Free chapter · Read without an account

Chapter 31

by Narrnarhh Bukar · BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

031

Cike da tsantsar takaici da kuma mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskarta ta ce

''Mara zuciya bai yi a rayuwa ba,shisshigi da katsadanla sun zama tufafin da kike yawo da su. Ni yanzu ban da lokacin ɓata da irinki,domin na gaba ya yi gaba. Mtsss!"

Murmushi maman Jawaheer ta yi sannan ta ce

''Kya dai ji da shi,an ji maza an saduda''

Banza Sahura ta yi da ita,gyara zama ta' yi ta ci gaba da kallonta. Juyawa maman Jawaheer ta yi kiran Hamida ta nuna mata ɗakinsu a shigo da gadajen. Zuciyar Hamida cike da tsoron Sahura ta shigo falon,kallo ɗaya Sahura ta yi mata ta watsar ta ci gaba da kallonta. Ɗakinsu ta fara kaita sannan ta nuna mata ɗakinsu Yasir. Fita maman Jawaheer ta kuma yi,katifun suka fara shigawa da su sai daga baya suka shigo da gadajen. Suka saka a kowanni ɗaki kasancewar ɗakin da girma sosai,ƙanwarta ta shimfiɗa zannuwan gadon masu kyau da ɗaukar hankali a gadajen. Bayan sun kammala suka fito falon sai maman Jawaheer ta dubi Sahura duk da ta san ba amsa mata za ta yi ba ta ce

''Ga gadajen su Hamida mun kawo,ba don yaranki aka kawo ba,idan kina da zuciya a jiki ki hana yaranki hawa gadajen,idan kuma zuciyar karnuka gareki bismillah'' tana gama faɗin haka ta ja hannun Hamida suka bar flat ɗin. Sahura ta daɗe tana bin ƙofar da suka bi da kallo. Lallai ma matar nan ta raina mata hankali,ta zo har cikin gidanta tana gaggasa mata magana saboda ta ga yanzu bata da iko da su,idan bata yi wasa ba za ta saisaita tunanin. Cije laɓɓanta na ƙasa ta yi da ƙarfi tana yin ƙwafa sannan ta ci gaba da kallon duk da ba fahimtar komai take ba.

Hamida da Yasir ba su dawo gidan ba sai a washegari da yamma bayan an tashi daga islamiyya. Sai da suka fara biyawa gidan maman Jawaheer suka canza kaya zuwa na gida sannan suka rataya jakar makarantar boko suka taho. Ƙirjin kowannansu na bugawa suka shiga flat ɗin. Lokacin Dauda Imamu na zaune a falon yana duba wasu takardun islamiyya. Gefe guda Sahura da yaranta suna ɗan taɓa hira kasancewar babu wutar lantarki. Da sallama a bisa laɓɓansu suka shigo falon, Dauda Imamu ya amsa cike da kulawa. Su Hamid kuma suka bi su da kallo kamar sun ga TV,Sahura ko kallon inda suke bata yi ba. Kai tsaye suka wuce ɗaki suka ajiye jakar makarantarsu sannan suka dawo falon,kusa da mahaifinsu suka zauna, lokaci bayan lokaci yana tambayarsu a kan karatunsu,cike da natsuwa suke ba shi amsa. Lokacin sallar magrib ya yi Hamid da Yasir suka bi Dauda Imamu masallaci. Hamida kuma ta wuce ɗakinsu ta ɗauro alwala a bayi ta ciro hijabinta a jaka ta kabbarta sallah. Bayan ta idar ta dawo falon,su Aunty Saudah babu wanda ya yi sallah a cikinsu,Sahura kam ba a maganarta ko karatun sallar bata iya balle ta koyama yaran. Gwara-gwaransu Hamid kasancewar yana bin Dauda Imamu masallaci. Lokacin Sahura ta kammala abinci,ta kira kowanne ya ɗauka,Hamida har ta cire rai ta ji ta kira sunanta. Da sauri ta je ta ɗauko ta dawo  falon. Su Yasir ma sun dawo, Sahura ta ce su je su ɗauko abincinsu. Yasir karan kansa ya kwankwaɗi madarar mamaki. Sun natsu suna cin abinci aka kawo wutar nepa. Da sauri  Hamid ya kunna TV, dukkaninsu suka mayar da hankulansu ga TVn har suka kammala cin abincin. Suna tsaka da kallo aka ƙwanƙwasa ƙofarsu. Sahura ta dubi Yasir ta ce

''Yasir ɗan je ka buɗe ƙofar ka ga wane ne'' ta yi maganar cike da sanyin murya. Ba komai ya sabbaba mata yin sanyin nan sai don bata manta tsauraran sharuɗɗan da madam Ngozi ta gindaya mata ba a kansu Yasir.

Yasir na buɗe ƙofa ya yi tozali da su Jalil cikin kyakkyawar shiga sai ƙamshi suke,hanya ya matsa musu suka shigo,ko kallon Sahura Jalil  bai yi ba balle kalmar gaisuwa ta ratsa a tsakaninsu. Ita da yaranta idanunsu kyar a kansu,ga ƙamshin turarensu da ya cika ɗakin. Turaren officer Kabir suka fesa shi da Muhsin. Baƙar leda ya miƙa ma Yasir yana faɗin

''Ga shi in ji  Dadinmu(Mahaifin Muhsin) ya ce ku ci ku kaɗai,sauri muke ana jiranmu a mota'' yana miƙa masa suka bar falon Jalil ya turo musu ƙofar. Ƙiƙam Yasir ya tsaya yana kallon ƙatuwar baƙar ledar hannunsa.

''Yarona Yasir me aka kawo muku haka na ji yana tashin ƙamshi'' ta yi maganar tana washe baki kamar gonar audiga,ta tabbata kayan daɗi ne aka kawo musu,eh lallai dole ta sauko ita da yaranta su ma su kurɓi romon demokradiyyar officer Kabir. A sanyaye Yasir ya ce

'' Ban san me aka kawo ba''

''Zo mu gani na tayaka dubawa''

Babu musu ya kai mata,da sauri ta amsa ta saka hannu ta ciro lemon 5alive guda biyu masu raɓa,sai takarda duƙunƙune duk jikinta maiƙo. Nan da nan miyon Sahura ya tsinke,da sauri ta cire takardar ta ɗora a saman cinyarta. Zumbur Nu'aymah ta mike daga zaune tana faɗin

''Mama zan ci''

''Kar ki damu yayyanki ba su da rowa. Za ku sammana ladar ganin ido ko?"

Da sauri Yasir da Hamida suka jinjina mata kai. Takardar ta buɗe, lokaci guda ta ware manyan idanunta ganin gasasshen nama da uban yawa ya ji kayan lambu ga ƙullin yaji a gefe.

''Hamid ɗauko tire''

Da gudu Hamid ya nufi kicin ya ɗauko tire ya miƙa mata,gabaɗaya ta juye naman, zuwa lokacin Nu'aymah ta ci kusan yanka biyar. Raba naman ta yi gida uku,ta kwashe ma su Yasir kashi ɗaya a takardar sai ta sake haɗa sauran kashin ta rarraba musu. Ta aiki Aunty Saudah kicin da ɗauko kofuffuka,cikin hanzari ta nufi kicin ta ɗauko guda bakwai. Buɗe gorukan 5alive ɗin ta yi ta zuba ma kowa,daidai ta zuba 5alive ɗin a kofukan sai ka ce don su aka kawo. Kowanne ya ɗauka suka ci gaba da kallo.

Tun daga ranar Sahura ta ajiye makaman yaƙinta a gefe,ko ɗaure fuskar da take musu ta daina,don ta ga alama za ta kwashi daɗi ita da yaranta ta hanyarsu,sannan hakan ba zai tabbatu ba sai idan ta ja su a jiki. lokaci bayan lokaci Jalil da Muhsin suna kawo ma su Yasir ice cream ko nama idan sun fita outing. Daidai gwargwado mahaifin Muhsin na ƙokari a kansu Yasir haka ma maman Jawaheer da mijinta. Da safe idan su Yasir suka ta fi boko ba su suke dawowa gidan sai yamma,a gidan maman Jawaheer suke cin abinci rana,kayan islamiyyarsu ma yana wurinta. Da yake yanzu ta ajiye aikin da take a wajen barikin sai ta nemi koyarwa da certificate ɗinta na diploma a primary school ɗin barikin. Cikin ikon Allah ta samu koyarwa a primary 4. Dauda Imamu kullum cikin yi musu godiya yake idan sun haɗu. Kwanci tashi babu wuya wurin Ubangiji lokacin kara ma su Officer Kabir matsayi ya yi. Officer Kabir aka ƙara masa matsayi zuwa Flying Lieutenant. A gefe guda mijin maman Jawaheer shi ma an ƙara masa matsayi zuwa Warrant officer da taimakon Madam Ngozi.

Bayan ƙarin matsayin wanda lokacin azumi bai fi kwana goma ba Mahaifin Muhsin ya shirya musu tafiya zuwa Zamfara wurin Mairi kasancewar su Yasir sun samu hutun boko,yana so su yi hutunsu a can zuwa bayan sallah su dawo. A ɓangaren Sahura a ranar wata Laraba babu zato babu tsammani Madam Ngozi ta yi mata zuwan bazata,ta yi matuƙar tozara da ita,'yan wasu tambayoyi ta yi mata da kuma sake jaddada mata sharuɗɗan sannan ta bar gidan...✍️

^^^^^^^^^^^^^

Mairi tun tana ƙirga kwanaki har ta koma ƙirga satitta zuwa watanni amma shiru bata ga keyar su Yasir da sojan ba. Hankalinta ya ƙara tashi,sau biyu tana zuwa Mada wurin Kawu a kan maganar,da yake bayan dawowar Kawu Rabi'u Mamman ya sanar masa komai sai ya ta fi a kan a gwara su gwadasu su gani. Gwiwa a saɓule take dawowa Gusau a duk zuwanta,bata san me ya sa sun kasa fahimtarta,sun kasa gane halin da take ciki,kullum cikin damuwa take duk da ta ɗan rage ba kamar da ba. Jamila ma tana goyan bayan 'yar'uwarta. Mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo,ita take jin zafin rashinsu a kusa da ita. Takanas ta kano ta je Mada ta nemi izini wurin mijin Jamila a kan za su Kaduna ɗauko yaranta kuma kwana daya ne rak za su yi. Fatan Allah ya tsare hanya ya yi musu,ya kuma kara musu kuɗin mota. Da rana suka dawo Gusau, duk abin da suke buƙata sun saka shi cikin jaka. Sun zauna suna hutawa HAFIZA na gefe tana zane suka tsinkayi muryar su Jalil kamar a mafarki,babu shiri HAFIZA ta saki pencil ɗin ta ruga da guda waje tana kiransu. A sukwane su Mairi suka fito wajen,mamaki kwance a fuskarsu,tsakar gidansu ta cika da baƙi har da waɗanda ba su san fuskokinsu ba. Momy ta yaranta,haka ma maman Jawaheer ta zo da yaranta. Da gudu su Jalil suka rungume Mairi,take ta rushe da kukan farinciki, sai ɗago su take tana sake duban su don tabbatar da ba mafarki take yi ba. Sake rungumesu ta yi tsam a jikinta kamar tana tsoron wani zai sacesu. Jamila ta yi musu iso zuwa falon. Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa sannan suka shiga gaisawa. Momy ta dubi Mairi ta ce

''Ko ba a sanar mini ba wannan ita ce mahaifiyar hamma Jalil,wannan kuma ƙanwarta''

Murmushi Mairi da Jamila suka yi suna jinjina mata kai. Maman Jawaheer ce ta ce

''Maman Raihan kin samu wuri kin manta ta Dadyn Muhsin''

Waro ido momy ta yi tana faɗin

''Innalillahi! Wallahi shaf na manta. Daman tare da mijina muka zo''

''Allah sarki! Jalil ku je ku shigo da shi'' cewar Mairi tana mikewa ta je ta saka hijabi haka ma Jamila. A Tare suka shigo bakinsa ɗauke da sallama. A one sitter ya zauna Jamila ta kawo mishi ruwa. Bayan sun gaisa sai shiru ya ratsa ɗakin. Can officer Kabir ya yi gyaran muryar,cike da natsuwa ya fara magana.

''To Alhamdulillah dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya ba mu ikon zuwa cikin ƙoshin lafiya. Sunana Kabir wannan ita ce mata Karima sai Maryam wadda mijin ya zama aminina sanadin yaraku. Kwanakin baya ɗan uwanku ya zo bariki ɗaukar su Hamida, lokacin ina tare da Imam. To dama Jalil ya dawo hannuna tun lokacin da na fahimci matar Imam tana muzguna masa,da yake ɗana Muhsin abokinsa ne kuma ajinsu ɗaya a boko da islamiyya. Tun kafin na san Jalil Muhsin yake faɗa mini wahalar da yake sha shi da 'yan'uwansa a hannun matar Imam. Ganin haka ya sa na roƙi Imam ya bar mini Jalil hannuna tun da yarona abokinsa ne,ni kuma zan kula da shi kamar ɗan cikina kuma Alhamdulillah ya danƙa mini amanarsa. Ina tunanin yadda zan kawo ma su Yasir ɗauki a kan izayar da take musu sai Ubangiji ya yi ikonshi a kanta,domin Ogata ta wurin aiki Madam Ngozi ta yi maganinta,wanda yanzu na san ta shiga taitayinta sannan ta bayar da gudummawa mai tsoka a lokacin da Hamida take gadon asibiti. Maryam ma ta yi matuƙar ƙoƙari a kansu wanda yanzu haka cikin ƙoƙarin take. Na so zuwa kwanakin baya kamar yadda na sanar ma ɗan uwanku amma sai na canja shawara a kan idan an ba su hutun boko sai su zo su yi hutunsu wurin mahaifiyarsu m,zuwa bayan sallah sai su koma. Ban san ra'ayinki a kan yaranki ba amma muna nemanmn wannan alfarmar,za mu yi iya ƙoƙarinmu a kansu sannan duk lokacin da suka samu hutu za su dinga zuwa har da yarana in shaa Allah. Amma ba za mu taruka miki ba, duk abin da kika ce ba za mu yi jayayya a kai ba''

Hawaye masu ɗumi Mairi ta share tana zuƙar majina,bata taɓa tunanin akwai irin waɗannan mutanen masu farar zuciya a doron duniya. A da ta fi son su dawo hannunta,amma kuma mutanen nan sun karyar mata da zuciya,sun taimaki yaranta a lokacin da suke tsananin neman taimako,ita kuwa wa ce ita ta watsa musu ƙasa a ido,tun daga Kaduna suka yi tattaki ƙwansu da kwarkwata zuwa  wurinta. Bata taɓa riskar kanta a cikin farinciki kamar na yau ba,tabbas Ubangiji ya amsa addu'arta ta inda bata yi tsammani,ya kuma shigo da waɗannan mutanen don su taimaka mata. Sake goge hawayen ta yi cikin muryar kuka ta fara magana

''Ban san da me zan saka muku da irin wannan taimakon da kuka ma yarana ba. Kun yi mini karamci,kun kawo ma yarana ɗauki a lokacin da suke tsananin buƙatar hakan,ta ya ni Maryam zan  butulce muku. Tabbas Allah ne ya turoku cikin rayuwata! Na gode! Na gode! Allah ya saka muku da alkhairi ya albarkaci zuri'arku. Na aminta da zamansu Jalil a wurinku,tun sa ga HAFIZA wurina. Allah ya tayaku riƙo. Ina kara godiya!"

''Mun gode sosai da taimakon da kuka yi ma yaranmu. Wallahi yanzu muka gama shiri zuwa gobe mu je Kaduna ɗauko su. Zuwanku ya sacar mana da gwiwa. Tun da duk hutu za su dinga zuwa hakan ma ya yi. Daga kallon jikinsu zuwa tufafinsu na tabbatar da suna samun kyakkyawar kulawa. Muna kara godiya'' cewar Jamila.

Wani irin sanyi Officer Kabir ya ji a ransa,tun a hanya yake tunanin ko mahafiyar Jalil za ta aminta ko A'a,sun yi mugun sabo da shi musamman Raihan. Idan taƙi aminta tabbas ya san Raihan za ta shiga cikin wani hali. Cike da jin daɗi officer Kabir ya ce

''Mu ke da godiya. In shaa Allah za mu riƙe amanar da hannu bibbiyu.''

''Muna godiya sosai takwarata'' cewar maman Jawaheer.

''Idan kika ce ba za ki bar mana Jalil ba ai sai mu haɗo da Raihan ki haɗasu ki riƙe. Don bata da yaya sai Hamma Jalil'' cewar momy tana dariya. Dariyar su ma suka yi. Mairi kuma da ɗan murmusa. Sallama officer Kabir ya yi musu sai momy ta bi bayan shi. Jamila ta fita ɗaura girki. Mairi da maman Jawaheer suka fara hirar yaushe gamo,momy ta dawo suka ci gaba da hirar,tsarabar da suka zo da ita ta miƙa mata. Sai bata labarin iskancin da Sahura take,da kuma wahalar da sha hannun Madam Ngozi. Babu abin da Mairi take sai murmushi zuciyarta fes,yanzu bata da wata damuwa sai ta Dauda Imamu. Shi ma tana rokon Allah ya dawo mata da shi cikin hayyacinsa. Bayan da ɗora girkin ta dawo falon aka ci gaba da hirar tare da ita.

A ɓangare guda yaran sun haɗe suna surutu,manyan suna gefe  yayin da ƙananun suke wuri ɗaya. Hamida da Jawaheer suna hirar boko. Raihan da take sa'ar HAFIZA ta zauna kusa da iya,sai dai kwata-kwata bata samu fuskar yi mata magana ba,don HAFIZA akwai tsare gida idan bata so magana ba,sai da Jalil ya yi mata magana sannan ta ɗan sake jiki da ita har suka fara hirar karatu,labari da ya yi daɗi zai HAFIZA ta fi Raihan zaƙewa,har da shiga uwarɗaka tana ɗauko mata result ɗinta na wannan karon tare da drawing books ɗinta. Mahaifin Muhsin ya nemi wani hotel ya kama ɗaki na kwana ɗaya tun da gobe za su koma,daga hotel ɗin ya shiga zaga garin.Cikin ƙanƙanin lokaci Mairi ta yi sabo da su momy,haka ma Jamila,sallah ce take tashin haka yaran. Bayan sallar Isha'i officer Kabir ya dawo gidan,a tsakar gida aka shimfiɗa masa tabarma momy ta fito masa da abinci,ƙatuwar leda ya miƙa mata ta shiga da shi ciki ta mika ma Mairi sannan ta dawo wajen. Tana tayashi hira har ya kammala cin abinci suka ɗan taɓa hirar sannan ya yi sallama da su,Mairi ta yi mishi godiya da abin arziƙi momy ta rakashi ya wuce hotel. Bayan ta dawo falon Jamila ta kakkasa tsiren da officer Kabir ya kawo a 'yan kwanuka ta miƙama kowa,suna ci suna hira. Sai wurin goma na dare suka kwanta. Washegari da safe bayan sun karya officer Kabir ya zo suka tafi inda aka bar Yasir,Jalil,Hamida,Raihan da Muhsin. Yaran maman Jawaheer gobe za su Kano hutu shi ya sa ba za su tsaya hutu nan ba. Cikin daɗin rai suka yi sallama tare da addu'ar Allah ya tsare hanya. Washegari Jamila ta koma gida. Walwalar HAFIZA ta dawo sakamakon zuwansu Jalil,sun yi azumi cikin farinciki da annashuwa tare da shagulgulan sallah da ziyarar 'yan'uwa a Mada. A ɓangaren Sahura bata san da tafiyansu Yasir ba,ko da ta gano sun je hutu Zamafara bata damu,ita dai fata take karsu daɗe saboda kayan daɗin da take ci ita da yaran ta dalilinsu. Bayan an dawo hutu abokin officer Kabir ya je Gusau ya ɗaukosu Yasir ta haɗa su da tsaraba. 

Rayuwa ta ci gaba da tafiya inda duk hutu Yaran suke zuwa Gusau tare da tsaraba niƙi-niƙi ciki har da tufafi, zuwa yanzu hankalin Mairi a kwance yake,bata da damuwar komai sai na rashin tozali da madubin rayuwarta, shi ma tana fatan zai dawo gareta ko ba daɗe ko ba jima. Har Kaduna Sadiƙu ya zo wurin Dauda Imamu,ya sanar masa da ci gaban da kullum suke samu a shagon,Dauda Imamu ya yi farinciki sosai da yadda ya riƙe amanar shagon da iyalansa,bayan sun ɗan zanta daga bisani ya dawo Gusau a ranar.A ɓangaren Sahura ta mayar da hankali wurin tsuma 'yan matan,bata damu da karatunsu ba musamman islamiyya, ta dora burin duniya a kan su idan sun girma. Tun ana ƙirga watanni suka rikiɗa zuwa shekara,daga shekara ɗaya ya linku zuwa shekaru masu ɗumbin yawa. Zuwa yanzu HAFIZA na da shekara sha uku a duniya,kuma ta haddace Alqur'ani tana maimaici a karo na uku,a boko tana Jss2. Ta taso cikin kyakkyawar kulawa,ga ta natsuwa da rashin son magana amma kuma bata ɗaukar raina,sam bata shiga sabgar kowa haka bata son a shiga sabgar. Tafi son ta yi rayuwarta ita kaɗai,a ɓangaren zanenta kullum gaba-gaba yake,ta ƙara ƙwarewa ba kamar lokacin da take yarinya ba. A waɗannan shekarun masu tarin yawa sau biyar Dauda Imamu ya yi kundumbalar zuwa Gusau,ko kwana bai yi yake dawowa saboda kamar ana ƙara masa tsanar Mairin,idan ya je HAFIZA yake ja a jiki su yi hira sannan ya bata kuɗi ya dawo Kaduna,magana bata taɓa haɗa su a waɗannan zuwan ba balle kuma kwanciyar aure. Idan ya koma Mairi ta shige uwar ɗaki ta ci kukanta ta more. Da Sahura ta gane yana zuwa Zamfara sai ta masa mummunan kashedi,tun daga lokacin bai ƙara zuwa ba wanda kusan shekara huɗu kenan da faruwar hakan. A ɓangaren Jamila har yanzu Allah bai bata haihuwa ba,abin mamakin duk asibitin da suka je magana ɗaya ce lafiyarta ƙalau sannan ƙwayoyin haihuwarta suna nan lafiyaba,lokaci ne dai Allah bai kawo ba,tun tana damuwar har ta fawwala ma Allah komai.

A ɓangaren su Yasir sun girma sosai,don Yasir da Jalil sun fara gemu,Hamida kuma maƙerin budurci ya fara ƙerata. Yasir yana a Kaduna state University level 4 yana karantar Civil Engineering shekararsa 23, Jalil yana da shekara 21 yanzu,yana son applying NDA shi da Muhsin next year,suna zuwa computer training a wajen barikin shi da Muhsin. Hamida kuma tana cikin shekara ta 17 tana SS3 ita da Amina. A waɗannan shekarun Officer Kabir ya samu ƙarin matsayi zuwa Wing commander,haka ma mijin maman Jawaheer ya samu ƙarin matsayi zuwa Air Warrant officer. Madam Ngozi yanzu tana matsayi mai girma wato Air Commodore,amma saura shekara biyar ta yi retire,duk da bata cika zuwa barikin Kaduna ba,ta wakilta wani daga cikin sojoji suna ziyartar Sahura lokacin zuwa lokaci.

A ɓangaren Sahura kuwa ta ƙara zama cikakkiyar uwa,inda yanzu Hamid dinta yake cikin shekara da 19 ya kammala secondary amma yaƙi shiga babbar makaranta,bai da aiki sai biyema yaran yare marasa jin magana,Dauda Imamu yana jin zafin hakan a ransa amma babu yadda ya iya, furfura ta fara ƙawata gashinsa sakamakon ɗawainiyar iyali. Aunty Saudah na cikin shekara ta 18 ita ma ta kammala secondary,ta zama budurwa son kowa ƙin wanda ya rasa,domin Sahura bata wasa da gyaran ciki da wajensu. Amina na cikin shekara ta 17 ajinsu ɗaya da Hamida,Halima kuma tana cikin shekara ta 15 tana SS 1, Nu'aymah kuma tana a shekara ta 13 ,JS 2 take. Autarsu Maryam mai shekara ta goma tana a primary 4. A cikin yaran Sahura Nu'aymah ce uwar rashin jinsu,ga shi Allah ya ɗarsa ma Sahura ƙaunarta fiye da sauran yaran, tana da mugum kwaɗayi da ɗanbanzan roƙo. Mazan ajinsu har sun santa a kan roƙo. Ta fi duka yaran ɗakin kyau shi ya sa Sahura take alfahari da ita. Ƙawancen Sahura da maman 'yar gayu yana nan daram hasalima ƙara aminta da juna suka yi,'ya'yan maman 'yar gayu biyu suna Adamawa wurin iyayenta,ƙaramar ce take hannunta wacce take sa'ar Nu'aymah.

Yanzu da su Yasir suka girma Sahura ta ƙara jansu a jiki,kayan Hamida tare da su Amina ake kashesu,haka idan Jalil ya kawo musu kayan ƙwalam tare suke cinyewa,wani lokacin idan Sahura na jin mugunta sai ta ɗan sammata kaɗan ta cinye sauran,da yake Yasir bai cika zama ba sai dai idan bai da lectures. Da Jalil ya gano abin da suke,rana ɗaya ya goge mata hadda don bai raga mata ko da farcen susa ne,Hamid ya ta so zai buge shi Jalil ya mishi dukan tsiya,Jalil ƙarƙƙarfa ne sosai ga tsawo sannan da 'yar ƙiba. Tun daga ranar Sahura ta ƙara tsanar Jalil wanda basa ga maciji,shi kuma tuno da irin azabar da suka sha hannunta wani lokacin yake ƙin rage mata.

^^^^^^^^^^^^

BAYAN SHEKARU MASU TARIN YAWA

Aunty Saudah ta samu wani Alhaji mai kuɗi sosai a wajen barikin ana kiransa da Alhaji Shu'aibu Shanawa,yana da gidaje da kantuna. Sosai yake kashe ma Aunty Saudah kuɗi kamar ɓarnar iska. Har babbar waya srceen touch ya siyan mata. Shekararsu biyu kenan da haɗuwa. Jiya da ya jo yake sanar mata yana son ya turo iyayensa a yi maganar aure. Bayan ya tafi Aunty Saudah ta sanar ma mamanta. Washegari Dauda Imamu na zaune,Jalil na gefe da wayarsa yana chatting Sahura ta dubi Dauda Imamu ta ce

''Ni ba na manta ba. Aunty Saudah jiya take sanar mini Alhaji Shu'aibu shanawa yana son ya turo iyayensa a yi maganar aure''

Shiru Dauda Imamu ya yi yana nazari,ya fi son ya fara bincike a kansa kafin ya ba shi damar turo iyayensa.

''Me zai hana a fara bincikar halinsa tukunna,idan mun ga yana da halin ƙwarai sai ya turo'' ya faɗa yana ɗan dubanta.

Wani irin mugun kallo ta wurga ma Dauda Imamu, kafin ta ce wani abu Jalil da ke gefe ya rigata cewar

''Ai Abba kar ka yi wahalar binciken Alhaji Shu'aibu shanawa,domin ba mutumin kirki ba ne,sana'ar....''

Narrnarhh Bukar's Amazing pen

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.