wani abun ya faru kuma?"

"A'a babu abinda ya garu,kawai dai zan baki shawara ne da kula da abokiyar zamanki,ko na ce kiyi hankali da ita,don babu alamun mutuniyar kirki ce "

A hankali Ammi ta koma ta zauna akan kujerar da ta tashi, Aneesa dai tana jin su bata saka musu baki ba,matar ta cigaba da fa蓷in 

"Mutuniyar kawai ce,na ji an ce gidansu maneman malamai ne,sannan idan suka shiga gida sai sun raba mutum da matarshi,ko dai su fitar da ita daga gidan ko su mayar da ita hoto,don haka ya kamata ki zage dantse,abin babu da蓷i ke da gidanki wata ta mallake miki gida"banda inna lillahi wa inna ilayhi rajiun babu abinda Ammi take maimaitawa a ranta,da 茩yar ta iya fa蓷in"ta Allah ba tata ba,in sha Allahu lafiya 茩alau zamu rabu da mijina "

"To Allah ya sa,don an ce idan suka auri mutum akwai su da saka mutum yayi ta musu hidima,amma iyalinshi babu abinda suke gani sai wahala,idan ma ba'a raba su ba

Cikin karayar zuciya Ammi ta ce"gaskiya ne,sai dai....."bata samu zarafin 茩arasawa ba ta ji Aneesa ta kar蓳e wayar,cikin azama ta kashe kiran ta saka wayar a Flight mode fuskarta a ha蓷e 

Cikin fa蓷a Ammi ta ce"ba Ni wayata!wanne kalar wula茩anci ne zai sa ina waya za ki amshe min waya?ko sai salon raini ne kika samo kika zo za ki gwada min?"

Ran Aneesa a 蓳ace ta ce"Ammi kema wani lokacin duk da ke wallahi,ya mutum zai kira ki ya yi ta tsara miki magana akan abbanmu amma ki tsaya kina saurarenshi?har tana gaya miki wai ki nemi taimakon malamai amma kika cigaba da biye mata?Ammi kar wata da baki sani ba ta yi nasara akan ki da iymaninki,茩ila ma ha蓷a baki suka yi ta zo tana yi Miki Wannan maganar kina saurarenta,don....."

"Ba ni wayata ko na mare ki Aneesa!ina ruwanki da maganata da har kike saka min baki?dalla fita ki bani waje"babu musu Aneesa ta mi茩a mata wayar ta fice daga kitchen 蓷in ranta a 蓷an 蓳ace,tana jin Ammin tata tana cigaba da fa蓷a amma bata ce komai ba ta koma 蓷akinta ta cigaba da kwanciya zuciyarta a 蓳ace



QUEBEC CITY, MONTREAL,CANADA



茦aton luxury room ne wanda ya 茩unshi abubuwan more rayuwa dabam dabam,kama daga kan gadon zuwa cupboard da sauran kayan more rayuwa ja 蓷an adam,蓷akin ya yi shiru tamkar babu wata halitta mai rai a cikin 蓷akin

Sai dai akan 茩aton luxury bed da ke 蓷akin wani matashi ne a kwance ya lullu蓳a da duvet yana ta shan baccinshi,蓷akin ya yi asalin shiru baka jin 茩arar komai sai na AC 

Daidai lokacin da tsadadden agogon 蓷akin yake buga 茩arfe takwas da mintuna sha biyar daidai na safe wayarshi 茩irar latest Samsung ta 蓷auki tsuwwa,a hankali ya bu蓷e idanunshi wa蓷anda ba su da maraba da na Maleeka,sai dai a fuska ba sa kama,ta fishi hasken fata,sannan kuma kamannin fuskarsu ba 蓷aya bane,sai dai shima kyakkyawa ne sosai

A hankali ya zauna a kan gadon yana jan tsaki,yana kallon wayar ta katse,sannan ya koma ya kwanta 

Yana kwanciya wayar ta sake 蓷aukan tsuwwa,蓷an gajeren tsaki ya sake ja sannan ya janyo wayar a fusace ya 蓷aga, ba tare da ya damu da kallon mai kiran ba ya fara sura masifa 

"Hello Rachel!how many times do you want me to warn you about calling me in this early morning?are you out of your sense? or do I have something to do with your fucking call?"

Daga can 蓳angaren Rachel kamar zata yi kuka take fa蓷in"I'm sorry love! I know I can't do without you,you are everything to me,I can't sleep last night just because you are angry with me, please baby!"

Tsaki mai 茩arfi ya ja,a gadarance ya ce"then, don't call me again until I call you back,for now I'm doing something important,I bet for now you know I'm more than important to you,I can live without you,and you can't do without me,so respect yourself!"bai jira amsarta ba ya kashe wayarshi ya yi jifa da ita ya mi茩e tsaye yana mi茩a 

Giant guy ne sosai,fari ne amma ba tas ba,shima Blue eyes ne dashi,amma gashinshi ba茩i ne wanda ya sha gyara sosai,daga shi sai shotneaker da singlet,kai tsaye ya nufi tangamemen ban蓷akin nashi da ke cikin 蓷akin

Ya kai a 茩alla mintuna talatin kafin ya fito sanye da bathrobe,a nutse ya 茩arasa gaban dressing mirror ya fara gyara 茩awatacciyar sumarshi,yana cikin shafa mai wayarshi ta yi 茩ara

Tsaki ya ja da 茩arfi,ya janyo wayar,ganin mai kiran bai yi tunani biyu ba ya yi rejecting ya jefar da wayar sannan ya cigaba da shirinshi a nutse ba tare da ya sake bi ta kan wayar da ta 蓷auki sabon ring ba

Tsaf ya shirya cikin riga hoodie baby blue riga da wando,sai p-cap da ya 蓷orawa kanshi,ya sanya wani ba茩in Boot,ya saka ba茩in glasses,ya 蓷auki key da wayar shi ya fito daga cikin gidan

Yana shirin fita aka 蓷age gate 蓷in,cikin takaici yake kallon motar da take danno kai cikin gidan, lokaci guda ya sake 蓷aure fuska tamau yana bin motar da mugun kallo,har zuwa lokacin da mai motar ya gama daidaita parking ya fito ya nufo India yake yana 蓷an murmushin ganin yadda yake ha蓷e rai 

"Ya dai babban likita!duk wannan fushin ganin nawa ne?"ya fa蓷a yana murmushi,har double dimple 蓷inshi suna bayyana a kumatunshi 

"Saif what do you want please?why kake son shiga rayuwata ne? You know that I hate disturbing ko?"

"Then so?"Saif ya fa蓷a yana masa kallon raini,"idan ma wata macen ka kawo kake shakkar na gani that's your own cup of tea,da har nake kiranka kake 茩in 蓷aga min kira, ASHRAF!do whatever you want,but I must be by your side "yana gama magana ya tsallake Ashraf da ya bishi da kallon takaici ya shige gidan,ya yi amfani da key 蓷in hannunshi, Ashraf kam bai samu zarafin magana ba,ya bu蓷e tsadaddiyar motarshi ya shige ya tayar ya bar gidan


#Nusy_bee

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.